NOVELSUncategorized

RAGGON MIJI 41-45

41
*duka buk dinnan fa sadaukarwa ne ga sister zulaihat rano, niko se rabarwa mutane pages nake ba neman izini ????????amin hakuri sister, ai nasanki da kirki da hangen nesa ko banfada ba kinsan inda na dosa, I really love you sister*????
*wannan pagyn ma de sadaukarwa ne ga maman nour the writer of (yanzu nake girba), kisani inasonki kamar yadda kike kamnata ????Allah ya rayamiki zuria ya barki da megidanki thanks for everything ????*
Hjya wani kololon bakin ciki yatsaya mata, itafa bataso ya rika wani kula sosai da mace,
Bayan kwana biyu wata kawar ummi tazo gidanta gulma suka gaisa anata labari dan Sun kwana biyu basu haduba,
Can labari yayi labari saude ta kawo gulmar data kawota,
“waiko hjy kinsan mijin faseelat har yayi aure? “
Ummi cikin mamaki tace “a, a bansaniba wlh ashe har yakara wani auren, amma hjya bata kyautamin ba dabata fadamin ba “
Saude tace “keda in tafada miki zuwa zaki? “
Ummi tace “yo me ze hana aibazan manta alherin da tamin ba”
Saude taja tsoki “yo wane alheri ta miki inba cutarki datayi ba, yoni fa wlh sede inbada labari dankuwa rakiya kut take da kawata, wai ke bakisan yadda akaiba ita rakiya taje tafadawa saratu ai danginku yan mallaka ne ta kuma bata shawara akan ayi mishi kwado kada ya kusanci diyarki ta mallakeshi, se yanzu da suka rabu suka koma gun malami suka samu ya rasu suka zo gida sunata jidali da saratun har dannata yaji ya fadi, ai ya dade asibity baya lafiya, se yanzu da abun ya kwabe ita rakiya kebawa zulai labari shine tafadamin, nace ai gwara da aka sakarmiki diyarki wlh”
ummi ta rike baki tana sallallami tace “ammade hjya bata kyauta min ba, da yarinyar nan ta afka zina fa tunda ita shegen zurfin cikin tsiya ne daita duk abinda ake bansaniba seda ya saketan, to Allah yakyauta bantaba jin irin labarinnanba se a wannan novel din na raggon miji ace wai uwa ce tayiwa danta makulli, “
Saude tace “amin kede ai hjya ba masoyiyarki bace yanzu wanga auren da yake tana sonshi ai bakiga yadda take rawar kai ba “
Ummi tace” Allah ya kyauta de “suka cigaba da jimami,
Faseelat nata kaikawo kitchen to daki taji firarsu tai tsaye tana jin tausayin khalil ashe dama hassashenta gaskiya ne bai lpyan, takoma daki ta dauki wayarta tai dialing number dinshi,
Khalil yana kitchen yanawa Amarya jamila girki wayarshi tai kara ya dauka yana kallon screen din dukda yagoge number dinta amma be manta digit daya na number taba, ya dauka dayin sallama,
Faseelat ta amsa tana murmushi tace “ango kasha kamshi “
Yayi shiru bece uffan ba tace “yau nakejin labarin kayi aure shine nakira naimaka fatan alheri, Allah yabaku zaman lpya yabaku zuria dayyiba,”
yace “amin Nagode “
tace “Tom se anjima agaida amarya “
Takashe kiran tayi deleting number dinshi, hakanan taji hawaye Sun zubomata ita da kanta take jin tausayin kanta,
tai dialing number fahad kamar kullum tana ringing baadauka, tai zaune tanata sharar kwalla dacewa “ni miye laifina? dazakamin wannan hukuncin fahad? Ai sunan bazawara kawai nake amsawa amma sunan be kamace niba “(toshi ina yasani malama faseelat) ????
fahad wata biyunnan da sati daya horo kawai yakewa kanshi saboda haryanzu memakon ya rage tunaninta sema karuwa yayi, duk nakusa dashi sunga sauya warshi, ita kanta aisha taga canji sosai kuma ta tabbatarwa kanta akwai abinda ke damunshi beso yafada mata ne kawai har kara takaishi gun mommy takirashi ta mishi magana amma yace bakomi haka suka hakura suka sa mishi ido, harta dan wasa da dariya da yakeyi da aisha duk yabari any time yana busy thinking of cutie dinshi, inkaga dariyar shi to amira na wurinshi ,kullum cikin duba pics dinta yake abinda ke kara hura mishi wutar sonta da shaawarta.
Suna cikin fira da best friend nashi sabeer da ya dawo daga Italy wani aiki kiran faseelat ya shigo, tunda kiran ya shigo har ya tsinke fahad be kyafta ido ba ya zubawa screen din wayar ido yanata kallon cutie na yawo don yakasa sauya sunan kuma yakasa deleting number din,
Sabeer na kallonshi ganin duk sauran annurin fuskarshi ya gushe yace “wai dude lpya nifa tunjiya nake da tarin questions da zanmaka, mike damunka plsss duk kafada sosai ka rame kuma bakada kuzari kamar da miye ke damunka? “
Fahad ya meda kanshi jikin seat din office dinshi ya rumtse ido,
Sabeer yace “bamu saba irin haka da kai ba just tell me komiye nikuma zanyi iya kokarina wurin temaka maka “
Fahad ya tashi zaune ya bude pic din faseelat yana kallo Kasakasa yace “I’m in love “
sabeer ya daga kafada “so whats going on “
Fahad yace “she deceived me, tabari nakamu da sonta while tasan she’s a divorcee”
Sabeer yace “me I don’t see something bad ai tunda kana sonta ka aure ta haka mana “
Fahad yace “u  known me, kana tunanin kishina zan iya auren disvirgin? a girl that someone slept with her uncountably? “
sabeer yace “so then karabu daita mana kahuta “
Fahad cikin shouting yace “I cant ,now it’s over 2 month and something nakasa cireta arai na,”
Sabeer yace “ni ko i want see the girl ,wadda sonta yasa ka koma haka “
Fahad ya lallatsa system dinshi yayi viewing pic din faseelat tana sanye da red material ya juyar da laptop din wurin sabeer yace “see her “
Sabeer zaro ido yayi tareda fadin “gorgeous girl, gaskiya dole ka rude to yanzu de tunda baka son disvirgin ni tamin inasonta ahaka kamin hanya plsss “
Fahad ya harareshi yana janye system dinshi da sabeer ya danne da hannu biyu, yana jin haushi ko Wow din da yace jiyayi kamar ya kai mishi naushi,
Yace “ni takeso bakaiba kuma I don’t think zata soka don kamata muni da yawa, nikuwa kaga 2 month ta dauka tana bina taimin missed call tamin message tana magiyar in yafemata amman ban kula ta ba kuma bata dena ba har yau,”
sabeer yace “gaskiya bakamata adalci ba, tunda ta baka hakuri yakamata ka hakura tunda kuna son junanku, ka dubeta fa son kowa kin wanda ya rasa ina maka tsoron karwani yazo yama shigar sauri, think mana kai mafa ba virgin dinnan bane to ita bindiga zatai, itada zata rika sharing dinka da wata fa, ni aganina ka cire kishinnan ka aure kayanka “
Fahad yayi shiru yana nazari yace “I’m missing all about her ina azabtuwa “
sabeer yace “stop following ur wrong decision and face the truth, call her back, kabata hakuri tunda tana sonka she’ll forgive you, irin wannan kyan nata ko baka taba ba kallonta kawai ya isheka jindadi”
Fahad yayi murmushi ya dauki wayarshi don he’s following sabeer advices always saboda tana mishi amfani yace “le me call her “ya dago ido ya kalli sabeer,
Sabeer yace “hakane dede “
Suddenly kiran fahad ya shigo wayar faseelat sede lokacin har tabar dakin tana kitchen ,
Fahad ya Kalli sabeer yace “she’s not picking”
