FAHIMTA FUSKA Complete Hausa Novel
Randa akayi hutu kuwa ta haɗa kayanta bayan an bada hutu ta ɗauka ta fito get sannan taje banki ta ciro kuɗi dan Yaya Lukman ya turo mata kuɗin motan komawa garin su Kaduna, tana cire kuɗin tayi tasha tahau mota saida ta jira motar ta cika sannan suka tashi.
Saidai kuma sha’anin ƙarfe saida suka shiga daji motar ta lalace a hanya, haka suka tsaya dan a gyara ta, amma bata gyaru ba, ƙarshe dai aka kira bakanike sannan me motar ya fara neman motar da zaisa fasinjojinsa, a hakan yake share motoci duk a cike wanda ba a cikin bane kuma sai a samu asa mutun ɗaya.
Mata masu yara ake sawa kasancewan Magrib ta kusa.
A hakan dai har isha ta cin musu a gurin da kyar aka sama wa Rahma mota ita ma ta shiga, duk hankalinta a tashe Allah-Allah take ta ganta a gida ga kuma garin ya haɗu da hadari hakan yasa garin yayi duhu sosai.
Suna cikin tafiya barci ya kwashe ta kar a mafarki sai ji tayi ana cewa “Innalillahi wa Inna’ilaihir raju’un”
Buɗe ido tayi taga hanken fitila me haske akan titi ji tayi suna cewa “Ku fito duka”
Rahma ta ɗauki kayan ta dama wayarta ta mutu ba chaji yasa ta tura ta cikin jakan kayan ta labtop ɗin ma tana ciki dan haka ta ɗauki jakan suka fito, suka basu umurnin su kwanta, itama ta kwanta tana yin hawaye, cikin ranta kuwa Addu’a take Allah ya ku’butar dasu daga hannun waɗannan azzaluman.
Shiga motar suka yi sukayi ta binciken su can kuma suka fito, suna kallon su ɗaya bayan ɗaya idon ogan yakai kan Rahma ya dalle mata ido da fitila ganin jikin ta da Uniform ya ce “Ke ƴar makaranta me kike har dare yayi baki shiga mota kin koma garin ku ba?”
Kasa magana tayi sai kuka da ta fashe da shi. Isowa gareta yayi da bindiga a hannunsa ya riƙo maya hijabi ya ɗagota ya ce “na miki wani abu ne”
Tuni ta haɗiyi wani miyau me kauri cikin rawan murya ta ce “Kayi haƙuri dan Allah”
Ya ce “Dawo ta nan”
Ta kinkimi jamar kayanta ta koma gefen sa tana kuka, ya ce “Kina son na?”
Shiru tayi ta kasa magana ɗaya daga cikin yaransa suka ce “kyale Aunty kawai oga nasan cewa tana no”
Ya ce “Yo Idan ma taƙi basai in farfarke cikin ta ba”
Ya kalleta yadda take kuka ya ce “Ƴar Baƙa faɗa min mana ko bakya sona”
Da sauri ta ce “Ina son ka”
Dariya suka kece dashi ya kalli sauran ya ce “Albarkacin Masoyiya ta na kyale ku ku tafi”
Suka tashi suka shiga mota wani tsoho ya kasa shiga ya matso gaban ogan ya durƙusa ya ce “Dan Allah yallabai ka kyale yarinyar nan, kaga ƴar makaranta ce, kuma yanzu haka zata tafi gun iyayen ta ne in yaso daga baya kaje gun iyayen ta”
Bai ce komai ba yasa bingiga a kirjin sa ya harbeshi tuni ya faɗi ya mutu.
Kuka tasa kai ƙara, wata mata bayan ta shiga motar tana kallon ta tana yin kuka koda Oga ya kalle ta ya ce “Ku fito min da matar nan ta faɗa min kukan me take yi ?”
Da Sauri Rahma ta miƙe ta tare motar tana cewa “Dan Allah ka kyale su su tafi ”
Ya ce “Driver ja akwalar motar ka”
Driver kuwa yaja motar suka tafi.
Durƙushewa tayi a gurin tana kuka, oga ne ya ɗauke mata kayan ta ya ce “Muje gida ko”
Ta tashi suka tafi, suna tafiya tana kuka, ya ce ” Nikan ma yadda za’a fara ruwan nan Fashi zaifi daɗi ku tsaya ku sama mana masarufi ni kan zan je naji amarci”
Duka suka haɗa baki suka ce ” To Oga”
Su suka tsaya yayin da su kuma suka tafi, ɗakin bukka suka shiga ta zauna ya ce “Kina jin yunwa?”
Ta ce “A’a
Ya ce “Ok ni to barin fara ɗanɗanaki daga yanzu ko Matata”
Wani Wari ne ya dosheta daya buɗe baki yana magana domin ɗakin matsatstsene shi kuma yayi kurkusa da ita.
Ganin ya fara cire kayanta yasa ta fasa kuka.
lιĸe
coммenт
ѕнare
????ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍????
