Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

112…..

Khaleel na shigowa clinic din ya nufi labour ward hnklinsa a tashe ba tare da ya bi ta kan nurses din dake reception ba, suka ci karo da Najeeb, Najeeb ya rikosa yace “kana da nmbr Dad dinta?” Khaleel ya fixge hannunsa xae ci gaba da tafiya Najeeb ya fixgosa a fusace yace “da’lla ka saurareni malam” Khaleel yace “me xa ayi da shi” Najeeb yace “dad din Ameesha yace I shud ask yhu, yhu knw! she’s just giving headache in there sae Abbanta take kira, just cal him kadda ta ja ma kanta da babies din cikinta wani harm” Khaleel ya dafe kansa ya juya xae shiga room din Najeeb ya kuma rikosa yace “Cool down man, she’s OK ka bani nmbr dad dinta kawae” khaleel ya girgixa kai da kyar yace “bani da shi, I dnt have” yana kai wa nn ya kuma juyawa da sauri Najeeb ya kuma rikesa yace “ka kwantar da hnklin ka frnd xata sauka lfya idan Allah ya yrda, ko nmbr mum dinta gare ka ka bani kawae, we will get to her dad through d mum” khaleel ya fiddo wayarsa a sanyaye ya shiga neman layin mum din Ashnaah, Najeeb ne ya karba wayar ya ja sa suka fita xuwa haraban asibitin, bin sa kawae khaleel yake ba don yasan yana yi ba, bugu biyu momy ta daga, Najeeb ya gaisheta snn yace “em momy abokin mijin fateema ne, dama da Abba muke son mgna don Allah” momy da lkci daya hnklinta ya tashi ta dake tace “lfya?” Najeeb yace “lfya lau, Fateemar ce dae ke nakuda, kuma ta dage tana son ganin abbanta, don Allah ki masa mgna momy kar wani abun ya sameta, kila idan ta gansa xa ta samu nutsuwa, har Allah ya sauketa lfya” momy da gaba daya hnklinta ya gama tashi tace “toh bari in gaya masa, wani asibitin ne don Allah” Najeeb ya gaya mata asibitin, momy ta katse wayar hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri don xuwa gun mai gidan nata da ke falo, kasa ce mata komae Abba yyi yana kallonta can ya mike a hnkli ya dauki makullin motarsa yace “wani asibitin ne?” Momy ta gaya masa ya juya ya fice. Duk ynda khaleel ya so shiga labour ward ya ga Ashnaah kin barinsa dad din Ameesha yyi, wani doctor faruqh ya ja sa suka fita can haraban asibitin ya ajiye masa kujera yace “ka xauna nn plss kar ka kuma shigowa ko da reception ne, sae kace ba likita ba khaleel cool down plss Allah xae sauke matarka lfya kai ta mata addu’a kawae” Khaleel ya xauna ya dafe kansa dake sara masa bae ce komae ba, Likitan ya juya ya koma cikin asibitin, har Abban Ashnaah ya shigo asibitin Khaleel bae lura da shi ba, Abba na shiga reception Najeeb ya nufo sa da sauri yace “sannu da xuwa Abba, mu je ka ganta” bin sa kawae Abba ya shiga yi bae ce komae ba, dai dai bakin ward din suka hadu da dad din Ameesha ya fito da wani likita da ya tura ya kira masa Khaleel kawae ya xo ya sa hannu ayi mata cs don bae ga alamar xata iya haihuwa da kanta ba, yana kallon Abba yace “kai ne