Sabeer yace “just try it again “
Fahad yakara dialing
Faseelat na kitchen
taji ringing din fahad, waqar umar m sheriff me taken tabbas,
tana gudu tazo ta dauka ganin vedio call ne yasa ta dedeta kanta ta zauna sannan ta dauka,
Shaf ta manta kayan jikinta vest ce kurum da zane gashinta kan kafada ,
Suna ganin fuskar juna dukkansu suka Saki ajiyar zuciya, ya kureta da ido tsikar jikinshi na tashi ganin breast dinta a zahirance ga nipples dinta fili dan ko bra babu jikinta,
Ganin kallon da yake mata ta sunkuyar da kai thinking that abinda ta mishi ne yasaka kallon nan da nan hawaye suka cika idonta tasa hannu ta share tadan dago ta kalleshi tace “I’m sorry plss “
Ya lumshe ido ya bude yana karabinta da kallo duk ta rame ashe itama tana wahala,
Yace “I’m sorry for what I did to you by avoiding you all that time “
Ta danyi guntun murmushi tace “don’t say that nice namaka karya i deceived you kai bakai komi ba “
yana kara kallonta yace “u look pale why? “
Ta lumshe ido ta bude ” I must I can’t bear to lose you, I suffered alot ,plss don’t leave me I can’t be able to live with out you “
Ya danyi guntun murmushi yace “look at me carefully “
Ta kura mishi ido yace “how do I look? “
Tace “pale too”
Yace “u are not suffering alone we all shared thesame thing, meyasa kika boyemin kintaba aure se da kika bari nakamu da sonki sannan ihhim why? “
ta share hawaye yayi saurin cewa “stop this crying abeg, just answer my question”
Ta dukar da kai” banason rabuwa da kaine, nasan inkaji ina da aure bazaka taba kulani ba “
Yana nazari yace “that means kina da aure muke conversations? Together? “
Hawaye suka zubo mata tace……
 You have to comments plsss????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY SHALELE*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
42
*dis page is for my bazawari, ina tsananin sonka son da nike maka ya zarce girman kiyashi????luv u irin a bit tiny ????thanks for the love and everything,i salute you*
Tace “dan Allah kayi hakuri karka barni “
Yana kallonta hannusa kan labbansa yace “faseelat kidena min boye boye just tell me everything about you, I’m not going to leave you do you get me ? “
Ta daga kai yace “alright tell me kinada aure muke conversation? “
Ta daga kai tace “bana son mijina aka Aura minshi, bayan auren mu baya kula dani, lokacin da na ganka nafara jin sonka dan Allah kayi hakuri sonka ne ya rufemin ido nai haka”
Yana mata wani kallo idanunshi sunyi ja yace “this means ranar da mukai last chart ranar aka sakeki? “
Ta daga kai “ranar ne kuma dama wata na takwas kadai “
Kanshi Duke ya dago “kina nufin kadai ne, kato yayi wata takwas yana squeezing dinki ki kira shi kurum, kinsan yadda nake da kishi kuwa? Wlh faseelat kin mameni da ba abunda zesa nafara sonki danasan haka, shikenan duk yagama kallemin ke yagama tande komi “
Sabeer dake gefe ya babbake da dariya,
Fahad ya wurga mai harara, ya kame baki ya daga mai hannu alamun yayi shiru,
Fahad ya meda kallonshi wurin faseelat idanu Jawur,
Faseelat ta fashe da kuka tana girgizakai, batasan ya zata mishi bayani ba,
tasaka tafin hannayenta ta rufe fuska da tafin hanayenta tana kuka,
Ya kawar da kai gefe yana hura iska da baki hannunshi kan kugu ya juyo yana kallonta kukan na tabamishi zuciya yace “stop shedding your tears ,plss “
Ta dan rage volume din kukan yace “ni kikeso ko? kuma kinsamu I will now going to treat you just so, u know I love you Very much 
Ta dago ta kalleshi
Tai shiru ta ajiye hannuwanta tana jan hanci,
Yace “yanzu yaushe zan ganki I want to see you cos I’m missing you “
Ta girgiza kai tace “not now”
Yace “why? “
Tace “bazaabarni ba”
Yace “ni inason ganinki gaskiya “
Tace “OK “
Yace “now smile I want to disconnect the the call “
Tai murmushi tana rufe fuska yace “that’s my cutie “yana sakin murmushi,
yana kara kallon breast dinta yace “plsss cover my thing baniso wasu suna ganinsu “
Ta dago tana kallonshi dan bata fahimta ba taga ita kawai yake kallo tabi setin idonshi taga breast dinta kawai ya kurama ido,
Ta zaro ido tana rufe fuska don tamanta kayan dake jikinta,
Yayi murmushi ganin tanajin kunya, yace “take good care of yourself sena kira anjima ko “?
ta daga kai tare da fadin “luv you my handsome “
yace “no, no ban yadda ba se kinmin kisss dina wlh I missed it too much “
Tai murmushi tana jindadi ta tura labba just like u r to kiss tai masa muhww
Ya lumshe eyes ya bude yace “thank you”
Ya mata bye da yatsu ta meda mishi ya kashe kiran,
sabeer yafara tafi yana fadin “amazing! Love birds gaskiya nima I want to find someone like her “
Fahad ya hura iska yana sauke ajiyar heart yace “kasan wani abu wlh senaji kamar an saukemin wani nauyi, gaskiya bansan irin son da nake mata ba “
sabeer yace “ai kaine kabawa kanka headache tuntuni kaga ma duka wata 8 ne tayi da aure “
fahad yace “dukda haka I feel bad, saboda ban tsarawa kaina auran bazawara ba kai ko mata biyu banyi niyyar aure ba amma this young lady tasa duk na watsar da komi,kuma kaga nima bazanso wani yana fira da matata ba, ni I’m afraid karda tamin haka nima “
Sabeer yace “haba bazata ma haka ba, kadena irin wanga tunanin inde kanason zaman lpya “
Fahad yace “naji mijin radiya “
sabeer yace “nima gaskiiya zan wa faseelat magana ta samar min irinta ko a dangi “
fahad yayi dariya yace “babu, kai kabar maganar nan kar naje nafadawa radiya yau ahanaka tabi “
Sabeer yace “ni yakamata nace haka, zuwa kawai zanyi nafada wa aisha cewa u r about to get the second wife “
Fahad ya dora hannu a baki yana zaro ido yace “rufamin asiri, ni har ka tunamin akwai big war gabana ita faseelat kawar aisha ce ni bazan iya tararta da maganar ba ma “
Sabeer yace “cabdi, ai dole tasani “
Fahad yace “wlh aisha ta cika kishin tsiya ranar nan ma fa daga ita faseelat tazo tayi girki nace ysyi dadi taita kuka ta kwashe girkin ta kaiwa baba tsoho, to inaga intaji zani aureta? “
Sabeer yace “Allah ya kyauta kasan mata da kishi haka yaruwarta radiya take kuma sede tayi hakuri dan bazan hakura da tsomawa wuri daya ba “
suna dariya suka kashe fahad yace “mu fita plss karakani wani wuri “
Suka mike suna tafiya sabeer ke cewa “kai gaskiya dude zaka huta wannan halitta haka zankadi kenan “
Fahad yana hararanshi yace “kuma kwalelenka ba”
suka cigaba da fira fuskar fahad a sake kamar bashine yayi 2 month ba faraa ba,
suna gama waya faseelat tafara tsalle saboda murna ta dauki wayar tanata manna mata kisss,
sega ummi ta leko ta taga tana kallonta tace “ke lpya kike? “
faseelat tai sauri ta ajiye wayar ummi na karemata kallo tace “sekije ga miyarki can ta kone “
faseelat ta zaro ido ta diba aguje se kitchen.
