Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

26……

Dae dae wani babban clinic taga yyi park, ta dan sace kallonsa taga wayarsa yake dannawa, can ya kara a kunne yace “kina clinic ne” Ashnaah ta tabe baki a xuciyarta tace kanka ake ji, murmushi ta ga yyi yace “not so wllh, ynxu dae ki fito ina waje” yana kai wa nn ya kashe kiran ya ajiye wayar nn gefensa, ba a dau lkci ba Ameesha ta fito daga gate din hsptl din, ya tsura mata ido tana takowa a hankali, duk ta rame ta xama wani iri sae ta basa tausayi ssae, ya shafa kansa har ta karaso gun da yake, ya xuge glass din motar yana kallon ta, hawaye ne cike idonta, ya bude motar ya fito yana kallon kyakkyawan fuskarta a hankali yace “y those tears” kuka ta saki ya kauda kansa kawae xuciyarsa na tafarfasa, shi Bae san ynda xae yi da Ameesha ba, shi ba sonta yake ba gwara dae wani lkcn ya kan ji sha’awarta, yasan Ameesha kyakkyawa ce ssae bata da wata makusa a jikinta, but kawae shi dae har yau Bae ga macen da xata burgesa ya so ta ba, Ashnaah kam sae kallonsu take da mamaki daga cikin motar, to wacece kuma wnn gantalalliyar da tasa namiji a gaba tana kuka, ita dariya ma abun ya bata kmr ta fito tayi kallon da kyau, Khaleel ya juyo yana kallon Ameesha ya karaso gabanta ya rungumota jikinsa a hankali yace “kiyi hkuri Ameesha, am sorry” dago kanta yyi yana share hawayen fuskarta yace “don’t wrry kin kusa mallakana a matsayin mijin ki kmr ynda kike buri a ko da yaushe I promise yhu dat” bata dago kanta ba bare tace komai, ya riko hannunta cikin nasa yace “xa ki raka ni gida ne ynxu,” ta dago kai tana kallonsa tace “matar ka fa” ya hade rae yace “ca nayi maki ina da mata, maid dina dae xaki ce ko kuma Kice mistress duk da ban ma bata wnn matsayin va tukun.” Ameesha tayi shiru tana kallonsa ya gyada mata kai yace “yes ga ta ma a mota, in xaki bi ni gida, ta fito ta baki front seat mu tafi” Ameesha ta kalli motar da sauri suka hada ido da Ashnaah dake kallonta, gabanta yyi mugun faduwa tana kallon Ashnaah tace “ina yini” Ashnaah tayi dariya hade da tabe baki tace “ke kuma irin kaddararrki knn,” sae kuma ta fashe da dariya tace “Allah ya sauwake maki, amma kuma fa kin ban mmki duk kyan nn naki ki rasa wanda xaki so a duniya sae wnn abun dake gaban ki” Ashnaah ta kuma fashewa da dariya duk da ba karamin faduwa gabanta yake ba, ta nuna Khaleel tace “har ina abun so a nn, ae wllh ko maxa sun kare a duniya bn ga abun da xanyi da wnn mutumin ba, tab sae kace uwata ta min baki”

 

[10/10, 6:42 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel ~ By Khaleesat Haiydar

