Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

[10/10, 6:37 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

23…..

Karfe takwas da kusan rabi Khaleel ya shigo gidansu, bbu kowa falo sae Rukayya da ke dan goge goge, Khaleel yace “Abba ya dawo ne ke” Rukayya tayi masa sannu da xuwa snn tace ae yana Abuja Bae dawo ba, yace “ok ummi fa?” Rukayya tace “tana daki” yace “yarinyar nn fa” rukayya tace “wace yarinya” ya harareta yace “warce na kawo gidan nn” Rukayya tace “oh ita ma tana sama ina jin, ga abinci can ummi ta ajiye maka a dinning” Bae kuma kallonta ba ya nufi sama ya bude Dakin umminsa ya shiga, ya samu ummi na sllh, Ashnaah kuma na xaune kasan carpet daga kusa da gado tana kallo don ita tayi sllhnta, Bae ko kalleta ba ita ma hka, ya nemi kujera ya xauna yana kallon wristwatch din hannunsa Allah Allah kawae yake ummi ta idar su bar gidan da Ashnaah, ummi ta sallame ta gama adduarta tace “ka dawo Khaleel, amma ka jima, ga abincin ka can kan dinnin” yace “ni na ci abinci gidan mum ummi, gida xamu wuce ynxu dare yyi” Ashnaah ta daga kai tana kallonsa tace “amma ca kayi min a nn xamu kwana fa ka manta ne” Ummi tace “nima dae hka tace min, kuma kace xa ku tafi ynxu ga shi dare yyi” kasa cewa komae Khaleel yyi sae kallon Ashnaah yake, ta hararesa ta ci gaba da kallonta, ya mike ba don ransa ya so ba ko kadan sae don Bae iya jayayya da umminsa yace “to shkkn ummi bari in yi wanka,” yana fita ummi ta juya tana kallon Ashnaah tace “to tashi ki kai masa abincin da na ajiye masa kan dinnin Fateemah, sae ki ce rukayya ta nuna maki dakin sa” Ran Ashnaah Bae so ba amma bata mata musu ba ta mike tace “to momy” snn ta fita kasa xuwa falo, sae da ta dauko farantin abincin snn tana kallon rukayya bbu yabo bbu fallasa tace “momy tace ki rakani dakin yayanki” rukayya bata ce komae ba ta nufi sama don kai ta dakin Ashnaah na biye da ita a baya, suna haurawa sama ta nuna mata Dakin Khaleel, Ashnaah ta murda kofar ta bude ta shiga abunta, yana xaune kan gado ya dafe kansa, ya dago da sauri don ganin wanda ya shigo fuskarsa a daure, ta ajiye masa abincin nn bakin kofa ta fice abunta ta koma Dakin ummi, ummi dae bata ce mata komae ba Ashnaah ta xauna ta ci gaba da kallonta tana ba ummi lbrin ynda film din yake, ummi na ta sauraronta. Karfe sha daya saura bayan an gama film din ummi tace “baxa ki kwanta ba Fateemah dare fa yyi” Ashnaah da har ta fara gyangyadi nn xaunen tace “xan kwanta momy” ummi ta kira Rukayya tace ta dauko ma Ashnaah kaya Mara nauyi tasa ta kwanta, rukayya ta dauko mata wani sabon kayan baccinta ta bata, Ashnaah ta karba ummi tace “to tashi ki tafi bayi ki canxa ko” Ashnaah tace “to” snn ta mike ta shiga bathroom ta sa kayan baccin snn ta linke kayan da ta cire ta maida hijab dinta har kasa ta fito. Xaune ta samu Khaleel a dakin, ta hade rae ta xauna inda take abunta, Ashnaah xata kwanta nn inda take a xaune ummi tace “ki tafi can dakin ki kwanta mana Fateemah” ta yi shiru bata ce komae ba amma ranta Bae so ba, can dae tace “to” snn ta mike tace sae da safe ta fice daga dakin ta nufi dakin Rukayya ta dan bude ta ga har ta kashe wuta abunta, tsaki tayi ta nufi dakin Khaleel ta bude a hankali ta shiga ta kwanta ta shige cikin bargo nn da nn bacci ya dauketa don dama baccin take ji”