Da marece faseelat akasha gayu se kace me miji ummi de se kallonta take ganinta cikin walwala yau,
As usual karfe 8:30 fahad ya kirata, tun da tai ishai bata bar dakin ba ,
hannu na rawa ta dauka takara a kunne,
yace “hi “
Tace “ihimmm sweetie na “
Ya lumshe ido ya bude yace “kullum voice naki nakara dadi meyasa? “
Tace “kamar yadda nakejin naka haka kullum “
Ya dan murmusa “I want to ask you something “
Tace “ask me “
Yace “when are you going to complete ur idda?  I’m very eager to have you as a wife”
tace ” in next 3 wks “
Ya meda kai jikin seat din mota yana murmurza gashin kanshi yace “I can’t wait to that date, kisan yadda zaki kifito naganki, I want to see ur beautiful face and smile “
Tai dariya tace “kana gani na fa, kabari se nagama “
Yana girgiza kai yace “no plsss nagaji wlh na azabtu ganinki kawai ze medani Dede “
Tace “alright duk time da kakeso ka kirani zanfada maka address “
Yace “gobe nakeso “
Tace “a, a ba gobe ba de kade samu rana “
Yayi shiru tace”ina my princess da momynta? “
Yace “suna gida “
Tace “agaidasu “
Yace “good night cutie I want to go inside “
tace “OK good night have a nice dream “
Yayi murmushi beko tambaya ba taimasa kiss takashe kiran ta sheme kan gado ta jawo pillow ta rungume,
Shima yanajin dadi sosai ya shiga gida,
Tunda ya shiga Aisha tagane yana cikin farin ciki da tazo tarar shi har daukarta yayi yana juyi daita looking very happy,
itama tanajin dadi suka shige ciki,
Daren Sun kashe arna sosai dan andade anayi kadan, itama faseelat tasha mafarkai kala kala nashi,
Tundaga nan suka kulle koda yaushe yaso yana kiranta susha vedio call dinsu da rana da daddare kuma voice call, ita faseelat kota mance cewa haryanzu da auran khalil akanta don yanzu in yace ya dawo daita shikenan, Da kuma ze mutu yanzu zsta zarce da takaba ne kuma zataci gadonshi ,soyewarsu kawai suke da fahad dinta ba ruwanta da kayan jikinta duk yadda yakira haka zata dauka, duk yabi ya rude kau, gabadaya giyar soyayya ta mantar daita addininta tunda tana da iliminta bare akirata jahila, tasan fahad bedaga cikin wadanda Allah subhanahu wataala yace a bayyanawa ado ba, cewarshi a alkurani me tsarki *=bismillahirrahmanirrahim,wa kul lil muuminati yagdudna min absarihinna wa yahfazna furujahunna wala yubdiyna zinatahunna illa ma Zahara minha wal yadribna bi kumrihinna ala juyubihinna wala yubdina ziynatahunna illa li buulatihinna au abnaihinna au abai buulatihinna au abnaihinna au abnai buulatihinna au ikwanihinna au bani ikwani hinna au bani akwatihinna au nisaihinna ,auma malakat aymanuhunna awittabiina gairi ulul irbati minal rijali awiddiflil lazina lam yazharu ala auratun nisai, wala yadribna bi arjulihinna li yuulama ma yukfina min zinatihinna wa tubu ilallahi Jamie’a ayyuhal muuminuna laallakum tuflihun.*
Bayan kwana goma ya matsa shifa he’s missing he want to meet her, akai saa ummi zataje Niger zatayi kwana ukku tace mishi yazo geben tareda yi mishi kwatancen gidansu dukansu suna murna sukai sallama, fahad har gani yayi dare ya masa nisa da safe wajen 11 yakirata akan he’s on the way,
Tana ta doki ta shiga wanka tafito ta tsara kwalliya sarkar zinari da yabata ta dauko tasanya, ta dauko veil dinta guda daya rak da akasamata a lefe ta yafa ta feffesa turare tana jiranshi don tun 9 yangidansu suka fita hidimarsu,
11 :15 yaiso yakirata ta fito tana faraa tana  ganin motarshi taje ta bude ta shige,
Tana shiga yaja numfashi “hmmmmm “yana lumshe ido,
Ta kalleshi tana murmushi tace “barka da zuwa jinin jikina “
Yace “yawwa cutie kinga yadda kikayi kyau kuwa?”ya daga kai sama “ya Allah kabarni da cutie dita kamallaka min ita harabada “
Faseelat tace “amin “ta shafa tana dariya yana karemata kallo yace “muyi pic mana”
Tace “anything for you dear “
Ta matsa har suna gogar kafada ya dauke su hoto so biyu,
Faseelat ta matsa tana kunkuni wai yafita kyau, yayi dariya yace “inkina wuri ai baa hangoni saboda haskenki “
Faseelat tace “hmmm gaskiya nida kai mundace pic dinnan yayi kyau “
Yace “Allah? “
Yana mata kallon kasakasa tace “eh, meyasa bakazo min da amira ba? “
Yace “tabb so kike tafasa kwan ko? “
Faseelat tafara dariya,
Yanata kallonta with emotion yafara zaulayarta da message na farko data mishi lokacin da ya shareta yace “a good believer always fulfill his promise “
Ta fashe da dariya ta dora kanta kan seat ta dora hannu akan bakinta tana cigaba da dariya,
Yanayin yadda take dariya nonuwanta rawa kawai suke,
Yakure ta daido yanajin kamar ya rungumota gabadaya ta rikitashi he’s losing control,
Tana ta dariya ba zato taji hannu saman breast dinta,
Tsit tai shiru ta dukar dakai tana kallon hannunshi dake kan breast dinta, ta juya ta kalleshi his eyes are closed ya lumshe su kanshi kan seat shima hannunshi nakan breast dinta ne kawai amma daga ni baya cikin duniyar,
Rai bace ta bude murfin motar tafita da gudu tana kuka tai gida,
Karar bude kofar ya dawo dashi tunaninshi ya bude yafita shima yana kwala mata kira harta shige gida, ya dafe kai ya rike kugu yace “oh my God what’s wrong with me? Yanzu seta canza min manufa, bayan duk ita tai cause din hakan ta kwaso gayu with everything open “
Yaja tsoki ya shiga mota yabar unguwar.
