Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

10…..

Shiru Zeenat tayi tana kallon Khaleel a dan tsorace, yace “yes dats d only way out, in ba dae ki fito da wanda kike so ba sae in san ynda xanyi convincing din dad dinki ya fasa hada ki da wanda ba kya so din ba” A sanyaye tace “to doctor Momy na fa ni dae ina sonta ssae” yace “daga baya we let her knw everythin” Zeenat na share hawayenta tace “am greatful doctor” yace “Neva mind” snn ya fice daga ward din ta bisa da kallo, Allah kadae yasan abinda take kitsawa a xuciyarta, shigowar kannin mum dinta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, ta sakar masu murmushi suka ce to ki tashi gimbiya an sallamemu, wanda ya shigo bayansu yasa ta hade rae, ya karaso kusa da ita da damuwa yace “sannu prettyna an sallame mu” harara ta galla masa ta mike da sauri ganin yana kkrin daga ta, ta figi hijab din ta tasa ta bi bayan wasu daga kannin mum dinta da suka fita da kayayyaki hannunsu, harabar hospital suka yi ido hudu da Khaleel dake xaune kan farar kujerar roba da wani frnd dinsa, Zeenat ta sunkuyar da kanta, Khaleel ya bi gayen da Zeenat tace shine wanda ake son hadata da kallo, yyi murmushi, yan uwanta suka yi masa sallama da godiya snn suka nufi parkin space inda motarsu yake, bin Zeenah yyi da kallo har ta isa gun mota, abokinsa na dariya yace “kai wnn kallo hka Khaleel, habit din nn naka dae baka bar shi totally ba knn” Khaleel yyi murmushi yana shafa sajensa yace “yarinyar tayi ne, ga ta doguwa ga shape ga diri, ga ga… Infact komai yaji” sae kuma ya tabe baki yana girgixa kai yace “amma sae dae baka ce” dariya abokinsa ya dinga yi yace “I knw yhu can Neva Change from hu I knw yhu Khaleel” Khaleel ya mike yana yar dariya yace “wllh Khaleel ya canxa” abokinsa ya rikosa yace “wait Khaleel wae ya maganar auren ka? Ka samu mata kuwa? Khaleel ya koma ya xauna yace ” ina fa, frnd na rasa ynda xanyi da parent dina” frnd din nasa yace “to ko baturiya kke son aura” Khaleel yace “ae baxa su bar ni ba, amma hkn bayi niyya da” abokin yace “to wae in tambayeka mana Ameesha fa, naga she is very beautiful, educated, in fact….” Katse sa Khaleel yyi a fusace yace to kai ka aureta mana, Allah ya tsareni auren macen da bata da class” Abokinsa yace amma ka mata shaidar karya, yarinya da ko kallon namiji bata yi amma don tana sonka sae kace bata da aji,” Khaleel ya mike yace “kaga ni na koma office” yana kai wa nn yyi gaba. Khaleel ne xaune ran Sunday da frnd dinsa a gidan wani abokinsu, ya Kai karshen lbrinsa yana murmushi ya dauki kwalban wine din gabansa yana sha, duk suka yi tsit suna kallonsa kowa da mamaki bayyane a fuskarsa, mikewa Najeeb yyi yana tabe baki yace “amma ka bada maxa Khaleel, na sha surprise dinka, duk wnn ajin naka da Kyan ka, da kudin ka da iliminka da wayewar ka mace ta mare ka ka kyaleta??? Yhu let her go scot free? Just like dat” murmushi kawae Khaleel yake, duk abokan nasa suka masa caa da surutu ko wannensu rae a bace” sae da ya bari suka yi shiru don Kansu snn yace “nima har kun bata min rae tunda kuka iya mance wanene Khaleel, an gaya maku Khaleel xata Mara ta tafi scot free” Abdul ya mike yace “nonsense, after she’ve disgraced yhu in public and yhu let her go, me kuma kke tunanin xaka mata da xa ka burge?” Dariya duk frnds dinsa suka dinga yi, ya daga kai yana kallonsu yace ae abinda xan mata sae ya sa ta

