Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

[10/10, 6:36 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

17…..

Abba ya tsura mata ido snn yace “to wa ya turo sa” Ashnaah ta shiga share hawayen fuskarta tana girgixa masa kai tace “wllh Abba ban san wanda ya turo sa ba, ni ban san shi ba, ban san daga ina yake ba,” tsawa Abba ya daka mata a fusace yace “ni kike ce ma baki san sa ba” Ashnaah ta fashe da wani sabon kukan tace “Allah Abba ban san shi ba sharri yake min, Abba ya kuma daka mata tsawan yace ” tashi ki ban waje” kin tashi tayi ta ci gaba da rusa masa kuka tana cewa ya yrda da ita, mikewa Abba yyi a fusace hkn yasa ta tashi da sauri ta bar wajen ta nufi sama, kasa komawa ya xauna yyi ya shiga kai koma a falon yana naxarin abinda Ashnaah ke cewa ynxu, wayarsa ya dauka ya kira mum dinta yace ta same shi falonsa, ba a dau lkci ba ta sakko kasa, ya nemi kujera ya xauna yana kallonta yace “A ina Ashnaah suka hadu da wnn yaro da ke shirin aurenta?” Momy tace “sae yau kasan da wnn tambayar?’ Tun da baka yi ta ba sae da aka daura aure, to ko kadan Ashnaah bata san daga inda mutumin yake ba, to da yake na ga Neman Kai kke da ‘yar taka shi yasa ban katse maku hanxarin Ku na aurar da ita ba,” Abba ya Mike tsaye ransa a bace yace “kar Ku raina min hankali, ni xa Ku maida yaro ko karamin mutum, Ku hada baki ke da yar ki Ku xo nn Ku caxa min kai, to bari kiji ko da ma da gsken ne bata san mutumin nn ba wllh wllh bbu abinda xae hanata xaman aure da shi, in an kai ta gidan nasa ma ya yanka ta karewar komae knn, yarinyar da bata dauki maganar uban da ya haifeta a bakin komae ba meye amfaninta, ba abun kunya bane ba ma ace kmr ni ana ganin ‘ya ta gidan cin abinci da holewa da saurayi, da na hanata wnn sae ta koma wancan sbda ta raina ni ke kuma kina kare ta, to ki koma Ki gaya mata plan din naku Bae yi aiki ba,” ya ja tsaki ya ce “mutanan bnxa kawae” dakinsa ya nufa ransa a bace, kan ya shiga ya juya yana kallon Momy da hawaye ya gama wanke mata fuska yace “kar kuma yar nn ta kuskura ta kwana gidana yau, maxa ana magariba a tafi da ita dakin mijinta” yana kai wa nn ya shige dakinsa. Momy ta nufi sama jikinta a sanyaye tana ci gaba da hawayen da take. Dai dai lkcn wa enda suka je yi ma Ashnaah Jere suka dawo kowa na yaba gidan da xa a kaita, kanwar momy ta ja ta xuwa daki tace “haba yaya kukan meye wnn baxa ki daina ba tun daxu, wllh Ki kwantar da hankalin ki, ni na tabbatar maki wnn mutumin ba don ya cutar da ita yyi hka ba, kawae tsabar sonta ne, sae kin ga gidan wllh, Ashnaah ta samu gidan Hutu ni na tabbatar maki yaya,” Momy tace “to da kike wnn maganan kin san aikin da mutumin yake ne” Anty farida tace “wllh likita ne, kuma ma babban likita snn mahaifinsa ma babban dan kasuwa ne, sae ma kinga ynda yan uwansa suka tarbe mu daxu wllh don duk suna gidan, ki kwantar da hankalin ki kawae yaya, ba mutanan bnxa bne” Momy ta share fuskarta tace “to Allah yasa, shi kuma Adam Allah ya shiryesa ya dawo da shi hanya”. Karfe bakwae da kusan rabi aka tafi da Ashnaah gidan mijinta da bata sani, bbu abinda take masu sae aikin kuka a motar, ita takaicin ta bbu wanda ke son yrda da ita idan tace bata san mijin ba, tafiyar kusan minti talatin suka yi kafin suka iso gidan mai gadi ya bude masu gate driven ya ja motar ya shiga ciki ya samu gu yyi parkin, ana bude ma Ashnaah kofa ta fito ta cire mayafin kanta da sauri tana kare ma kantamemen gidan kallo tana huci ae kam mai gidan nn ya aurar ma kansa fitina da tashin hnkli, aka ce ta fito da kafarta na dama bata ko sauraresu ba ta fito da ta hagu abunta kuma da gangan, suka kama yi mata masifa wae bata jin mgna, bata ko kallesu ba ta shiga bin kanwar mum dinta suna biye da su a baya har suka iso babban falon gidan, bbu abinda bbu cikin falon ba jin ddin rayuwa, Antynta ta juya da sauri ganin yan uwan khaleel a falon tace ” ke baki da kunya ko Ashnaah, baxa ki rufe fuskar ba, ” Ashnaah ta wara idonta da mamaki tace “ji Anty fa, akwae me bina bashi a nan ne ya fadi in ji da har xan rufe masa fuska” ganin ynda antynta ke kallonta jikinta yyi sanyi don ba Karamin nasiha aka mata ba kan su bar gida daxu yasa Ashnaah ta daura mayafin hannunta a kanta fuskarta a daure ta rike kugu tana kare ma mutanan dake xaune falon kallo.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

18…..