Comments, comments
Team faseelat on top????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
          *(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
43
*Dedicated to husnah ta riri yar fullo,inasonki sister kamar yadda kike sona Allah yakara mana son juna yabarmu tare har karshen numfashi luv u dear, ga good addua ta agareki , Allah ya kara maki dadin…..????????kita  zama tauraruwa awurin oga*
*FANS I’m sorry wani dan bayani da nayi abaya cewar faseelat tana da gadon khalil I’m sorry namanta romance ba sex bane ???? tunda be taba kusantar ta ba ko idda ma batada ita, inafatan kungane, sannan masu cewa haramunne fahad ya aureta to gaskiya  ba haramun bane Sabida shi besan tana da aure ba kuma Allah baya kama bawa da lefin da besaniba kuma koda yasani aure be haramta tsakaninsu ba, sannan akwai masu cewa halak ne namiji yakarewa macen da yakeso kallo eh hakane amma seta suturce jikinta, mazhabobi da dama sunyi magana akan haka wasu suna ganin zata iya bayyana ado gareshi toni gaskiya nafi ganewa wadanda sukace bazata bayyana ado gareshi ba, sena fuska da tafukan hannaye da kafa,, kuma yawancin malamai suntafi akan haka, ga misali namiji yazo yana sonki se yazam yasan komi na jikinki to in yazo yafasa fa? Shikenan ya kalli banza? ???? kuma hakan mabudin aikata zina ne, to nide shawara ta yanmata ko gobe ne aurenki da namiji ki kame kamkam ta hanyar zumbula katuwar hijabinki komi kenan in an daura yagani, amma ki tabbatar bawani aibu kike boyewa ba wannan kam kin yi yaudara da zalunci , kuma inyagani komi na iya faruwa, Allah yasa mudace.*
*koda yaushe in anga kuskure amin magana plsss zan kasance me daukar gyara, haka ma kuna iya bani shawara, Nagode da irin kaunar da kukewa buk dinnan.*

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Yana tuki yanajan tsoki, yarasa ina hankalinsa ya tafi harya kai hannu jikinta, ta madubi ya kalli siyayyar da yamata da suke aje a back seat yakara jan tsoki, ya fiddo waya yayi dialing number dinta tana ta ringing bata dauka ba cikin takaici yace “pick my call mana I want to apologize for my mistake”yakara dialing number din,
Faseelat nashiga gida ta fada kan bed tana kuka,cikin kuka take cewa “ya daukeni yariska ne kome? Daze tabani kamar wata matarshi, saboda inasonshi doesn’t mean zan bari ya rika tabamin jikina “
Tana kukan tace “duk laifina ne da nake sonka sosai tunda kasan haka ai zakamin komi kaga dama don kasan bazan iya rabuwa da kai ba “
Tanaji wayarta na ringing bata dauka ba se kuka kawai take aganinta bama sonta yakeba jikinta kawai yakeso,
Ganin ya mata 3 missed calls bata dauka ba yasa ya aje wayar, direct kofar gidan sabeer yawuce ya mishi waya ya fito,
Yana shiga motar fahad ya dago da kanshi daga jikin sitiyarin motar yana kallon sabeer,
sabeer yace “mutumina lpya de? “
Fahad yaja tsoki mtswwww yana shafar sumanshi da hannu daya yace “ansamu matsala wlh”
sabeer yace “wace kalar matsala kuma?”
Fahad yace “daga gun faseelat nake, cikin kuskure muna fira na taba breast dinta, shine fa tai fushi tafita tana kuka nakirata fiye da 2 taki dagawa “
Sabeer ya fashe da dariya yace “kai meyasa kai haka ko Kasa aisha ce? “
Fahad ya daga mai hannu yace “please stop joking take it seriously “
Sabeer yace “gaskiya u have made a very big mistake, kaga yanzu setayi tunanin ko ba aurenta kakeson yi ba, wai kana aikinmi ma kayi haka? “
Ya hura iskar baki yace “bana cikin hayyaci na ne, ni tunda na shaki kamshin perfume dinta ma naji ni somehow gashi taci gayu, Allah nema ya takaita don jinayi kamar nai hugging dinta “
Sabeer ya fashe da dariya yace “plsss katafi dani wataran nima in shako irin perfume dinnan inji me kaji “
Fahad ya harareshi yace “bazako kataba jinshi ba, nide kawai kabani shawara “
Sabeer yace “yanzu ka tura mata text kabata hakuri kafada mata u didn’t do that intentionally “
Fahad yace “bana tunanin zata hakura na lura taurin kai ne daita amma bari natura mata “
Sabeer yace “zata hakura mana tunda tana sonka kai de ka kula kar hakan ta sake faruwa “
Yace “OK I will try “
Sabeer yace “bari na shiga ciki se munhadu anjima “
Fahad yace “OK thanks “
Sabeer ya bude mota yafita,
Fahad ya turawa faseelat message,
Tana ta ajiyar heart ta bude message din “cutie I’m very sorry karki daukeni da wata manufa I don’t did it intentionally, I just lost control ,kiyi hakuri ki dauki wayata, ina tsananin sonki cutie I’m ready to marry you ko da gobe ne, kimin hakuri I apologize for my misbehaving amma kisani ke kika rudar dani har nayi haka ,kuma I’m regretting forgive me please “
Tana karantawa setaji dan sauki aranta unlike b4 da takejin kamar zuciyarta naci da wuta,
Tanata bin message din ya kira ta vedio call ta dauka tana kwance,
Yana kallon fuskarta duk hawaye yayi fuskar tausayi yace “cutie I’m sorry kidena kuka “
Tai shiru kawai tana kallonshi yace “kinmin hakurin? “
Seda akadau minutes ta jijjiga kai alamun eh,
Ya lumshe ido ya bude yana sauke ajiyar heart yace “thank you very much “
Ta daga kai yace “talk to me mana “
Tai shiru yace “kince kin hakura kimin magana “
Tana turo baki tace “nayi hakurin shikenan”
Yace “I’m happy, wai dama cutie dina ustaziya ce bansaniba, ai da I’m about to hug you and give you a good kiss”
Tai dariya tace “just try it u will see “
Yayi dariya yace “I’m just joking, nayi miki shopping baki bari kin amsa ba, zandawo nakawo miki “
Tace “noo Nagode banaso kabarsu “
Yace “plsss mana bangaji da ganinki ba”
Tace “aa karka dawo”
Yace “to I will tomorrow “
Tace “aa bazan fito ba “
Ranshi ya baci yace “for god sake ya kkso nayi ne? Tunda nabaki hakuri ai komi yawuce kuma bawani abu zanmiki ba wani abu kawai zanbaki”
Cikin bacin rai tana ganin yama rainata tace “nace bazan fito ba ko dole ne? E ye “
Rai bace yace “saboda kawai na tabaki kike wannan abun amma ahaka kikaje kina bari wani ya kwana samanki, bakiji komi ba sedan tabawar da namiki itace tashin hankali “
ta kure shi da ido tana mamaki kuka ne yazo mata tace “kome zaka fada kafada amma bazan fito ba, ka daukeni yar iska ne? Da kake kiran dan tabawa?kuma naje nabari wani ya kwanta akaina din bama kwanciya yayi ba cinye ni yayi “
Idanun fahad sukai jawur yace “dan kinga ana sonki kike gayawa mutane magana bayan cutata da kikayi?kada kifito din nima bana bukatar ganinki useless girl “
Diff yakashe wayar ta kara rushewa da kuka saboda kalamanshi Sun mata zafi, tai ta kuka har tagaji kanta na ciwo barci ya dauketa.