yi da ta sanin haifota da uwarta tayi duniya, ni ina da reason dina na kyaleta. Najeeb ya bushe da dariya yana nunasa yace “ya wuce kace xaka yi rapin dinta ko kuma ka sa a xuba mata acid, ko a nakasata, kai dae nasan baka kisa, dats d only thin yhu can do, nothing more then dat, kuma still baka burge mu ba, yarinya ta sa hannu ta sharara maka mari ka bar ta ta wuce baka babbala bnxa ba mu ga wanda ya tsaya mata, nayi mmkin canxawar ka lkci daya, ni kam bn ji ddin dawowarka Nigeria ba Khaleel, kawae an bata maka rayuwa ne, iyayenka basu maka adalci ba.” Dariya kawae Khaleel yake yana rike da kansa, ya mike yana kallonsu yace “da kun san abinda na tanadar ma yarinyar nn ko, da ta Baku tausayi” yana kai wa nn ya mike ya fice daga falon rike da makullin motarsa.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

11.. Shiru yyi yana kallon small mum dinsa da ta bude baki da mamaki tana kallon sa, can tace “lallai ma Khaleel, sae yau nasan baka da tunani kasan hukuncin abinda kke shirin yi kuwa” Khaleel yace “bbu wani hukunci mum, Kinsan abinda ke iya faruwa da yarinya nn idan ban yi hka ba” Tace “to ina ruwan ka, ka fi iyayenta sanin abinda su ke yi ne” Khaleel ya sassauta murya yace”don Allah mum ki fahimce ni, wllh in kin ga yarinya nn sae ta ba ki tausayi, mu hadu mu ceci rayuwarta plss” da kyar Khaleel ya shawo kan ta, can bayan dan shirun da tayi tace “to shkkn amma ni dae ba ruwana” yyi dariya yace “dama mana, ruwana kadae ne ki kwantar da hankalin ki mum,” tace “Atoh” sallama ya mata yace da yamma xae dawo snn ya bar gidan. Ashnaah na xaune a aji da frnds dinta bayan sun gama lecture tana basu lbrin abinda ya faru shekaranjiya tsakaninta da Khaleel, duk suka tsaya kallonta baki bude, Maryam tace “kika maresa Ashnaah?” Ashnaah tayi yar dariya tace “kuna mamaki ne, dan dae hannu baya magana ne da ya Baku lbri” duk suka kwashe da dariya amma bnda Nafeesa da tace “to ki dae bi a hnkli, don in kin mari wani kin xauna lfya to wani ba kyaleki xae yi ba,” Ummi tace “to wnn din ma ca yyi maku kyaleta yyi, ba dae ya ga layinsu ba kawae dae Allah ya tsare” Ashnaah tace “to uban me xae iya min? In Baku da abin fadi kuyi shiru pls kar Ku bata min rae, ya dde bae min abinda xae yi ba” Duk suka yi shiru Nafeesa ta mike tace “ki dae bi a hankali” tana kae wa nn ta fice, Ashnaah ta bi ta da masifa wae aniyarta ya bita, canxa hira kawayen nata suka yi, Maryam tace ” wae ina saurayin nn naki me kawo ki makaranta Ashnaah” Ashnaah tace “uhn ki bari kawae akwae abokan babana masu lecturing a nn duk abinda nayi ana kae masa info, hka ma layin grandmum dita, shine ranan Abba ya kirani wae daga ynxu ya sake gani na da saurayi ko ma wani iri ne shi to aura Min shi xae yi tunda ba karatu nake son yi ba, Abbana kuma baya magana biyu shiyasa na ji tsoro don ni ban shirya aure ba, ina abun aure a jikina ynxu ni kam, ynxu dae ko xa mu hadu da Uthman a eatry Muke haduwa don ko layin mu ya daina xuwa, shiyasa nayi ma gayen nn abinda nayi masa, amma da don haduwa ya hadu kuma courage dinsa ya burgeni ssae,” duk suka kwashe da dariya, Ashnaah tace “eh mana ni dae ina son in yi karatu ssae daga fara remedial kawae sae a aurar dani ko Jami’an ma ban Shiga ba,” karfe shidda Khaleel yyi horn gidan small mum dinsa mai gadi ya bude gate ya shiga yyi parkin snn ya juya yana kallon Zeenah da tayi jigum yace “mu shiga” ba musu ta bude mota ta fita shima ya fito ya kulle motar yace “to ae sae ki cire nikaf din” ba musu ta cire, da ganinta kasan a tsorace take, tana biye da shi a baya suka shiga gidan, bbu kowa falon sae Tv dake aiki, ya nuna mata kujera ta xauna snn ya haura sama, tare suka sauko da mum, ta karaso cikin falon tana amsa gaisuwar Zeenah, Meenah ce ta sakko Mum tace Ku tafi sama da ita Amina, Meenah tace “to mu tafi,” Zeenah ta mike suka nufi sama tare, har sun fara hawa stairs mum tace Amina ba ki ga Khaleel bne?” Meenah ta juyo tace “au Ashe shine, ina yini ya Khaleel?” Khaleel ya dake yace “qlau” snn suka wuce sama. Yau ma kmr jiya Khaleel ya iso anguwarsu Ashnaah yyi parking yana bin anguwar da kallo a xuciyarsa yana addu’ar Allaah yasa kar yyi wahalar bnxa kmr ta jiya.

