Allon Sihiri 5HAUSA NOVEL

Allon Sihiri 5

__OKACIN DA Yarima Mangul da Barde Ruhaisu
suka
ruguntsume da azabbaben yaki mai tsananin
muni,sai wani abin mamaki ya afku domin kuwa
gashi a zahiri Yarima Mangul yafi barde Ruhaisu
karfin damtse da iya yaki,domin da kyar ma
barde
Ruhaisun ke iya kare saransa saboda nauyin
saran,amma da yake Barde Ruhaisu nada
matukar
zafin nama gami da juriya da mugun naci sai
Yarima
Mangul ya kasa cutar dashi.Saida suka shafe
sa’a
guda cur suna wannan mugun artabu amma
dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin dayan
ba.Al’amarin daya fusata su kenan kowa yaja da
baya suka tsaya suna kallon kallo suna haki
kamar
zakaru.Koda Yarima Mangul ya karewa Barde
Ruhaisu kallo ya fahimci cewar ba sa’ansa bane
a
kallah Barde Ruhaisu zai iya girmarsa da tazarar
shekaru kusan goma sai takaici ya kamashi yaga
cewa ai yakamata yayi ace tuni ya gama da
wannan
JARUMI tunda yafishi kuruciya,idan kuwa kafi
mutum
kuruciya zaka iya finsa kuzari,saidai kawai ya
nuna
maka tsohon kashi.Gama aiyana hakan keda
wuya
sai Yarima Mangul ya daga hannunsa sama yana
mai baiwa dakarunsa inkiyar su afkawa su barde
Ruhaisu.Ai kuwa shima Barde Ruhaisu sai ya
baiwa
nasa dakarun umarnin su taresu.Nan fa kowacce
RUNDUNA ta ruga da rugu izuwa kan dayar ana
haduwa a tsakiya aka ruguntsume da azababben
yaki.Karar karafa gami da ihun mazaje ya cika
dajin
gaba daya.Jini ya rinka fallatsi da fantsama sai
gashi
al’amarin ya rinciba a tsakanin dakaru dubu da
guda
dari.Kodaga nesa ne mutum ya zuba ido yana
ganin
abinda ke faruwa bazai iya gane bangaren
mutum
zai zuba ido da kyai a cikin lura zai gane cewa
anfi
ragargazar dakarun Yarima Mangul.Lokacin da
aka
fara wannan gumurzun ne Yarima Mangul ya
sami
damar matsawa kusa da inda Yazarina ke
tsugunne
saboda duk Badakaren Barde Ruhaisu da yazo
gabansa kwaf daya yakeyi masa.A lokacin Barde
Ruhaisu ya shiga cikin tsakiyar dakarun Yarima
Mangul yana ta ragargazarsu yana yi musu sarki
ya
hana dawa tsayuwa.Hakan ne yasa ya sha’afa ya
bar
daidai wajen da Yazarina ke tsaye.A wannan
lokaci
da yakin yai tsamari ne Yazarina ta dimauce
kuma ta
firgice saboda wannan ne karon farko a
rayuwarta
da akayi yaki a gabanta.Koda taga an sare wani
Badakaren ya fado a gabanta jininsa yai feshi
akan
fuskarta bata san sa’adda ta kurma uban ihu ba
ta
daka tsalle sama.Faruwar hakan keda wuya sai
rawanin fuskarta ya subuce ya fadi
kasa.Kyakkyawan
dogon gashin kanta ya tarwatse a sama ya zubo
kasan kafadunta.Koda Yarima Mangul yayi arba
da
fuskar Yazarina yaga itace sai ya kamu da
tsananin
mamaki ya daka tsalle sama ya dira a bayanta
yasa
takobinsa a wuyanta ya ritsata kuma ya daka
tsawa.Take aka daina yakin kowa ya juya ya
dubeshi.Take aka daina yakin kowa ya juya ya
dubeshi.A sannan ne Barde Ruhaisu ya hango
abindake faruwa sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun.Yarima Mangul ya bushe da dariyar
farinciki a
lokacin daya dora yankakken hannunsa akan
kafadar
Yazarina ya sumbaci wuyanta yace,marhaban da
ganinki ya abar kaunata.Tabbas nayi matukar
farin
cikin sake saduwa dake a wannan lokaci da ban
taba
zata ba.A tsammani sai na karbi karagar mulkin
ubana sannan zan sami damar sake ganinki na
kashe mijinki Lubainu koda yana raye domin na
mallakeki amma sai gashi yanzu na sameki a
banza
ba tare da wata matsala ba.Ki sani cewa yanzu
ina
gama kashe wadannan abokan tafiya naki zan
tafi
dake can sansani na a daura mana aure bisa
dole..Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa
tuni
Yazarina ta tofa masa yawu a fuska sannan tace
karyarka tasha karya saidai ka auri gawata
amma
bani ba.Yaza’a yi na auri azzalumin daya lalata
rayuwar wani saboda son zuciyarsa?Ka sani
cewa ni
yanzu bana tsoron mutuwa tunda kasa mijina ya
tafi
izuwa inda zai iya rasa rayuwarsa gaba
daya.Idan
kuwa har Lubainu ya mutu to nima banga
amfanin
tawa rayuwar ba saidai na bishi.Koda Yazarina
tazo
nan a zancenta a lokacin da jikin su Barde
Ruhaisu
duk yayi sanyi sun sauke makamansu kawai suna
kallon abin da ke faruwa tsakanin Yarima Mangul
da
Yazarina cikin alamun tsananin tsoro da
fargaba.Har
izuwa wannan lokaci Yarima Mangul bai cire
kaifin
takobinsa daga kan wuyan Yazarina ba don haka
sai
ya sake bushewa da dariya,kuma yayi amfani da
dan
yatsansa guda daya ya lakuci yawun bakin
Yazarina
data tofa masa akan fuskarsa ya lashe a bakinsa
yace,ban taba jin abu mai zakin yawun bakinki ba
yake MASOYIYATA.Yana gama fadin hakan sai
ya
dubi Barde Ruhaisu ya daka masa tsawa yace
maza
ku bude fuskokinku kaida yaranka kuma ku zubar
da
makamanku ko yanzu nan na shaftare
makogwaron
yazarina.Har su Barde Ruhaisu zasubi wannan
umarni sai Yazarina ta daka musu tsawa
tace,kada
ku yarda ku aikata hakan domin bazai kasheni ba
saboda bashi da burin dayafi ya mallakeni a
rayuwarsa.So yaje kawai ya yaudareku ku zubar
da
makamanku yasa a kasheku a banza.Koda ma ya
kasheni din bani da asara ko nadama,domin
babban
bakin cikina shine ya mallakeni din.Ku ci gaba da
yaki har sai idan karfinku ya kare,domin ku
zamto
masubin umarnin sarki.Zaku iya bude fuskokinku
domin ko baku bude ba su ba yanzu yasan cewa
ku
dakarun sarki Sailur ne.Koda Yazarina tazo nan a
jawabinta sai Barde Ruhaisu da dukkan sauran
yaransa kimanin mutum saba’in suka bude
fuskokinsu kuma suka daga takubbansu sama
suna
masu niyyar cigaba da yaki.Koda Yarima Mangul
yayi arba da fuskar Barde Ruhaisu sai ya jinjin
kai
yace,tabbas babu mamaki domin banda sarki
yakin
garinku da Yarima Lubainu babu wanda zai iya
tarata muyi GUMURZU na tsawon wannan lokaci
ba
tare dana sami nasarar hallakashi ba face kai.Ai
kuwa dayanmu bazai bar wannan
wuri ba a raye saidai a dauki gawarsa!Yarima
Mangul na gama fadin hakan sai ya wurga
Yazarina
izuwa hannun sarkin yakinsa ya cafketa ya
dubeshi
yace,mazaka ka tafi da ita izuwa sansaninmu a
tsareta kuma ka dawo nan tare da dakari dubu
goma.Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu
ya
falfalo da azababben gudu izuwa inda Yazarina
take
ya kutsa ta tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana
karkadesu da karfin sara da suka domin ya isa
inda
sarkin yakin Yarima Mangul yake a lokacin daya
ja
Yazarina da karfin tsiya izuwa kan wani
doki.Koda
ganin haka sai shima Yarima Mangul ya falfalo
da
gudun tsiya da nufin yasha gaban Barde Ruhaisu
ya
hanashi isa inda su Yazarina suke.Koda ya rage
saura baifi taku goma ba tsakanin Barde Ruhaisu
da
Yarima Mangul sai Ruhaisu ya daka wawan tsalle