fahad huci kawai yake fiddawa yana tada mota yakecewa “what she take her self?  da zata rika medomin magana ni tsaranta ne? “
Yana tuki da hannu daya dayan kan bakinshi yana tunani yace “bazata fito ba,nitake fadawa haka it’s okay duk ni najawo danake sonki sosai harma nadamu da son ganinki, yanata surutu har ya shiga gida aisha na ganin yanayinshi taja baya fuuuu ya haye Sama ya shige dakinshi ya kulle,aisha bata bishi ba don karta kai kanta karamin aikinshi ne ya wanka mata mari inta tsaya tambayarshi meke faruwa,
Faseelat taita barci har 2 dawowar Mubarak ne ya tadata yana tambayar “yaya ina abinci na? “
Idanu kumbure tace “banyi ba ban lpya kaina ke ciwo ka bari ishak ya dawo ya dafa maku ko taliya ce “
Cikin jin tausayi yace “sannu yaya amma ni yunwa nakeji “
Tace “jeka kitchen kaduba akwai sauran tuwo se kaci”
Ya juya yafita ta tashi tayo alwala ta kabbara salla cikin salla tana kuka take rokon Allah zabi in fahad ba alheri bane agunta Allah ya cire mata sonshi,
Har dare be kira ba itama bata kirashi ba cikin dare batai barci ba kwana tai salla da addua, shima fahad sama sama yayi barci tunanin faseelat ya hanashi barcin, seda ga baya ne yake ji be kyauta ba,
Da safe yayi ta kiranta taki dagawa yaja tsoki ya aje wayar,
Har akai kwana ukku bata daukar kiranshi har ummi ta dawo,
Gabadaya fahad so yake yaji muryarta saboda tafiya zeyi yanaso ya fadamata amma taki dauka wanda seda ta nuna jarumta sosai sannan take hakan don ji take kamar ta dauka inyakira amma take sharewa dan yagane itace yayiwa laifi,
ummi taga sauyawar walwalar faseelat ta Kasa hakuri yau da safe take tambayarta “mike damunki faseelat? Naganki sukuku tunda nadawo “
Faseelat ta kakaro murmushi tace “bakomi ummi “
Ummi tace “hmmmm”ta kyaleta Amman tasan da wani abu kam,
Karfe biyu na rana jirgin su fahad ze tashi karfe 1 saura ya tura mata message “cutie I’m sorry for everything that happened, nata kiranki Amman u ignored my calls, zan tafi Italy I will  spend only 10 days there need ur prayer and remember that I love you ,take care of yourself bye “
Tana karantawa tafara hawaye tana jiran yakirata ta dauka itama she’s suffering ,amma shiru be kira ba setayi niyyar kira zuciyarta seta bata shawara karta kira tajirashi ina har 2 be kira ba koda ta yakice shawarar zuciyarta ta kirashi har Sun daga, ta aje wayar tasa kuka don takaicin wahalar da kanta da takeyi gashi har ya tafi,
Shima yana cikin jirgi yana tunaninta, saboda he’s wondering rashin kiranshi da tayi bayan karanta text nashi,
Faseelat na kwance tana duba pictures nashi da yanzu dasu take fira ummi tashigo, tana kallonta tace “ke tashi ubanwa ye akaganku dashi shekaran jiya?”
Faseelat tai wuf ta mike tana sadda kai tana mamakin yaakai ummi tasani bayan ranar ma bakowa unguwar tasu “
Ummi tace “dake nake magana “
Faseelat na inda inda tace “saurayi nane “
Ummi ta watsa mata harara tace “saboda bakida gaskiya seda nayi tafiya sannan kika gayyaceshi gidannan ko? Wato ni bama haushin fitar nakeji ba haushina mutane zasuyita ganin baki gama idda ba kike fita gun wasu tunda ba kowa yasan abinda ke faruwa ba yanzunnan daga fitata can gidan safiya take cewa wai ranar nan ta leko ta ganki zaki shiga mota, ina amfanin haka faseelat? Shi din waye shi saurayin naki? “
Tace “sunanshi fahad ga pic dinshi nan “
Ta nunawa ummi,
ummi ta amsa tagani tace “immm shi kinasonshi kenan? “
Faseelat ta daga kai ummi tace “Allah yasa alheri anshi nan”
tamika wa faseelat wayarta tafita,
Bayan su fahad Sun isa Italy be kira faseelat ba itakuma ko takira bata samu, faseelat takara shiga tashin hankali kar ya shareta don istiharar da takeyi setaji tana kara sonshima fiyeda da,
Shi ko fahad kyaleta yayi yabata lokaci amma da niyyar ranar da ya dawo zeje gidansu.
************************
Bangaren khalil lpya lau suke zaune da jamila har yasata islamiya tana zuwa kullum, yana iya kokarinshi wurin kyautata mata itama haka kuma yana hakuri da yarintar ta, maganar harka kau yanzu Sun zama yan hannu itama har magani yake siyomata yabata tasha suji dadinsu,
Kullum inbe shiga da leda ba inyadawo daga shago jamila zatai ta kumburi wani lokaci taita jaje har se yafita ya siyo mata wani abu, hjya ko tananan tana fama da haushi don duk jumaa se yakai jamila gidan, bayan antaso masallaci ya dawo su zauna su baje hira suna dariya, jamila ba ruwanta da wani taya hjya aiki intaga tanayi shi kuma be taba mata maganar ba,
Yau jamila tun tsakar dare take sheka amai gabadaya ta jigata, khalil na gefe yanata mata sannu yana zubda hawaye, saboda tausayi cikin kuka jamila tace “yaya ka temakamin cikina zafi “
Yace “kiyi hakuri kinji kibari 4 dede zamu tafi asibity kita innalillahi zaki warke”
tun karfe ukku da rabi ya mike ya daura mata zani don zindir tayi daurin zanen daban ita daban yasa mata hijab suka tafi asibity da temakon makwabciyar jamilan,
suna zuwa aka bata gado ana dubata dan tayi yaushi sosai, sukai mata tests,
Bayan tests din sunfito likita yakira khalil office yabashi albishir matar shi na dauke da ciki wata daya,
Khalil ya daga hannu sama cikin tsananin farin ciki yake fadin “alhamdulillah, alhamdulillah Nagode likita “
Likita yayi murmushi yace “Amma tana bukatar kulawa sosai saboda ta wahala yanzu zaku cigaba da zama anan hospital har taji sauki dan gudun matsala “
khalil yace “to mungode doctor Allah yasaka “
Ya tashi ya fita yana murna lokacin anata kiraye kirayen salla cikin zumudi yakira hjya, ganin kiranshi hjya dake zaune tana tasbihi ta dauka cikn faduwar gaba tace “lpya de khalil? “
Yana murna yace “ai ai muna asibity jamila ce ba lpya likita yace she’s 1 month pregnant “
to bari muga ya hjya zataji,
      Amma a next page ????
comment da yawa inkunason one more page in the night ????????
