FAHIMTA FUSKA Complete Hausa Novel

Ta ce “Yanzu Ina ne garin ku”
Ta ce “Kano”
Ta ce “To Amma kafin ki hau mota ki fara kai su asibiti dan yaran basu da lafiya, dan kinga yadda suke numfashi ba a daidai ba”
Ta ce “To”
Tashi tayi Salma ta saka mata biyu a baya ta goyesu ɗaya kuma a hannu sannan tasa jakarta a wuya jakan Babies ɗin kuma a ɗayan hannun, Asibitin Barau dikko tayi tana zuwa aka nuna mata shashin yara, tana zuwa da akaga jarirai ne sai akayi da ita Matanity anan kuma aka kaita gunda ake kula da jarirai,
Tana zuwa gun likitan da sauri ya amshi na hannunta yayi sauri ya cire mata kaya ya bar mata Pampas ya sata a cikin Kwalban da ake sa jarirai sannan ya sa mata naƙuran ƙarin numfashi.
Ta sauƙe sauran ya amshe su cire musu kaya ya bar musu Pampas suma ya musu yadda yayi wa ɗayar saidai kuma bai sa musu naƙuran numfashi ba ya rufe du duka sannan ya dawo ya zauna ya ce “Madam kinyi kusa ki kashe yaranki, yakamata a ce suna fitowa duniya a sasu a nan, dan haka yanzu ma Addu’a zaki musu dan suna gab da su mutu”
Durƙusawa tayi ta Fara hawaye tana ce wa “Dan Allah Doctor ka taimaka mana”
Ya ce ” Ki kwantar da hankalinki ki roƙi Allah ya ɗaga miki yaran ki”
Ta dawo ta zauna ta ce “To Dan Allah akwai maganin da zaka bani don in samu ruwan Nono?”
Ya ce “Ruwan Nono be zo bane”
Ta ce “Yaran Yayata ce kuma ta rasu shine nake son in shayar da su ”
Ya ce “to kin ta’ba aure ne”
Ta ce “A’a”.
Ya ce “Akwai Maganin da zan baki saida da kyar ruwan Nono yazo saboda kina budurwa, kuma me ƙarancin shekaru nasan baki wuce 14 ba, amma idan munyi Sa’a zai iya zuwa, saidai kuma idan sun ɗan sake girma sai a haɗa musu da Madara, amma yanzu barin baki yankan musu kati sannan in rubuta miki magungunan da zaki siyo musu, ya Sunan su da Sunan Mahaifin su?
Shiru ta tana tunanin me zata ce, tasan dai sunan Mahaifinsu Al’amin dan taji a bakin Maƙiyansu, Su ɗin ne dai bata san sunan su ba, hala ma ba’a sa musu sunan ba.
Sake cewa yayi “Madam Ina Sauraron ki”.
lιĸe
coммenт
ѕнare
????ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍????
[18/07 8:51 PM] MIM✍????: ???? _*????ιĸιмaн ????rιтer’ѕ ????ѕѕocιaтιon*_
????( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍????
???? _*FAHIMTA FUSKA*_
Written by
UMMU MUFEED
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
BILKISU
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
AMANATA
MAIMUNATU
YAƘI A SOYAYYA
And now
FATIMTA FUSKA
_Ina kuke Masoyan Hikima, kuma Masoyan Maimuna Isah Musa (Mrs Aliyu) masu son ci gaban ta, gata ta yunƙuro ta farfaɗo muku da wani Sabon shahararren littafinta me suna *Fahimta fuska*_
_Tab ay ko daga jin sunan ma kasan labarin zaiyi Sugar, sannan tazo muku da salon rubutu salon labari wanda baku saba gani, domin labarin yasha bam-bam da sauran labarai, ga duk me buƙata zaibi wannan tsarin????????????????????????????????_
*FAHIMTA FUSKA Na kuɗine Naira 300 kacal????????Zaka/ki biya ta wannan account*
*0019138715*
*Maimuna Isah*
*StanbicIBTC*
*Sai ka/ki tura min shaidan biya ta wannan number 09034313679*
*Ko katin MTN na 300 ta wannan number*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 9&10
Shirun ta ƙara yi tana tunani kamar baza tayi magana ba can kuma sai ta ce “Babbar Sunanta ISLAM AL’AMIN”
Ya sake tambaya Sunan Mahaifiyarsu fa, ta ce “Rahma”
Ya tambaya ya ce “Ta biyun fa”
Ta ce “IMAN AL’AMIN”
Ya mata tambayoyi ta bashi amsa
Sannan ya ce “Ƙaramar fa?”