mahaifinta koh Alhaji?” Abba ya gyada masa kae kawae, dad din Ameesha ya koma cikin ward din ba a dau lkci ba ya fito yace “ka shiga ka ganta Alhaji,” Abba ya tura kofan ya shiga Najeeb na biye da shi a baya, kasa karasawa ciki yyi yana kallon yar tasa, idonta rufe gam ta rike hannun Ameesha da ke ta tofa mata addu’a, bbu abinda ke fitowa bakinta sae salati in tayi tayi ta gaji sae kuma tace ina Abbanta ita a kira mata shi, nurses uku ne kanta da likita daya, Abba ya karaso ya dan duka kusa da ita yana kallonta yace “am here daughter,” bude ido tayi da sauri lkci daya ta tsaida surutan da take ta shiga kkrin mikewa xaune ya dakatar da ita ya rike hannunta cikin nasa yace “kar ki damu fateema, yhu will b alryt in’sha Allah” ta kuma fashewa da kuka da kyar ta bude baki muryarta na rawa tace “don Allah don annabi ka yafe min Abbana” Abba ya girgixa mata kai a hnkli yace “na yafe maki da ddewa fateema, yhu will b alryt dota, kiyi ta addu’a” ta fashe da wani matsanancin kuka ta rike hannunsa gam muryarta na rawa tace “da gske Abbana” Kae kawae Abba ke iya gyada mata, ta saki salati tana girgixa ta dalilin wani axaba da take ji lkci daya ta shiga kkrin mikewa kuma, Abba ya mayar da ita shi ma ya shiga tofa mata addu’an, axaban da take ji bae sa ta rufe baki ba tace “Abba momyna fa ina take” Abba bae ce mata komae ba sae adduan da yake ta tofa mata yana rike da ita. Ba karamin wahala Ashnaah ta sha ba don har an fara shirin shiga da ita theatre ta sullubo santalelen danta ko minti daya ba ayi ba dan uwansa ya biyo sa, bbu abinda ke fitowa bakin ta sae salati tana rike da hannun Abbanta da ke kanta har lkcn idonta a runtse, a hnkli ta bude idanuwanta ta shiga kkrin bude baki da nufin yi ma abbanta mgna amma ta kasa, ya duka don jin me xata ce ya ga ta soma cika hannunsa daga nata a hnkli har ta sake gaba daya, lkci daya ya ga kmr komae na ta ya tsaya, a rude ya kamo hannunta yace “fateema” Ameesha da ke kallon duk abinda ya faru ta koma baya da sauri lkci daya ta juya masu baya ta runtse ido xuciyarta na bugawa, dad dinta ya taho da sauri yana kallon Ashnaah a sanyaye, Dr Faruqh ne yyi karfin halin dauko stethoscope ya dawo ya shiga duba ta, Najeeb ya ajiye yaron hannunsa ya karaso da sauri ganin ynda faruqh ya tsaya kmr gunki yana kallonta, fixge stethoscope din yyi ya shiga dubata, faruqh ya juya ya fice daga ward din kawae, Abba da gaba daya ya gama rudewa yace “plss ku gaya min wats wrong, wats wrong with my dota” Najeeb ya hade kansa da abun gado ya kasa dagowa.

Infact duk Wanda yasan chapter din nn yyi masa sugar ya taho mu kwashi shoki, lol, Wanda kuma yasan bae masa sugar ba toh I assure him dogon suma tayi. Masu kkrin hacking fcbk accnt dina kuma su rufamin asiri su yi hkuri bata mutu ba ehe, Lol.

I dedicate this page to Rukayya Usman Adam Allah bar min ke kawalli.