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
       *(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
44
*Dedicated to raggon miji fans group 1 inajin dadin comments naku wannan pagyn na wadannan zaratan matan ne*
*samira yahya*
*lady*????
*F ????*
*Aisha kd*
*yanshana*
*jamila adam*
*Nana bilkisu*
*balkisu ishak….*
*husnah yar niger*
*maman zainab*
*halimatussaadiyya*
*mss L*
*yayana abin alfahari na*
*zainab*
*momyn abdul*
*asiya aliyu*
*se suwa ma ?????kuna da yawa duk wacce bataji sunan ta ba ta jira a next page kuci gaba da comments ????yanuwa*
Anata kara tambayata akan idda da takaba, na tambayi wani malami ga abunda yace ????????
*_Idan Miji Ya Saki Mata Be Kusanceta ba Babu Idda a Gareta. Amma Idan Mutuwa Yayi Wajibi Ne tayi Masa Takaba  Koda Kuwa Ranar Auren Ne Ya Rasu. Sannan Zataci Gado Cikakke._*
Hjya cikin farin ciki tace “alhamdulillah naji dadin wannan labarin Allah yabata lpy anjima kadan zanzo da gari yayi haske zantaho muku da breakfast “
Yana murna yace”nagode hjya se Kinzo “
ya kashe wayar ya koma wurin jamila da akawa alurar bacci ya zauna ya kamo hannunta ya rike yanajin tsananin son ta aranshi,
Karfe 7saura hjya tazo ta shigo dakin har lokacin jamila na bacci yana sadda kai ya aje hannun jamila,
Hjya cikin murna tace “ya jikinnata dasauki ko? “
Yace “eh dasauki tana bacci ne “
Hjy tace “to Allah yaraba lpya “
Yace “amin “yana sosa kai ta harareshi tana murmushi wato ko kunya ma bayaji yake amsawa da amin hmm,
Ta samu wuri ta zauna shima yayi zaune hjya tace “katashi ka tafi school mana lokaci na wucewa “
Yana sosa kai ba dan yaso ba ya tashi ya fita,
Hjy tabishi da kallo har ya fita tace “kaganmin Marar kunya nan zakaita zama tomiye amfanin zuwa na mtsww “
Karfe 10 jamila ta farka tana ya mutsa fuska saboda jinta weak,
Hjy tace “sannu jamila “
Jamila tazo tashi hjya ta temaka mata saboda ruwan dake shiga hannunta, tana yamutsa fuska tace “kubani abinci hjy”
Hjy ta jawo danwake data dafo ta bude kular ta dora kan cinyar jamila,
Jamila naganinshi ta yamutsa fuska ta dauke kai tana dade hanci tace “hjy farfesun kai nakeso, kibugawa yaya yakawo “
hjy ta dan harareta tace “to bari akirashi”
Takira khalil tafada masa, ko minti 30 baaiba se gashi da katuwar kula taff da naman kai maybe kan rago daya ne ya siyo duka don yasan abarshi daci bare yanzu da suka zama biyu , hjy na kallon ikon Allah ya zauna yana bawa jamila  a baki tana ci yana mata sannu,
Hjy ta hadiyi miyau da niyyar a rage ta samu taci Amman tasss jamila ta cinye naman ta yabata ruwa tasha tabuga gyatsarta ta koma ta kwanta tana fidda nishi ????shi ko se sannu yake jera mata, shiyasa lokaci daya takara jibgewa ta mulla kibarta yo dadi take ci .
hjy cikin hadiyewa tace “ka kira gidansu kafadamusu? Kakira kafada musu susan abinda ake ciki “
Yace “Tom hjy “
ya dauki waya yabuga ma mahaifiyarta yafada mata jamilar bata lpya,
Wurin karfe 2 yan gidansu sukazo dubata seda laasar suka koma ,
hjy taga takaici yadda khalil yayi ta rawar kafa, kullum cikin tambayarta yake me xakici? Me kikeso ?wanda hakan ke bawa hjya haushi sosai, wani lokaci ma jamilar tai ta kuka tana cikinta shi ko yayi ta hawaye hjy taji kamar ta samishi kota,
Bayan 7 days aka sallamosu suka koma gida,
Kullum shike girki tana kwance tana baccinta yaci ya tafi gaida hjy sannan yawuce school ganin da hjy tayi yana makara tace yarika bari yanazuwa da daddre suna gaisawa,
Daganan yafara zuwa gaidata da dare, abun da yake ba hjy mamaki kullum se yazo da leda wani lokaci biyu har da ita wani lokaci guda daya su gama hira ya dauki abunsa yawuce, sosai takejin haushin shi gani takema kwara lokacin faseelat beyi rawar kai haka ba, itako wannan kullum cikin kwalkwalarsa take,
Se hjy ta fiddo da sabon salo in yazo da daren taita janshi fira har 10 wani lokaci ma har 11 ,tasamu fura ko gyada ko wani abu ya zauna suna ci suna fira,
yau ya shigo da katuwar kaxar da jamila tace a saimata akasha fira ya tashi tafiya ya dauki ledarshi,
Hjy takasa jure wannan tace “khalil shikenan de kazama bawa kulum cikin kashin kudi kake ita batasan babu ba? da zaace kullum se ka saimata nama, abunma be tsaya nanba yanzu de khalil jamila tafini agunka kafi sonta akaina,”
Cikin kwantar da murya yace haba hjya?  Yazaki hada kanki da jamila kefa ke kika haifeni kikai duk wata dawainiya ta yazaayi na hadaki da wata, wlh hjy duk ranar da kikaga banyo muku leda biyu ba rashin kudi ne, kuma naga ita ga larurarta shiyasa, ya mazaayi na kwatanta fifitata akanki bayan nasan manzon Allah (S. A. W) yace” wanda ya fifita matarshi akan mahaifiyarshi yana tare da tsinuwar Allah data malaiku da ta mutane gabadaya, bazaa karbi aikinshi na farilla kona nafila ba harse ya tuba zuwa ga Allah ya kuma rika kyautata mata kuma ya nemi yardarta”
“wlh hjy kinfi kowa aguna matsyin ku ba daya ba, amma nagane kuskurena kuma zan gyara kiyi hakuri Dan Allah “
Hjy tace ” nayi amma ka rage wannan rawar kan tsiyar ko nima haka kakemin rawar kan? “
Ya girgiza kai yace “Allah yabaki hakuri “
Tace “amin “yafita
Tace “shashasha gabadaya baya adana komi ciki ciki kawai yasa agaba ita kuma shegiyar taita bashi wahala “
Can zuwa ya shigo da rabin kaza ya ajiye mata ya mata seda safe tace “Allah yakaimu “ta jawo plate din tafara yagar kazarta tana “haka kawai ita ta haifamin kai da kullum abinda kake samu kanta zaya kare? “
Khalil na shiga gida ya iske jamila tsaye tagaji da jira, cikin rarrashi yace “kanwata amin hakuri nadawo daga gidan hjya mashin dina yayi faci”ya mata karya.