a
sama ya tsallake Yarima Mangul ya doki gadon
bayan sarkin yakin nasa.Ba shiri sarkin yakin ya
saki
Yazarina ya fadi can gefe daya.Kafin Yarima
Mangul
ya juyo baya da gudu yazo ya riskesu tuni Barde
Ruhaisu ya daka tsalle sama ya haye dokin dake
gabansa.Kawai sai ya mikawa Yazarina
hannunsa ta
kama ya dagota sama cak ya dorata a bayan
dokin
kuma ya zaburi dokin da gudu izuwa cikin
daji.Koda
ganin haka sai shima Yarima Mangul ya ruga
izuwa
inda nasa dokin yake ya daneshi kuma ya
zabureshi
da gudu yana mai bin bayan dokin su
Ruhaisu.Nanfa
filin yakin ya watse kowacce runduna hankalinta
ya
tafi izuwa tafiya neman shugabanta tamkar ma
an
manta mummunan yaki da ake fafatawa.Lokacin
da
Barde Ruhaisu ya sami nasarar gudu da Yazarina
akan doki suna tsala gudu a cikin daji ba tare da
sanin inda suka dosa ba sai suka jiyo sukuwar
doki
a bayansa.Cikin firgici Yazarina ta waigo baya
kawai
sai taga ashe Yarima Mangul ne ya biyosu kuma
tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin
da
biyar ba,kuma dokin nasa gudun bala’i yake yi
yana
rike da linzaminsa da lafiyayyen hannin nasa sai
dada zungurar dokin yake da kafafunsa yana kara
masa kaimi ga zabgegiyar takobinsa rataye a
bayansa.Cikin tsananin firgici Yazarina ta juya
tace,yakai Ruhaisu kayi sani cewa wannan
azzalumin
makiyi makiyin namu yana daf da riskarmu.Koda
jin
haka sai shima Barde Ruhaisu ya karawa nasa
dokin
kaimi.Nanfa dawakan suka cigaba da kasa
mugun
gudu,tseren gudu na ban al’ajabi.Koda karfin
gudun
dokin Ruhaisu ya karu sai Yazarina taji tana
neman
fadowa kasa don haka ba shiri tasa hannayenta
biyu
a zagayen cikin barde Ruhaisu ta rukeshi gam
gam
da kyau ta kwantar da kanta akan gadon
bayansa.Haka dai aka cigaba da wannan tseren
gudu
na tashin hankali har izuwa tsawon sa’a
guda.Kwatsam sai dokin Barde Ruhaisu dana
Yarima
Mangul din suka iso wani wuri mai tudu wanda
basu
ankara dashi sukayi tuntube suka zube kasa
gaba
dayansu har su Barde Ruhaisu.Cikin gaggawa
Barde
Ruhaisu ya mike tsaye zumbur ya kama hannun
Yazarina ya tasheta tsaye suka sake
ruguntsumawa
da gudu izuwa cikin daji.Shima Yarima Mangul a
dimauce ya mike tsayen da sauri yabi su a guje
suka kasa sabon tseren gudu kafafunsu tamkar
zasu
tashi sama saboda karfin gudu.Faruwar hakan
keda
wuya sai Yazarina ta sare ta fadi kasa kuma a
lokacin tazarar dake tsakaninsu da Yarima
Mangul
bata wuce taku ashirin ba.Koda Yarima Mangul
yaga
Yazarina ta fadi kuma gashi babu makami a jikin
Barde Ruhaisu sai yayi wuf ya zaro sharbebiyar
takobinsa yayi kansu da nufin ya riskesu kafin
Barde
Ruhaisu ya tasheta tsaye ya sare masa
kai.Amma
sai yaga Barde Ruhaisu yayi wuf cikin wani bakin
zafin nama da bajinta ya suri Yazarina tamkar
sillan
karah ya daga ya goyata a bayansa.Ita kuma ta
rukunkumeshi ya cigaba da falfala azababben
gudu.Sai gashi sun ci gaba da tseren gudun nasu
tamkar mai kaya ya biyo barawo.Yarima Mangul
ya
dage iya karfinsa domin ya cimmusu amma sai
abu
ya gagara.Al’amarin daya daurewa Yarima
Mangul
kai kenan ya cika da tsananin mamakin yadda
akayi
ya kasa cimma Barde Ruhaisu duk da cewa yana
fama da nauyin Yazarina wacce ke goye a
bayansa.Barde Ruhaisu na cikin wannan gudu ne
ya
riski wani katon tsauni mai fadi,girma da tsawon
tsiya a gabansa,kuma babu wata hanya da zai
iya
ratsewa tsaunin dole ne yabi ta kansa in ba haka
ba
kuwa saida ya tsaya ya jira isowar Yarima
Mangul
ayi wacce za’ayi.Ta yaya zan fuskanci Yarima
Mangul alhalin babu makami a hannuna?Tabbas
bani da wani zabi wanda yafi na hau kan wannan
tsauni.Ya bawa kansa amsa a cikin
zuciyarsa.Yaba
gama aiyana hakan sai ya hau kan tsaunin goye
da
Yazarina a bayansa yana cigaba da gudun.Shima
Yarima Mangul yana isowa bai tsaya jiran komai
ba
sai yabi shi izuwa kan tsaunin a guje yana ruri da
kururuwa mai ban tsoro,cikin murna domin gani
yake kamar ma ya gama samun nasarar kashe
Barde
Ruhaisu gami da mallakar Yazarina.Nanfa duka
cigaba da gudu akan tsaunin tun sunayi da
karfinsu
da guzarinsu har saida suka sare suka fara
faduwa
kasa suna mikewa da kyar suna haki.Saida suka
shafe sa’a daya da rabi suna gudu gudu,tafiya
tafiya
akan tsaunin sannan suka iso can kokoluwar
karshensa.Koda Yazarina Da Barde Ruhaisu suka
leko kasan tsaunin wanda saboda tsananin nisan
zurfinsa mutum baya iya hangi abinda ke xan
kasan
nasa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,a
lokacin
da suke ta fama haki saboda tsananin gajiya
tamkar
ransu zai fita.A daidai wannan lokaci ne shima
Yarima Mangul ya iso kusa dasu da kyar yana
haki
da layi rike da takobinsa.Koda yaga cewa ai sun
iso
karsshen tsaunin sai ta dubesu ya bushe da
dariyar
farin ciki duk da cewa makogwaronsa a bushe
yake
saboda muguwar kishirwa gashi babu ruwa a
kusa.Suma su Yazarina haka suke jin tsananin
kishirwa tamkar zata kashesu domin yawun
bakinsu
ma daukewa yake
kamar babu shi.Yarima Mangul ya gyara
tsayuwarsa
irin ta wadanda suka sami nasara ya dora
zabgegiyar takobin tasa kan kafadarsa ya dubesu
cikin izaa yace,yanzu kuma ta yaya zaku iya guje
mini tunda gashi kunzo makura?Tabbas yanzu
zan
kasheka yakai Barde Ruhaisu,amma fa ka
burgeni
domin kayi jarumtakar da ban taba zaton kana da
ita
ba,kuma dole ne na rubutaka a cikin KUNDIN
TARIHIN rayuwata,saidai kash,jarumtakarka taka
ta
zama ta banza tunda baka cika aikin sarki Sailur
ya
baka na kare Yazarina kuma gashi zaka mutu a
banza.Koda Yarima Mangul yazo yazo nan a
zancensa sai Barde Ruhaisu ya tari numfashinsa
yace,kaicinka yakai wannan azzalumin dan sarki
wanda rayuwarsa ta gama tarwatsewa.Ka tuna
cewa
ka rasa masoyiyarka yazarina kuma ka rasa
abokinka amininka YARIMA LUBAINU,Kuma ka
cutar
dashi bisa son zuciyarka don kawai ka rabashi da
wacce ya riga ka SO da KAUNA kun zama
ABOKAN
GABA!Yanzu gashi ka rabu da mahaifinka ka rabu
da
matsayinka na Yarima tunda Mahaifin ya zama
abokin gabarka,kana hada runduna ta YAN
TAWAYE
domin kaje ka kashe shi,kaga kenan kai yanzu
abin
tausayi ne tunda baka ga tsuntsu ba bakaga
tarko
ba.Baka da komai bakada kowa sai mafarkin
zuciya
wanda ina tabbatar maka da cewa har abanda ba
zai
taba tabbata gaskiya ba.Da wannan furuci nake
yi
maka bankwana domin ko zaka sami nasarar
mallakar Yazarina saidai ka mallaki
gawarta.Nima
saidai ka tusa gawata amma ba dai ka kasheni
da
hannunka ba!!!Barde Ruhaisu na gama fadin haka
sai ya juya da sauri ya daka tsalle ya fado kasan
wannan tsauni mai zurfi shi da Yazarina suka
kurma
ihu saboda sun san cewa mutuwarsu ce tazo.
