HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kammala cin abinci kowa ya nufi part dinshi, jameel ya dauki matarsa suka tafi gidansu da yake basu da nisa da gidan iyayen nashi.

[3:19PM, 7/11/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣3⃣

 

Fatu bata farka ba sai bayan la’asar, kallon agogo tayi ta saka salati ta shige bathroom. Wanka tayo da alwala ta bada farali kana tasa kaya hade da light make up. Palour ta fito taji shiru tace ba dai har sun kammala ba. Kitchen ta shiga ta samu dija na aikin girkin dare ta tsaya tambayanta hajia dasu jameel, dija tace “ai tun dazu su lubna suka tafi, mahmud kuma inaga ya shiga cikin gari. Fatu tace “mmn isya yanda kika san an mini duka haka nake jin jikina dazu, ina shiga daki kawai na kwanta in huta ashe bacci ya kwashe ni” Dija tace “kinyi kokari ai” fita daga kitchen din tayi dakin hajia, sai da ta knockin tayi sallama aka amsa ta shiga. Hajia ta samu zaune a bakin gado tana waya da aunty sadiya (maman sultan). Kujera na dressin mirrow taja ta zauna Sai da hajia tayi hangin fatu tace “mummy ya gajiyan yau? Hajia tayi mrmshi tace “ai ke za’a cewa ya gajiyan yau, kikayi ta bacci abunki” daria fatu tayi tace “Allah mummy nima bansan tym din da bacci ya debe ni ba, kuma farouq ma ko yazo ya tasheni” mummy tace “ni nace ya barki ki huta. Ki dauki wancan jakan ki kaiwa hajia sadia tsaraban su ne, naki kuma sai kin dawo ki gani” fatu tace “tooo” daukan jakan tayi ta fito, room dinta ta shiga ta dauko hijabi iya gwuiwa tasa ta fito.

A palour ta tarar da qanwarsa Amrah tana danne danne a waya, zata kai 13 yrs, “anty fateema oyoyo” amrah tace da fatu yayinda take zuwa gurinta ta karbi ledan hannunta suka zauna, fatu tace “washhh, Ina mammi” amrah tace “tana dakinta, bari in kirata” bata jima da shiga ba suka fito tare, hajia sadia na cewa “amrah bi kitchen ki daukowa fateema ruwa” zama tayi akan kujera fuskarta dauke da murmushi tace “sannunki da zuwa fateeman mummy” murmushin fatu ma takeyi amma fuskarta a qasa, ta zamo daga kan kujeran ta gaisheta kana ta koma ta zauna. “Mummy ne tace in kawo muku tsarabanku” ta fada yayin da take miqawa hajia ledan. Amrah ta kawo wa fatu ruwa ta tsiyaya mata ta koma kusa da hajia sadia ta zauna tana cewa “mammi ina nawa” hajia sadia tace “gashi nan, kinga na kowa Anyi wrapping dinshi da suna” ta karba tace “anty fateema kice nagode sosai” fatu tace “to amrah” amrah ta wuce dakinta don ganin tsarabanta. Fatu ta miqe tace “mammi sai anjima” hajia sadia tace “daga zuwa? Ko ruwa baki sha ba” fatu tace “mammi na sha” sultan ne ya shigo a dai dai inda hajia sadia ke cewa “ki gaishe min da mummyn naki” sultan yace “muje in raka ki” saurin dago da kanta tayi ganin ita yake kallo yasa ta fara tafiya tana cewa “to mammi” hajia sadia kuma ta koma ciki tana jindadi, don tun ba yau ba take son sultan da fateema, don yarinyar ta mata, ga nitsuwa da hankali, har cikin ranta take son fatu. A bakin gate ya cim mata, wani sauri takeyi bata son wani abu ya hada su, gudun kar ta kopsa ya ganeta. Sultan yace “madam ba haka tafiyanki yake ba” dolenta ta fara tafiya yanda ta saba, hakan ya bashi daman jerawa da ita. “Ina wuni” fatu tace dashi, yace “lafiya kalau fateey, kina lafiya” a gajarce tace “lafiya” dai dai nan suka iso bakin gate ta shige abunta, shi kuma ya juya ya fara tafiya, tana shiga taga bai biyota ba, sai taga sam bata kyauta ba, ko godia babu, leqawa tayi tace “hey” ya juyo ta sakar masa murmushin da ya saka shi jin sansanyar iska na bin jinin jikinshi. Yace “yess” tace “thanks” bata jira amsar sa ba ta shige. Samun kansa yayi da tsayawa a gurin yana doka uban murmushi da yasa hakoransa shan iska yana kallon kofar, yafi 5mins a gurin wucewar wata mota ce ta sa shi dawowa hayyacinsa ya koma gidansu. Ita kuma tana shiga a farfajiyan gidan ta hadu da mahmud zaune a irin kujerun shan iska nan yana karanta newspaper tazo ta gurinshi tace “sannu da hutawa” ya sauqe jaridan yace “yauwa” tayi wucewarta. A ranshi yace wacece wannan? May be dangin su sultan ce don tana kama dasu, amma dai ta hadu ba laifi, tashi yayi ya shiga cikin gidan shima, mummy ne ta fara ganinshi tace “mahmud har ka dawo? Yace “ehh” ya nemi guri ya zauna. Fatu tace “mummy shine ya mahmud? Mummy tace “shine” fatu ta gaishe shi ta masa sannu da dawowa ya amsa. Tace “na hadu dashi a waje ban zata shi bane ai” mummy tace “ayya, kina bacci suka dawo shiyasa” mahmud yace “mummy banganeta ba” mummy tace “yar uwarku ce daga bauchi tazo karatu ne” tana fadan haka ta tashi ta shige kitchen. Kallon fatu yayi yace “a gidan wa kike a bauchin, don ban taba ganinki ba duk zuwa na” shiru tayi ta rasa me zata ce can ta qakalo murmushi ta ce “ko na fada ma baza ka gane ba” zai qara magana mummy ta fito da basket a hannun ta tace “fateema ko zaki kai abincin gidan jameel? Ta nan sai ki musu sannu da dawowa” da dokin ta tace “ai kuwa mummy” “amma ki jira yanzu farouq zai dawo daga islamiyya sai ku tafi tare driver ya kai ku” yamma liss farouq ya dawo driver ya kaisu gidan jameel da amarya lubna.