 

[10/10, 6:37 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

24……

karfe sha biyu saura Khaleel ya bude kofar dakinsa ya shigo ya kulle yana kallon Ashnaah dake bacci hankalinta kwance cikin bargo, ya tsaya daga nn bakin kofar yana kallonta da mamaki, can yyi murmushi ya gyada kansa alamar xaki gane kurenki snn ya nufi bathroom, wanka ya kuma yi ya fito daure da towel yana goge gashin kansa da karamar towel, bude wardrobe dinsa yyi ga ciro sleepn robe dinsa fari ya sa, wayarsa dake gaban madubi ya shiga kara ya karasa gaban madubin yana kallon screen din wayar, karan wayar ya farkar da Ashnaah ta bude fuskarta a hankali tana kallonsa, yana tsaye gaban madubin yana kallon wayar har ya katse snn ya kashe wayar gaba daya, Ashnaah ta maida kanta cikin bargo da sauri, bargo babba ya dauko cikin wardrobe ya shimfida a kasa snn ya karasa daya side din da Ashnaah take ya dauki pillow ya ajiye kan bargon snn ya kashe wutan dakin ya kunna bedside lamp, sae a snn Ashnaah ta kuma bude fuskarta ta ga ya nufi fridge ya bude da key ya ciro wata kwalba, ya xauna gefen gado can nesa da ita ya bude ya shiga shan abun sa, sae kallonsa Ashnaah take har daga karshe taga ya mike ya kulle kwalban ya mayar cikin fridge din ya dawo ya kuma xaunawa gefen gadon ya dafe kansa, Ashnaah dae sae lekansa take ta cikin bargo don wutan dakin na da duhu, juyawa taga yyi yana kallonta, nn da nn gabanta yyi mugun faduwa ta rumtse ido da sauri, ya dde yana kallonta daga karshe ta ga ya mike ya sauka kasa ya kwanta kan bargon da ya shimfida nn kasan, sae a snn hnklin Ashnaah ya kwanta, tana nn kwance har kusan daya na dare bacci ya ki xuwa mata ta mike xaune a hankali tana lekan khaleel taga ya juya ma gadon baya, fridge ta kalla a xuciyarta tace ko me ya sha a kwalba da yaki xubawa a kofi ae sae na gani, mikewa tayi a hankali ta cire bargon jikinta da hijab ta sakko kan gadon ta isa gun fridge din ta bude taji shi a rufe, ta bude baki da mmki to meye na wani rufe fridge, gaban madubinsa ta nufa a hankali ta ga ko wayarsa na gun, ta laluba ta samu wayoyinsa duka biyun a wajen, daukan daya tayi ta danna ta ji a kashe ta dauka dayan ta danna sae ga haske, fridge din ta nufa da wayar a hannunta ta duka tana haska fridge din ta ga ashe keyn ma na jiki, budewa tayi snn ta jawo fridge din a hankali, duk wnn abinda take Khaleel na kallonta, duk a xatonsa ruwa xata sha, ya ga ta fiddo da kwalban da ya maida ta shiga haska wayarsa jikin kwalban don karanta menene, Alcohol kadae idonta ya sauka kai taji an daka mata tsawa “keee” a tsorace ta sake kwalban hannunta ta mike tsaye jikinta na rawa, ba karamin tsorata tayi ba don bata taba tunanin idonsa biyu ba, ya mike tsaye da sauri ya nufi gun kwalban da ya tarwatse kasan dakin, Ashnaah ta nufi kofa da gudu don duk tunaninta kama ta xae yi, fixgota yyi ganin fita xata yi ta bare baki a tsorace xata fasa ihu ya juyota ya matse ta jikinsa ya rufe bakinta da hannunsa yace ” nayi maki wani abu ne” kkrin cire hannunsa daga bakinta ta shiga yi amma ta kasa, tuni jikinta ya fara rawa ya jefata kan gado ya hau gadon shima yana kallon fuskarta cikin dim light din dakin, kkrin sauka ta shiga yi da sauri, yyi saurin fixgota ta fado jikinsa, kan tace komae ya rufe bakinta da hannunsa ya matse ta jikinsa, yana kallon fuskarta cikin dim light din dakin yace “kika ce baki da banbanci da budurwar dake gidan iyayenta ynxu ko?” Ashnaah ta shiga kallonsa a tsorace tace “ni? Yaushe na fadi hka?”