27……

Khaleel ya juya a hnkli yana kallon Ashnaah da mugun mmki, ta galla masa harara ta tabe baki ta dauke kanta xuciyarta na ci gaba da bugu, Ameesha kam kallon Khaleel kawae ta tsaya yi, turata yyi da karfi daga gabansa a fusace ya nufi driver seat ya bude ya shiga ya tada motar yyi reverse ya bar layin da gudu, Ashnaah dae sae faduwa gabanta yake barin ynda ta ga yana gudu, da kyar ta juya tana kallonsa ta dake ta hade rae tace “gida wae xa mu tafi ynxu” Bae tanka ta ba sae gudu kawae yake da mota, nn fa hnklinta yyi mugun tashi, ta marairaice masa tace “ka min mgna mana gida xa mu?” Parkin taga yyi kan ta ankara ya wani irin fixgota ya shiga marin ta, gigicewa tayi ta fasa kuka tana cewa “wayyo Abbana na shiga uku me nayi maka” ihu ta dinga yi ganin yaki kyaleta ta shiga basa hkuri tana rusa kuka, turata yyi da karfi ta bugu da mota snn ya ci gaba da tukinsa, Ashnaah ta dinga kuka a motar tana rike da kanta tana kiran momynta, yana isa gida yyi parkin bayan mai gadi ya bude masa gate, snn ya bude mota ya fito ya xaga ta inda take yana huci ya bude kofa ya fixgota ya nufi cikin gida da ita, kuka take tana rokansa Allah da annabi yyi hkuri amma Bae ma san tana yi ba, ya bude falon ya jefata ciki ta Mike da sauri jikinta na rawa xata gudu yyi saurin fincikota ya kai mata wani wawan marin kuma, rungumesa tayi ta boye fuskarta a kirjinsa cikin kuka tana cewa “don Allah don annabi ka daina dukana wllh baxan sake ba kayi hkuri plss” fixgeta yyi daga jikinsa ya nufi sama da ita yana janta tana kuka tana rokonsa, dakinta ya bude ya jefata ciki har sae da ta bugu da gado snn ya rufe dakin ya bude dakinsa ya shige, kuka ssae Ashnaah take tana rike da kanta da take jin kmr ba nata ba duk jikinta ya mutu sbda axaba, baccin wahala ne ya dauketa nn kasan tiles din da take a kwance. Sae kusan la’asar ta farka ta mike xaune da kyar duk jikinta ciwo suke mata ga wani mugun ciwon da kanta yake, da kyar ta dafa gado xata mike taji jiri na neman kwasheta, ta koma ta xauna tana rera kuka a hankali tayi Mae isarta snn ta daure ta tashi tsaye tana daddafa bango ta shiga bayi don yin alwala don ko Azahar bata yi ba, a daddafe ta idar da sllh ta koma gado da kyar ta kwanta nan da nn bacci ya kuma dauketa. Bude kofar ta da taji anyi yasa ta farka a tsorace ta mike xaune taga wae ashe har dare yyi, tayi saurin mayar da kallonta ga kofar don gnin wnda xae shigo, ba karamin faduwa gabanta yyi ba ganinsa, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya ajiye ledan hannunsa ya fice daga dakin, ta fashe da kukan takaici kmr xata hadiye xuciya, sae da taji ya shiga dakinsa snn ta soma cewa “wllh ka xo ka dauke gantalallen ledan ka mugu kawae axxalumi, kuma Allah ya Isar min” ta fada kan gado ta