~Dr Khaleel~ 12 By Khaleesat Haiydar

Khaleel yyi murmushi hangota da yyi tana Tahowa daga layin da ke ranan lahadi ne layin shiru bbu mutane, mayafi ne yafe jikinta yau, ya kafa mata ido har ta karaso titi ta tsaya daga gefen motarsa ta tsayar da abun hawa ta hau, tada motarsa yyi ya hau kan titin ya bi bayan napep din da ta hau. Bae wani sha wahalan bin napep din ba don bbu motoci ssae kan titin, Tafiyar minti kusan goma suka yi keken ya sha kwanan wani layi shima ya bi bayansa, dai dai gate din wani duplex mai napep din ya paka, Khaleel yyi parkin dan nesa da gidan, Ashnaah ta fito ta mika masa kudinsa ta shige gida abunta. Khaleel ya fito yana kallon mai gadin dake xaune bakin gate ya karasa ya gaishesa snn yace “wnn yarinyar da ta shiga nan ne gidansu” mai gadin yace “eh nan ne” Khaleel yace “ok, mai gidan na ciki ne?” Mai gadin yyi shiru snn yace “da matsala ne” Khaleel ya girgixa kansa yace “ko daya, kawae na xata sa ni a kwana tayi da tace nn ne gidansu, ynxu dae ka min sallama da mai gidan in yana ciki” Mai gadin ya mike ya shiga ciki, Khaleel ya xauna yana murmushi, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo ya masa iso har balcony ya nuna masa kujera ya xauna snn ya koma bakin aikinsa, bude kofar falon aka yi wani mutumi da baxae wuce shekaru hamsin ba ya fito yana kallon Khaleel ya basa hannu Khaleel ya ki amsa ya sunkuyar da kansa snn ya gaishesa da ladabi, Mahaifin Ashnaah ya xauna snn ya shiga tambayarsa daga ina, Khaleel yyi shiru yana kkrin tuna sunan da ya gani jikin receipt din Ashnaah snn da sauri ya maxa yace “dama tare da Fateemah muke shine tace in shigo in gaida ka,” shiru Abban Ashnaah yyi, sae kuma ya dan yi murmushi yace “to nagode” Khaleel yace “to ni xan koma Abba” Abba ya kuma masa godiya snn ya mike ya bar balconyn Abba ya wuce ciki. Dakin mum din Ashnaah ya nufa ran sa a bace, Ashnaah na kwance tana danna waya, mum dinta kuma na kallon wani program ita da Ashraf, ya tura kofan duk suka juya da sauri, Abba na nuna Ashnaah yace “lallai kin rika Fateema, har ni xa ki turo ma wani ya xo ya gaida ni ko, wato ni kika raina, to daga yau na yanke xuwan ki makaranta a gidan nn, in fact ko nn da gate bana son ki sake fita, wayar Hannun ki kuma Ki kai min shi Daki ynxun nn” yana kai wa nn ya fice daga Dakin, kuka Ashnaah ta fashe da tana kallon mum dinta dake kallonta da mmki, “Ashnaah wa kika tura ma Abbanki” cikin kuka ssae tace “wllh ban sani ba mum,” Mum dinta tace “to daga ina kike ynxu” tace “daga gidan inna wllh nake mum, ni ban turo kowa ba” ta karashe maganar tana kuka ssae, mikewa Mum tayi ta fice daga Dakin, sae kuka Ashnaah take, usman ta kira bugu biyu ya daga a fusace ta fara magana “kai ne ka xo gidanmu yau?” Ya dan yi shiru snn yace “ni kuma?, kin manta ina Abuja?” Kashe wayar tayi ta kuma saka kuka don cikin samarinta Usman kadae ne yasan gidansu, kashe wayar tayi gaba daya don ma kar ya kuma kiranta, mum ta dawo ranta a bace tace “ki bar dauko min mgna Ashnaah, mahaifin ki gani yake kmr ni ke xuga ki ni fa ba ruwana ynxu gashi ni ma kin ja min, in kuma auren kike so to ae shkkn.” Kuka kawae Ashnaah take duk jikinta yyi sanyi, to waye wnn yyi mata hka, gashi Abba ya dakatar da ita daga xuwa makaranta. Har Khaleel ya isa gida murmushin dake dauke a fuskarsa tun bayan fitansa gidansu Ashnaah Bae bace ba, falonsu ya