FAHIMTA FUSKA Complete Hausa Novel
***
Mama kuwa tasan yau ƴarta zata dawo har da yi mata girki
Ya Lukman kuwa Kaji ya siyo aka soye mata, duk suna farin cikin zata dawo, Saidai tunda La’asar tayi Mama ta fara sarewa dan tasan tsakan Kano da Kaduna yayi ace ta iso amma shiru har yanzu.
Dan ta kirasu ta ce tana hanya, ga wayanta a kashe. Koda Magrib tayi kowa ya shiga damuwa Musamman Ya Lukman.
Da dare kuwa sunyi cirko cirko dukan su a tsaye, karshe dai ba wanda yayi barci a cikin su.
***
Batayi barci ba har asuba tayi taimama tayi Sallah, Saida gari yayi hanke ta miƙe ta ɗauki yaran dan yunwa suke ji tun daren sukayi ta kuka, data je tasa musu Nonon gawar Uwarsu a baki koda zasu samu ruwa, duk da tasan ba abin da za’a samu a jikin mamaci.
Tana zuwa gurin taga wayam, dube dube ta fara yi ko ba gurin bane amma kuma sai taga wayar ta a gurin da jakarta, tabbas gurin ne amma gashi ba gawar matar. Wata zuciyar ta ce “Kodai sun dawo sun ɗauketa ne ”
Durƙusawa tayi tare da sa wani kuka me ban tausayi ta kalli yaran da suke yin kuka, ta cire musu Pampas taga duka Mata ne, tausayin su ne ya kamata, kawai ta gyara zama ta ɗaga rigarta ta bawa wacce tafi yin kukan Nonon ta ay kuwa ta fara ja duk da Bakwaini ne, Zabura tayi dan wani irin zafi taji, ta cire bra ɗin dake jikin ta ta ɗauko ɗaya ma ta ɗosana mata Nonon Itama ta fara ja, Duk zafin da take ji ba hanabta cire musu ba, A haka sukayi barci ta sasu a kan bargon ta ɗauki ɗayar ma ta fara bata, itama tayi barci duk da ba Wai sun sha wani Abu bane Illa tsotsan fatar ta da sukayi tayi.
Canja taya tare da Tattara sauran kayanta tayi, buɗe jakarta tayi ta ciro zaninta tayi ƙokari tasa biyu a bayan ta ta goye su kamar yadda taga ana goyon ƴan biyu sannan haɗa kyar ta tukuikuye ɗaya a cikin bargo ta riƙeta da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta ɗauki jakarta, tana miƙewa ta fara hango motoci Alamun titi ne a gurin da sauri tayi Titi tana zuwa ta tare mota dama tana da ƴan Sauran kuɗinta, duk cikin motar kallonta ake aganin jarirai ƙanana a hannun ta saidai ba wanda yayi magana.
Suna Isa kaduna Ta hau Napep tayi gida, ana sauƙeta ta shiga gida taga Mama, Baba da Ya Lukman. Ganin ta da Jarirai yasa suka waro ido cikin Mamaki…
lιĸe
coммenт
ѕнare
????ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍????
[18/07 8:51 PM] MIM✍????: ???? _*????ιĸιмaн ????rιтer’ѕ ????ѕѕocιaтιon*_
????( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍????
???? _*FAHIMTA FUSKA*_
Written by
UMMU MUFEED
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
BILKISU
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
AMANATA
MAIMUNATU
YAƘI A SOYAYYA
And now
FATIMTA FUSKA
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 7&8
Mama ta ce “Me nake gani ne haka ni lariya, dama abin da mutane suke faɗa akan ki gaskiya ne, waɗannan yaran su suka hanaki dawowa tun jiya, dama haihuwa kika tsaya yi”
Baba ya ce “Rahma waye uban yaran nan”
Ta ce “Ban sani ba Baba nima…”
Ji tayi Mama ta bata mari har saida yariyar hannunta zata faɗi ta saki jakan hannunta ta tallafeta tare da rungumeta tana kuka ita ko Yarinyar ta saki ƙara ta calla kuka.