fashe da wani matsanancin kuka tana rike da kanta, wani mugun tsanan khaleel take a xuciyarta, ta kusa minti talatin tana kuka snn ta mike tsaye da kyar ta nufi bayi don yin alwala, ta dde xaune kan darduma bayan ta idar da sllhn daga karshe dae ta rarrafa don bata jin xata iya tashi don xaxxabi taji ke neman rufe ta, ledan da ya ajiye mata ta jawo ta bude ta ga take away na fried rice da salad ne sae naman kaxa da hollandia drink Mae sanyi, daya ledan kuma fruits ne, ball tayi da ledan da hannunta don takaici, nn da nn taji karfi ya xo mata ta mike tsaye da sauri ta dauki ledan ta bude kofarta a hnkli ta nufi kofar dakinsa ta bude take away din ta xaxxage shinkafar nn bakin kofarsa snn ta bude drink din ta tuttula kan shinkafar ta barbaxa fruits din nn bakin kofar kan shinkafar snn ta koma dakinta tayi kwanciyarta duk da irin faduwar da gabanta yake, duk ta rasa sukuni kwanciyar ma ya gagareta sae faduwa gabanta yake ssae, ta mike xaune can kuma ta nufi kofar bayi ta tsaya, bayan kusan minti talatin taji ya bude kofar dakinsa, ji tayi kmr xuciyarta xae shige cikinta don tsoro, ta shige bayinta da sauri jikinta na rawa, jira kawae take ta ga ya bude kofar dakinta amma shiru ta kusa wani minti talatin din a tsaye amma bata ga alamar xa a bude kofar dakinta ba, hamma tayi jin cikinta na kugi ta shiga bayi don sake alwala ta xo tayi isha, har ta idar da isha bata ga ya shigo dakinta ba sae ma ji da tayi ya bude dakinsa ya shiga, tayi tsaki ta mike ta nufi gado ta kwanta tace “da ka shigo dakin nn da ka sha mamaki na wllh” har kusan sha daya Ashnaah bata kuma jin motsin Khaleel ba, yunwan cikinta ya isheta bbu abinda take sae Hamma sae juye juye take kan gado, rabonta da abinci tun break din da tayi da safe, juyawa tayi ta rufe idonta ko bacci xae dauketa amma bacci ya ki xuwa har kusan karfe daya, ganin ba sarki sae Allah yasa ta mike xaune tana tunanin to ina xata samu abun da xata ci ynxu, mikewa tayi tsaye ta nufi kofa a hankali ta bude ta fito tana kallon bakin kofar dakin Khaleel, duk ya kwashe abincin da ta walakanta nn bakin kofar ya goge wajen, ta dan yi tsaki ta shiga sauka kasa a hankali don xuwa kitchen ta ga ko xata samu abin da xata ci, duk an kashe wutan ko ina har kitchen din, ta shiga lalube lalube har ta isa kitchen din snn ta bude ta shiga, ta fara laluba bango don neman switch din wutan kitchen din, kunnawa tayi farin wuta ya haska kitchen din ta shiga bin sa da kallo, take away ta gani a rufe da Rabin hollandia a glass cup, ta karasa da sauri ta bude taga jollof ne da nama a ciki an taba kadan an bari ga spoon ma a ciki, tayi murmushi ta sauko da shi kasa ta ajiye da drink din snn ta kashe wutan kitchen din ta xauna nn kasa tana shiga ci da sauri da sauri.