shiga ya tarda Abbansa xaune a falo da wani abokinsa, ya karasa cikin falon ya gaishesu, Abokin Abban nasa yace “har yau dae ka ki aure ko Khaleel ga Ma’aruf ynxu ‘ya yansa har uku, Khaleel yyi murmushi yana shafa kansa yace ” ni ma na kusa Abba, in Allah ya yrda watan da xa mu shiga” Abbansa ya sace kallonsa , Khaleel yyi dariya yace “Allah kuwa Abba na samu mata ynxu” Abban nasa yace “to Allah yasa” mikewa yyi ya masu sallama xae haura sama announcement din da ya ji ana yi a Tv yasa ya juya da sauri yana kallon tvn, murmushi yyi ganin hoton Zeenah boldly kan screen din Tvn snn ya haura sama. Satin Ashnaah biyu a gida bata je makaranta ba duk ta fice hayyacinta ta xama abun tausayi ga shi Abba ya amshe mata waya, duk irin lallaba Abba da mum dinta ta dinga yi tana basa hkuri hkn vae sanya ya canxa hkuncin da ya yanke ma Ashnaah ba don Bae yrda bata san daga inda mutumin yake ba, wani amininsa mum ta kira tayi ma bayanin komai don har inna ma yaki saurarenta, ranan da safe aminin nasa ya xo, bayan sun gaisa aminin yasa a kira masa Ashnaah, ta shigo falon da hijab dinta har kasa ta durkusa ta gaida abokin Baban nata, shi dae Abbanta Bae ko kalleta ba, Alhaji Salisu yace “Ashnaah me yasa Baki jin maganan iyayen ki ne?” Kasa cewa komai tayi kanta a Kasa, fada ya shiga yi mata daga karshe yace bbu ruwanta da ko wani saurayi daga ynxu har sae ta gama karatu, tace “to Abba ngdd” Abbanta yace ” Allah yasa ya shiga kunnenta, so nawa Mike yin hkn da ita, Alhaju Salisu yace wnn kuma tsakanina da ita na Alhaji, tashi ji tafi gobe ki shirya ki tafi makaranta, Ashnaah taji ddi ssae, kuma tayi vow a xuciyarta daga ynxu bata sake kula saurayi, har usman ma ta bar kulasa don bbu abinda take so kmr karatu a rayuwarta. Karfe biyar na yamma Khaleel ya shigo falonsu Meenah, mai aiki kadae ce a falon tana shara, ya xauna bayan ya amsa gaisuwarta yace “masu gidan basa nn ne” tace “Anty Amina da bakuwa ce kadae a gidan, Momy ta fita, sama ya nufa ya bude kofar Dakin Meenah, Zeenah ce xaune gaban madubi tana comb din gashinta da ya kusa bayanta, ta juya da sauri sae kuma ta mike ganin Khaleel ne ta dauki hijab dinta ta rufe kanta tace “ina yini ya Khaleel” yyi murmushi ya amsa yana kallon ta, Meenah ce ta fito daga bayi tace “haba meye hka Ya Khaleel xaka shigo ma mutane Daki ba sallama in mutum bbu kaya jikinsa fa” Khaleel yyi shiru yana kallonta, hararansa tayi ta koma bayi da sauri ta sa key don tasan me xae biyo baya, yyi murmushi a xuciyarsa yace”Allah ya taimake ki yarinya” waya ya Ciro a aljihunsa ya mika ma Zeenah yace “gashi xa mu dinga magana, hope ba matsala dae” ta gyada masa kai ta karbi wayan snn yyi mata sallama ya wuce. Ashnaah ta karasa gun da motar usman yake da sauri a dan tsorace tace don Allah ka dinga rufa min asiri ya usman,ba na maka bayanin komae ba wae, ynxu idan wani ya ganmu ya je ya gaya ma Abbana fa” da dan damuwa usman yace “to ya kike son in yi Ashnaah yau fa sati uku Rabon da in ganki ga shi ke ba waya ba, to a ina xan ganki in ba nn ba” Ashnaah na kalle kalle kmr munafuka tace ka ga mu hadu a eatryn da ka taba kai ni ranan” yace to da yaushe?” Tace “karfe hudu xan bar makaranta sae mu hadu a can kawae, ki ban xo ba ka jirani” yace to ynxu me kike da baxa mu tafi ba, tace tutorial Muke, tana kai wa nn tayi gaba da sauri, shi ko yyi reverse ya bar wajen.