 

 

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar113…..Najeeb ya mike da kyar idonsa ya kada yyi jajur ya juya xae fita daga dakin, Abba ya fixgosa hnkli tasheyace “na ce ku gaya min me ya sameta pls” hawayene suka sakko idon Najeeb yana kallon Abba, ya juya kawae ya fice daga ward din da sauri, Abba ya bi sa da kallo a sanyaye lkci daya ya xare glass din idonsa yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un ya juya yana kallonta yana girgixa kai ya nufe ta da sauri ya rike a rikice yana cewa “No! No! It can’t be, y fateema, plss kar kiyi mana hka” hawaye suka shiga xubo masa shi ma ya hade kai da abun gadon har lkcn yana rike da ita, dad din Ameesha ya xare glass din idonsa shi ma idonsa ya kada ssae ya karaso kusa da Abba ya dago sa yace “dats nt the right thing to do now Alhaji,” a hnkli ya kara da cewa”pray for ur dota” Abba ya rikosa a rude yana girgixa kai yace “are yhu tryn to tell me she’s no more” dad din Ameesha bae ce komae ba, Abba ya kuma hadekae da gado yana hawaye ssae, Dad ya juya yana kallon Ameesha da ke durkushe sae rusa kuka take kmr ranta xae fita, ya karaso kusa da ita ya dagota, cikin rawar murya tace “dad she’s gone” rungumeta yyi a hnkli yace “yes dota, yhu only pray for her now,” ta kuma fashewa da wani matsanancin kukan da yafi da muryarta ta rawa tace “Khaleel….” Dad dinta ya dago kanta yana rarrashinta, Najeeb na fita daga asibitin Khaleel da ke xaune har lkcn a haraban hsptl ya mike da sauri ya nufo sa, da damuwa kmr xae masa kuka yace “plss frnd ka gaya min halin da ake ciki, how’s my wife” Najeeb da ke ta ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya kallesa ba yace “da’alla malam ka rabu da ni, I’ve told yhu several times, she is OK” yana fadin hka ya fice daga gate gaba daya Khaleel ya bi sa da kallo, mancewa da warning din dad din Ameesha yyi ya nufi cikin asibitin da sauri, ko wacce nurse ya tambaya sae tace “she is OK dogon nakuda take” duk ya xama abun tausayi, ya ja gefe ya tsaya a reception din. Abba ya kusa minti goma kansa na kife kan gadon da Ashnaah ta ke har lkcn, Dad din Ameesha ya dago sa ya lulluba mata xanin gado yace “take heart Alhaji kar ka mance cewa kullum nafsin xa’ikatul maut, addu’a kawae xaka yi ma ‘yar ka, mu ma idan ta mu ta xo Allah sa mu cika da imani” Abba da hawaye ya kasa tsaya masa bae ce komae ba ya ciro wayarsa da ke ring a aljihunsa, momy ce ke kiransa, ya mayar da wayar yana kallo. Ashnaah ya duka yana kallon Ashnaah hawaye ba sakko masa, a hnkli hawaye yace “Allah ya ji kan ki fateema ya yafe ma ki duk kurakuranki yyi maki rahama ya haskaka kabarin ki, ya raya abinda kika bari, na yafe maki duniya da lahira baki min komae ba fateema……” Kasa ci gaba yyi ta dalilin tokarewa da muryarsa yyi hawaye na ci gaba da sakko masa, dad din Ameesha ya dago sa yace “Ameen Alhaji, Allah yyi Mata rahama ya amshi shahadar ta” da kyar Abba yace “Ameen,” snn ya ciro wayarsa jin momy na ta kiransa, ya fiddo handkerchief ya sharefuskarsa ya daga kiran, daga daya bangaren momy tace “ta haihu ne Alhaji, wllh hnklina ya kasa kwanciya tun daxu” Abba da wasu sabbin hawayen suka xubo masa ya dake yace “ehh ta haihu Alhmdllh” cike da murna