Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar20….Cikin hanxari ta gama wanke bakinta ta kuskure da mouth freshner ta tube kayanta ta shiga gun wanka, sabon towel fari ta samu ta dauka ta goge jikinta snn tadaura ta fito ta shiga bubbude wardrobe din dakin don neman inda kayanta suke, undies ta fara ciro wa snn fito da wani lafiyayyen Holland dinta an mata Riga da skirt ta ajiye kan gado ta nufi gaban madubinta ta xauna tana duba man da xata shafa, ta gama shafe shafenta snn ta shiga yi m fuskarta make up lafiyayye, wani hadadden kyau tayi dama ga ta kyakkyawan karshe, ta Mike ta dauki kayanta ta saka, tana cikin daura dankwali gaban madubi aka bude kofar Dakin, duk da ba karamin tsorata tayi ba hkn Bae sa ta daga kai ta kalli wanda ya shigo ba ta wani dake tana kkrin daura dankwalinta, sallamar mace da taji yasa ta juya tana kallon warce xata shigo mata, Rukayya ce kanwarsa ta shigo rike da basket din abincin breakfst, da gani ba sae an gaya mata ba tasan kanwarsa ce don ga kama ta gani, ta wani tsuke baki ta hade rae tanaci gaba da daurin dankwalinta, rukayya ta karaso dakin da dan fara’arta tace “ina kwana Anty amarya?” Ba tare da Ashnaah ta kalleta ba can ciki tace “Qalau” Rukayya ta dan yi jigum inda take tsaye, Ashnaah ko sae faman daurinta take, Rukayya tace”Break fst na kawo” Ashnaah tace “to ae basae kin shigo da shi nn ba mana, ba sae ki barsa can falo ba” Rukayya bata ce komaeba ta juya ta fita jikinta a sanyaye, Ashnaah ta ja dogon tsaki ta shiga fesa turare abunta, Rukayya ta kusan cin karo da yayanta xae haura sama yace “ina xa ki”tace “ca tayi wae in saukar da shi kasa” Khaleel ya bata hanya ta sauka, snn ya haura sama ya nufi Dakin Ashnaah ya buga shi da karfi, har lkcn tana xaune gaban madubi ta gama sa jewelries dinta tana kare ma kwalliyarta kallo, kallo daya tayi masa ta dauke kanta duk da irin faduwar da gabanta yake, ya daka mata wani tsawa yace “a gidanku hka aka koya maki idan kin tashi da safe kar ki fito kiyi aikace aikacen gida” ta juya tana masa wani matsiyacin kallo tace “ae ba yar aiki aka kawo maka ba, sae ka jira ran da…..” Wani ihu ta fasa ta mike da sauri ta nufi bayi ganin ya yo kanta, yyi saurin fincikota ya juyo da ita yana kallon fuskarta, ta hadehannayenta biyu jikinta na rawa tace “don Allah kayi hkuri ba da kai nake ba pls” mariya wanka mata ta fasa kuka ya buga bakinta snn ya shiga janta suka fita daga dakin har suka sauko downstairs snn ya jefar da ita tsakiyar makeken falon da ya shigo da ita yace “ki tabbatar every blessed day kin share ko ina na falon nn kin goge snn kin fita waje ma kin share duk compound din nn and dat shud b done every morning as early as possible, motata ma daga dis very moment ke xaki dinga wanke shi duk safiya, snn ki hada breakfast ki kai ma duk masu aikin gidan nn da masu gadi, kowa ki bi sa inda yake ki ajiye masa hka ma lunch da dinner, lastly daga yau ko mai bana son in kara ganin kin shafa a gidan nn bare hoda ko jan baki don ba gidan iyayenki bane nn, ko wa kike tunanin kike ma kwalliya da wnn kodaddiyar fuskar taki” Ashnaah ta mike tsaye tana masa wani matsiyacin kallo tace “Sannu ubana, to wllh bari ka ji, kayi kadan ka kawo ni gidan ka in maka bauta, ashe gidan ka xae rube ba gyara, motar ka kuma xae dafe ba wanki, masu gadin ka dama’aikatan ka kuma xa su mace da yunwa,kwalliya kuma ba sbda wani bnxa nake yi ba don bae isa nayi masa kwalliya ba, shi a su wa” kallonta kawae Khaleel yake da mugun mamaki, da ganin ynda take maganar kasan a tsorace take, ya juya da sauri ya nufi sama Ashnaah ta xaro ido ta bi sa da gudu xuciyarta na mugun bugu.