Ta ce “IHSAN AL’AMIN”
Nan ma ya rubuta tare da yib tambayoyi bayan ya gama fitar musu da kati ya kalleta ya ce “Islam kenan na fara amsa dan naga ita ce Babba”
Ta ce “Eh”
Suka je tare suna ganin su yaga Temprature ɗin ƙaramar wato Ihsan yayi High da sauri ya buɗe kwalban sannan yaɗan rage zafin kwalbar ya kalleta ya ce “Me kika basu ne haka”
Ta ce “Madaran jariraine”
Ya ce “Kash waɗannan fa ba jariran da kika saba gani ana haifa bane, waɗannan lokacin haihuwansu baiyi ba aka haife su, dan haka ba komai za’a na musu ba, Ba wanka, ba bada ruwa sai ruwan Nono Zalla Idan bamu samu bane ba yadda muka iya dole mu basu madara, ba kowa zai na ɗauka ba, zaki barsu anan zansa Metro ta kaiki wani ɗaki duk bayan awa daya zaki na zuwa duba su kina basu Abincin su”
Ta ce “To”
Ya rubuta mata magani ya ce “Ga waɗannan kije ki siyo yanzu ki kawo”
Ta fita da sauri taje Pharmacy ta haɗo magungunan ta dawo, Drip ya saka musu ya samu, ko wannen su a bayan hannunsu na hagu aka samu jijiya, sannan kuma ya buɗe magungunan ya ciro wani ya ce bata tablet ƙwaya uku ya ce “Kisha wannan zuwa yamma mu gani ko ruwan Nonon zai zo nan da yamma”
Ta amsa ta shanye sannan ya ce ta zauna ya gwada mata yadda zata na goge musu cibi da sprit da Auduga Iman ta fara ɗauka tana gogewa sannan ta ɗauki Ihsan, lokacin da ta gama wa Ihsan kuwa Ya cirewa Islam Naƙuran ƙarin Numfashi har numfashin ta yayi daidai sannan tayi barci, itama ta ɗauketa a hankali tana goge mata tana gamawa aka fara kiran Sallah Azahar, ya kira Metro ta nuna mata ɗakin da zata zauna sannan, Mata ce a ciki su biyar sai gadaje uku Metro ɗin tayi Sallama ta ce “Maman A.J ga Abokiyar kwana na kawo miki”
Wacce aka kira Maman A.J ta ce “A sannu da zuwa su Maman Najeeb nima nayi wata, ba Maman Salma ta tafi kuna min iya shege ba to ga wata tazo, wannan kan ma ƙanwata ce”
Tayi gun Maman A.J ɗin ta zauna a bakin gadon da suke ta gaida su suka amsa, Suna haka Maman Sayyid ta shigo ta ce “Kece me ƴan uku ko”?
Maman Najeeb ta waro Ido ta ce “Ƴan uku ta haifa”
Maman Sayyid ta ce “Sa wasa”
Maman Najib ta jinjina mata ita ko sai murmushi take.
Sallah duk kan su suka je suka yi sannan suka dawo saura suka je suka dubo nasu jaririn.
Kafin kace me Nonuwan Rahma sun ciko da ruwa saidai kuma zafi yake mata, bata damu da zafin da yake ba sai murna ma da take tayi, zuwa tayi ta samu likitan ta ce “Doctor mun samu nasara”
Ya ce “Masha Allah to ki shiga ki basu zan turo nurse ta gwada miki yadda zaki basu”
Ta shiga, Islam ta fara ɗauka ta bata Nonon tana ji ta fara tsotsa ta zabura saboda zafi saidai kuma bata fizge mata ba ta daure taci gaba da bata, Nurse ɗin ne ta shigo ta gwada mata yadda zata yi, ta yadda zata sa yaron ta ba tare da ya zuƙi iska ba.
( Wajen shayarwa mata suna yin sakaci da yawa, da yawan mu idan zamu bada Nono bamu san yadda zamuyi ba, sai yaro yayi ta tsotsan Iska idan yana tsotsan Nonon yana ɗan zuƙa yana yin ƴar ƙaran zuƙa kamar Babba yana zuƙan pure water sai kaji ana cewa ahhh yaron nan da tsotso yake, alhalin kuma iska yake ja ya shiga masa ciki, sai kaji cikin yaro ya kumbura ka sara me yasa, Wannan Iskan nan ne da yasha yake damun su, sai kaga yaro yayi ta yawan tusa, sannan idan an gaba bada Nono kawai sai a kwantar dashi tanan kuma yaro sai ya dawo da Nonon da yasha. Yadda zakiyi ki bada Nono kuwa abu me sauƙi ne, Zaki ɗauke shi, ki sashi a cinyar ki, kisa kansa a gwiwar hannun ki, tafin hannun ki kuma ya tallafo ɗuwawunsa ta yadda zaki manna cikin ki da nashi, sai ki ciro Nononki da ɗaya hannun zaki sa Babbar yatsarki a Saman Nonon sannan sauran yatsunki huɗu suna ƙasan Nonon kin riƙe masa, kiyi bismillah ki sa masa a baki, ki tabbatar wannan baƙin ya shige bakin sa duka, wallahi zakiji yana sha sosai, sanna idan yasha sosai sai ki juya shi ki bashi ɗayan kiyi yadda kika yi a wancan, Idan ya gama kuma ki sa shi a kirjin ki kina shafa masa baya har sai yayi gyatsa, da yawan mu kuma ba haka muke ba, sai a ɗauki yaro kawai a sashi a cinya a sake masa Nono yana sha wanda ta riƙe ne ma zata sa yatsan ta manuniya da ta kusa da ita ayi kamar almashi, to taya yaronki bazaiyi ciwon ciki ba. Ƴar uwa idan kina da yaro ki gwada wannan shawara ki gani.)