momy tace “Alhmdllh, me aka samu?” Abba ya juya yana kallon yaran da ke kwance nurses sun gama gyara su a hnkli yace “yanbiyu ne duk maxa” ciki da jin ddi momy tace “Allah sarki, to ya fateemar?” Abba ya dan yi shiru a sanyaye sae kuma yace “Alhmdllh,” momy tace “tohdon Allah ka bata wayar” Abba ya girgixa kai da kyaryace “ni ina waje ne” momy tace “toh shknn, Ashfah ma bata jin ddi wllh amma na kira Mata likita ya xo har ya dubata ya mata allura, daxu muna kitchen ta yanke jiki ta fadi wllh ko minti talatin ba ayi ba ma ynxu, dama kuma tun jiya na lura bata jin ddi, kaga da mun xo” Abba da hawaye kawae yake ya daure yace “to sae na dawo” yana fadin hka ya katse wayar, bbu abinda Ameesha take har lkcn bn da kuka kmr ranta xae fita, dad dinta ya kamo hannunta ya share mata fuskar ta yace “maxa ki tafioffice dina ki xauna, dnt say a word to any body” kaekawae take gyada masa a sanyaye har lkcn tana hawaye, ya kuma share mata fuska snn ta juya jiki ba kwari tana jan kafa ta fita daga ward din, Khaleel ta hango tayi saurin canxa hanya amma tuni ya ganta ya nufo ta da sauri, tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da tafiya da sauri da sauri, bin ta yyi shi ma da sauri har ya risketa ya rikota yace “wait Ameesha, don Allah ta haihu ne?” Ameesha ta ki juyowa ta dake tana ci gaba da tafiya ta ce “ehh ynxun nn ta haihu, sauri nake dad ya aike ni office” juyo da ita yyi da sauri yace “wait, don Allah is she OK” Shiru yyi yana kallonta ganin idanuwanta ynda suka kumbura, ta kirkiro murmushi tana gyada masa kai tace “yes she is OK, amma ta sha wahala ssae, ta ban tausayi” tana fadin hka tayi saurin juya masa baya ta dalilin hawayen da ya shiga taruwa idonta ta ci gaba da tafiya tace “bari in dauko abindaaka aikeni” Khaleel ya kuma bin ta ya juyo da ita hawayen da take mayar wa ya xubo mata lkci daya ta kasa daurewa ta fashe da kuka ssae, tsayawa kallonta yyi yana girgixa kae yace “no, no ki gaya min ina fateema ta, me ya faru” juyawa yyi da sauri ta rikosa cikin kuka ssae tace “wllh she is OK Khaleel, bbu abinda ya sameta” tura ta yyi ganin fuskokin dukka nurses din yasa ya nufi ward din da suke da sauri ya tura kofan ya shiga, kallo daya yyi ma Abba da boss dinsa ya nufi kan gadon da take da sauri dad din Ameesha ya taresa yace “kai ina xaka, me ya shigo da kai nn wat did I yell yhu, so kke ka tashe ta tana bacci,” Khaleel ya girgixa kai cikin rudewa yace “No,no no don Allah ku gaya min me ya sami matata me yasa aka rufe ta hka” bae jira amsa ba ya fixge hannunsa da karfi daga rikon da dad din Ameesha yyi masa ya nufi kan gadon da sauri ya cire xanin gadon da aka lullubeta da yana kallonta yace “fateema,” ya kira ta ya fi sau goma yaji shiru hkn ya sa ya shiga jijjigata har lkcn yana kiran sunanta a rikice, duk ynda dad din Ameesha ya so janye shi daga wajen bae yiwu ba, jikin Khaleel na rawa ya kama hannunta ya shiga feel dinPulse dinta lkci daya ya fasa wani karan da ya girgixa duk wani mahalukin da ke cikin asibitin, lkci daya kuma ya yanke jiki ya fadi wajen.114…..Allah sarki rayuwa, bbu Wanda bae ji mutuwar fateema ba, tun daga kan kawaye har yan uwa da abokan arxiki ba a mgnr iyayenta, Ummin Khaleel tayi kuka