~Dr Khaleel~ 13 By Khaleesat Haiydar

Karfe hudu saura Ashnaah ta bar sch bayan tayi la’asar a mosque, a dai daita sahu ta d auka ta nufi Eatryn da tace Usman ya jirata, bata yi mmkin ganinsa xaune yana jiranta ba, ta ja kujera ta xauna kujeran dake kallon nasa, shi kam sae bin ta da kallo yake, ta dan yi tagumi tana kallon sa, ya sauke ajiyar xuciya yace “me xa a kawo maki,” ta girgixa kai tace “aa ni a koshe nake kuma ban ma dde da shan soft drink ba a makaranta” Bae ce komae ba sae kallonta da yake, hkn yasa tace “ya usman ba laifina bne wllh, Abba baya son ganina da kowa ne, aurar da ni yace xae yi idan ya kuma gani na da saurayi,” Usman yace “to muyi aurenmu mana Ashnaah, wllh ina sonki tsakanina da Allah, xan bari ki ci gaba da karatun ki har kice kin gaji Ashnaah, yhu won’t regret marryin me” Ashnaah tayi masa wani mugun kallo tace “ta baxan yi ba din, yar yarinya da ni xaka wani dinga kira min aure? Am just 17 fa ko ka manta ne xaka dinga ce min aure” kmr xata yi kuka ta karashe maganar. Usman yyi shiru yana kallonta, juyawa tayi da xummar kallon agogon dake manne da bango taga karfe nawa suka yi ido hudu da Abbanta dake xaune da wasu mutane sun kai biyar da gani abu suke tattaunawa, Alhaji Salisu ta gani a gefenta shima yana kallonta, mikewa tayi da sauri kuma a rude ta bar eatry din, usman ya bi ta da kallon mamaki don shi Bae san Abbanta ba, ya mike ya bita da sauri, ko da ya fita har ta hau Napep. A rude Ashnaah ta isa gida ta dinga rusa ma mum dinta kuka, mum dinta duk ta rude tana tambayarta me ya faru hka ma Ashraf, da kyar ta shiga gaya masu abinda ya faru, mum dinta ta mata wani mugun kallo ta fice ta bar mata dakin kawae. Gidan inna ta nufa tana kuka, inna duk ta rude tana tambayar me ya faru, cikin kuka ta yi mata bayani ita ma, inna tace “shine xaki daga hankalin ki uwa kin kashe dan mutum, kai ni fa Adamu ya fara kai ni iyaka, to ya xo nn ya same ki in ya isa in ga, hka kawae duk ya bi ya takura ki don shine ya haife ki” Khaleel ya tsura ma lafiyayyun xannuwan dake kwance cikin akwatin dake gabansa ido snn ya ciro wani blue mai kyau da wani colour daban ya ajiye ma mum dinsa yace “ga wnn ummi” Ummi tace “aa ka bar mata kayanta kawae,” yace “ae ni na baki mum” ya cire wasu uku ya dauki daya yace “ke ma mum ga naki” small mum dinsa tace “aa da ka barsu kawae Khaleel” ajiye mata yyi kusa da ita ya rufe akwatin, Ummi tace “su kuma biyun hannunka fa” yace “Ameesha xan ba daya, dayan kuma ina da warce xan ba,” mum ce ta komar da lafiyayyun akwatunan har shidda inda suke, shi kuma ya fice daga Dakin, mum tayi dariya tace “kai! Allah yyi, sae dae kuma an ki kawo mana ita mu gani.” Washegari lahadi Ashnaah na kwance Dakin grand mum dinta duk ta rasa me ke mata ddi ga shi Abba Bae xo ba har lkcn bare ta ji hukuncin da xae yanke mata , to ko wani hukuncin xae yanke mata wnn karan kuma, wasu hawaye suka shiga gangarowa daga idonta, duk Usman ne ya ja mata komai. Karfe uku na yammacin ranan Abban Ashnaah na xaune falo yana duba jaridar da Bae duba ba da safe mai gadi ya danna kararrawar falon Ashfat ta bude yace da ita ana sallama da Alhaji, ta nufi falo ta ba Abbanta sakon snn ta wuce sama abunta. Mikewa Abba yyi Da yake daga anguwa yake har lkcin manyan kaya ne jikinsa ya fita xuwa gun bakin nasa, mamakin ganin bakin yyi su uku kuma duk Bae san su ba, yyi masu sannu da xuwa snn ya shigar da su har xuwa falonsa aka kuma gaggaisawa, da kansa ya kwaso masu ruwa da lemo a fridge suka masa godiya snn ya koma ya xauna.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

14….