 

 

[10/10, 6:37 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

22….

Zeenat da Meenah ta gani tsaye bakin kofar dakin, duk da bata san sunansu ba ta gane fuskarsu, ta hade rae tana kallon agogon dake manne jikin bangon dakinta ta ga karfe sha biyu saura, Zeenah tace “bacci kike Anty amarya” Ashnaah tayi kmr bata ji ta ba, Meenah ta karaso cikin dakin rike da kulan abinci ta ajiye, Zeenat ma ta shigo ta xauna kan stool din dake gaban madubin dakin tana kallon Ashnaah tace “ya kewa” Ashnaah tace “kewan me” bata jira ne xata ce ba ta mike ta nufi bathroom abunta, Meenah ta kalli Zeenat tace “tashi mu je” mikewa Zeenat tayi a dan sanyaye ta bi bayan Meenah, suna sauka kasa Meenah ta fara mata masifa tana cewa “sae wani shishshige ma yarinya kike tana sha ma mutane kamshi, da gani yar talakawa ce wllh, bnxa da ita kawae xata kawo ma mutane rainin hankali yarinyar da bata wuce kanwar mu ta uku ba, ni ba din momy ba ma bbu abinda xae shigo da ni gidan nn,” Zeenat tace “to ae dan sbda ya Khaleel wae, idan batun hka ita ta isa, meye hadina da ita” Meenah na mata wani irin kallo tace “to fa, shi kuma Khaleel din meye hadin ki da shi” Meenah ta fashe da dariya Zeenat dae bata kuma cewa komae ba har suka isa gate dai dai bakin gate suka ci karo da Khaleel yyi parkin motarsa a waje xae shigo, wani mugun kallo yake ma Meenah yace “me ya shigo da ke gidana” bata ko kallesa ba tayi gaba abunta da sauri ta nufi titi, ya kalli Zeenat yace “me kuka xo yi” Zeenat tace “abinci momy ta ba mu mu kawo” yace “ok mu shiga ki dan min abu, xan mayar da ke gida” shiru tayi tana kallonsa, ya juya ya shige gidan, ta juya ta bi sa a hankali. Ashnaah na jin fitarsu Zeenat dama ta mike da sauri ta sauko kasa don ganin me aka kawo mata a kula, jollof ne ya ji nama da plantain, har wani rawa jikinta yake ta bude kulan kasa ta ga lafiyayyen farfesun kaxa, da gudu ta mike ta shige bathroom da sauri ta wanke hannunta ta kuskure baki ta fito ta xauna ta shiga tura abincin ta, Khaleel ya juya yana kallon Zeenat dake tsaye daga bakin kofa yace “abinci xa ki girka min, ko baxa ki iya ba” ta dan yi shiru snn tace “me xa a dafa” ya xauna kan kujera ya dauki remote yana canxa tashar tvn dake aiki yace “simple food, da kika ga ya fi sauri,” mikewa yyi yace “mu je in nuna maki kitchen din da kayan abinci” ba musu ta bi bayansa suka isa kitchen din ya Ciro makulli ya bude, ita dae sae kallonsa take da mamaki, to meye na wani rufe kitchen” nuna mata komai yyi ya juya ya fice daga dakin ya nufi sama, Dakin Ashnaah ya bude ta tura kulan gabanta da sauri tana kkrin goge bakinta ta tashi ya shigo dakin, kunya ya kamata gashi da hannu take cin abinci, dariya ya shiga yi yana kallonta, ta wani hade rae har lkcn hannunta na boye bayanta tana masa mugun kallo, yace “duk yunwarce hka” tsaki tayi ta kauda kanta, yana shafa kansa yace “kadan kika fara gani yarinya,” juyawa yyi ya fice daga dakin, ta ja tsakin takaici tace “kae dae ne mayunwaci, bnxa