tayi kuka har ta gode Allah, Dad kansa yyi kukan ssae don bae bata mutuwa a lkcn ba, ba a maganan momynta da bata taba xaton mutuwar yartata a lkcn ba, mutuwar ta girgixa ta ba kadan ba tayi kukan tayi kukan tayi haukan har ta gode Allah, da ta tuna ganin yar ta na karshe da daddare da cewan da tayi ta yafe mata sae tayi kuka ba kadan ba, Abba ya fi kowa shiga damuwa, barin idan ya tuna a kan idonsa ta rasu sae ya ji hawaye na xubo masa, Ashfah kam sumanta yyi biyar duk ta xama kmr wata me jinnu kullum sae an mata alluran bacci, wayyo ba a mgnan Khaleel da ke neman bin ta, shi ma din kullum cikin masa alluran bacci ake don komawa yyi kmr wani xautattce, Najeeb ya ji ddin sae da ya nemi gafarar fateema ta bar gidan duniya duk lkcn da ya tuna hka sae yyi kwalla, bbu Wanda ya kai sa tausayin abokin nasa don shi ma ya shiga damuwa ssae kmr matarsa ce ta rasu, hka ma Al-ameen da matarsa, kowa kuka bbu me ba wani baki, sae ka rantse kace yar uwar Zeenat ce ta rasu ynda ita ma Mutuwar ya girgixa ta, ba a mgnr Meenah da suka dan saba, bbu Wanda ya samu courage din daukan yaran ya kula da su bnda Momyn Meenat, ta kwashe su kawae ta kai su gidanta, a hnkli a hnkli ranaku suka dinga ja har Fateema tayi wata biyu cif da rasuwa, amma Khaleel har lkcn an rasa gane kansa, ko ta kan yaran da ta bari baya bi, kullum ba shi da aiki sae tunanin fateemarsa wife dinsa, bbu ranan Allahn da xae wuce da baxae yi kuka ba, gashi yau lfya gobe ba lfya, ssae dad dinsa da umminsa ke tausayinsa, kullum dad ne ke sa shi gaba ya ci abinci ko kadan ne, duk ya rame ssae ba kadan ba, ba shi da aiki saetunani, sau dayawa Abban late Ashnaah kan xo har gidansu ya dubasa, don shi ma mugun tausayinsa yake, ya fi kowa jin mutuwar, wasa wasa har aka yi wata biyar da rasuwar fateema, har lkcn yaranta na gun momyn Meenat sun yi wayo abunsu gasu tubarakalla manya da su duk fateema suke kama da. Lkci lkci momyn meenat kan kai su gidan kakanninsu su gansu, in ta kai su gidansu Khaleel wnn satin, wani sati ta kai su gidansu Abba, ssae Abba ke son jikokin nasa amma ya kasa cewa a bar masa su, ranan wata Sunday Abba yace Khaleel ya xo yana nemansa, da yamma Khaleel ya isa gidan bayan sun gaisa da momy ya shiga falon Abba ya xauna don jiran sa, har lkcn gashi nn gashi nn dae ne, Ashfah ce ta shigo falon rike da faranti dauke daruwa ta ajiye masa ta gaishesa ba tare da ta kallesaba, ya daga kai yana kallonta yyi shiru, a hnkli ya bude baki ya amsa ta bar falon da sauri, lkci daya hawaye suka xubo masa don ta tuna masa da fateemarsa wife dinsa, goge hawayen yyi da sauri jin muryan Abba, ya sauka har kasa ya gaishesa, Abba ya amsa da fara’arsa yace “ya jikin, daxu dad din ka ke ce min baka ji ddi ba jiya” Khaleel ya sunkuyar da kansa yace “da sauki Abba”115…..Abba ya dan yi shiru snn yace “dama wata shawara na yanke Ibrahim, Allah yasa xaka amince da ita” Khaleel ya dago kai yana kallonsa bae ce komae ba ya kuma dukar da kansa, Abba ya numfasa yace”Na yanke shawarar hada ka da yar uwar marigayiyane, Allah yasa xaka so hkn Khaleel,” Khaleel ya dagokai lkci daya hawaye suka shiga xubo masa a hnkli yana girgixa kai yace “A’a Abba ni baxan sake aure ba, fateema ce kadae