FAHIMTA FUSKA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

FAHIMTA FUSKA Complete Hausa Novel

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

 

 

 

 

Page 1&2

 

 

 

 

 

Fitowa tayi daga cikin ɗaki tasa riga da wando sannan ta matse cikinta da belt tasa takalmi me tudu wanda da kyar take tafiya tasa abaya akan riga da wandon ta yafa ɗan kwalin abayan ta fito a kicin ta shiga ta samu Mamanta tana faman hura wuta ta ce “Mama na tafi ”

 

Mama ta ce “Ina zaki je kuma Rahma?”

 

Ta ce “Birthday ɗin ɗan ajin mu mana ba na faɗa miki ba”

 

Mama ta ce “To da kika faɗa min kuma sai na amince ko?”

 

Ta ce “Haba Mama dan Allah ki kyale ni naje mana”

 

Ta ce “Rahma bawai ina hana ki bane baki san kallon da ake miki a unguwar nan ba, saboda yawon zuwa biki da kike yi, har cewa fa ake ciki gare ki saboda yanzu idan zaki fita ɗaura belt kike a cikin ki, kuma nima na fara zargin hakan duba da yadda fatan ki ta dawo kiga yadda kika canja Salma fatan ki sai sheƙi take ”

 

Tuni Rahma ta durƙusa ƙasa ta ce “Wallahi tallahi Mama ban ta’ba sanin ɗa namiji ba, balle nayi ciki, Mama ki min kyakykyawan zato ba haka nake ba, Allah ne shaidata, nidai nasan ina da son zuwa biki da fita birthday amma wallahi Mama bana bin maza”

 

Mama ta ce “Na yadda da ke Rahma, saboda nafi kowa sanin halinki, abin da nake so da ke kibar maganan zuwa biki da kike Idan kika yi hakan wannan zaisa mutane su fara zargin ki sannan kuma maganan ɗan ajin ku kuma ki barshi tunda yanzu fita zakiyi daga makarantar tunda kin zana jinior waec ay yanzu ma ana shirye-shiryen tafiyanki boading school ne, ki karasa babban secondary acan tunda kince kinfi son makarantar kwana , dan Allah Rahma kada ki bamu kunya kinga ku biyu ne kawai muka haifa a duniya keda yayanki shima fatan mu Allah ya bashi nasara akan aikin da yake nema ”

 

Ta ce “Amin”

 

Komawa tayi ɗaki tana zubda hawaye ta fara cire kayan tana duba jikin ta, tabbas ta canja kuma ba komai bane illa shafe-shafen kurkur da lalle da ta fara yi saboda Allah yayi ta baƙa, baza tayi bleaching ba amma tana son ta gyara fatar ta to gashi fatar tata tayi sheƙi kalanta ya fito da kyau,

 

Mama ce ta shigo ta ce “Kije amma ki dawo kafin magrib”

 

Ta ce “A’a Mama bazan je ba, kuma daga yau biki idan ba na dangina bane na barshi”

 

Asalinsu…

 

Garin Kaduna gari ne wanda ya haɗa yarika da dama wanda duk cikin yarikan Nigeria ɗaiɗaiku ne babu haka kuma suke auran junan su, mafi yawanci zuwa suka yi ɗaiɗaiku ne wada zaka ji suna cewa su ƴan garin Kaduna ne. Malam Auwalu kuwa Maraya ne a gidan Marayu ya girma a cikin gidan ya haɗu da matarsa Lariya ya aureta, shekaran su ɗaya da aure ta haifi ɗa Namiji aka sakabmasa suna Lukman. Saida Lukman ya shekara shida kafin Lariya sake samun wani cikin ta haifi ƴarta mace sunan ta Rahma, Lukman fari tas kyakykyawa, sa’banin Rahma da take baƙa sannan ita ɗin ma ba baya ba wajen kyau.

 

Rahma akwaita da rawan ga galli shiko Lukman yakan tsokaneta ya ce Ƴar baƙa, haka zata yi ta kuka har sai Mama tayi magana.

 

Baban Su Auwalu kuwa sana’an gwanjo yake yi dan haka baza ka kira su masu arxiki ba sai dai ace suna da rufin asiri.

 

Rahma ta tashi idan dai ta ji kiɗa ko ana biki a wani gurin haka zata tafi, duk wani biki idan dai a unguwar ne sai ka ganta a gurin, ta taso da son sa ƙananan kaya, duk gwamjon da Baba ya ɗauko sai ta fara za’bewa kafin yakai kasuwa koda ta gama primary rawan kai ya ƙaru, ita da kanta take shiryawa ta ce “ta tafi biki” ƴan unguwa suka fara kawo wa Auwalu tsegumin wai idan baiyi da gaske ba ƴarsa zata lalace, ya ce “Shidai yana bin ƴaƴansa da Addu’a kuma Allah zai kare ta, wannan abin ma da yaga ay yarinta ne.

