FATIMA XARAH Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

FATIMA XARAH Complete Hausa Novel

“Allah dr nagaji motsa jikin yayi haka. Zarace take mgnr gamida tumfarar kasar wana bishiya taje tazauna’ “shima karasawa yayi yazauna kusa da ita. Kedai Allah yayiki raguwa kawai bakison motsa jiki. Haba nayi kokari ai….bawani kokarinda kikayi’ kwatakwata minti nawa kikayi……zaro idanu tayi tana masa kallon mamaki mintima zakace ba hour ba? Shima yazaro nashi idanun yana kwaikwayan yanda tayi mgnr. Dukkansu suka kyalkyale da daria. Daidai lkcnda mus’af yakaraso inda suke.

Ranshi idan yayi dubu yabaci amma haka yadanne. Yayi musu sallama. Afirgice zarah tadago suna hada ido takawar dakanta. “Abdul ne yayi jarumtar amsa mishi sallamar. Cikin sakin fuska suka gaisa har yana tambayarshi lfyr amarya. “Bbu yabo bbu fallasa ya amsa da tana lfy.

“Gyara tsayuwarshi yayi ssai yana kallon zarah dahar lkcn bata ko kalli inda yakeba. Inason yin mgn dakene fatima… “Jitayi tamkarda anzuba mata garwashi akahon zuciyarta. Cikin bqcin rai tamike dakyar tanufi cikin gida.
“Dasauri yasha gabanta fatima kitsaya kiji mana abunda zanfada. Har lkcn banza tayi mishi tacigaba da tafiyarta. “Ganin batada niyar tsayuwa yasa yadamko hannunta.
Duk akan idon abdul suke wannan rigimar yanzukam anxo inda bazai jureba.
Takawa yayi yakarasa indasuke zarah tanakan kiciniyar kwace kanta amma takasa. “Idanu yazubawa mus’af cikeda tambaya hakan yasa mus’af yasaki hanunta sukashiga kallon kallo. Itakuwa dagudu tashiga cikin gida tafada kan mom tana rusar kuka.

“Idan ransu yayi dubu toh yakai kwaleluwa wajen baci. Babu yakamar mus’af dahar karkarwa yakeyi shikuwa abdul idanunsa gaba daya sunsauya kala sunyi jajir jijiyoyin kanshi duk suntashi.
Mus’af ne yadunkule hannu zekaimishi gula mommy tayi saurin shiga tsakaninsu.

Wani wawan kallo tayi mishi kafin takejanye hanun abdul sukayi ciki sukabar mus’af awajen.
“Baze yuwuba wllh baze yuwuba toh shi wannan din meye gaminshi da zarah? Kodai shima wai yanasontane no! Noooooo it can’t be! Wllh karyane. Haka yakaraci surutanshi shikadai yashige motarsa yabar gidan…

“Toh dota banda abunki miye abun kukan? Yatafi ai shikenan ko? Mother miye yakawoshi don Allah karkibari yasake shiga rayuwata natsaneshi shima, tunda har yakasa daukar kaddara i hate him mother….is ok sweetheart ya isa haka kinrabudashi kenan ai har abada. “Tadago kanta tana kallon mum dinnata dagaske mommy. Dagaske dota kikwantarda hankalinkk kinji? Tashi maza kidauko muku abincinku keda abdul. “Se’a lkcn takalli indayake har tamanta dashima. Murmushi yqyi mata zatamike yarugata…..mommy kyace zarah takawo mana abinci bayan kinsan tafi dutsen uhudu nauyi..yakarasa mgnr sunayimata daria itakuwa tazo har wuya shikam bemasan tanayiba dan haryatafi kitchen. Biyoshi tayi tatsaya abakin kofa kameda kugu tahada gabas da yamma.
Jiyowa yayi da flask da plate& spoons ahanunshi yaganta yanda taci boom kamar zatafashe aikuwa yadunga kyakyata daria kamar ba dr abdul ba. Ganin yanda yake dariyar yasa itama tasaki fuskarta tayi murmushi kawai takarbi flask din hanunshi shikuma yadauko drinks sukafito a kitchen din zuwa dinning area.

Dakanshi yayi servng nasu. Sunacin abincinsu hankali kwance suna fira idan kagansu gwanin sha’awa kai kace yaya da kanwane.
“Bayan sun kammala sukatattare kayayyakin kowanne yakoma mazauninshi. Kafin yayi sallamawa mom zarah tayi mishi rakiya har jikin motarshi kamar karsurabu kowannensu yakeji….