Shiru Abba yyi da mugun mamaki yana kallonsu jin me ke tafe da su, can ganin kar ya maida kansa karamin mutum a gabansu yyi saurin cewa “Eh hka muka yi da ita, amma bn yi tunanin yau xata sa ya turo Ku ba, bari in kira yan uwana ayi komae gaban su kun ga ba dadi inyi komae gaban kai na” suka ce “gskya ne wnn, ba matsala xa mu jira su in Allah ya yrda” Abba ya Mike yana jin jina abinda Ashnaah tayi a ransa, lallai Ashnaah ta fi karfinsa ta nuna masa iyakarsa, wato kan yace mata komae kan inda ya ganta jiya da saurayi bari ta sa a kawo masa gaisuwa, sama ya nufa xuciyarsa na tafarfasa ya shiga dakinsa ya dauki waya ya shiga kiran wasu daga yan uwansa da abokinsa Alhaji Salisu, ba a dau lkci ba duk suka iso gidan, duk suka yi mamakin abinda suka ga Abban Ashnaah na shirin yi kuma ba tare da saninsu ba don Ashnaah yarinya ce karama amma bbu wanda yyi query dinsa ganin bakin, aka yi duk abinda ya kamata bakin suka bada dubu hamsin kudin gaisuwa, suka kuma kirgo dubu Dari suka bada kudin sadaki, suka kuma bada kudin da xa’a siya wasu abubuwan da ya kamata da basu kawo ba, mai gadi aka sa ya shisshigo da akwatunan da suka kawo na gaisuwa, nan take Abban Ashnaah yasa aka sa ranan daurin aure, wata daya kacal, nan da sati biyu kuma xa’a kawo lefe, kallonsa kawae yan uwansa ke yi da mamaki, sae kusan la’asar bakin suka bar gidan bayan sun rakasu har bakin mota ana ta godiya, ita dae Momy tana ta mamakin meeting din da ake yi a fali ba tare da ya sanar da ita xae yi baki ba, ko falo ba su shiga ba daga rakiyan da suka yi Alhaji Salisu yace “ynxu Adamu duk maganar da na maka jiya Ashe baka dauka ba, abinda kayi a tunanin ka ya dace knn, did yhu think dis is d ryt decision” Abban Ashnaah yyi murmushin takaici ya ma rasa me xae ce ma abokin nasa, nan yan uwansa suka hau sa da fada wae ya nuna masu ba su suka Haifa masa Fateemah ba kuma da sun san kiran da ya musu knn da bbu me xuwa tunda lkcn da yace a kawo gaisuwar Bae nemi shawararsu ba, Abba yace “mu shiga ciki in maku bayanin komai, ko kadan banda laifi a nn, hasalima mutanan nn rana tsaka kawae na gansu” nan Abban Ashnaah yyi masu bayanin abinda ya faru tun daga ran da ya hana Ashnaah kula samari har ixuwa yau a cewarsa da ta nuna masa iyakarsa tasa aka kawo gaisuwa ba tare da ya sani ba, duk kowa yyi shiru da mamaki yana kallonsa, Alhaji Salisu yace “anya Ashnaah xata iya hka Adamu, gani nake fa kmr set up ne wnn ni dae, ynxu dae tana ina?” Abba yace “set up fa kace, to ni tun jiya da na dawo gidan nn ban ganta ba tana gidan inna, ae bbu abinda xae sa ni janye ra’ayina na aurar da yarinyar nn nan da wata daya, ba dae aure take so ba, xan aurar da ita” su kam yan uwan Abba Kasa cewa komae suka yi don abun ya daure masu kai. Abba na raka yan uwansa ya dauki wayarsa ya kira Momy tana dagawa yace ta sakko yana jiranta a Kasa, ba a dau lkci ba ta sakko ta shigo falon, ta dinga bin akwatuna da kudin da ta gani da kallon mamaki tace “wnn kuma fa Alhaji” da kyar ta iya masa tambayar don tuni jikinta yyi sanyi, bbu yabo bbu fallasa yace “Ah! yar ki ta turo a kawo min gaisuwa da kudin sadakinta” Momy tace “ya ta kuma?” A tsorace tayi masa tambayar, yyi bnxa da ita ya haura sama abunsa, kuka Momy ta saka tana tunanin anya Ashnaah ce xata yi hka kuwa?. Khaleel ya fada kan gado ya fashe da wata dariya yana shafa kansa snn ya mike xaune da sauri yace “yes! It all worked well at last”. Da kyar Ashnaah ta bude kofar falonsu tana lekan falon, har lkcin jikinta Bae daina rawan da yake ba tun lkcn da kiran Abba ya shigo wayar inna wae yana kiranta hankalinta ya Kasa kwanciya, ta juya tana kallon inna da ke bayanta, inna tace ” mu je mana kin tsaya kmr warce ta ga mugun abu, mu je in ji kiran da yake maki” Ashnaah ta shiga falon inna na biye da ita a baya.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

15…..