Just now · PublicALLON-SIHIRI
Littafi na Biyar (5)
Part B
Suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu
tazo.Shi kuwa Yarima Mangul sai bakin ciki ya
turnukeshi ya durkuse kasa bisa guiwoyinsa
sannan
ya wangame baki shima ya kwarara uban ihu
kuma
ya fashe da matsanancin kuka saboda yasan
cewa
shike nan har abada bazai sake ganin Yazarina a
raye ba.Kafin Yazarina da Barde Ruhaisu su kai
rabin nisan tsaunin tuni sun sume saboda karfin
iskar dake kadasu da kuma jirin daya kwashesu
don
haka sa’adda suka iso can karshen tsaunin sun
zama tamkar gawarwaki sai ji kake tunjum…!sun
fado cikin kogi.Lokaci guda suka nutse kasa
amma
sai suka taso sama igiyar ruwa ta rinka kadasu
cikin
tsananin sa’a da rabon sauran rayuwa ta kaisu
can
gefe kogin ta watsar.Saida suka shafe kusan
rabin
sa’aa kwance a gefen kogin a sume basu
farfado
ba,iska mai sanyi ce ta rinka kadawa a wajen ta
yadda utace ta zamo sanadin farfadowarsu daga
dogon suman da sukayi.Koda suka bude
idanunsu
suka kalli juna suka tabbatar da cewa suna raye
basu mutu ba sai suka kamu da tsananin mamaki
suka kama kyalkyala dariya.Saboda tsananin
farin
ciki Yazarina batasan lokacin data rungume
Barde
Ruhaisu ba.Faruwar hakan keda wuya ta tuna
cewa
ita fa matar Yarima Lubainu ce,kawai sai tayi
saurin
janye jikinta daga cikin na Barde Ruhaisu ta
sunkui
da kanta kasa ta budi baki cikin rawar murya da
kunya tace ka gafarceni.Take shima Barde
Ruhaisu
yaji kunya ta lullubeshi yama rasa abinda zaice
da
ita.Kawai saiya juya mata baya ya fada kogin
tunanin
abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi
yana
mamakin al’amarin da ya kasance hakan.Wannan
shine abinda ya faru tsakanin Barde Ruhaisu Da
Yazarina a lokacin da suka baro Birnin Zamrul
domin neman Yarima Lubainu.
쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼
AL’AMARIN SU Bakon Jarumi kuwa lafiya sumul
suka kwana a cikin fadar Boka Darbusa kuma
dukkaninsu suka wayi gari cikin koshin lafiya ba
tare
da fuskantar wata matsala ba.Da sassafe bakon
jarumi da bawansa Dazyan suka shiga daji suka
farauto wani katon tsuntsu suka zo suka fisgeshi
sannan suka gasashi.Da naman wannan tsuntsun
kowa yayi kalaci.Bayan an gama kalacin ne
bakon
jarumi ya dubi Dazyan yayi masa inkiya shi kuwa
sai
ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima
Lubainu
da Sarki Darmanu yace,yaku abokan
tafiya,maigidana yace na gaya muku cewa zamu
cigaba da tafiya gaba dayanmu izuwa kogin
BAHAR
IMFALkamar yadda akayi alkawari da farko
domin
ya nuna muku karfi da iko na ubangijin musulunci
amma badon ya yarda da tsafinku ba.Zai baku
dama
ku tsirar da rayuwarku da karfin ababan bautarku
da
karfin sihirigami da karfin damtsen ku har sai
yaga
kun kasa kare kan naku sannan zai taimakeku da
taimakon ubangijinsa.Yace na dada jaddada
muku
cewa idan fa har aka isa can kogon Bahar Imfal
aka
samo abinda akaje nema da taimakonsa to dole
ne
ku karbi addininsa ko kuna so ko bakwa so,in ba
haka na kuwa zaku zamo abokan gabarsa babu
abinda zai rabaku face yaki!Daga yanzu zai ci
gaba
da ajiye ALLON SIHIRI a wajensa har izuwa
wannan
lokaci don haka tun yanzu kuna da sauran damar
da
zakuyi shawara bisa abinda kuke ganin cewa
shine
zai fissheku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa
sai
su Yarima Lubainu suka dubi junansu suka rasa
abinda zasu ce kawai sai Yarima Lubainu yajasu
gefe daya ya dubesu cikin nutsuwa yace,abinda
nake
so daku shine,kada dayanku ya bigire sharadin
wannan bakon jarumi domin yanzu a hannunsa
muke sai yadda yayi damu,idan muka ce zamuyi
masa tawaye dayanmu bazai tsira da rayuwarsa
ba
bare ya cika burin rayuwarsa.Ko kuwa akwai mai
korafi a cikinku akan wannan shawara dana
kawo?
Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul
Sauwara da sarki Darmanu suka budi baki a
lokaci
guda sukace bamu da wani korafi face bin
sharadinsa.Dajin haka sai farin ciki ya lullube
Yarima
Lubainu yaja su suka koma wajen bakon jarumi
ya
sanar dashi cewa sun amince da dukkan
sharadinsa
kuma basu da wani korafi.Da jin haka sai bakon
jarumi ya mike tsaye ya dubi Dazyan yayi masa
zancen kurame shi kuma ya dubi su Yarima
Lubaiun
yace,shugabana yace kowa ya debo kayansa
zamu
cigaba da tafiya yanzu.Dajin haka sai kowa ya
ruga
izuwa cikin fadar Boka Darbusa ya dauko jakar
guzurinsa ya dora akan dokinsa kuma ya hau kan
dokin nasa ya zauna.Saida kowa ya gama
kimtsawa
sannan bakon jarumi ya hau nasa dokin ya wuce
gaba,Dazyan ya jere dashi.Sarauniya Akisatul
Sauwara ce ke biye dasu sannan Yarima
Lubainu,Sarki Darmani ne na karshe.A wannan
lokaci bakon jarumi ya lullube ALLON SIHIRI a
cikin
wani babban mayafi ya dora akan wuyan dokinsa
ya
daureshi tamau.Ana fara yin wannan tafiya ne
sarauniya Akisatul Sauwara ta waigo ta dubi
Yarima
Lubainu sai taga ya sunkui da kansa kasa yana
tunani mai zurfi.Koda ganinsa a wannan hali sai
ta
tsayar da dokinta har saida taga ya iso daf da ita
sannan suka cigaba da tafiya a tare a jere,a
sannan
ne ta dubeshi cikin alamin tausayawa tace,yakai
Yarima menene yake damunka ne?Tun jiya na
lura
da kai baka yin magana sosai,kuma baka cin
abinci
kamar yadda ka saba,sannan ko yaushe sai naga
kayi shiru kana tunani mai zurfi ina dalilin hakan?
Koda Yarima Lubainu yaji wannan tambaya daga
bakin sarauniya Akisatul Sauwara sai ya kawo
gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta
yace,yake wannan sarauniya mai daraja,kiyi sani
cewa tun jiya ne naji zuciyata tana yawa bugawa
da
karfi haka kawai ba tare da nasan dalili
na,sannan
kuma a daren jiyan nayi wani mafarki mai ban
tsoro.A cikin mafarkin an nuna mini katon bakin
kumurcin maciji yana bin inuwata da gudu a cikin
daji har inuwar rawa tana yin tuntube tana
faduwa
amma a karshe
sai inuwar tawa ta yanke jiki ta fadi kasa ta kasa
cigaba da gudu har macijin yazo daf da ita ya
fasa
kai.Yana shirn saranta ne na farka daga barci a
cikin
daren naji jikina na kyarma saboda firgita danayi
kuma gaba daya jikina a sannan ya jike sharkaf
da
gumi tamkar abinda na gami a mafarki ya faru ne
a
gaske.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a
zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi
ajiyar
zuciya sannan tace,indazaka tuntubi bakon jarumi
akan wannan mafarki naka da zai iya gaya maka
fassararsa.Koda jin haka sai mamaki ya kama
Yarima Lubainu yace yaya akayi kika san cewa
ya
iya fassara mafarki alhalin bashi da bakin yin
magana?Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ji
nayi
wancan bawan nasa dan wada Dazyan ya bashi
labarin wani mafarki dayayi shi kuma ua fassara
masa mafarkin a cikin yaren kurame,al’amarin
daya
bani sha’awa kenan na tambayi Dazyan nace
yakai
Dazyan naji kana gayawa shugabanka cewa kayi
mafarkin wata kaza wacce tayi kwaikwaye biyu
kala
daban daban.Kwan farko data sako FARI ne fat
na
biyu kuma JA ne,kawai sai tayi kwanci akan farin
ta
kyankyashe UNGULU da kuma tayi kwanci akan
jan
saita kyankyashe ZABUWA.To waishin menene
fassarar dayayi maka akan wannan mafarki
naka?
