KannywoodLabarai

IRINKU YA KAMATA A DAINA HAIFOWA BA ALMAJIRAI BA…..Martanin Dr. Juwairiya Grema ta film din kwana Casa’in ga Nafisa Abdullahi.

DAGA Saifullahi Lawal Imam

“Babu wanda ya isa ya tsarawa kansa abunda Allah bai tsara mishi ba. Don haka ku daina hantarar Almajirai ba su da laifi,kuma Allah ne ke ciyar da su baku ba”.

Dr. Grema ta bayyana hakane a cikin wata zantawa da wakilin Arewa Media ya yi da ita game da dambarwar da sa-toka-sa-katsin da ke tsakannin Mawaki Naziru sarkin Waka,da Jaruma Nafisa Abdullahi game da Haihuwar yara gaba-gadi,inda ta bayyana cewa ” Ita wacce ta fito tana daga muryar a daina Haihuwar yara ai ba nan ya kamata ta zo tana Surutu ba,Allah da ya nufa kuma ya rubuta za su shugo duniya ya kamata ta baiwa shawarar daina Halittarsu tunda abunda ta ke so kenan.

Dr. Grema wacce fitacciyar Jarumar Fina-finai ce da take fitowa a cikin mashahurin shirin nan mai dogon zango da ake nunawa a tashar Tauraron dan Adam na Arewa24 wato KWANA CASA’IN,ta kara da bayyana cewa.

“Ya kamata ne a ce irinta aka daina haifowa,domin Almajiri shi kullum neman abunda zai ci yake yi ta hanyar Halas,wai ma da ta fito tana hayayaga akan a daina Haihuwa ku tambayeta Almajirai ko marasa galihu nawa ta taba tallafawa ko ta inganta rayuwarsu?,don haka Sarkin waka Naziru ya fita gaskiya,Almajirai ba ababen wulakantawa ba ne. Domin suma y’ay’ane kamar kowa,kawai haka yasu rayuwar ta zo,kuma haka Allah da ya haliccesu yake son ganinsu. Don haka ya kamata a shawarce ta iya bakinta ta daina shiga Hurumin Allah”

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button