FAHIMTA FUSKA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

FAHIMTA FUSKA Complete Hausa Novel

 

Bayan Islam ta ƙoshi ta bawa Iman sannan Ihsan.

 

 

 

 

 

lιĸe

coммenт

ѕнare

????ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍????

[18/07 8:51 PM] MIM✍????: ???? _*????ιĸιмaн ????rιтer’ѕ ????ѕѕocιaтιon*_

????( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)

Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

 

 

 

loadιng………..✍????

 

 

 

???? _*FAHIMTA FUSKA*_

 

 

 

Written by

UMMU MUFEED

(Mrs Aliyu)

 

 

 

Marubuciyar:-

BILKISU

INA DANGINA

IZZAR MULKI

JININA

AMANATA

MAIMUNATU

YAƘI A SOYAYYA

And now

FATIMTA FUSKA

 

 

 

_Ina kuke Masoyan Hikima, kuma Masoyan Maimuna Isah Musa (Mrs Aliyu) masu son ci gaban ta, gata ta yunƙuro ta farfaɗo muku da wani Sabon shahararren littafinta me suna *Fahimta fuska*_

_Tab ay ko daga jin sunan ma kasan labarin zaiyi Sugar, sannan tazo muku da salon rubutu salon labari wanda baku saba gani, domin labarin yasha bam-bam da sauran labarai, ga duk me buƙata zaibi wannan tsarin????????????????????????????????_

 

 

 

*FAHIMTA FUSKA Na kuɗine Naira 300 kacal????????Zaka/ki biya ta wannan account*

*0019138715*

*Maimuna Isah*

*StanbicIBTC*

*Sai ka/ki tura min shaidan biya ta wannan number 09034313679*

*Ko katin MTN na  300 ta wannan number*

 

Last free page

 

Daga yanzu free page ya ƙare duk me buƙata sai ya biya 300 yasha labari.

 

 

 

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

 

 

 

 

Page 11&12

 

 

 

 

 

 

 

Duka saida ta sasu ka kafaɗa suka yi gyatsa sannan ajiye su.

 

***

 

Saida suka tabbatar tayi nisa sannan Mama ta buɗe shi ganin sa suka yi yasha kuka, wanda rabon da yayi tun yana yaro, bai musu magana ba ya fita Mama ta kalli Baba ta ce “Wai mu yarinyar nan zata yi wa haka? harda haihuwa, ka duba kallon da mutanen unguwar nan suke mana mun sangarta ta ashe da gaske ne”

 

Ya ce “Yanzu ay sai taje ta nemi uban yaran”

 

Lukman ne ya dawo ya ce “Da ba a gabana aka haifi Rahma ba wallahi da nace ba ku kuka haife ta ba, dan tayi cikina waje Allah ya azirta ta da ƴaƴa har uku sai mu kore ta don me, meta muku yarinyar nan ko Abinci bata ci ba ga jego, to me yasa ma baza mu hamshi ƙaddaran da Allah ya aiko mana da ita ba, mu rungumeta, yanzu da kuka koreta kunfi son ta koma gun ɗan iskan kenan suci gaba da zaman zina, tayi kuskure abaya amma a yanzu duk abin da Rahma tayi bata da laifi, Wai Mama kun manta da asalinku ne, a gidan Marayu fa  kuka rayu, bamu da dangi to dan me yasa mun fara haɗa family zamu guje su, Baba kai da kanka ka ce kana son mu haɗa zuri’a saboda kasancewar ku baku da ƴan uwa, to ga Allah ya fara Azirta mu kuma kunyi watse da mu, shin kuna zaton Allah zai barmu haka nan ne ba tare da yayi fushi da mu ba?” zai ci gaba da magana yaga Mama tana hawaye da sauri yaje ya kama hannun ta ya ce “Banso in saki hawaye ba Mama, amma kun aikata babbab kuskuren da baza mu ta’ba gyarawa ba, dan ba musan inda zamu samu Rahma ba”

 

Ta girgiza kai ta ce “Ba kai ka sani kuka ba, Ina nadaman kuskuren da na aikata ne, lalle ni ba uwa ta gari bane, bai kamata in mata hukunci ta wannan hanya ba, ya kamata in rungumeta a jiki ita da abin da ta haifa”

 

Baba ya ce “Gaskiya mun aikata kuskure amma yanzu kira mana number ta muji kota kunna”

 

Lukman ya ce “A kashe ne, Baba da ka bari na bita da duk haka baza ta faru ba, nasan kuna cikin fushine yasa kuka aikata hakan a niyyata duk inda muka je idan kun huce sai mu dawo gare ku”

 

Baba yace “Yanzu tashi muje ko zamu samu labarinta”

 

Tashi suka yi suka fita suka bar Mama tana kuka.