 

Haka aka gyale shi sai kuma aka fara gulmace-gulmacensu. Koda ta fara secondary tayi ƙawaye to duk bikin da za’ayi a gidan ƙawa ko aboki ɗan ajin su sai taji, musamman ma kuma ace an gayyace ta, tana JS 3 suna shirin zana jinior waec ne take jin labarin wai idan kana shafa Kur-Kur da lalle hasken fatan ta zai yi kyau, kasancewan ta baƙa kuma tana son tayi kyau yasa ta tambaya ko zai sata bleaching aka tabbatar mata bazai sata wani bleaching ba, saidai zata yi kyau da sheƙi. Haka kuwa da take yi tayi kyau baƙar fatan ta ta sake fitowa da kyau, a lokacin kuma take da shekara sha uku lokacin kuma duk alamomin budurcin ta suka ƙara ha’baka hip ɗinta yayi babba ƙirjinta ma ya ciko, ga hasken da tayi ta ƙara kyau, lokacin kuma ta tsiro da wani kwalliya na ɗaura belt a ciki, idan ta ɗaura ta fita abin ta, ganin magulmata sunyi yawa yasa bata gaida kowa a unguwar wannan yasa suka fara raɗeraɗin cewa hala ciki gare ta, ay dama wannan yawon bin maza da take dole tayi ciki, abu har yaje kunnen Auwalu ay kuwa ya nuna musu ‘bacin ransa. Koda ta jana jinor waec ya cire ta a makarantar ya ce “Zai kaita ta kwana saboda saboda ya huta da tsegumin mutane itama zata fi nutsuwa dan ya lura itama tana da rawan kai.

 

Ci gaba…

 

Tun lokacin bata ƙara fita ba haka tana jin ana biki amma bata zuwa ita komai ma ya fita mata a rai so take ma ta tafi makarantar ta ko ta huta a can.

 

Ganin ta a takure kamar bata da lafiya yasa Mama ta fara yarda da Maganganun mutane gashi sai ƙara yin sheƙi da haske take kuma hips ɗinta sai ƙara ciƙo wa take, kuma wannan ya faru ne saka maka kurkur da take shafawa sannan tayi wanka da lalle. Kiba kuwa saboda a lokacin ne alamimin budurcin suke fitowa gaba ɗaya, a hakan aka mata aka shirya mata komai aka kaita Makarantar kwana da ke cikin garin kano, Baba da Lukman ne suka rakata saida tabbatar sun gama mata komai sannan Baba ya bata babbab waya da labtop ya ce ”

Na siya miki waɗannan ne saboda karatun ki ko kuma idan an baki assingment kiyi anan”

 

Lukman yayi Dariya ya ce “Kai Baba sai kace jami’a me a karatun secondary”

 

Baba ya ce “Kai zaka ce haka tunda ka riga ka wuce ita yanzu zata fara”

 

Idon ta ne ya ciƙo da kwalla ta ce “Na gode Baba, Kuma ku ya yafe min ka faɗa wa Mama ma dan Allah ta ya fe min”

 

Lukman ya ce “Me haka,  dalla shiga ciki, kije ki samo mana likita, ohhh na manta ashe ma lowyer ce”

 

Juyawa tayi tana kuka zata shige cikin sauri ya kamota, sai da suka tabbatar sun lallasheta harda sata dariya sannan ta shiga ciki.

 

Har ta ɗan yi nisa sai ta juyo da sauri ta ce “Lah Yaya na manta da Lallena da Kurku dan Allah kace Mama ta ajiye min kada ya ‘bace idan zaka zo sai kazo min da shi”.

 

 

 

 

 

lιĸe

coммenт

ѕнare

????ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍????

[18/07 8:51 PM] MIM✍????: ???? _*????ιĸιмaн ????rιтer’ѕ ????ѕѕocιaтιon*_

????( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)

Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

 

 

 

loadιng………..✍????

 

 

 

???? _*FAHIMTA FUSKA*_

 

 

 

Written by

UMMU MUFEED

(Mrs Aliyu)

 

 

 

Marubuciyar:-

BILKISU

INA DANGINA

IZZAR MULKI

JININA

AMANATA

MAIMUNATU

YAƘI A SOYAYYA

And now

FATIMTA FUSKA

 

 

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

 

 

 

 

Page 3&4

 

 

 

 

 

 

Murmushi yayi ya ɗago mata hannu alamun bamsuwa, saida taga fitansu a get sannam ta juya tana share kallan dake zubo mata.

 

Ss 1 ta shiga, tunda ta shiga makarantar ba ruwanta da kowa karatunta kawai tasa a gaba, bata da ƙawa, ƙawarta kenan biro da takarda, yawancin ɗalibai suna mata ganin mai girman kai dan bata fiya magana ba sai akan karatu, hakan kuwa da take ba ƙaramin birge ɗalibai yake ba domin suna son yara irin haka. Rayuwan makaranta yasa ta rame wannan hasken da ta fara babu shi don yanzu ba shafe-shafen take ba karatunta tasa a gaba, takura kanta da tayi ne yasa ta ƙara min bakin akan asalin baƙin ta. Koda ranan Visting yazo ba wanda yazo mata, haka wani watan ma ba wanda yazo, da wani watan yazo kuwa wanda shine ƙarshe sai kuma hutu Ya Lukman yazo saidai kuma kuma yazo a ƙurarren lokaci bai samu ganin ta ba, ita kuma dama ta ce baza ta fito ba dan tasan ba wanda zaizo mata, dalilin hakan yasa ta zauna a hostel.

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button