kawae” mikewa tayi don takaici ta shige bathroom wanke hannunta, duk sae ta ji abincin ya fice ranta, kamshin soya miya da taji kasa yasa ta kasa xama daki ta sakko kasa, to wa ke girki, bbu kowa falon hkn yasa ta nufi kitchen da sauri, da mamaki take kallon Zeenat, ita dae Zeenah kallo daya tayi mata ta ci gaba da abinda take, Ashnaah tayi tsaki tace “Aikin bnxa, da kawae yyi xaman auren da ke, karewar kawo ki ki masa girki knn” Zeenat ta juya tana kallonta bata dae ce komai va, amma ba karamin bata mata rae kalaman Ashnaah suka yi ba, ita Ashnaah duk tunanin ta kanwarshi ce, ta ja dogon tsaki ta fice daga kitchen din suka kusa cin karo da shi, yana mata mugun kallo yace “me kika sakko yi” hararsa tayi tace “kai me ya sakko da kai xaka min wnn silly tambayar” ya tsaya kallonta daga sama xuwa kasa snn ya wani wanke fuskarta da mari, ta dafe kuncinta a gigice tace ka mareni? ” bata rufe baki va ya kuma sauke mata wani, ya fixgota da karfi ya nufi sama da ita ya bude dakinta ya jefata ciki, sae da taga ya kulle kofar snn cikin kuka ta shiga cewa “Allah ya Isar min mugu kawae mahaukaci kuma wllh sae na….” tsit tayi jin ya bude kofar Dakin ta Mike da gudu har tana neman faduwa ta shige bathroom ta kulle kofar da key, ya juya ya fice daga dakin, karfe daya da kusan rabi Zeenat ta gama hada masa Shinkafa da miya ta ajiye masa nn tsakiyar falon, ta dan jingina jikin kujera tana jiran saukowarsa, ta kai minti goma a tsaye sae gashi ya sakko cikin kananan kaya yana kallonta yace “har kin gama” tace “eh gida xan tafi” Bae ce komae ba ya karaso cikin falon ya xauna yana kallon abincin yace “sllh fa” ta dan yi shiru snn tace “idan naje can gida na yi” ya daga kai yana kallonta da kmr baxae ce komae ba sae kuma ya jawo plate ya shiga diban abincin gabansa yace “sae ki ce min kina period” ya daga kai yyi murmushi yana kallonta yace “ki ba hka ba” kasa cewa komae tayi, ya fara cin abincin gabansa yace “ki xo ki diba kema” ta kauda kai tace “na koshi” Bae ce mata komae ba sae cin abincin sa yake, ta kasa daina kallonsa, cokali biyar yyi ya daga kai ya kalleta suka hada ido ta dauke kanta da sauri yyi murmushi ya mike yace “kwashi abincin ki kae min dinnin anjima idan na dawo xan ci, ba musu ta karaso cikin falon ta duka ta kwashe farantin abincin ta nufi dinnin da shi, shi kuma ya haura sama, dakinsa ya shiga ya fara wanke bakinsa a bathroom snn ya fito ya dauki makullin motarsa ya fita, dakin Ashnaah ya nufa, tana xaune kasan dakin ta hade kanta da gwiwa, tana jin an bude kofarta ta dago da sauri, ya hade rae yace “ke nake jira” tayi tsaki ta dauke kanta, ya karaso cikin Dakin ta Mike tsaye a tsorace tace “ni me nayi kuma” ya wani hade rae yace dauki hijab din ki ki fita muje, ta nufi drawer dinta kmr xata yi kuka ta dauki hijab din tasa ya nuna mata kofa ta nufi kofar yana biye da ita a baya, suna sauka downstairs ya kalli Zeenat yace “mu tafi Zeenah” Zeenah ta nufi kofar fita Ashnaah ta juya tana masa kallon bnxa