 

***

Tana dawowa daga Sallah la’asar Maman A.J ta ce “Wai Maman ƴan uku har jinin ya ɗauke miki ne, naga kina zuwa Sallah”

 

Murmushi tayi ta ce “Ay washe garin da na haihu jinin ya ɗauke yanzu baya zuwa”

 

Maman Sayyid ta ce “Ni kwana na uku da haihuwata jini ya ɗauke”

 

Maman Najeeb ta ce “Mukan gamu muna ta fama ”

 

Zuwa tayi ta goge musu cibi sannan ta musu Addu’a zata wuce likita ya ce “Akwai Sallan gawa idan zakuyi wani bawan Allah ya kawo matarsa da ta rasu a haihuwa ba ɗan garin nan bane shine ya kawota nan don al’umman Musulmai su sallaceta”

 

Ta ce “Allah ya jiƙanta barin je in fada wa ƴan ɗakin mu waɗanda zasu iya zuwa sai muje”

 

Ya ce “Kice wa Maman Najeeb Najib na kuka tazo ta bashi Nono”

 

Ta ce “To”

 

Tana zuwa ta sanar dasu Maman Sayyid Maman Abdul ne kawai suka ce “Zasu je, Maman AJ.da sauran suka ce su ba daman zuwa dan basu da tsarki”

 

Maman Sayyid ta ce “To ga Sayyid, Abdul da ƴan uku duk suna ƙarkashin kulawar ku”

 

Suka je suka samu an kawo gawar mutane da yawa sun halarta maza da mata Saida maza suka yi Sahun su sannan mata ma suka yi nasu a baya.

 

(Da yawan mu mata bamu san cewa Mata na Sallah gawa ba, Idan an mana mutuwa sai maza su fita suje suyi Sallah mu kuma a barmu a gida muna ta kuka bamu je mun samu lada ba, yakamata muma muna fita muna yin Sallah Idan an tafi da gawa sai mu dawo gida muna gurawa mamacin Addu’o’in mu”

 

Koda suka dawo saida taje ta duba su Islam taga suna barci ji tayi ƙaunarsu ta mamaye mata zuciya wanda taji zata iya sadaukar da rayuwanta a kansu kuma koda  yanzu ƴan uwan su sun zo baza ta iya bada su ba, koda kotu za’a shiga cewa zata ita ta haife su, sannan ta dawo ɗakin su.

 

Ƙarfe biyar suna zaune Likita ya aiko kiranta, ta tashi ta je ta same shi tare da wani mutum Fari ne dogo yana da kyau sosai kuma idan ka ganshi zaka san Naira ta zauna.

 

Likita ya ce “Wannan Sunan sa Al’amin, ɗan Mai duguri ne wanda Matarsa ta rasu muka mata Sallah, to ya dawo ne dan ya taimakawa maras sa ƙarfi da suke asibitin nan, shine na bashi labarin ki, sai ya ce a kira ki”

 

Cikin sanyi Murya ya ce “Da Mamaki amma ke kika haifi ƴan ukun nan kuma har zaki iya shayar da su”

 

Ta ce “Da ikon Ubangiji zan iya”

 

Ya ce “Ko da yake ay Saniya bata gazawa da ƙahon ta zaki iya ɗin”

 

Likita ya ce “Da yake ay bakwaini ne ƙanana ne baza suyi tsotso sosai, amma idan sun girma dole zata haɗa musu da Madara”

 

Ya ce “Kina da Account?

 

Ta ce “eh”

 

Ya miƙa mata biro da takarda ya ce “Rubuta anan”

 

Ta amsa ta rubuta ta miƙa masa nan take ya mata transfer na 2m sannan ya ce “ki duba zaki ga na tura miki kuɗi kya siya musu madara”

 

Ta ce “Bani da waya”

 

Ya ce “To na sa miki 2m ”

 

Zamewa tayi ƙasa ta ce “Mungode Allah ya biya maka buƙatar ka ta alheri”

 

Ya ce “Amin, Ki sani a cikin Addu’anki, Ina buƙatar ƴaƴa, sau uku matana tana haihuwa suna mutuwa, wannan haihuwar ne aka mata C.S kaka ciro mata ƴan wata bakwai duka suka rasu daga ita har su”

 

Ta ce “Ayya, Allah ya kawo masu Albarka”

 

Ya ce “Amin, muje muga yaran naki?”

 

 

 

 

 

lιĸe

coммenт

ѕнare

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button