matata a duniya….” Kasa ci gaba yyi ya rike kansa yana hawaye ssae, Abba yyi shiru yana kallonsa cike da tausayinsa, a hnkli yace”abun da yyi fateema shi yyi khadija, hasalima rana daya suka fito duniya don hka ka dauki khadija a matsayin fateema na baka ita halak malak, ni xan biya maka sadaki bayan shi kuma ba ma bukatar komae, amma ina son ka min alfarma daya Khaleel,” Khaleel ya dago kai yana kallonsa har lkcn yana hawaye, Abba yace “ina son ka bani daya dagayaran naka in rike ko hkn xae dinga debe min kewar fateema, in nuna masa son da ban nuna ma uwarsaba, don ita son boye na mata” Khaleel ya gyada kae da kyar yace “na baka Abba” Abba yyi murmushin jin ddi shi ma hawayen cike idonsa yace “toh ngdd Khaleel, amma kayi shawara da iyayenka, tashi ka je Allah yyi maka albarka” Khaleel ya mike da kyar yyi masa sallama ya fita daga gidan, yana fita Abba ya jinginar da kansa jikin kujera, lallai Allah ya nuna masa ishara, rabon sae fateema ta bar masu mata addu’a xata bar duniya ne ya janyo komae, don ko da abubuwan nn basu faru ba wa’adin da Allah ya dibar mata a duniya knn, lallae Allah da iko yake, Ashfah ya kira ta shigo falon ta xauna kasa tace”Abba ga ni” Abba yana kallonta yace “ba ki taba tsallake duk wani umarnin da na maki ba khadija, duk abinda xae faranta Mani rae kike yi, wnn karan ma bana fatan xa ki tsallake” Ashfah tayi shiru bata ce komae ba, Abba yace “ina son hada ki aure da Khaleel ne khadija,” dago kai tayi da sauri tana kallonsa sae ga hawaye can kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace “Wayyo Abba don Allah kayi hkuri ni baxan iya auren mijin yar uwata ba” Abba yyi shiru yana kallonta, sae kuka take ssae, a hnkli Abba yace “do dat for my sake dota, nd for the sake of the kidz she left, baxa su taba rashin uwa ba, xa ki daukesu ne tamkar ke kika haifesu” ssae jikin Ashfah yyi sanyi bbu abinda take sae kuka, Abba yace “tashi ki je, Allah yyi maki albarka” ta mike da kyar tana kuka ta nufi sama, da kyar ta iya gaya ma momynta abinda Abba ya gaya mata, momy tayi murmushi ta rungumeta tace “do dat for d sake of the kidz dota”Bayan sati biyu aka daura auren Ashfah da Khaleel, don kowa ya ji ddin shawarar da Abba ya kawo bariniyayen Khaleel, Abba ne ya biya sadakin kmr ynda yace ya kuma yi mata kayan daki da komae, a ranan kuma aka kai ta gidan mijinta Khaleel da dad dinsa ya mallaka masa halak malak. Bbu abinda take bnda kuka har aka watse aka bar ta ita kadae, gani take kmr ta ci amanar late sis dinta, Karfe tara da rabi Khaleel ya shigo gidan rike da twinz dinsa a hannu da wani leda, yan kwanakin nn kam suna samun kulawan ubansa ssae sabanin da da ko kallonsu baya yi, dakin da Ashfah take ya nufa a

sanyaye ya tura kofar tare da yin sallama can ciki ya shiga, kasa amsawa tayi har lkcn tana hawaye, ya kwantar da yaran hannunsa kan gadonta suna ta wasa abunsu, snn ya fiddo feedernsu da madara da ke cikin ledan ya ajiye a kasa, ya bude daya ledan ya ajiye mata a hnkli yace “ga abinci nn na siyo maki” yana fadin hka ya juya ya fita daga dakin. Ashfah ta daga kai tana kallon yaran da ke ta wasa abunsu kan gadon hawaye na bin kuncinta.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button