Mum din Meenah ce ta taso tana kallon Ashnaah duk da jikinta yyi sanyi tace “sannun Ku da xuwa amarya” Ashnaah ta dan yi tsaki ta saki mayafin kanta ta rufe fuskarta da shi, mum din Meenah ta kama hannunta suka nufi sama su anty na biye da su a baya su ma a sanyaye, duk nasihan da aka taru ana ma Ashnaah a Daki kawae shiga kunnenta na Dama yake yana fita ta hagu, duk ta kagu su rabu da ita sae wani kallon banxa take ma Zeenah da Meenah dake dakin su ma suna kallonta, Anty da sauren yan uwan mum duk jikinsu yyi sanyi ssae, ynda kasan ba amarya suka kawo gidan ba ta wani sauke mayafin kanta xuwa kafada tana bin kowa dake dakin da kallo, Meenah da taji kmr ta sake dariyan dake cin ta ta mike kawae ta fice daga dakin Zeenah ta bi bayanta, sae da suka sakko kasa snn Zeenah tace “wnn ita ce amaryar ya Khaleel din wae Meenah” Meenah ta fashe da dariya har da kyakyatawa tace “to gashi kin gane ma idon ki kuwa, dai dai shi ya dauko ma kansa,” Zeenah ta kasa cewa komae tana mamakin duk ajin Khaleel ya rasa warce xae auro sae yarinya karama kuma fitsararriya, Meenah tace “ni dae tace xata kawo min iskanci naka da mata duka xan yi wllh, wnn ta wuce kanwata ta uku ma”. Sae kusan karfe tara duk aka watse aka bar Ashnaah daga ita sae halinta a gidan, nn fa hankalin ta ya tashi ssae ta soma rera kukan da bata yi ba tunda aka kawota gidan, kasa xaune tayi ta mike tsaye ta shiga xarya a dakin tana rusa kuka tana tunanin to yau wani irin mutumi xa su kwana gida daya da, wa ya sani ma ko dan yankan Kai ne, kila yau ma shine rananta na karshe a duniya, tunanin hkn yasa jikinta ya soma rawa ta fara tunanin to ko dae ta gudu ne kawae, tana cikin yanke decision din taji an bude gate din gidan, xuciyarta ya kusa shige wa cikinta son tsoro, wani sabon kukan ta saki ta durkushe wajen ta daura hannunta a ka tana kiran momynta, can kuma ta mike da sauri jikinta na rawa ta nufi window ta ga irinsa kan ya shigo gidan, har ya gama parkin motarsa a parkin space ya nufo kofar shiga gidan, bata ganin komae sae tall figure dinsa don bbu haske tsakar gidan sae daga can bakin gate, wani sabon kukan ta rushe da ta koma gefen gadonta da sauri ta xauna jikinta na rawa. Takun sa da taji a stairs yasa ta gane har ya shigo gidan ta mike a hnkli ta nufi gun inda ta ga switch din wutan dakin cikin sanda ta kashe wutan dakin snn ta koma da sauri ta xauna xuciyarta na bugawa tayi saurin share hawayen fuskarta da Mayafin jikinta, suma ne kawae bata yi ba da taji ya bude kofa Ashe wani kofa daban ya bude, ta sauke ajiyar xuciya, ta xamo kasan tiles a hnkli ta xauna don ji tayi xaman gadon ma ya gagareta, yau tata ta sameta, ko minti biyar bata yi da sauka kasan tiles din ba baccin tsoro ya sace ta nn xaune, a firgice ta farka jin an bude kofar dakin da take, ta ga mutum tsaye bakin kofa kuma har lkcn wutan Dakin a kashe yake, a hnkli ta mike ta koma kan gadon ta xauna xuciyarta na wani mugun bugu da Bae taba yi ba, shi ko har lkcn yana tsaye bakin kofar, sae a snn tayi da ta sanin kashe wutan dakin ko ba komae ae da ta ga fuskarsa ynxu, shknn har ya kashe ta baxata ga fuskarsa ba knn, ji tayi kmr ta sake fitsari ganin da tayi ya rufe kofar dakin, to ko dae ta fara rokonsa ne kawae ya ceci rayuwarta, ko kuma ta saki ihu kawae, duk da ba wuta dakin amma ana iya ganin inda take, karasowa taga yana yi xuwa gun da take, ta mike da sauri ta isa jikin bango jikinta na bari, nan da nan dubara ya xo mata cikin rawan murya tace “wllh xan caka maka abinda ke hannuna in ka karaso inda nake,” tsayawa ta ga yyi cak nn inda yake, ganin hkan yasa ta samu kwarin gwiwa ta ci gaba muryarta a dake tace “in kuma karya ne ka karaso ka ga” komawa taga yyi ya nufi gun switch din dakin nn da nn hankalinta ya tashi ta sake kuka ba tare da ta sani ba ta bi bayansa da sauri muryarta na rawa tace “wllh kar ka kunna min wuta, kana kunna wa xaka sha mamaki,” da sauri ya isa gun switch din ganin tana bayansa, kan ya Kai hannunsa ta wani fixgosa da karfi ya fado kanta duk suka fada kasan dakin, ba ita ba shi kansa sae da ya tsorata, ya tura ta daga jikinsa ta kuma rikosa da sauri cikin kuka tace “wllh na ce kar ka kunna min wuta xan baka mamaki,” kkrin mikewa tsaye ta fara yi ya fixgota ya kai ta kasa, snn shi ya mike ya nufi gun switch din ya kunna da sauri, xae juya suka kuma cin karo don Magyar har ta taso, ta cukumosa ta rufe fuskarta a kirjinsa tana rusa kuka tana cewa “wllh ka mai da ni gidanmu” ita ko kadan bata ma son ganin fuskarsa, duk da irin kamshin da yake ya dan kwantar mata da hankali, tura ta yyi da karfi ya jinginata da bango ynda xata gansa da kyau, amma kememe taki bude idonta.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