[10/10, 6:41 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr khaleel~ By khaleesat Haiydar

25…..

khaleel yyi murmushi ya kashe bedside lamp din dakin har lkcn yana tana jikinsa ya dago kanta yana kallon fuskarta yace “yhu re asking me ryt?” Ashnaah ta saki kuka ta shiga turasa tana cewa “don Allah kayi hkuri ni ba da kai nake ba fa” ya shaketa yace “kika sake tura ni sae na maki abinda baki yi xata ba, just stay calm idan ba hka ba yhu will regret it” kallonsa kawae take xuciyarta na bugawa, to me xae mata, rigar ta taga ya soma cirewa, ta rike hannunsa a tsorace cikin kuka tace “don Allah don Annabi kayi hkuri, kar ka min hka ka ga ni yarinya ce wayyo Allah na” dariya ssae ta basa, yace “ohw I c, ke yarinya ce ko?” cikin kuka tace “eh wllh am just 17” yace “to xan nuna maki ke ba yarinya bace” bata jira ya rufe baki ba ta fashe da wani kukan tana cewa “don Allah fa na ce maka kayi hkuri, wllh ni yarinya ce karama” ya dago kanta yana kallon for fuskarta da yyi shabe shabe da hawaye yace “ke yarinya ce kika iya daga hannu ki mari namiji” ta girgixa masa kai da sauri cikin kuka tace “kayi hkuri ban san xan mare ka ba, sharrin shaidan ne, kuma ae kai ma ka rama ranan” ya dauke fuskarsa don ta basa dariya ssae, ta shiga komawa baya a hankali, mikewa yyi ya sauko daga kan gadon ya fixgota kasa ya nufi bathroom da ita ya jefata ciki yace “kin ci sa’a ban ga abun burgewa a kwailan jikin nn na ki ba, in nace xan maki abinda ke raina ynxu ma sae dae in ba kaina wahala in cuce kai na, da yau kin gane kuranki don sae kin gwammace kida da karatu, mum dita kuma da kika ki gaisarwa daxu in mun je gida xa ki ban dalilinki nayin hka, wawiya kawae, ashe ke karamar yar iska ce tunda kika iya bude baki ki ba mutum hkuri, kinga gun kwananki yau don baki kai matsayin kwana cikin daki na ba” kallonsa kawae take kmr munafuka tsaye a bathroom din, ya rufe kofar daga waje ya sa key, Ashnaah tayi murmushi tana gyada kai a xuciyarta tace “xaka gane baka da wayo” bata damu da bathroom din da ya shigo da ita ba tayi xamanta abunta ta Jingina jikin tiles din dakin kalamansa na mata yawo a ka. har asuba Ashnaah bata yi baccin kirki ba a bathroom din, bude kofar bayin da aka yi yasa ta mike tsaye da sauri ganinsa tsaye bakin kofa, fixgota yyi ya wurgota waje ya shige bathroom din don yin alwala, ta nufi kofar dakin da sauri ta murda ta ji sa a rufe, ba karamin haushi hkn ya bata ba, tana nn tsaye ya fito daga bayi, ya nufi kofa yana kallonta yace “oh fita xa ki yi, to fita don Allah” hanya ta basa bata ce komae ba, yyi kwafa ya bude kofar da key ya fice don xuwa masallaci, gajiya tayi da tsayuwa ta nufi bathroom din ita ma tayi alwala ta fito ta sa hijab dinta ta tada sllh, har gari ya fara haske bata mike daga gun da tayi sllh ba ga wani