tace “ina xaka kai ni,” irin kallon da taga yana mata yasa ta nufi kofa da sauri tana tsaki, Khaleel ya bude seat din gaba yana kallon Zeenat dake tsaye jikin motar yace “shiga” ta dan xaro ido tace “ni” hararanta yyi yace “ki shiga nace” kasa shiga tayi har lkcn tana tsaye, ganin ynda yake kallonta yasa ta dan raba ta gefensa ta shiga gaban motar, Ashnaah dae na kallonsu tayi tsaki ta bude bck seat ta shige abunta a xuciyarta tace “ki ba komae ka xama driverna dae” har suka bar gidan Ashnaah bata kalli gaban motar ba idonta na kan glass kawae, firarsa kawae yake da Zeenat da bata cewa komae, can dae ya juya ya kalleta ya mayar da idonsa kan titi yace “ni kike sharewa ko” ta kallesa tace “ae ina jin ka,” Bae kuma ce mata komae ba har suka iso traffic light snn ya juya yana kallonta yace “to me nace na karshe” ko kadan bata san me Khaleel ke cewa ba don duk a takure take a motar sbda Ashnaah dake baya, ta fara kame kame tace “aa ina fa jin ka ya Khaleel” ya kamo hannunta yana kallonta yace “tsoron warcan abar ta bayan mota kike” Zeenat ta fixge hannunta da sauri duk jikinta yyi sanyi, maganar sa tayi confuse dinta, yyi murmushi ya kalli Ashnaah ta madubi yaga murmushi take ma wani mutum dake gefen su cikin lafiyayyen motarsa yana daga mata hannu, Khaleel ya hade rae yana kallonta yace “na ga alamar ke jahila ce da auren nawa a kanki kike ma wani kato dariya” Ashnaah tace “da auren ka a Kansu dae ba ni ba, don har ynxu ni bbu abinda ya raba ni da xama budurwar da nake, ko ina budurwa xata shiga nima xan shiga don ni ba matan auren kowa bace,” Khaleel yyi murmushi yana kallonta yace “hka kika ce ko? xaki raina kan ki yarinya, sae kinyi da kin sanin furucin ki” Ashnaah ta tabe baki tace “kai ma hka” Zeenat ta kasa daga kai don tuni suka gama daure mata kai, Khaleel dae yyi murmushi kawae ya ja motarsa, dae dae kofar gidansu Meenah yyi parkin Zeenat ta bude motar xata fita ya riko hannunta yace “bbu sallama” ta sunkuyar da kanta bata ce komae ba, ya dago kanta yana kallon fuskarta, sae kallonsu kawae Ashnaah take da mmki, ba sae an gaya mata ba tasan Zeenat ba kanwarsa bace, nn da nn taji wata mugun tsanarta ya dirar mata a xuciya ta dauke kan ta daga kallonsu da sauri, Khaleel ya saketa yace “ltr da daddare xan xo” Zeenat bata ce komae ba don duk ya birkita mata kwakwalwa, ta fice daga motar da sauri ba tare da ta kuma kallonsa ba, yyi murmushi yyi reverse suka bar anguwar. Khaleel ya gama parkin a parkin space din gidansu ya fito yana kallon Ashnaah yace “ni kike jiran in fiddo ki koh” dauke kanta tayi, tayi kmr bata san da ita yake ba, ya bude back seat ya fixgota ta kusan faduwa ya rufe motarsa ya nufi cikin gida, kin bin sa tayi har yyi nisa ya juya ya ganta tsaye, ya dawo a fusace ta shiga tahowa da sauri dae dae gabanta ya ja burki yana mata mugun kallo yace “Ki dinga kiyayata fa” dauke kai tayi yyi kwafa ya ci gaba da tafiyarsa ta shiga binsa tana masa mugun kallo har suka shigo falonsu, sama ya nufa