Khaleel ne xaune office dinsa aka kwankwasa masa kofa ya bada ixini aka shigo wato nurse ta shigo ta gaishesa snn tace “Dr ne yace in kira ka can sama” Khaleel ya gyada mata kai ta juya ta fita snn ya mike ya fita daga office din ya nufi office din dad din Ameesha, yana tsaye Khaleel ya samesa a office din, Khaleel ya xauna snn ya gaishesa, ya juya yana kallon Khaleel snn ya ja kujera ya xauna ya fara magana a nutse “Khaleel don’t tel me that duk son da Ameesha ke maka ynxu baka sani ba,” Khaleel yyi shiru yana kallonsa, ya suke ajiyar xuciya snn ya ci gaba kmr hka “wacce yarinya kke shirin aure ynxu?” Khaleel ya kauda kansa yace “budurwa ta ce mun dde tare” Abban Ameesha ya dan yi shiru snn yace “shknn tashi ka tafi” mikewa Khaleel yyi ya fice daga office din nn da nn ransa ya bace ae ko me xae faru bbu abinda xae sa shi auren Ameesha. Ashnaah na kwance dakinta da daddare bayan inna ta koma gidan ta duk abun duniya ya isheta tun safe bbu wanda ya sake mata a gidan gashi har inna ta tafi Abba ya ki fadin kiran me yake mata, Ashfa ce ta shigo Dakin ta ce mata Abba na kiranta, Ashnaah ta mike da kyar gabanta na faduwa ta sauka kasa xuwa gun abban, Momy ma na xaune falon ta dan rabe jikin kujera tace “ga ni Abba” wasu kudade ta ga ya jefa mata yace “ga kudin gaisuwan da sadakin da kika sa aka kawo ma ni, amma ki sani ko kwandala ta baxae yi ciwon kai ba wnn auren naki, kuma kar ki taba nuna Kinsan ni ki je can ki nemi wani uban, xan maki alfarma daya in daura maki aure amma bayan nn ko hanyar gida na kar ki nuna kin sani, snn bbu me min biki a gidana a je can gidan mijin naki ayi” Tunda ya fara magana Ashnaah ke kallonsa kmr wata wawiya, ko kadan bata fahimce me yake cewa ba, anya ma da ita yake kuwa, juyawa tayi ta ga bbu kowa bayanta ta kuma kallonsa da sauri tace “Abba ban gane ba,” tsawa Abba ya daka mata yace “get out dama bana bukatar ganewarki” mikewa tayi da sauri tana kallon Momynta taga kuka take, sae ita ma ta fashe da kukan tace “don Allah ban gane ba Abba” mikewa da Abbanta yyi yasa ta bar wajen da sauri ta haura sama tana kuka. Ba karamin tashin hankali Ashnaah ta shiga ba bayan Ashfa ta mata bayanin abinda ya faru, ta mike da gudu ta nufi dakin momynta ta dinga rusa mata kuka wae ita wllh bata turo kowa ba bata san ko waye bane Sharri yake mata, Momy taki ko da kallon inda take, hkn yasa ta fice daga dakin ta koma dakinta ta dauki hijab dinta ta sauka kasa da sauri xata gidan inna amma mai gadi yace abbanta yace kar ya bari ta fita, Ashnaah ta rasa me ke mata ddi a duniya sae rusa kuka take ta daura hannu a ka, to waye wnn ke Neman ruin din mata rayuwarta, a ina ta san shi, tasan usman baxae mata hka ba, Allah ma yasa shi ne abun xae fi xuwa mata da sauki, da kyar ta koma balcony ta xube kasa nan tana ci gaba da Kukanta, tana nan har kusan rana mai gadi ya shigo balcony rike da envelop a hannunsa xae danna bell ta mike da sauri ta fixge a hannunsa snn ta shiga duba menene a ciki, IV ta gani gabanta yyi mugun faduwa ta bude da sauri, kan sunanta idonta ya fara sauka snn Khaleel Muh’d, mutuwar tsaye tayi a gurin xuciyarta na ci gaba da nanata sunan Khaleel, tayi wurgi da envelop din hannunta ta fasa wani ihu tayi cikin gida da gudu ta shige dakin mum dinta tana kuka tana cewa “wllh Momy ban sansa ba, ban taba jin sunansa ba, kin ga wae Khaleel, ni tunda aka haifeni ma ban taba jin sunan ba, don Allah Ku ceci rayuwata kar Ku hada ni da shi momy kila ma kudi yake so yyi da ni wllh” kallonta kawae Momy ta tsaya yi ita ma jikinta yyi sanyi, to waye wnn ya xo Neman auren ‘yar ta, tasan ko da wasa ynxu baxata tunkari mai gidan ta da wnn mgnan ba.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

16…..