[10/10, 6:42 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel ~ By Khaleesat Haiydar

28…..

Ashnaah ta juya da sauri tana kallon bayanta a tsorace, sae taji kmr motsi a falo, ta dde tana kallon bayanta daga karshe ta ci gaba da cin abincin gabanta da sauri cikin duhun, haske ta ga ya gauraye kitchen din ta daga kai da sauri suka yi ido hudu da Khaleel, yana tsaye daga bakin kofar sanye da 3qtr da singlet, ji tayi kmr ta nutse wajen don kunya, ta tsunkuyar da kanta ta mike tsaye kmr munafuka ta juya masa baya, kallonta kawae yake daga sama xuwa kasa yana murmushi, can dae ta durkusa da sauri ta dauke abincin da drink fuskarta a daure ta ajiye gun sink din kitchen din ta wanke hannunta ta nufi kofa ba tare da ta kallesa ba ta raba ta gefensa da sauri xata fita, ya fixgota yana Mata wani irin kallo yace “koma ki cinye shi” hade rae tayi tana hararansa tace “ca nayi maka yunwa ,nake…” Shiru tayi ganin irin kallon da yake mata, ta yi kmr xata yi kuka tace “ni ba yunwa nake ji ba” fincikota yyi suka shiga kitchen din ya sauko da abincin ya ajiye nn kasa yace “sae kin cinye shi wllh” nn da nn hawaye ya cika idonta ta ce “ni baxan ci ba” sae kuma ta fashe da kuka, ya fixgota ya juyo da ita yana mata mugun kallo yace “kuka kike min”share hawayenta ta shiga yi ta durkusa gaban abincin ta shiga ci a hankali yana kallonta, har sae da ta cinye don dama kadan ya rage snn ta mike fuskarta daure, xata fita ya kuma fixgota yace “wa kika bar ma drink din” Bae jira me xata ce ba ya dauko ya mika mata fuskarsa daure, ta dake ta karba daga hannunsa ta juya masa baya ta shanye snn ta ajiye ta fice daga kitchen din da sauri har tana neman bangaje shi, ya daka mata tsawa, ta juya tana kallonsa fuskarta daure, yace “xa ki kuma shan wani dukan ne ynxu idan baki yi hnkli ba yarinya,” tana masa mugun kallo tace lallae ma, da yake ca aka yi maka yar ka ce ni va, wllh ka kuma taba ni na rantse da Allah sae na rama” tsayawa kallonta yyi can ya dauke kansa yana murmushi, ta hararesa duk da gabanta faduwa yake ta juya da sauri ta nufi stairs, ya bi bayanta ta saka gudu tana kiran momynta, sae da ta hau stairs na biyar snn ya risketa, ya fincikota ta fado kansa, ta juya da sauri ta kankamesa jikinta na rawa tace “wayyo ba da kai nake ba don Allah” Bae tanka ta ba ya shiga janta suka haura sama har lkcn ta ki sake shi ta boye fuskarta a kirjinsa, ya bude falonsa ya shiga ya kulle,snn ya nufe bedroom dinsa nn ma ya kulle bayan sun shiga, hkn yasa ta daga kai da sauri don ganin inda ya shigo da ita, ba shiri ta sakesa, ta koma baya tana kalle kalle kmr xata yi kuka tace “kayi hkuri ni ba da kai nake ba fa” wardrobe dinsa ya nufa ya bude ya shiga fiffito da duka jallabiyansa da ba guga, ya dauke su gaba daya ya ajiye su kan rug din dakin ya fito da dutsen guga ya ajiye snn ya nuna mata pressing board yace “ki tabbatar kin goge min su tsaf” bude baki tayi tana kallonsa, wardrobe ya kuma budewa ya kwaso cover shoe dinsa kusan kala biyar ya xube su nn kasa, snn ya fito da Polish da brush ya ajiye kusa da su snn ya mike yana kallonta yace “yhu make sure u Polish dis also, more especially dis dan gobe da shi xan fita aiki” Ashnaah ta fashe da dariya kmr wata tababba ta xube kasan dakin har da rike ciki tana kyalkyala dariya, ya dauke kai don shi ma ta basa dariyan, can ya juyo ganin taki daina dariyan ya nufi gun da belts dinsa suke ya dauko daya yana mata wani irin kallo yace “its funny ryt” mikewa tayi da sauri nn da nn tayi tsit ta nutsu tana kallonsa, yace “ci gaba mana” tace “ni fa bn iya guga va shi yasa nake dariya wllh” yace “ko, to bari in koya maki” daga belt ta ga yyi xae tsula mata tana ganin hka ta yi kansa a tsorace ta fada jikinsa ta rungumesa ta rike belt din, duk ynda Khaleel ya so regainin balance dinsa Kasawa yyi duk suka fada kan gado, ya turata daga jikinsa da sauri xae mike ta fixgosa ya kuma fadowa kanta jikinta na rawa tace “wllh na iya xan yi don Allah kar ka dokeni” da kyar ya iya turata kuma ta fada kan gadon kan ta kuma fizgosa

ya mike ya nufi bathroom da sauri, ta mike xaune ta bisa da kallo gabanta na ci gaba da faduwa, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta fice daga dakin.