Lokacin da Dazyan yaji wannan tambata dana yi
masa sai yace,fassarar da maigidana yayi mini
itace,Allah ne yakeyi mini nuni dana nutsu nayi
hankali da duniya.Wannan kasa itace
duniya,kwan
farko ya kasance FARI shine hali nagari idan
mutum
ya rikeshi zuciyarsa zata zama fara mara
mugunta
da kyakkyawan nufi.Kwai na biyu data
kyankyashe
wanda shine JA alama ce ta mugun hali.Ai bakaji
karshen mafarkin nawa ba saboda a cikin yaren
kurame na karasa bashi labari.Cigaban labarin
kuwa
shine,bayan kazar ta kyankyashe kwaikwayen
biyu
sai unguku taka jewa.Koda tazo giftawa ta gaban
zabuwar sai zabuwar ta cafko kanta ta gutsure
mata
kai,kuma ta hau bayanta ta zauna.Wannan alama
ce
ta cewar mutane a yanzu sunayin UNGULU da
KAN
ZABO!Ma’ana idan sukaga yan’uwansu masu
kyawawan halaye sai su jasu a jiki kamar suna
koyi
dasu,amma a karshe sai suyi amfani da wannan
dama su turmushesu su hallakasu.Sa’adda
maigidana yazo nan a jawabinsa saina dubeshi
cikin
alamun mamaki nace,to yanzu menene matakin
daya kamata na dauka don kada irin haka ta
sameni?Maigidana sai yace,kayi gaskiya,amana
da
rikon alkawari.Idan kayi hakan Allah zai kareka
daga
sharrin dukkan mai son cutar dakai.Koda
Sarauniya
Akisatul Sauwara yazo nan a jawabinta sai
Yarima
Lubainu yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta
tashi,take
yaji a cikin ransa cewa lallai akwai alamun
gaskiya a
cikin wannan addina na bakon Jarumi saboda jin
irn
wannan hikima da aka zuba a cikin mafarkin dan
wada Dazyan.Kawai sai Yarima Lubainu ya dubi
Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ai kuwa duk
sa’adda muka yada zango zanje na sami bako
jarumi na sanar dashi nawa mafarkin don naji irin
fassarar da zaiyi.Waishin ke bakiji wani abu a
ranki
ba ko a jikinki sakamakon labarin wannan mafarki
mai dauke da dumbin hikima da basira.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta numfasa tace,tabbas naji
gaba
dayan tsigar jikina ta tashi kuma zuciyata ta
daskare
tamkar na tsomata a cikin ruwan kankara.Koda
kin
wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima
Lubainu
yace,ai nima irin abinda naji kenan sak da
naki.Anya
kuwa wannan addini na bakon Jarumi bashi ne
ADDININ GASKIYA BA?Koda jin wannan tambaya
sai
sarauniya Akisatul Sauwara ta gyada kai tace,ai
kuwa ita gaskiya bata buya har abada,idan har
shine
ADDININ GASKIYAR to da sanni zamuga babbar
shaida dazata tabbatar mana da hakan.koda jin
wannan batu sai Yarima Lubainu ya girgiza kai
yayi
shiru bai kara cewa komai ba aka cigaba da
tafiya
ba sassauci.Ba’a tsaya ba har saida bakon
Jarumi
ya fuskanci cewa lokacin sallar Azahar yayi
sannan
ya bayar da umarnin a tsaya a yada zango,kuma
sai
akayi sa’a a wannan lokaci an iso wani wuri mai
magudanar ruwa.Koda su Yarima Lubainu sukaga
wannan ruwa sai suka kamu da matukar
sha’awarsa
suka ruga izuwa cikin ruwan suka kama shansa
suna wanke fuskarsu suna zubashi a kansu.Koda
bakon Jarumi yaga duk hankalinsu ya tafi izuwa
cikin wannan ruwa hardashi kansa Dazyan ya tafi
cikin ruwan ya tsugunna yana alwala.Nan take
bakon jarumin ya sulale daga wajen ba tare da
dayansu ya ganshi ba ya zagaya bayan duwatsun
da
wannan ruwa ke fitowa ta cikinsa inda babu mai
ganinsa.Da zuwansa sai ya tsaye cak ya dubi
gabas
da yamma,kudu da arewa yaga babu wani
mahaluki
mai ganinsa,kawai sai ya tsugunna a gaban
ruwan
yasa hannayensa biyu ya cire rawanin dake
kansa,wanda ya rufe fuskarsa.Dogon bakin gashi
ne
mai tsananin haske da kyalkyalu ya zubo kasa
bisa
kafadunsa,a lokacin da kyakkyawar fuskar ‘YA
MACE
ta gaban kwantace ta bayyana.Idan mutum ya
kwatanta kyawun wannan mace dana sarauniya
Akisatul Sauwara sai yaga ashe sarauniya
Akisatul
Sauwara ma mummuna ce akan wannan
BAKUWAR
JARUMA saboda bambancin a bayyana yake
babu
gami!”Ni kaina a matsayina na marubicin wannan
littafi an shammaceni a cikin labarin,domin ban
taba
zaton cewa bakon jarumi MACE ce ba NAMIJI ba
musamman da nayi la’akari da irin abubuwan
dayayi
na jarumtaka”.Nan take kyakkawar jarumar ta
ajiye
rawanin nata daf da ita sannan ta sanya zara
zaran
yan yatsun hannayenta guda biyu a cikin ruwan
ta
kwarfoshi tana mai yin bismillah.Ina jin sautin
muryarta zuciyata ta buga da karfi naji kamar
kirjina
zai tsage saboda tsananin zakin muryar,domin
kamai dacin ran mutum idan kunnuwansa suka ji
wannan murya mai zaki da taushi sai yaji kamar
ruwan sukari aka watsa masa ya gauraye da
dukkan
JININ JIKINsa.Nan take ma’abociyar kyawun ta
fara
alwala
a nutse cikin ilmi da kwanciyar hankali saida tazo
kan wanke kafar hagu a karshen alwalar sai
kawai
taji takun sawu a bayanta.Cikin bakin zafin nama
ta
suri rawaninta ta kifa a kanta,take ya rufe
gashinta
da fuskarta kamar yadda ya saba rufeshi koda
yaushe,sannan ta yunkura da nufin ta waiga don
taga ko waye ke tahowa ta bayan nata,kawai sai
taji
ansamata tsinin takobi akan tsakiyar wuyanta ta
baya ana bata umarnin kada ta kuskura ta
motsa.Sautin muryar data bata umarni ne ta
firgitata
ainun fiye da tsinin takobin dake kan wuyan nata
ba
don komai ba sai saboda ta shaida cewa ba wani
bane mai wannan murya face YARIMA
LUBAINU.Yarima Lubainu ya kurawa kyakyawar
jarumar idanu ta bayanta a lokacin da gaba
dayan
jikinsa ya kama kyarma saboda dimauta dayayi
tun
farko hango kyakkyawar fuskarta.Ko a mafarki
Yarima Lubainu idanunsa basu taba siffanta
masa
mace mai irin kyawun ta ba.Inda za’a dauki
matarsa
Yazarina a ajiyeta kusa da bakuwar Jarumar da
kyawunta disashewa zaiyi ta koma mummuna
saboda kwarjini da haibar bakuwar jaruma.Yarima
Lubainu ya sake budar baki da kyar muryarsa na
rawa yace,saboda me zaki yaudaremu tun farko
ki
boye wannan kyakkyawar fuskar taki da kuma
siffarki ta ‘ya mace da wannan murya taki mai
tsananin zaki da naushi tamkar sarewa?Koda jin
wannan tambaya sai Jarumar ta mike tsaye ta
juyo
ta fuskanceshi tace,Kamar yadda bawana Dazyan
ya
gaya muku tun farko ina da hujjar da tasa na
boye
fuskata,muryata da jikina wacce ba lallai bane na
sanar dakai a yanzu,amma kadan daga cikin
hujjar
ka gani yanzu da idanunka,kuma kaji ta a
jikinka,domin naga yadda jikinka ya kama tsuma
a
lokacin dakayi arba da kyakkyawar fuskata.Ina
mai
tabbatar maka da cewa in da kuma gaba daya
surata
ka gani zaka iya fita daga hayyacinka.Har izuwa
wannan lokaci da jarumar ke magan zuciyar
Yarima
Lubainu bata daina daka ba kuma jikinsa bai
daina
kyarma ba.Abinda zuciyar tasa ke raya masa
shine,wannan ma’abociyar kyau dazata kasance
sarauniya to zai iya yarda tsafanceshi ya zamo
gadonta na barci don kawai ya kasance kullum
yana
tare da iya yana ganinta kuma yana jinta a
jikinsa.Ai
kuwa nan take ya fada cikin kogin tunanin
yiyuwar
hakan tamkar a mafarki.Koda jarumar ta lura da
cewa Yarima Lubainu baya tare da ita ya tafi
izuwa
wata duniyar ta tunani sai tayi murmushi ta tafa
hannyenta a daidai kunnuwansa.Yarima Lubainu
yai
firgit tamkar wanda ya farka daga barci mai
nauyi ya
kura mata idanu.Ita kuma sai ta dubeshi cikin
nutsuwa tace,yakai wannan dan Sarki ka yi sani
cewa tun a farkon danaji labarinka na kamu da
tausayinka kuma a cikin zuciyata sai na yanke
hukuncin taimakonka koda kuwa ba zaka karbi
addinina ba saboda ina kishin halin da matarka
zata
shiga sakamakon rabuwarku.Abinda nakeso dakai
shine ka cigaba da rufe sirrina kada ka kuskura
ka
nuna wata alama da zata nuna cewa ka gane
cewa
ni mace ce.In dai ka ruke wannan al’amari ni
kuma
zan cigaba da taimakonka harka rabu da wannan
lalura.Amma inason nayi maka wata tambaya
guda
daya,kuma lallai ka bani amsarta bisa gaskiya
idan
kayi mini karya ka sani cewa anan gaba zakaji
kunya.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu
yayi
ajiyar zuciya sannan yace,babu yadda za’ayi nayi
miki karya saboda kafin na baro gida mahaifiyata
ta
bani guzurin abubuwa uku wadanda tace dani in
dai
na rikesu sai na sami nasarar abinda na fita
nema.Abu na farko shine lallai duk abinda zan
fadi
ko zanyi nayi shi bisa gaskiya.Abu na biyu
shine,na
zamo mai cika alkawari.Abu na karshe shine na
zamo mai rike amana idan har an bani na
karba.Tace idan na rike wadannan abubuwa
dukkan
wani burina na duniya zan cikasu,kuma makiyana
tasirinsu kalilan ne akaina na dan lokaci
kankani.Yake wannan ma’abociyar kyawu na ban
al’ajabi ki yi mini tambayarki ni kuma na rantse
da
darajar uwata da ubana zan baki amsa iyakar
gaskiya.Koda jin wannan batu sai murna ta kama
jarumar tace,daga lokacin dana hadu daku kawo
iyanzu me kaji a zuciyarka dangane da addinina?
Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu
yayi
murmushi yace,ai tun a ranar farko da muka
kusan
hallaka a cikin fadar Boka Darbusa naga kin
baiyana
tsulum,kin cecemu naga irin gagarumin karfinki
na
ban al’ajabi na gane cewa al’amari ne wanda yafi
karfin tsafi ko na Aljan.Lallai karfi ne na wani
ubangiki da babu kamarsa.Koda Yarima Mangul
yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube
jarumar
tace,shin hakan yana nufin cewa zaka iya karbar
addinina.?Yarima Lubainu yace,kwarai kuwa ko a
yanzu ina muradin karbarsa,amma na fuskanci
cewa
sauran abokan tafiyar tawa basuyi imani dashi ba
kuma akwai alamin cewa in suka sami dama
zasu
iya yaudararmu su sace ALLON SIHIRI su
gudu.Koda
Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai farin
ciki
ya lullube bakuwar jarumar saboda ganin cewa
ko
ba komai yanzu ta sami nasarar jawo hankalin
mutum daya ga ADDININ GASKIYA.Jarumar ta
dubi
Yarima Lubainu cikin nutsuwa tace banaso
yan’uwanka su san cewa ka karbi addina a yanzu
saboda in hakan ta faru bazan sami damar jayo
nasu ra’ayin ba.Ba komai ne yasa na amince na
biku har izuwa kogin Bahar Imfal ba face saboda
inason na nunawa sarakanku na wannan nahiya
cewa nayi abinda su bazasu iya ba da taimakon
ubangijina,saboda hakan ne kadai zaisa
zuciyoyinsu
su karaya su bada gaskiya ga Addinin
nawa,saboda
na fuskanci cewa ba karamin aiki bane a rabasu
da
addininsu da suka gada tun iyaye da
kakanni.Koda
Jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu
yayi
ajiyar numfashi yace tabbas zancenki dutse ne
kuma
nima nayi miki alkawari zan taimaka miki iyakar
kokarina wajen ganin mun shawo kan jama’a sun
fuskanci gaskiya sun karbeta.
1 hr · PublicALLON-SIHIRI
Littafi na Biyar (5)
Part C
Mun shawo kan jama’a sun fuskanci gaskiya sun
karbeta.Ina da wata alfarama guda daya danake
so
na nema a wajenki.Cikin mamaki bakuwar
jarumar ta
dubi Yarima Lubainu tace,kai kuwa wacce irin
alfarma kake son nayi maka?Yarima Lubainu ya
numfasa yace,sarauniya Akisatul Sauwara ta
gaya
mini cewa kina da.ilmin fassarar mafarki,kuma
nayi
wani mafarki ne wanda ya razanani ainun wanda
nake son ki fassara mini shi.Nan take Yarima
Lubainu ya kwashe labarin mafarkinsa ya
zaiyana
mata.Koda jin labarin wannan mafarki na Yarima
Lubainu sai nan da nan fuskar bakuwar jarumar
ta
sauya izuwa alamun damuwa tayi shiru tana mai
sunkui da kanta kas.Al’amarin dayai matukar
dugunzuma hankalin Yarima Lubainu kenan ya
budi
baki da nufi yace wani abu,sai kawai suka hango
Dan wada Dazyan ya rugo izuwa garesu.Da
zuwansa
gaban bakuwar jaruma sai ya zube kasa cikin
girmamawa yace,ya shugabana tun dazu nayi
alwala
nake jiranka kazo muyi sallah amma sai naji shiru
ban ganka ba shi yasa na taho nema.Koda jin
haka
sai bakuwar jaruma ta mike tsaye suka nufi wani
waje mai rairayi suka tsaya.Dan wada Dazyan ya
tsaya a gaban bakon jarumi ya tayar da sallah ita
kuma ta tsaya a bayansa tana binsa.A daidai
wannan
lokaci ne Yarima Lubainu yaji kamar daga sama
an
kirawo sunansa.Yana waigowa bayansa yaga
ashe
sarauniya Akisatul Sauwara ce ta nufoshi
fuskarta
cike da annuri.Saida tazo daf dashi sannan ta
tsaya
suka fuskanci su Dazyan dakeyin sallah.Sarauniy
a
Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu
tace,nifa
wani abu yana daure min kai duk sa’adda Dazyan
da
maigidansa suka zo yin wannan ibada tasu sai
naga
Dazyan ya wuce kan gaba,shi kuma maigidan
nasa
ya koma baya.Ai kamata yayi ace maigidan nasa
ne
yake jagorantarsa a komai.Abu na biyu kuma
shine
a duk sa’adda na kalli idanun wannan bakon
jarumi
sai naga kamar mace ce ba namiji ba!zuciyata
zata
dade tanayi mini zargi da wasi wasi akan
hakan.Inda
ina da iko danaje na tuje rawanin dake kansa
munga
gaskiyar al’amari.Koda jin wannan batu sai
Yarima
Lubainu ya turbune fuskarsa ya dubi Sarauniya
Akisatul Sauwara cikin alamun fishi yace,kada ki
kuskura kiyi irin wannan tabargaza domin idan
muka
sami matsala da wannan bakon jarumi nine zanfi
kowa kwaruwa.Keda Sarki Darmanu kun fito ne
domin neman duniya,ni kuma neman lafiya ne ya
fito
dani.Koda jin wannan batu sai jikin sarauniya
akisatul Sauwara yayi sanyi tace,shike nan nayi
maka alkawari bazanyi duk wani abu dazai kawo
matsala a tsakaninmu da wannan bakon jarumi
ba.Shin yayi maka bayani kuwa akan mafarkinka?