 

Afuwan fans, sai yau Allah yayi na turo FATU A BIRNI. Ba jan ranku nayi ba, lokaci ne ban samu ba. Barka Da Sallah. Allah ya maimaita mana. Ameen

 

Taku a kullum

Maman Fa’iz????????

[9:14PM, 7/13/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣4⃣

Gefen sultan kuma yana komawa gida ya wuce dakinsa ya kwanta yana tunanin fateema, wayarshi ce ta katse masa tunaninsa, ganin number jameel yasa shi miqewa tare da amsa wayar “ka shigo ne?…….. ok bari in fito. A haraban gidan ya ga jameel bayan sun gaisa ne kai tsaye suka shige cikin palourn gidan, mammi ce kadai zaune tana rubutu a wani memo, sallaman da sukayi yasa ta cire tabarau idonta “lale marhabin da mutanen S Africa” zama sukayi, bayan sun gaisa da mammi ne suka fito haraban gidan, sultan yace “dude yau ma tazo gidan nan wallahi, har rakata bakin gidanku nayi” ya fada yana shafa sajensa daya kwanta luff a fuskar sa, jameel dai kallon mamaki yake binshi dashi, tunda suke sultan bai taba cewa yana son wata ba, shi har ya fara tunanin ko yana da matsala ne, mata sunsha warce kansu a gurinshi amma ko kallonsu baya yi, amma akan wata wai fateema ya gama rudewa. Koyaushe sukayi waya sai sultan yayi maganar ta, jameel yana so yaga  wacece fateeyn nan da take qoqarin zautar masa aboki. “Wai dama haka love din yake? Da ita nake bacci da ita nake tashi, jameel na rasa yadda zanyi” Jameel da ya tsaya kallonshi sai yanzu ya samu bakin magana “why not ka tunkareta? Ajiyar zuciya mai qarfi sultan ya sauke yace “I cant! Tana min kwarjini da yawa, to me zan ce mata ma? Kuma I asked farouq bata riqe waya nd tura wasiqa ka gane yayi yawa” Jameel yace “amma ka taba sanin tana da saurayi? Sultan yace “ko a skul bata kula kowa qawarta ma daya ce, a gida ma babu wanda yake zuwa mata, all I know shine ita TAWA CE! “Bravo alaika” jameel ya fada yana tafa masa, “ka iya yanda zakayi ka samu details akanta amma baka san yanda zakayi ka mata magana ba” sultan yace “kai dai ka taimakeni” “yanzu dai muje gidana ma qarasa maganar acan” shiga cars dinsu sukayi suka fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button