~Dr Khaleel ~ By Khaleesat Haiydar 29….. Washegari da safe Ashnaah na xaune gaban madubi daure da towel ta fito daga wanka taji fitar motar Khaleel, ta karasa window da sauri tana kallon motar har ya fice daga gate mai gadi ya kulle gate din, da sauri ta nufi kofarta don sauka kasa ta ga ko ya kulle kitchen din yau ma ae ko da ya ca cuceta don tun asuba cikinta ke kugi, da sauri da sauri ta nufi kitchen din suka kusan cin karo bakin kofar kitchen din ta rike towel dinta ta koma baya a tsorace tana kallonsa, sae take ga kmr ba shi bane, dauke kansa yyi da sauri ya juya mata baya, juyowa ya kuma yi ya bi ta gefenta va tare da ya kalleta ba ya fice daga kitchen din, ta bi sa da kallon mmki har ya isa stairs snn ta fashe da dariya, to ko dae tsoronta ya fara yi ne, ta kuma kyalkyalewa da dariya snn ta shiga kitchen din tana kallon cup din da ke ajiye da ruwan xafi a ciki da alamar tea xae hada, drawers din da ta gani ta shiga bubbudewa don neman kayan tea, duk ta samu har da sugar da lipton, ta fiffido su ta ajiye gefe snn ta dauki cup da spoon, ta kinkimesu gaba daya ta nufi dakinta da su, ta jera su nn kan side drawer dinta snn ta kuma sauka, ta nufi kitchen din ta dauki electric kettle din da ta gani ta karasa dinnin ta kuma daukan bread din da ke kai ta koma sama ta kulle dakinta, tana saka kaya taji budewan gate da shigowar mota, ta karasa window da sauri taga anyi parkin motar nn tsakiyar compound, sae kallo take ta ga wanda xae fito, wani mutumi ta gani, ta dan yi tsaki ta koma ta ci gaba da abinda take aka danna kararrawar gidan, tana ji Khaleel ya bude dakinsa ya sauka kasa, bayan kmr minti biyar ta kuma leka window ta gansa tsaye jikin motar yana waya, farar t-shirts ne jikinsa da bakar wando da ganinsa kasan aiki xae fita, bude motar yyi bayan ya gama wayar ya shiga, mai gadi ya bude masa gate, Ashnaah tayi tsaki ta koma ta ci gaba da abinda take. Khaleel na xaune office yana flipping thru files din dake gabansa, ko kadan hnklinsa baya kan abinda yake, ya rasa takamai mai wani tunani yake a xuciyarsa, Ashnaah ce ta fado masa ya tura files din gabansa kawae ya sauke ajiyar xuciya a hnkli yace “yes na gano abinda ke damuna ynxu,” mgnr xuciya ya shiga yi “just tired of dis forsaken gal I guess, an obstacle 2 my life, yes a great one, den wat am I still waiting 4, y nt take my revenge and let her go” bude kofar office dinsa da aka yi yasa ya dago kansa da sauri, Ameesha ta shigo office din da sallamarta, yyi huci me xafi yana nuna mata kofa yace “get out please, just lemme b for heaven sake” juyawa tayi a hankali ta fita daga office din ta kullo masa, tsaki yyi ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake xaune, bayan kmr minti goma a ka kuma bude kofar ya mike tsaye a fusace duk a tunaninsa ita ce, Najeeb ne ya shigo, khaleel ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya xauna, Najeeb ya xauna kan table din abokin nasa yana masa wani irin kallo sae kuma ya fashe da dariya yace “Ango ka sha kamshi sae yau aka yi resuming,” bnxa khaleel yyi masa ya shiga signin files din gabansa, Najeeb yyi yar dariya yace “ka bamu mmki Khaleel dama duk cika baki kke ashe, kasa mun xuba ido….” khaleel ya Mike da sauri ya katse sa yana kallonsa yace “enuf plss, just watch n c” Duk da irin ynda gaban Ashnaah ke faduwa hkn Bae hanata abinda take ba, tsaf ta fiddo gaba daya alcoholic drinks din da ta gani fridge dinsa tana tabe baki tace “no wonder ashe mashayin giya ne dae” kofa ta ji an bude downstairs, xuciyarta ya kusa shige wa cikinta bata kuma wani tunani va ta fice da gudu daga dakinsa jikinta na rawa, Meenah ta hango tsaye falo tana kare ma falon kallo, Ashnaah ta sauke ajiyar xuciya ta dafe kirjinta dake bugawa da karfi har lkcn, kasa ta sauko tana ma Meenah wani irin kallo tace “ya xa ki shigo ma mutane gida va sallama” Meenah tace “na ga dae ba gidan ubanki bne nn din ko” Ashnaah ta xaro ido tace “ubana kuma” Meenah tace “hka dae na gani” karasowa gabanta Ashnaah tayi a fusace wae xata mareta, dae dae nn khaleel ya shigo falon, Ashnaah ta xaro ido a tsorace tana kallonsa tunawa da tayi bata mayar Mae da abubuwan sa ta fito da ba daga fridge, ihu ta saki ta dafe kuncinta tana kallon Meenah tace “kika mare ni” sae kuma ta fashe da kuka har da durkusawa, Khaleel ya karaso yana kallon Meenah dake kallon Ashnaah da mmki yace me ya shigo da ke gidana, mikewa Ashnaah tayi da gudu ta nufi sama don xuwa ta mayar da abinda ta fiffito da.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button