bacci da take ji, kwanciya tayi nn kan darduman nn da nn bacci ya dauketa, can kusan karfe takwas ta farka ta mike xaune da sauri tana kallon agogo, kamshin sabulu da taji ya gauraye dakin yasa ta gane ana wanka a bathroom, ta mike tsaye ta nufi kofa a hankali ta bude ta fice daga Dakin ta nufi dakin Ummi, bata samu Ummi a dakin ba, hkn yasa ta shiga bathroom dinta ta wanke bakinta da mouth freshener kawae, ta wanke fuskarta snn ta fita ta fita daga dakin ta sauka downstairs jin kamshin soye soye, kitchen ta nufa ta same ummi da Rukayya suna hada break fst, ta gaida ummi cikin ladabi ummi ta amsa da fara’arta tace “an tashi lfya” Ashnaah tayi murmushi kawae, rukayya ta gaida ta ba tare da ta kalleta ba, Ashnaah ta amsa snn ta karasa cikin kitchen din don taya su, ummi tace “haba dae tafi kiyi xaman ki kawae ae mun kusa gamawa” Ashnaah tace “aa xan taya ku momy” ummi bata kuma ce mata komae ba ta shiga taya su juya potatoes din dake cikin mai kan gas. karfe goma Khaleel ya shiga dakin mum dinsa ya xauna yana kallon Ashnaah dake kallo yace “ke fa nake jira na ga kuma ba ki shirya va” Ashnaah na masa wani irin tace “ina xa mu” ya dake yace “gida” ta dan tabe baki tace “ni dae ina nn, ko ba ca kayi sati xan ma momy ba” Khaleel ya dubi mum dinsa da ke danna waya ya rasa me xae ce, Ummi ta ajiye wayarta tana kallon Ashnaah tace “Fateemah ki bari in kin kwana biyu sae ya kawo ki kiyi adadin kwanan da kike so a nn, kinga Bae kamata bakya dakin ki ba ynxu, kuma akwae masu xuwa ganin daki, ki bari sae an kwan biyu sae ki xo nn ko da kanki ma” Ashnaah ta dauke kanta ta hade rae bata ce komae ba, Khaleel ya mike ya fita daga dakin, ummi tace to tashi ki shirya ki wuce, bata mata musu ba ta mike ta sa hijab dinta kawae ta koma ta xauna, Khaleel ya dawo dakin rike da car key dinsa, yyi ma umminsa sallama yana kallon Ashnaah yace “mu je” mikewa tayi ita ma tayi ma ummi sallama fuskarta dae a daure ta fice daga dakin, bayan mota ta shige abunta ta daga ma su Ummi dake daga mata hannu, hannu ita ma, Khaleel dae Bae ce komae ba ya bude driver seat ya shiga ya tada motar suka bar gidan, sae da suka bar anguwar snn yyi parkin ya juya yana mata mugun kallo yace “ke ance maki ni driven ki ne da xa ki jabe min a bayan mota” tace “warce ka saka gaba jiya ka kuma dauketa ka sa ta gaba ni kam ga maxaunina” ya bude mota a fusace ya fito ita ma ta fito da sauri ta daya bangaren tana hararansa tace “wllh ka taba ni sae na rama, in kuma karya ne ka gwada ka gani” tsayawa kallonta yyi, ta tabe baki ta dauke kanta tana rike da kugunta tana girgixa Kafa, ya dauke kai yyi murmushi ya koma seat dinsa ya shiga ya xauna, snn ta ja tsaki ta nufi front seat ta bude ta shiga ya ja motar suka bar wajen.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button