ita kuma tayi xaman ta kan kujera fuskarta a daure, ko ba a gaya mata ba ta ga alamar kmr gidansu ya kawota, ba a dau lkci ba ya sakko tare da mum dinsa da wasu yan uwanta suka shigo falon, kallo daya Ashnaah tayi masu ta dauke kai, suka xaxxauna suna mata sannu da xuwa taki ko da kallon inda suke, momy ce tayi karfin hali tace “ina yini amarya” Ashnaah ta dan kalleta ta maxa ta dauke kai snn tana wasa da xoben hannunta tace “lfya lau” Khaleel ji yyi kmr an Sara masa guduma a ka, ya kasa daina kallon Ashnaah ga wani kunya da ya ji kmr ya nutse, yan uwan momy suka mike kowa ya nufi sama, momy kam bata fasa cewa ya bakunta ba, ba kunya ba tsoron Allah Ashnaah tace “da gdya” momy ta mike tace “bari a kawo maki ruwan sanyi” Ashnaah tace “to” kuma ko ba a gaya mata va tasan mahaifiyar Khaleel ce don ga kama, kitchen momy ta nufa, Khaleel ya taso da sauri ya isa gabanta yace “ita mum din tawa kika ki gaidawa sbda ba a maki tarbiya gidan Ku ba” Ashnaah tayi tsaki tace “a hka ka gan ni ka aura ae, bnyi niyyar gaidatan ba sae me” ta ja dogon tsaki tana hararansa ta maida hankalinta kan kallon da take, ransa yyi mugun bace ya mike da kyar ya dunkule hannayensa ya haura sama Ashnaah ta bi sa da harara ta tabe baki, momy ta dawo falo rike da farantin Ashnaah ta mike ta dan Risina ta karba tace “dama kin bar shi momy daga gida Muke ae” momy tace “shine kuma baxa a sha ruwa ba don daga gida ake” sae da momy ta xauna snn Ashnaah ta sauko har kasa ta gaisheta, momy tace “lfya lau Fateemah ya kewan gida” Ashnaah ta dan yi murmushi bata ce komae ba, momy ta kira Rukayya ta sakko snn suka wuce sama da Ashnaah, tsaf momy ta kare Ashnaah gaban yan uwanta dake ta mitan ba yar gidan mutunci Khaleel ya auro va, bbu ynda suka iya da Yayar tasu duk suka ja bakin su suka yi shiru, karfe biyar da kusan rabi duk bakin dake gidan tun biki suka watse kowa ya kama gabansa, Khaleel ya kai kanwar mum dinsa da suke daki daya gida, ssae yaji kunyar fadan da take masa wae ya je ya auro yarinyar da va yar gidan mutunci va don bata da kunya surkarta ce xata gaisheta kuma ta amsa, in ma su baxata mutuntasu ba ae ya kamata ta mutunta uwar mijinta, har muka bar gidan ko sallama bata fito tayi mana ba sbda rashin kunya, ta girgixa kai tace “me ya kai ka Khaleel, a ina ka samo ta, kai ynxu kaji ddin abinda tayi ma uwarka, yarinyar da bata wuce xama jikarta ba idan da kae mace ne” Khaleel ya kasa cewa komae xuciyarsa sae tafarfasa yake yana tunanin me xae ma Ashnaah ya ji sanyi, irin fadar da mum din Meenah tayi masa knn jiya da daddare wae yaje ya auro ya Mara mutunci wato fitsara xata dinga yi ma danginsa ko, Khaleel yyi murmushi xuciyarsa na raya masa irin abinda xae ma Ashnaah, har ta gama bambaminta Khaleel Bae ce komae ba, bayan driving din kusan minti talatin ya isa gidanta ya ajiye ta ya bata hkuri ssae snn ya kama hanyar gida xuciyarsa na tafarfasa.

45 mins · Khaleesat Haiydar…

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button