Ummi tayi shiru tana kallon Khaleel snn tace “to don me baxa su yi taron biki ba Khaleel” Khaleel ya daga kafada yace “basa taron biki wae su,” Mikewa yyi yace bari in je inyi wanka ummi, Ummi tace “to ynxu har biki ya karato baxa ka kawo min yarinyar ba inga” Ya koma ya xauna yace “kar ki damu ummina har sae kin gaji da ganinta, bana son tana fita ne ynxu, kwana nawa ne ya rage ki kwantar da hankalin ki” Tace “to Allah sa ayi a sa’a yasa tsohuwar gida ce” ficewa Khaleel yyi Bae ce komai ba. Ana ta shirye shirye gidansu Ashnaah don yau kwana biyar ya rage a daura mata aure, mamaki kawae take wae ita xa ayi ma aure, wae yaushe tayi birthday dinta na shekara sha bakwae ne ma dae, ko wata biyu ba ayi ba, shine wae xa a mata aure da wanda ma bata taba jin sunansa ba a cewarta, tunanin hkn nasa ta kukan takaici, Abba kam ca yyi bashi da ko sisin yi mata kayan daki Bae yi wnn budget din ba na wnn watan, takaici yyi ma Momy yawa ta rasa ynda xata yi, har da xata hadasa da mahaifiyarsa sae gashi amininsa da yayansa sun mata iya ynda xa su iya, da ka ga inna kasan tana cikin farin ciki, ita dae ayi a daura aure a fitar da jikarta waje, ko kadan bata ko maganan mijin da aka ba jikar ta ta. Ranar Juma’ah bayan an sauko daga masallaci aka daura auren Khaleel da Ashnaah, daurin auren da ya samu hallatar jama’a da dama, Khaleel ya nufi motarsa yana murmushin da shi kadae yasan dalilinsa bayan ya gama gaisawa da mutane da dama dake masa Allah sanya alkhairi da fatan xaman lfya da amaryarsa, frnds dinsa suka bi sa suna kiransa da ango cikin xolaya, ya hade rae yace “irin wnn wasan ne kuma ban so, Ku bari ran da na xama angon kwa kirani da hkn” ba su bar tsokanansa ba har suka bar wajen da motarsu, Najeeb yace “bari mu je mu dauko amaryarmu tunda ba biki.” Ashnaah ta mike tsaye da kyar ta dauki lafiyayyan lace din da kanwar mum dinta ta fito mata da ta sa, kkrin mayar da hawayen idonta take, taki barin Antyn ta dake ta lallashinta tun jiya ta gani don ta mata alkawarin daina koke koken da take, bbu abinda ta sa a cikinta ranan sae dan tean da aka tilastata ta sha, ba a wani yi mata make up ba ranan gaba daya, kawayenta na makaranta duk suka ji tausayinta, kowannensu na tunanin in shi ne aka ma hka ya xae yi. Karfe shidda saura Ashnaah ta sauka kasa da mayafi lullube fuskarta xuwa falon Abbanta kmr ynda aka umarceta, kallo daya ya mata ya dauke kansa, ta karaso a sanyaye ta durkusa gabansa ta shiga xubda a hawaye cikin rawan murya tace “don Allah don annabi Abba kayi hkuri ka yafe min,” kasa ci gaba tayi ta shiga rusa masa kuka ta kife kanta kan kujerar da yake xaune, ya cire glass din idonsa yace “tashi ki je Allah yyi maki albarka ya Baku xaman lafiya ke da mijin ki” Kasa dago kanta tayi hawaye na ci gaba da xuba idonta a raunane tace “to Abba karatuna fa” da kmr baxae ce komae ba sae kuma yace “da kina son karatun kika xabi aure” ta dago kanta da sauri cikin kuka tace “wllh Abba sharri aka min ni bance kowa ya turo ba, ka yrda da ni” Abba na kallonta yace “sharri aka maki?” Ta gyada masa kai tace “eh Abba ni ban turo maka kowa ba wllh”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button