Zulfer zulfer zulfer isarshi gidan kenan yaketa gwalla mata kira kamar zetsaga gidan. Bbu inda bedubaba batanan don haka yazarce side din hjy murjanat.
“Banko kofar dayayi ita kanta uwarshi sedata razana…haba son babu sallama kashigo da nutsuwa mana. “ina yarinyarnan take? Wace yarinya kuma? Zulfer datake kitchen tun shigowarshi takejin hayaniyarsu tadada mannewa abayan kofa, tana zazzare ido. Yaukuma dame yazo oho.
Mother wai kekike goya mata bayako? Kai son banison rashin hankali wace yarinya ka aiko? Wacce kuwa banda zulpher….mitayi maka? Banison wannan halin banzan nadukafa inagaya maka kakiyayeni. “Ok dama kubiyun kunhada bakine kenan to shikenan ninedai ina mijinnata ko sedai tabar kwanan dakinta takaura nan kenan…..”son danifa kake mgn…ohonku kuma. Yafice adakin kamar mayunwacin zaki.

Yana fita zulfer tafito fuskarta jikeda hawaye. Nashiga uku mother wllh dukana zeyi dan Allah ki kirashi kibashi hkr.
“Bazemiki komaiba tashi maza kibishi kibashi hkr…wllh mommzebigenine????
“Nace kije mana keba mace bace kidaure kawai kitafi babu abunda zefaru.

“Adari dari take shiga ahankali taturo kofar taduba parlon kaf bayinan kafin tasauke ajiyar zucia. “Seda tagama zamanta harda kwanciya akan 3seater taji anshako wuyarta. Yashiga fella mata mari tana ihu babu wanda yake iya jiyosu yamata shegen duka yadaureta yafita yakulle gidan abunshi…..????????????????

*********
“Yau yakasance ranar jumma’a aranar zarah ta tashi da matsanancin ciwon mara ssai nakuda gadan-gadan yataso mata. Gashi rabonda abdul yazo gidan kwana uku kenan ko wayama basuyiba. Mommy kuma tatafi kasuwa.
Haka tayita aikin nukurkuso daga bisani tasamu tararrafa zuwa cikin daki tadauko wayarta dialing num. din shamsiya tafarayi coz itakadaice takeson sanarwa batason tatashi hankalin mom dinta ko dr abdul.
“Amma kashsh layin babu kati aciki…..

Abdul neh yake kwance gaba daya kwanakin bayijin dadi ssai. Shine musabbabin dayasa beje gidansu zarah ba kwana biyu dasuka wuce. Dasauri yamike daga kwanciyar dayakeyi sakamakon bugawarda kirjinshi yake mishi. “Ambaton Allah yashigayi musamman dayatuna watan zarah yayi nisa yakamata kullun yakasance yana kula da ita. “Wayarshi yadauka yadanna kiran dr sani…..”helo sani..yes sir!….nace wayene me duba zarah acikin nurses dinnan?.. Uhmm ehhh Aisha ce ammadai tace this week akesakaran haihuwar….bebari yakarasaba yakashe wayar.
“Car key dinshi yadauka yazura jallabiya awaje parlor yatararda mommy dinshi agurguje yayi mata sallama yabar gidan. “Drivng yayi bilhakki dagaskia don ko bintakan drvr beyiba.
Da isarshi yashiga gidan aikuwa tundaga kofa yakejiyo salatinta beyi kasa a guiwaba yasunkuceta se mota yadireta yafinciki motar sukayi hsptl……

 

Bintufannah????
[16:52, 3/1/2017] BintuFannah????: [14:35, 12/25/2016] BintuFannah????: *FATIMA XHARAH* 55

“Tun ahanyarsu taxuwa hsptl yake kiran dr sani. “Alo sani! Na’am sir….maza-maza kushirya nurses banison wasa kushirya komai intact gamunanda zarah tawahala kuyi maza. Bejira jin tabakinsaba yayi hanging wayar.

“Juyawa yayi yakalli zarah yanda gaba daya tafita ahayyacinta. Nantake yakara speed. “Minti biyar suka kara suka iso hsptl din.
Yana yin perking shikanshi begama fitowaba nurses sukacirota akan gadon turawa namarasa lfy sukasata kafin sukayi cikin labour room da ita.
“Har cikin room din abdul yashiga hankalinshi duk yadada tashi ganin yanda numfashinta yana kaikawo. “Hannu tadaga tanayi mishi alamar yazo. Karasawa yayi cikin room din har kwalla yafara zubo mishi. Kai tashiga girgiza mishi alamar yayi shiru taruke hannunshi daya tanakallon fuskarshi ahankali yakekai dayan hanunshi kan sumarta yakawar da gashindayarufe mata fuska.
“I’m so sorry my dear take heart plxx sister Allah zesaukeki lfy…..dr muna bukatar waje daya daga cikin midwife din take mgn. “Ok yafada yana kallon zarah da itama shi take kallo ahankali idanunta suke rufewa.
‘Kagani ko, u see ur life! Dan Allah kafice idan kanason rayuwarta. Komotsawa yakasayi awajen tamkarda gunki yazama yana kallonta.
Dr sanine yajanyeshi zuwa waje kafin sukasamu damar kula da’ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button