Na
san cewa saboda hake ne ka biyoshi izuwa nan
bayan wannan dutse?Koda jin wannan tambaya
sai
Yarima Lubainu yai caraf yace,to banda abinki ta
yaya kurma zaiyi mini wani bayani na fahimta
alhali
ni ban iya zancen kurame ba,kuma babu Dazyan
a
lokacin danazo wajensa.Sarauniya Akisatul
Sauwara
ta jinjina kai ta dubi Yarima Lubainu cikin alamun
rashin yadda tace,amma kuma ai naga ka dade
anan
tare dashi,hirar me kuke tayi ne?Cikin fishi
Yarima
Lubainu ya mike tsaye yace,ai wannan tambaya
ce
ta rainin hankali to gaki nan gashi sai ki bari ya
gama ibadar tasa ki tambayeshi irin hirar da nayi
dashi.Kinsa ance waka a bakin mai ita ta fi
dadi.Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike zumbur
tasha gaban Yarima Lubainu tace,ka gafarceni
yakai
Lubainu tabbas nayi kuskure bisa wannan
tambaya
danayi maka.Kodajin haka sai Yarima Lubainu yai
shiru baice da ita komai ba,ya tafi ya barta tsaye
a
wajentana mai binsa da kallo sannan ta juya ta
kurawa bakon jarumi idanu wanda keyin sallah
tare
da Dazyan tace a cikin ranta.”Komai naka irin na
mata ne,ta yaya zuciyata zata gamsu cewa kai
namiji
ne?Tunda muka hadu dakai ban taba ganin
lokacin
daka cire kayan jikinka ba bare naga zahirin
jikinka,kaki ka bude fuskarka mu gani.Amma zan
kafa naci da zuba ido har sai naga gaskiyar
al’amari.Sarauniya Akisatul Sauwara na gama
aiyana
hakan a cikin ranta sai ta juya ta koma can inda
aka
yada zango.Bayan su bakuwar jaruma sun idar da
sallah sai suka dawo wajen su Yarima Lubainu
suka
zauna akaci abincin rana.Daga nan aka mike
kowa
ya kimtsa aka cigaba da tafiya.Ba’a sake
tsayawa a
ko ina ba saida lokacin sallar La’asar yayi nan
ma
Dazyan da bakon jarumi suka gabatar da sallar
aka
sake cigaba da tafiya ba sassauci.Da yammaci
ne
sakaliya suka shigo cikin wani daji mai katon
fili.Shidai wannan fili ana yi masa lakabi da
sunan
Dajin MUJALLUN HARBUN.Shidai wannan daji na
Mujallin Harbun daji ne wanda sama da shekari
dubu ba’ayin komai a cikinsa face yaki.Duk
kasashen dake nahiyar idan zasu yaki juna a
wannan fili suke haduwa a fafata.Da isowarsu
Sarauniya Akisatul Sauwara farkon wannan
fili,dama
bakon jarumi ne akan gaba,sai kawai sukaga
bakon
jarumi yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak,yana
mai
daga hannunsa sama alamar cewa kowa ya
tsaya.Nan take kuwa Yarima Lubainu,Dazyan,
Sarau­
niya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu sukabi
umarnin bakon jarumi kowa yaja linzamin dokinsa
suka tsaya cak,gaba dayansu,sai suka kama kalle
kalle suna duban gabas da yamma kudu da
arewa
amma sai sukaji shiru basuga komai ba kuma
basuji
motsin komai ba.Kawai sar Sarki Darmanu ya
bushe
da dariya ya dubi bakon Jarumi ya sake bushewa
da
dariya tace,yazaka tsayar damu haka kawai
muna
cikintafiya?To idan ma kana zargin akwai wani
mugun abu ne anan babu komai face tarin
kwarangwal na bil’adama saboda wannan wuri fili
ne
na yaki asali kimanin shekaru dubu baya.Koda jin
wannan batu sai bakon jarumi ya dubi Dazyan
yayi
masa magana a cikin yaren kurmanci.Dazyan ya
dubi sarki Darmanu yace shugabana yace na
gaya maka cewa,lallai akwai alamun wani mugun
abun daya buya a cikin wannan duhowoyi ko a
sama kan bishiyoyi saboda haka kowa ya zauna a
cikin shirin yaki.Gama fadin hakan keda wuya sai
bakon jarumi ya daga garkuwarsa sama kuma ya
zare takobinsa.Nan take kowa ma yayi koyi dashi
suka sakarwa dawakansu linzami suka cigaba da
tafiya suna masu ratsawa ta cikin filin Mujallun
Harbun suna waife waige don ganin ta inda za’a
fara
kawo musu hari.Saida suka iso tsakiyar filin
sannan
sukaga kasa na tsagewa da darewa.Kafin suyi
wani
yunkuri sai sukaga wadansu dodanni gabza gabza
suna fasowa ta cikin karkashin kasa suna dira
kan
turba rike da MUGGAN MAKAMAI su da yawa ba
adadi.Tun da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo
duniya bata taba ganin halitta mai tsananin muni
da
ban tsoro kamar wadannan dodanni ba.Saboda
tsawonsi kuwa saisu Yarima Lubainu da
dawakansu
suka zamo ‘yan kananu a gabansu bayan
dodannin
sun gama yi musu KAWANYA.Gurnanin da
dodannin
keyi ne ya fara firgita dukkan tsuntsaye da
dabbobin
dajin suka kama canja sheka.In banda bakon
jarumi
da dan wada Dazyan babu wanda jikinsa bai
kama
tsuma ba saboda razana sakamakon ganin
wadannan dodanni.Kawai sai bakon jarumi ya
mayar
da takobinsa cikin kufe,shima Dazyan sai ya
mayar
da tasa takobin ya dubi Sarauniya Akisatul
Sauwara,Sarki Darmanu da Yarima Lubainu
yace,maigidana yace yanzu sai ku yaki
wadannan
dodanni da karfin damtsenku gami dana
sihirinku,kuma ku hada da neman taimakon
ababan
bautarku domin ya gani ko zaku iya kubuta.Koda
jin
wannan batu sai tsoro ya kama su Sarauniya
Akisatul Sauwara.Sarki Darmanu ya dubi dan
wada
Dazyan cikin alamun firgici yace,saboda me
shugabanka zaiyi mana haka alhalin ko ba’a
gwada
ba linzami yafi karfin bakin kasa?Dan wada
Dazyan
yayi murmushi yace,ai idan baka manta ba haka
ka’idar take,kafin mu fara wannan tafiya tare
daku
saida muka yi sharadin cewa duk masifae data
taso
kune zaku fara tunkararta da dukkan karfin
damtsenku da karfin sihirinku,saidai idan mun ga
kun gaza saimu kawo muku agaji.Koda gami
fadin
hakan sai bakon jarumi da Dazyan suka sauko
daga
kan dawakansu suka zauna a kasa dirshen suka
rintse idanuwansu suka kama karanta wata
addu’a ta
musamman.Faruwar hakan keda wuya sai suka
bace
bat daga filin tamkar basu taba wanzuwa ba
awajen.Al’amarin daya sake firgita su sarauniya
Akisatul Sauwara kenan kuma ya girgiza
hankalinsu.Su kuwa dodannin nan da suka ga
mutum biyu sun bace musu da gani sai suka
fusata
sukayo caa!izuwa kansu Yarima Lubainu suna
masu
yin wani irin ruri mai tsananin firgitarwa.Koda
ganin
haka sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi
Sarki
Darmanu da Yarima Lubainu tace bamu da wani
zabi wanda yafi mu kare kanmu muyi iya
kokarinmu..Kafin ta gama rufe bakinta tuni wani
dodo ya dako tsalle ya dira a gabanta ya kawo
mata
wawan sara da wata irin kakakifar adda mai cako
cakon tsini kamar zarto.Cikin bakin zafin nama ta
sunkuya addar ta sari iska amma saita fille kan
dokin
sarki Darmanu fit,dokin da sarki Darmanu suka
zube
kasa.Nanfa wuri ya hargitse aka rincabe da
mugun
azababben yaki mai tsananin muni da tayar da
hankali.Ai kuwa ana fara wannan yaki su
sarauniya
Akisatul Sauwara suka raina kansu suka gane
cewa
yau sun gamu da gamonsu,domin dai wadannan
dodanni basa jin SARA DA SUKA da zarar an
saresu
saidai kaji kara kal!tamkar karfe da karfe ne suka
hadu,kuma a fuska ne kadai suke jin naushi,kuma
saboda zafin namansu su sarauniya Akisatul
Sauwara basa iya naushin nasu ko saransu a
fuskar.In badin ma suma suna da nasu zafin
naman
ba da tuni dodannin sun hallakasu farat
daya.Haka
dai su Yarima Lubainu suka cigaba da yin iya
kokarinsu waje kare kansu gami da maida
martani.koda aka shafe sa’a guda anayin wannan
BAKIN GUMURZU sai yaki ya sauya salo,ya
zamana
cewa su Yarima Lubainu sun fara gajiya,ai kuwa
a
sannan ne dodannin suka fara samun nasarar
gabza
musu naushi suka rinka hada musu JINI DA
MAJINA
har ma ka yanki kowannensu sau daidai jini yayi
tsartuwa a jikinsu.Su ukun suka kurma ihu a
lokaci