19…..

Tsayawa Khaleel yyi yana kallonta har lkcn taki bude idonta, sae wani shishshige wa kirjinsa take tana cewa ya fita ya bar mata dakinta, sae a nn ya ga ashe ma yarinya ce karama, dago kanta yyi yana kallon fuskarta ya watsa mata wani lafiyayyan mari ta bude idonta a gigice ta daura kan fuskarsa, yana murmushin mugun ta yace “kin gane ni” kallonsa ta tsaya yi a tsorace tana kkrin tunano inda ta taba ganin fuskarsa, bata ankara ba ya kuma kai mata wani marin da yafi na da gigitata, ta saka kuka ya shaketa yana mata mugun kallo yace “nace kin gane ni” sae a snn ta tuno inda ta taba ganin sa, da sauri ta shiga gyada masa kai a tsorace, ya sake ta yana mata wani irin kallo yace “sae kin gwammace mutuwar ki da xaman aure a gidana, sae kin yi da kin sanin xuwan ki duniya yarinya, in yhur next lyf, yhu wil Neva raise ur filthy hand to slap a guy” yana kai wa nn yyi murmushin mugun ta yana shafa sajensa ya juya ya nufi kofa, kuka ta saki a rude tace “amma Allah ya isa tsakanina da kai, mugu axxalumi macuci, kai ma sae ka gwammace mutuwar ka da auro ni da kayi ka kawo ni rubabben gidan ka, sae na xame maka jaraba da tashin hnkli” da mamaki ya tsaya kallonta, ta fasa ihu ta durkushe inda take jikinta na raaa ganin ya yo kanta, yyi wani irin ball da ita da karfi har sae da ta buge kanta da gado, snn ya cakumota yana huci, a tsorace ba tare da ta sani ba ta shiga cewa “don Allah kayi hkuri ba da Kai nake ba wllh” janta ya shiga yi ya bude wani kofa dake dakin ya jefata ciki ya fito ya rufe kofar da key, waige waige ta shiga yi a tsorace don muguwar matsoraciya ce ita tana kallon inda ya jefota taga balconyn dakin ne, mikewa tayi ta shiga bubbuga kofar tana rusa kuka amma Bae bude ba, hkn yasa ta dinga xaginsa, bbu irin xagin da bata masa ba amma ba a bude dakin ba, ta sulale Kasa tana cigaba da aikin Kukanta cikin rashin kuxari don duk jikinta ya mutu, a hka bacci ya sace ta, bata san adadin lkcn da ta dauka tana bacci ba taji an bude kofar ta farka a firgice don bata da nauyin bacci, tsaye ta gansa bakin kofa ya fixgota ya jefata cikin dakin snn ya rufe balconyn ya juya ya fice daga Dakin, ta kife kanta kan tiles din dakin ta shiga rera kuka a hankali, can ta dago kai tana kare ma dakinta kallo, ynxu fa shknn wae aure aka mata da wnn xakin da take gani, ba ita ta koma bacci ba sae kusan asuba, bata kuma farka ba sae da gari ya waye, agogo ta kalla baki bude taga bakwae har ya wuce ta mike da sauri ta nufi kofar da take tunanin bathroom ne, alwala ta daura ta fito yin sllh, ta dde xaune kan darduma tana addu’ar Allah yyi mata iyaka da Khaleel daga bisanni ta mike ta shiga bathroom don wanke Bakinta, ido ta xaro ganin ynda idonta ga kumbura tace “tabdi ae baxan bari yyi tunani ya ci nasara a Kai na ba, sae nasa ya raina kansa wllh,”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button