Cikin kuka Rahma ta ce “Mama Yaran nan yunwa suke ji ki taimaka ko ruwan ɗumi ne ki basu ”
Wani Marin ta kuma ji tana ɗaga kai taga Baba ne, kuka tasa yayin da yaran duka sukayi ta calla kuka Ya Lukman ya ce “Rahma waye Uban su, ki faɗa min mun ɗauki ƙaddara kuma muna farin cikin zuwan su duk da cewa ba ta hanya me kyau aka same su, amma zamu rungume su”
Zatayi Magana sai gani tayi An watso mata kaya Ya Lukman ya miƙe ya ce “Mama me haka kuma”
Ta ce “Baza ta zauna min da shegu ba, dan haka ta koma gun Uban su”
Ya Lukman Ya ce “Yanzu Ina zata je ga yara suna kukan yunwa ”
Baba ya ce “Rahma kin cuce ni kin cuci kanki kije na sallama ki a duniya”
Ya Lukman ya ce “Baba harda kai”
Rahma ta ce “Bani na ha…”
Mari Mama ta kuma mata a baki tare da ɗauko muciya zata buga mata Ya Lukman ya Amshe yarinyar hannunta da take ta tsala kuka yana kuka ya ce “Indai Rahma zata bar gidan nan nima bazan zauna ba, Me yasa baza ku bita a hankali ba, ga yara suna jin yunwa, ko ruwa kun kasa basu, ita kanta nasan tunda ta haihu bata ci komai ba, ya kamata abi komai a sannu amma kunƙi kun yanke mata hukunci cikin fushi ”
Amsan Yarinyar Mama tayi ta tunanin ta ta huce ne, sai gani yayi ta miƙa wa Rahma, shi kuma Baba ya hankaɗa shi ɗaki ya kulle tare da sa kwaɗo.
Mama ta kalli Rahma ta ce “Ki tattara kayan ki ki bar min gidan nan Idan ba so kike na rotsawa yaran nan kai ba”
Ta ce “Wallahi Mama bani na haife su ba, idan ƙarya ne muje ki duba ni”
Ba ke kika haife su ba uban wa zai baki yara har uku ko zaki ce tsintansu kika yi, daga ganin su yara ma Basu cika tara ba, bakwaini ne waɗannan yara, to ma waye zai zubda yara Uku kuma Bakwaini dama can kin tafi da ciki makaranta gashi kin haife su sai ki koma gun uban su”
Zatayi Magana Mama ta ɗaga Muciyar “Idan baki tafi ba zan rotsa muku kai dada ke har su”
Tashi tayi tana kuka ta ɗauki jakan da tazo dashi ta rataya a wuyanta sannan ta gyara biyun da suke bayanta ta tallafi ɗaya kirjinta ta riƙe da hannun hagu sannan ta ɗauki jakan kayan ta, taji ya mata nawi kawai sai ta ajiye ta ta fita daga gidan tana kuka. Tana fitowa anguwa kuwa aka ringa kallonta yayin da wasu suke mata dariya, koda tazo wata majalisa sai ji tayi wani ya ce “Ƴar gidan Auwalu Me gwanjo ne cikin shege tayi gashi har yara uku hala koranta yayi”
Wani kuwa ya ce “Ba ana faɗa masa irin shigar da take ba yana ƙin yadda ba yaƙi tsawatar mata”
Wani ko ya ce “To ay shi yake bata kayan idan yayi Dilan gwanzo”
“To ba gashi ta ja masa abin tsiya ba”
Suka kwashe da dariya harda tafawa
Da saurin ta ta wuce gurin kasuwa tayi ta siyar da Labtop ɗinta 35k, wanda zata kai 50k da wayar ta, wayar ne ma ta siyar da ita araha banza saboda ruwa ya ta’bata, su kuma zasu shanya idan ta bushe sai su siyar ma wani.
Shagon kayan jarirai tayi kayan sanyi ta siya musu sai kuma ƴan ƙanana masu Arha sannan ta siya Madaran yara Nan da abubuwan da zasu buƙata haka ta fito kasuwa ta shiga Napep kawo tayi tana zuwa taga ya kamata ta sa musu kaya, wani gida ta shiga cikin ta yi Sallama bayan sun gaisa da matar ta ce “Dan Allah zan ɗan bawa yara Abinci ne, na sa musu kaya”
Ta ce “To shigo mana ki basu”
Ta shiga har ɗakin matar ta roƙi ɗan ruwan zafi aka haɗa musu madaran ta fara basu sai da ta basu duka suka sha, saidai atishawa suke tayi Matar me Suna Salma ta ce “Yaran kin nan suna Mura gashi ba kaya a jikin su ko za’a musu wanka ne”
Ta ce “eh”
Salma ce ta musu wanka duka aka buɗe su da powder sannan aka sa musu kayan sanyi tuni suka fara barci, Sannan Matar ta ce “To ko kema zakiyi wankan kafin su tashi”
Ta ce “To”
Ruwa me zafi ta sirka mata sannan ta kai mata soso da Sabulu bayi tayi wanka ta fito tasa kayanta riga da zani tana kallon su, Sai yanzu ta ƙare musu kallo ta gane Guda biyu suna ka da juna saidai ɗayar kamanninta daban. Barci suke amma kuma suna fitar da wani irin numfashi ga atishawa da suke akai akai.
Salma ce ta shigo ta ce “Keko baiwar Allah Ina zaki nufa da jariran nan haka gashi ko cibi bata faɗi ba ?”
Ta yi shiru tana tunanin abin cewa can ta tuno wata ƙaryan ta fashe da kuka ta ce “Yaya ta ce ta haife su sai ta rasu, shine Mijinta ya ce mu tafi garin mu da su shi bazai iya ciyar da su ba”