guda sakamakon jin tsananin zafi da zogi,suka
durkushe a kasa yayin da jiri ya kwashesu.Ai
kuwa
sai dodannin sukai caaa!izuwa kansu da nufi su
dasa musu wawa su daddatsa su.Kwatsam ba
zato
ba tsammani sai su sarauniya Akisatul Sauwara
sukaga bakon jarumi da danwada Dazyan sun
faso
karkashin kasa a tsakiyar dodannin suna masu
kwalla KABBARA sun tarwatsasu da karfin tsiya
kuma
suka hausu da SARA DA SUKA ba
sassauci.Nanfa
jinin dodannin ya kama fallatsi a sama sassan
jikinsu ya rinka shawagi a sararin sama yana
zubowa kasa suna ruri da kururuwa suna zubewa
kasa mattatu.Koda su Sarauniya Akisatul
Sauwara
suka ga dan wada Dazyan yana yaki da
wadannan
dodanni cikin gagarumar jarumtaka ta ban
al’ajabi
sai suka sake kamuwa da tsananin
mamakinsu,saboda su dai a saninsu rago ne
bashi
da wata jarumta tunda a baya ma da suka shuga
rintsin yaki kan bishiya ya haye ya buya saida
aka
gama yakin sannan ya sauko.Haka dai bakon
jarumi
da dan wada Dazyan suka cigaba da ragargazar
dodannin nan suna cigaba da kwallah Kabbara
har
saida suka karar dasu gaba dayansu,ya zamana
cewa babu dayansu daya tsira da rayuwarsa.A
sannan ne Dazyan ya ruga wajen su Yarima
Lubaimu ya kama duba raunikan dake
jikinsu.Sa’ar
da sukayi ma shine babu wanda rauninsa yayi
zurfi
saidai darewa kawai da yayi.Nan da nan cikin
gaggawa dan wada Dazyan ya dinke musu
raunikan
aka saka musu magani.Bakon jarumi ya taho
garesu
ya bisu da kallo daya bayan daya yana maiyi
musu
sannu da hannu.Koda yazo kan sarauniya
Akisatul
Sauwara da nufin yayi mata sannu sai ta
murtuke
fuska ta daka mata
harara kuma ta tari numfashinsa ta dubeshi cikin
fishi tace,yanzu a haka kake nufin zamu cigaba
da
wannan tafiya duk sa’adda muka hadu da masifa
saidai ku barmu da ita?Ai kafin mu isa ma can
duk
jikinmu ya lalace da raunika kuma raunikan ma
zasu
iya zama sanadin ajalinmu.Koda jin wannan batu
sai
shima bakon jarumi ya fusata ya dubi Dazyan
yayi
masa zancen kurame.Dazyan ya dubi sarauniya
Akisatul Sauwara yace,idan bakwason jikinku ya
lalace ko kuma ku rasa rayuwarku to ku karbi
Addininmu.Idan kuka karbeshi munyi muku
alkawarin zamu roki ubangijinmu akan ya biya
muk
dukkan bukatunku muddin bukatun bazasu cutar
da
wani ba!Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai
jikin
sarauniya Akisatul Sauwara yayi sanyi sai kuma
kunya ta kamata ta rasa abinda zatace.Shi kuwa
Yarima Lubainu kansa na sunkuye ko kallon
bakon
jarumi baiyi ba.Sarki Darmanu kuwa ya bata rai
sai
muzurai yakeyi kawai.Nan dai aka samu aka huta
har izuwa lokaci mai dan tsawo,sannan aka kafa
sansani aka kwanta domin a kwana a wajen in
yaso
gobe da safe a cigaba da tafiya.Har dare ya raba
Yarima Lubainu bai iya yin barci ba a cikin
tantinsa
shi kadai.Gashi dai ya kishingida amma zuciyarsa
cike take da tunani da wasi wasi gami da
fargaba.Yana cikin wannan hali ne yaga bakon
jarumi tsulum ya shigo cikin tantin nasa.Cikin
kaduwa da alamun tsananin mamaki Yarima
Lubainu
ya mike tsaye zumbur ya kurawa bakon jarumi
idanu
amma alamomin tsoro duk sun bayyana akan
fuskarsa.Koda gin haka sai bakuwar jaruma ta
dubeshi tace,kwantar da hankalinka yakai Yarima
Lubainu,kayi sani cewa babu wanda zai ganmu
ko
yaji zancen da zamuyi a yanzu saboda nayi wata
addu’a barcin kowa yayi nauyi hatta na Dazyan
kuwa.Ba komai ne yasa ba kowa maka ziyara a
cikin wannan dare ba face saboda na fahimci
kana
cikin damuwa da tashin hankali wadanda bazasu
barka kayi barci ba.Ta gama fadin hakan sai ta
cire
rawaninta ta ajiye gefe daya kuma ta zauna nesa
kadan dashi inda suka fuskanci juna.Koda yai
arba
da kyakyawar fuskarta sai yaji cewa inda zai
rinka
ganin wannan fuska to bazai sake yin bakin ciki
ba a
rayuwarsa har abada,kuma yunwa da kishirwa
bazasu taba damunsa ba.Saboda kallonta ne zai
hanashi jinsu ya sanyashi cikin farinciki mara
misaltuwa.Har bakuwar jaruma ta budi baki zata
ce
wani abu sai Yarima Lubainu ya tari numfashinta
yace,kafin kice komai ina rokonki da girman
ubangijin musulunci daki fara sanar dani
sunanki.Koda jin haka sai bakuwar Jarumar tayi
murmushi tace,gaskiya banso na sanar dakai
sunana ba yanzu sai a karshen tafiyarmu,a
lokacin
dazan bude fuskata da jikina kowa ya ganni,to
amma
tunda ka hadani da girman Allah dole ne na
sanar
dakai.Da farko sunana SUHAILAT IBINI
AFUWAN,kuma na fito ne daga can wata nahiya
dabam a wata kasa da ake kira DARUL
ILMUN.Yanzu
sai ka nutsu ka saurari fassarar mafarkinka.A
takaice
wannan mafarki naka yanayi maka nuni da cewar
matarka Yazarina ta baro kasarku ta fito
nemanka
amma kuma ta fada hannun wani babban abokin
gabarka wanda ke kokarin rabaka da ita.Saidai
mafarkin bashi da karshe bare musan halin data
shiga,walau abokin gabar taka ya kamata ko
kuma
ta tsira daga sharrinsa.Koda Suhailat tazo nan a
zancensa sai hankalin Yarima Lubainu ya
dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya rasa
abinda
ke masa dadi a duniya,ya mike tsaye zumbur da
nufin ya ruga waje ya hau dokinsa ya tafi neman
Yazarina,amma sai Sulailat tayi wuf ta ruko
hannunsa a karon farko da hannunta ya fara taba
wani ‘da namiji ba muharramin ta ba.Cikin sauri
ta
saki hannun nasa tana mai istigifari a cikin
zuciyarta
sannan ta sha gaban Yarima Lubainu tace,ka
kwantar da hankalinka yakai Angon Yazarina,kayi
sani cewa da izinin ubangijina babu abinda zai
sami
matarka domin zan cigaba da rokonsa akan ya
bata
kariya kuma ya kareta daga sharrin wannan
makiyi
naka.A yau din nan zanyi istihara domin na ga
halin
da take ciki,kuma kafin mu cigaba da tafiya zan
sanar dakai duk halin da take ciki.Abinda nakeso
dakai kawai shine ka cigaba da rike alkawari na
boye sirrina ya zamo amana a tsakaninmu.Koda
gama fadin hakan sai Suhailta ta juya ta fice
daga
cikin tantin sai Lubainu ya kira sunanta ta waigo
ta
dubeshi cikin mamaki tace,mene ne?Nan fa
Yarima
Lubainu ya rasa abinda zaice da ita,dama bashi
da
abin fadar,kawai ji yayi baison rabu da ganin
fuskarta gami dajin muryarta.Ashe Suhailat ta
fahimci hakan,sai kawai ta dubeshi tayi masa
murmushi mai dauke da alamar tambaya(?)tace
saida safe.Take ta sake juyawa ta fice daga
cikin
tantin ba tare data sake waigowa ba.Kashe gari
kuwa da sassafe jaruma Suhailat ta fito daga
cikin
tantinta ta iske Dazyan kwance a filin Allah bisa
shimfida ya lulluba da bargo.Kawai sai tasa
hannunta guda ta yaye bargon,take Dazyan ya
farka
yai firgigit.Koda yaga itace sai ya dukar da
kansa
kasa ya gaisheta cikin girmamawa.Kawai sai
Jaruma
Suhailat ta sunkuyo tayi masa rada a kunne
sannan
ta ruga izuwa cikin jeji domin farauto naman
daza’ayi kalacin safe.Tafiyarta keda wuya sai
Dazyan
ya zaga bayan tantin Yarima Lubainu yayi kamar
bawali zaije yayi domin a lokacin tuni sarauniya
Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantinta ta
tsaya
tana mika da kallon yanayin dajin,kuma taga
sa’adda Suhailat ta dashi Dazyan daga
barci.Koda
Dazyan ya zagaya bayan Tantin Yarima Lubainu
sai
ya kira sunansa a cikin karamar murya mai kama
da
rada.Yarima Lubainu ya amsa kiran,shi kuma
yace
dashi shugabata tace kayi sauri ka sameta a daji
bangaren gabas domin ku tattauna ta tafi
farauta.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu
ya