Tace”karya Kake wlh wai haka ake kasan kanada iyali Amman kaje kai zaune wurin hjy ni kabarni ni kadai, wani lokaci ma senayi barci zaka dawo nide wlh ana shiga hakkina “
Yana mata wani kalar kallo dukda beyi mamaki ba don ita bata wani tsayawa tauna magana takeyinta kuma bata barin abu cikinta setai magana, yace”nike karyar jamila? “
Tace “eh karantse faci kayi”
Yace “hmmm “
ya mika mata kazar ta yace “ga sakonki “yawuce,
Ta ansa tana maganganu Kasa Kasa ta dauko plate kitchen ta dawo falo ta bude sega rabin kaza,
Ta bata fuska ta dan iba ta meda miyau tabishi daki yana fitowa wanka kenan tasameshi tana ya mutsa fuska tace “ya naga rabin kaza? kasan de tamin kadan “
Yace “eh nasani kiyi hakuri da wannan banda kudine shiyasa “
yawuceta tabishi tana cewa “amma kasan de baa seda rabin kaza ko? Kawai kace hjy ta raba shine “
Ranshi ya baci ya juya ya zaro ido yace “eh hjy ta raba se meee “cikin tsawa
taja baya ganin yadda ya tasomata ta juya tana kunkuni, yaja tsoki ya saka rigar shi ya kwanta,
Wanshe kare da ze fita tace asiyo mata tsire yace “banda kudi “yayi hanyar fita
Tabishi har zaure tana bashi hakuri hardasu zukunnawa itade yasiyo ta samu taci, badan ita ba yace ze siyo albarkacin cikinta,
Bayan kwana ukku
yau tunda karfe 5 na asuba jirginsu ya sauka Nigeria, suna isa gida suka fara gyaren gidansu sannan aisha ta dafa masu indomei suka ci seda suka kashe arna bacci ya kwashesu,
Karfe 12 ya farka har lokacin aisha na barci a gaggauce ya diro yayi wanka shaf shaf ya shirya ya sauka kasa,
yaje ya bude jakar tsarabarsu ya fiddo wani akwati ya fice ya bude motarshi haryanzu kayanda yamata shopping sunanan ya fiddosu ya meda a motar da ze fita daita ya shiga motar yayi hanyar gidansu faseelat,
Faseelat ko jiya tata kiranshi bata shiga dan kwana goma yace ashe basu taso da wuri bane se yau,
Tagaji ta hakura Amma ta cika tai famm,
Tana daki tana charting dan yau gidansu hutun girki suke abba yasiyo fura da yoghurt da kwakwa daita zasuyi lunch dan sungaji da abincin,
Ummi na waje itako tana yankan farce yaro ya shigo gidan yace “ana kiran faseelat inji wani me mota “
Ummi tace “jeka ce gatanan zuwa “
Tamike ta leka ta window faseelat nata charting dinta hankalinta kaf yana kan wayar ummi na kallonta cikin zolaya tace “tsuntsuwar soyayya”!
Faseelat tadago tana zumburo baki ummi na dariya tace “ga tsuntsun soyayya can yazo yana jira “
faseelat tafashe da dariya tanajin dadi ta mike ba shafa komi ta jawo katuwar hijab dinta tasaka tafito tanawa ummi dariya tafita,
Ummi ta girgiza kai “ansamu wanda akeso inyazo zaafita ana dokin ganinshi “
faseelat nafita ta hangoshi tsaye bakin Ash din motarshi yana sanye da dark Blue Jeans da red shirt,
Bakaramin kyau yayi ba setaga har fari yakara sede yadan rame tundaga nesa take karemishi kallo ,shima yanata kallonta,
Tana karasowa kusa ta sadda kai,
Sheik kabir gombe yace ????su mata munafukaine tundaga nesa suke karemaka kallo da sunzo kusa su sadda kai,
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
      *(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
45
*dedicated to Dr fatee the writer of matar bahaushe????*
Tana zuwa tai tsaye ta sadda kai, yanata kallonta kamar yau yafara ganinta dariya taso kufcemishi ganin doguwar hijabin data saka abun dariyar abunda ake boyemishin de sunfito dan hijabin roba ce tsawonta yakara sa saman yayi shape,yana kara kallon tudun breast dinta yace “enter the car mana kinyi tsaye “
Ta dago tace “a, a daga nande “
Yana mata wani kallo yace “wlh zanzo in daukeki nasaki ciki da tsiya, gwarama kishiga”
Ta tunzuro baki ta bude marfin motar ta shiga, shima yabude yashiga yana kallonta yace”yanzu ni na zama abin tsoro kamar ba fahad naki ba “
Ta dago ta kalleshi tai murmushi, shima ya murmusa yana juyawa ya jingina jikin kofa dan yaji dadin karemata kallo yace “kinbani wahala cutie dan kinga inasonki da yawa ko? “
Ta harareshi, wanda hakan ya matukar birgeshi tace “munsha wahala, zakace kasan yadda nai missing dinka kuwa? Nasha kuka many times saboda shareni da kayi “
Abun ma yabashi dariya yadan shafi sajenshi ya kalleta yace “ke zakice haka? Kira nawa nai miki kikai ignoring dina dubi duk yadda nafada saboda tunaninki, kincika taurin kai tunda nabada hakuri ai shikenan amma se lokacinne ma kika kara hawa kawai dan na “se yayi shiru ya saki murmushi yana shafar kanshi da hannu ya dan kalleta yaga tanata watsa mai harara, yayi dariya yace “bada gangan nai hakan ba, nide inarokon ko hakan yafaru anan gaba amin hakuri, wlh kamshin turarenki kanshi rudani yake “
Ta balla mai harara “Allah karka kuma dan bazan daukeshi a kuskure ba tom “
Yayi dariya “kinganki ko, hmmm ki koyi hakuri dani shiyafi miki “
Ta turo baki gaba, yana dariya yana nuna setin breast dinta da hannu yace “harda jibgo hijab amma dukda haka ga yan albarkannnan sunfito gaidani “
Dasauri tadora hannu biyu saman breast dinta takare su, ya kwashe da dariya itako se kallon saman hannun take taga wai dagaske ne,
Ya sassauta dariyar yace “to yazakiyi ne tunda suna sona kome zaki sa se sunfito sede in a akwati zaki rika sakasu “
Ta zumburo baki tana so tayi kuka,
Yace “I’m sorry,im joking, nadena amman kicire hannunki plsss kibari ko daga cikin hijab din nasamu narika meda miyau na,”
Taki cirewa yace “kicire kigani wasa nake yi “
Ta zame hannun tana kallon gaban nata ashe dagaske yake sunfito tai sauri tameda hannuwan akai,
Ya dafe goshi “oh ni bakina yajamin dama nai shiru na cigaba da kwasar romo na “
Su duka suka fashe da dariya,
Yanda take dariya bakaramin burgeshi yakeba, yayi shiru yana kallonta cikinso da kauna,
Jin yayi shiru itama tai shirun ganin ita yake kallo suka kure juna da kallo dukkansu sunajin feeling like to hug thereself,
itace ta dauke ido, sannan shima ya dawo tunaninshi cikin inda inda yace “I love you cutie “
Ta kalleshi ta sakarmai murmushi tace “I love you more”
Jiyayi kamar yakai mata kisss yayi sauri ya dukar dakai kamar me nazari,
Faseelat na kallon sumar kanshi dake kwance takatse shirun da “where’s my angel?”