[18/07 8:51 PM] MIM✍????: ???? _*????ιĸιмaн ????rιтer’ѕ ????ѕѕocιaтιon*_
????( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍????
???? _*FAHIMTA FUSKA*_
Written by
UMMU MUFEED
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
BILKISU
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
AMANATA
MAIMUNATU
YAƘI A SOYAYYA
And now
FATIMTA FUSKA
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 5&6
Torch light ɗin hannun sa ya faɗi haka ya haska Sama ta hango ƴar ƙaramar wuƙa a damtsen sa, yana ƙoƙarin cire wandon tayi tsalle ta zare wannan wuƙar batayi wata-wata ba ta luma masa a cikin sa tabar wuƙar a jiki faɗuwa ya kama gurin tuni ya fara malala a gurin ta tsallaka shi zata wuce ya ja ƙafarta ta faɗi a kan cikin sa wuƙar ta kuma shige ciki ya kuma tsala ihu ita kuwa tayi azama ta fito daga ciki kwashi kayanta ta fita tayi cikin daji da gudunta saida tayi nisa sannan ta tsaya tana haki saida ta ɗan huta sannan taci gaba da tafiya, hanyan da zatayi titi ma ta ‘bace mata ita dai tafiya take gaba daji baya daji, buɗe jakan ta tafi ta ɗauko wayarta ta kunna sai taga 5% ne haka ta ringa haskawa daga bisani kuma ruwa me ƙarfi da ƙankara ya zuge ta juya ba inda zata ra’be dan haka tasa wayar cikin aljihunta taci gaba da tafiya, jin kukan jarirai ta riga yi wanda ba guda ɗaya ba, tsoro ya kamata cikin ranta ta ce “Shikenan na haɗu da Aljanu”
Ta ɗaga kai ta ce “Ya Allah kai ka ce kana amsar Addu’a lokacin da ake ruwan sama ya Allah ka fidda ni daga cikin wannan daji, Allah ka ka kare ni daga mungwayen Aljanu”
Ji tayi ba sauran tsoro kuma a ranta kuma tana ci gaba da jin kukan, ba tare da tsoro ba tayi inda taji kukan tana zuwa gurin akayi walƙiya haɗe da tsawa ya haska mata wata mata da jarirai a kan kirjin ta ta rungume. Addu’a ta fara yi sannan ta ce “Mutum ce ke ko Aljana?”
Sai taji shiru ɗauko wayar ta tayi ta haska taga da sauran chaji saidai da yake ruwa ya ta’ba wayar screen ɗin yana rawa, ta haska matar cikin ranta ta ce “Ƴar Adam a wannan dajin kuma”
Sa kunne tayi a ƙirjin ta taji zuciyar bata bugawa ta saka a wuyanta nan ma shiru ta kalli yaran su uku taga yadda suke tsala kuka gasu ƙanana ne sosai kuma ba kaya a jikin su daga su sai pampas ta ɗauke su ta rugume cikin hijabin ta ta kama jijjiga matar tana cewa baiwar Allah ki tashi ki basu Nono, ɗaga kai tayi ta hango hanken torch light sai ji tayi nuna cewa “Bata Mutu ba, ga can hasken waya ina kalli”
Sai kuma taji wani daga cikin su ya ce “Ku kasheta sannan ku kashe ƴaƴan, na faɗa mata Bana son ganin gudan jinin AL’AMIN a duniya, amma tabar taurin kai shine zata haifa masa har uku”
Duba wayan tayi tana ƙoƙarin kashewa sai kuma ta mutu gaba ɗaya, tashi tayi da yaran ta sake nausawa cikin daji dasu, ‘boyewa tayi a cikin wani shinge tana kallo suka zo gurin taji suna cewa “Ta mutu, Amma Ina yaran suke”
Taji wani ya ce “Dalla kyale su kasan Bakwaini ne, basa son sanyi musamman ma yadda ake ruwan nan mutuwa zasuyi”
Ya ce cikin ɗaga Murya “Al’amin bana son ganin ka haihu, yau ga Masoyiyar ka nan ta mutu, yaran ka sun mutu sai inga yadda za’ayi ka sake haihuwa”
Ɗaya ya ce “Ni duk randa na ga yayi aure sai na masa dandaƙar ɗan taure na fasa ƙoyayen haihuwar”
Dariya suka fashe dashi sannan suka bar gurin, ta kalli yaran cikin duhu duk da ba kallonsu take ba sabo da duhu dan ma yanzu an ɗauke ruwan.
Ganin sun tafi yasa ta isa gurin tana zuwa ta kuma jijjigata sai kuma ta tuna ta mutu, ta kwantar da yaran a jikin gawar sai itama ta kwanta lokacin duk sunyi barci, Can kuma ta tuna ay zasu iya dawowa da sauri ta tashi ta buɗe jakan kayanta ta ɗauko bargonta ta sanya su a ciki ta ɗauke sy ta tafi dasu sai da tayi nisa da gurin sannan ta shimfiɗe su, Tunawa tayi batayi Sallah ba yasa tayi taimama ta rama sallolin da ake bin ta wato Magrib da isha”