mike tsaye zumbur,dama a tube yake ko riga
babu a
jikinsa sai wani gajeren wando.ALLON-SIHIRI,
Littafi na Biyar (5)
Part D
Dama a tube yake ko riga babu a jikinsa sai wani
gajeren wando.Cikin hanzari ya sanya kayansa
ya
dauki KWARI DA BAKA sannan ya leko da kansa
waje kadan sai ya gano Sarauniya Akisatul
Sauwara
a tsaye a bakin tantinta tana yin asuwaki.Cikin
hanzari ya maida kansa cikin tantin don kada ta
hangoshi a lokacin da zuciyarsa ta cika da
damuwa
saboda yasan cewa indai ta ganshi zai tafi daji
farauta cewa zatayi saita bishi.Jim kadan sai
Yarima
Lubainu ya sake lekowa waje,saiya hango
Sarauniya
Akisatul Sauwara ta bar kofar tantin nata ta nufi
inda
tanti sarki Darmanu yake.Cikin hanzari yayi
amfani
da wannan dama ya fice daga cikin tantin nasa
yana
sanda da labiya ya nausa cikin daji ba tare da an
ganshi ba.Da shigar Yarima Lubainu cikin daji ya
nausa gabas yana duban sawun Jaruma
Suhailat.Ai
kuwa bai dade da fara duba sawun Suhailat ba
ya
ganshi don haka sai ya cigaba da binsa da sauri
har
dayayi tafiya mai dan tsawo.Kwatsam sai ya
hango
Jaruma Suhailat daga nesa kadan ta ratayo wata
matacciyar barewa a kafadarta ta tunkaro inda
yake.Tun daga nesa suka kurawa juna idanu
suna
murmushi har ta iso daf dashi.Kawai sai ta
dubeshi
tace,zo mu cigaba da tafiya muna hirar mu don
kada
abokan tafiya su ga mun dade bamu koma ba
suyi
zargin wani abu.Ba tare da wata gardama ba
Yarima
Lubainu ya jera da ita suka cigaba da tafiya don
komawa can masaukin nasu.Suna cikin tafiyar ne
ta
dubeshi tace,yakai Yarima Lubainu,kamar yadda
na
yimaka alkawari jiya nayi istahara kafin na
kwanta
barci kuma ubangijina ya nuna mini halin da
matarka ke ciki tun kafin ma ta baro kasarku
Zamrul.Shin kasan wani mayakinku mai suna
BARDE
RUHAISU?Koda jin wannan tambaya sai Yarima
Lubainu ya dubi Jaruma Suhailat cikin tsananin
mamaki yace,kwarai kuwa na sanshi,abokina ne
na
amana,kuma na daukeshi tamkar dan uwa na
jini,domin a hannun mahaifina ya girma.Ko na
takaice miki labarin ma mahaifina yana kaunarsa
fiye
da yadda yake kaunata ni da ya haifa a
cikinsa.Koda
jin haka sai Suhailat ta jinjina kai sannan
tace,hakika
Barde Ruhaisu dan halak ne kuma ya cancanci
mahaifinka ya so shi fiye da kai,saboda mutum
ne
mai karfin amana kuma yana kaunarku kai da
mahaifinka fiye da yadda yake son kansa.In
badin
Barde Ruhaisu bada tuni yanzu makiyinka kuma
abokinka Yarima Mangul ya mallaki Yazarina.Nan
take Suhailat ta kwashe labarin duk abinda ya
faru
tsakanin Yazarina da Barde Ruhaisu tun daga
lokacin da suka baro Birnin Zamrul tare da
dakaru
dari kawo izuwa sa’adda Yarima Mangul ya kawo
musu harin bazato suka fafata kazamin yaki
dashi,inda a karshe suka ruga izuwa cikin daji
suka
hau kan wannan dogon tsauni mai mugun
nisa,Yarima Mangul ya bisu har izuwa karshensa
suka fado kasan tsaunin don su tsira daga
sharrin
Mangul.Koda Suhailat tazo nan a labarinta sai ta
dubi Yarima Lubainu tace,wannan shine iyakar
abinda ubangijina ya nuna mini a mafarkina don
haka daga lokacin da Yazarina da Barde Ruhaisu
suka fado kasan wannan tsauni bansan abinda
ya
samesu ba.Wata kila sun hallaka wata kila kuma
suna nan a raye,amma dai kayi hakuri izuwa wani
daren zan sake yin istahara domin naga halin da
suke ciki.Koda Suhailat tazo nan a zancenta sai
Hawaye ya zubowa Yarima Lubainu yace,yanzu
ni
dame zan sakawa barde Ruhaisu bisa wannan
gagarumin taimako dayayi mini?Ki dubi yadda ya
sallama rayuwarsa don kare ta matata.Koda jin
wannan tambaya sai Suhailat tayi murmushi
tace,tabbas akwai abinda zaka iya saka masa
dashi
anan gaba,amma fa sai ka danne
zuciyarka,domin
wani abu ne mai daraja a wajenka zai bukaci ka
sallama masa shi..Koda yake amma a wannan
lokacin kaima ka sami wanda ya ninka wancan
din
daraja.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu
ya
dimauce ya kasa fahimtar abinda Suhailat take
nufi,don haka sai ya dubeta cikin alamun
matukar
mamaki yace,wane abu ne haka mai daraja a
wajena
wanda Ruhaisu zai bukaceshi kuma nima zan
sami
wanda yafishi daraja?Sa’adda Suhailat taji
wannan
tambaya sai ta hade fuska tace kasan komai
yana da
lokacinsa to ka yi hakuri lokacinka na sanin
wannan
al’amari baiyi ba.Idan kuwa ka matsa har ka sani
din to tabbas zakayi nadamar sanin!!!Tana gama
fadin hakan ne suka jiyo sautin haduwar takubba
daga bangaren wajen da suka yada zango.Cikin
firgici suka dubi junansu sannan suka falfala da
azababben gudu suka nufi wajen.Ai kuwa suna
isowa inda suka yada sansani sai suka hango
sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da
dan
wada Dazyan a tsakiyar wasu narka narkan
SAMUDAWAN MARIDAI kimanin su saba’in suna
yaki
dasu.Kowanne maridi guda tsawonsa yakai kamu
ashirin da biyar kuma fadin kirjinsa ya kai kamu
ashirin.Suna rike da manyan sungumai guda
bibbiyu.Sungumin dake hannunsu na dama da
dutse
akayi shi,don dunkulalle ne mai kauri da
nauyi,duk
abinda suka rotsawa shi sai ya dagargaje.Daya
sungumin dake hannunsu na hagu da zallan
kashin
wata katuwar dabbar daji akayi shi mai KAIFI DA
TSININ TSIYA!Komai kaurin bishiya idan suka
caketa
dashi sai ya hudata ya bullo ta karshenta.Su dai
wadannan maridai sun kasance suna da tarin
kwanji
mai girman gaske gami da jijiyoyi tamkar jikin
nasu
ma na dutse ne bana tsoka ba.Ita kanta Jaruma
Suhailta da ta jango wadannan samudawan
maridai
daga nesa saida ta firgita ta tabbatar da cewa
karo
dasu ba wasa bane,dole ne a sha BAKIN
GUMURZU
da wahalar gaske,don haka tun kafin ma su iso
wajen su kawowa su Sarauniya Akisatul Sauwara
dauki tuni maridan sun galabaitar dasu,sun kaisu
kasa sun kasa koda mikewa tsaye saboda
kowannensu ya sami rauni a jikinsa sama da
guda
uka sai zubar da jini suke,jiri na dibarsu.
Koda ganin haka sai Suhailat ta dubi Yarima
Lubainu
ta gargadeshi da kada ya kuskura yace zai tayata
yakar wadannan samudawan maridaiTana gama
fadin
hakan sai ta kara kardin gudun nata tana mai
neman
taimakon Allah a cikin zuciyarta.Ai kuwa sai
karfin
gudun nata ya zama tamkar na TAURARUWA MAI
WUTSIYA!!!Nan da nan ta baiwa Yarima Lubainu
tazara mai yawan gaske.Saura kiris samudawan
maridansu hallakasu Sarauniya Akisatul Sauwara
a
lokacin da suka daga sungumayen hannayensu
zasu
mammaka musu sai kawai Suhailat ta daka tsalle
sama tamkar an harbota daga cikin BAKA ta dira
a
tsakiyar samudawan maridan ta tarwatsasu da
karfin
naushin kafafunta biyu,sannan suka sake taso
mata
aka ruguntsume da sabon masifaffen yaki..
WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN YAKI
TSAKANIN
JARUMA SUHAILAT DA WADANNAN
SAMUDAWAN
MARIDAI?
A WANE HALI YAZARINA DA BARDE RUHAISU
SUKE?
SHIN YARIMA MANGUK ZAI SAKE TARFA SU
BARDE
RUHAIUS HAR YA MALLAKI YAZARINA?
SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIKA BURINSA NA
KASHE MAHAIFINSA DON HAWA KARAGAR
MULKIN
BIRNINSU?
WANE ABU NE MAI DARAJA WANDA BARDE
RUHAISU
ZAI NEMA NAN GABA A WAJEN YARIMA
LUBAINU?
YAUSHE NE YARIMA LUBAINU DA YAZARINA
ZASU
SAKE SADUWA KUMA YAUSHE NE ZA’A ISA
KOGIN
BAHAR IMFAL?
Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI(ALLON-SI
HIRI-6)don
jin cigaban wannan kayataccen labari.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button