Ya dago yayi murmushi yana jindadin yadda takeson yarshi yace “tana gida, tana missing naki sosai, wani lokaci takanwa mommynta kuka akaita gum anty ita “
faseelat tai murmushi tace “I’m missing her too, inaga zanje ganinta very soon “
yace “baki tsoron aisha tagane muna soyayya? “
Faseelat ta girgiza kai tace “a, a banajin tsoro, bana tunanin akwai abinda zeban tsoro inde akanka ne, anty nasona nasan zata fahimceni, “
Yace “hmmmm”cikin ranshi yana cewa “bakisan true colors na aisha ba”
Ta katseshi da cewa “komiye de ni inasonta saboda ta dalilinta na sanka, and saboda kana sonta saboda inason duk abinda kakeso “
Ya cije lips yace “really? “
Tace “eh, insha Allah nida anty zamu zauna lpya bawanda zeji kanmu “
Yayi murmushi ya girgizakai yace “I wish so “amman yana ganin wuyar abun,
Sunata fira kusan 40 minutes ya zaro akwatin zoben da yasiya mata ya bude, tace “Wow” tana zaro ido da rufe baki ganin haduwar zoben na diamond me shegen kyau,
Yakara matsawa kusa daita yace “here’s our engagement ring,plsss let me put it on your hand”
Tai mai wani kallo tana murmushi ta make kafada tace “nagano wayon naka, so kake katabani hankalinka ya kwanta”
ya kalleta yayi guntun murmushi yace “don’t take me wrong Allah my intention is not to do that ,kawai I want to put it on you “
Tace “ban yarda ba “
Ya rufe akwatin ya dora akan cinyarta yace “alright have it “ya dauke kai
Ya tamke fuska tatsaya tana kallonshi feeling sad ya juyo yana kallonta yace “I want to go back home”
Tai fuskar tausayi ta dauki zoben ta dora a kan lap dinshi ta dora hannu kan dayar,
Tana mishi good look tace “feeling happy now? “
Yayi murmushi ya bude akwatin ya zaro zoben ya dago hannunta yanajin wani diffirent soft ya saka mata zoben,
Ta lumshe ido har yasaka mata tanajin nice bazato taji yayi kissing din hannun ta bude ido dasauri jin yarrrrr jikinta,
Idanunsu suka hadu yana mata love looking yace “will you marry me? “
Tanata kallonshi batare data saniba bakinta ya furta “I’m ready to marry you “
Fahad ya Saki dariya yana kallonta tai sauri ta dawo tunaninta ta rike baki not knowing me tace yake dariya,
Ya dago “inasonki me kyau da duk wani abunda kikai “
Tai dariya ta rufe fuska yace “yanzu zankoma, very soon zan aiko parents nawa yanzu mufita inbaki tsarabarki “
Tace “thank you “tana kallon hannunta
Yace “u r beautiful kome kikasa dole yamiki kyau “
Tai murmushi ya bude yafita itama tafito ya bude gidan baya ya dauko ledar ya mika mata,
Ta amsa tace “Nagode “tana murmushi
Yana mata kallon shaawa yace “I’m going “
Tace “bye take good care of yourself for me “
Ya daga kai kurum, taki tafiya yace “just go sekinshiga gida zantafi “tai murmushi ta juya tana tafiya,
Yabi kugunta da kallo da suke sababurna baburna ???????? ya lashe lips yanata kara kallonsu, harta kusa shiga gida ta juyo ya sakarmata murmushi ta daga mai hannu tana murmushi ta shiga gidan, ya girgiza kai yana kara cusa lip abaki ya shiga mota yabar unguwar,
Faseelat nashiga gida taga ummi tsaye bakin kofa da hijab a hannu tace “ummi lpya inazaki? “
Ummi ta harareta tace “wace irin fira ce kuke haka har 1 hr Allah da bakishigo ba sede kiganni awajen”
Faseelat tace “yi hakuri ummi bawani abu fa dan Allah kiyarda dani ummi “
Ummi tace “bahaka bane ba rashin yarda bace ai se anayi ana duban bakin gatari ko faseelat “
Faseelat tace “hakane umminmu zan kiyaye, kinsan ummi muje kiga zoben da yabani da kayanda ya siyomun a Italy da yaje “
Ummi tace “hmmmm marar kunya muje nagani “suka wuce ciki,
Suka zauna suka fara fiddo kayan, wasu dogayen riguna biyu da turare da agogo, se dayar ledar sweet ne kala kala tun wadanda ya taba semata,
Ummi tace “kaya sunyi kyau, zobenma yayi yanzu idan abbanku ya dawo se anuna masa “
Faseelat ta kwantar da kai kan cinyar ummi tanajin dadi tana ta kallon zoben hannunta,
Ummi ta kalleta itama she’s happy ganin faseelat din na son abun awannan karan,
Anahaka abba ya shigo ummi ta nuna mai kaya yagani,
Yace “naga kaya Amman waye wannan ya sunanshi aina yake, saboda inyi bincike kanshi donke ba budurwa bace da zaaita jan jiki gwara in dagaske yake yafito ayi aure shine “
faseelat kanta duke tace “sunanshi fahad dawood kuma a GRA gidanshi yake “
Abba yace “yanada mata kenan? “
Tace “eh “kanta kasa,
Ummi tabata fuska, “wai wannan yaron da bewuce 30 ba shine yake da mata har yana neman ta biyu? Gaskiya nikam abun ya siremin “
Abba yace “wannan ba matsala bace inde  beda matsala, kuma ke faseelat ai kina iya zama da kishiya ko? “
Faseelat tai sauri tadaga kai ummi ta watsa mata harara tace “tashi kiba mutane wuri sakarai ni nan kinganni da kishiya ne? Kike wani murna zaki auri me mata “mtsssw

Faseelat ta tashi ta shiga daki
Abba ya duko kasakasa yace “angayamaki ita irinki ce me shegen kishi “yayi cikin zolaya.
abu a duhu abba wayasani ko itanma hakan take ????
ai comments ko infasa auren fahad ehe ????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button