FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gidan jameel ya hadu shima ba laifi, dai dai zaman mace daya. Driver na ajiyesu farouq ya fito da gudu ya shige cikin gidan, fatu ma ta fito tacewa mal habu ya jirasu yanzu zasu fito. Tana shiga motocin su jameel suka shigo. Bayan sun fito ne jameel yake tambayan mal habu ko aika ne ya kawo, yace masa ya kawo farouq da fateema ne, sultan dake gefe yayiwa jameel ido, jameel yace “ok kaje zan dawo dasu anjima” ba musu habu ya tafi. Su kuma suka tsaya anan suka cigaba da maganansu. Farouq a daki ya tarar da lubna tana gyara cikin wardrobe dinta, tace “farouq yaushe kazo” yace “yanzun nan, ni da anty fateema ne” tace waye kuma anty fateema” yayinda ta riqo hannunshi suka fito palour inda fatu tayi wa kanta masauqi a daya daga cikin kujerun da suka qawata palour.
Sannu da zuwa lubna tayi wa fatu tace bari in dauko miki ruwa, fatu tace “a’a nagode, ban jima da sha ba” suka gaisa anan lubna tace “sai dai ban ganeki ba” farouq yace “nace miki sunanta anty fateema kuma tazo karatu ne gurin mummy” daria sukayi lubna tace “to uban yan surutu, kai na tambaya? Bai kulata ba don ya danno tashan cartoon. Maida hankalinta tayi kan fatu tace “ke yar uwarsu ce kenan, kamar na taba ganinki, daga bauchi kike ko? Fatu tace “ehh, mummy tace a kawo muku abinci, kun dawo lafiya? “Lafiya kalau” lubna ta bata amsa. Fatu ta kalli farouq tace “my sojaa lets go” ba musu ya miqe yace “bye anty lubna, kuma sai na fadawa mummy kince nine uban yan surutu” zaro ido lubna tayi tace “kaji dashi” fita yayi zuwa inda sukayi parking amma wayam ba mota, sai motoci biu da ya gani, zai juya ya koma ya hango sultan da jameel da bayan cars din. Gurinsu ya nufa dai dai nan su fatu suka fito suma. Fatu tana ganin ba motan su tace “ba dai mal habu tafiya yayi ya barmu ba? Sai dana ce ya jiramu fa” ta karisa maganan kamar zatayi kuka. “DJ” lubna ta kwalawa jameel kira suka taho dukansu sultan n Nna cewa “oyoyo uwargida, don yanzu kin tsufa wata sabuwa zamu kawo” lubna ta harareshi na wasa tace “hurul ain kenan? Suna can suna jiransa insha Allah” gaisawa sukayi tsakaninsu fatu na gefe riqe da hannun farouq tana wasa dashi, can tace “ya jameel sannu da dawowa” yace “yauwa, fateema ko? Tace “ehh” gaisawa sukayi tace sai anjiman ku. Da sauri sultan yace “ina zaki je” bata kalle shi ba taja hannun farouq tace “gida” jameel yace “ni nacewa mal habu ya tafi zan maida ku in munyi sallah” ba yanda ta iya dole ta koma, su kuma suka wuce masallaci da farouq. Lubna taja fatu dakinta sukayi sallah, sai tadi sukeyi kamar sun jima da sanin juna, anan ta tayata qarisa gyaran wardrobe din, suka share dakin duk da kafin su dawo an share da gyara ko ina na gidan. Su sultan basu dawo ba sai bayan sunyi sallah isha. A palour suka tarar da su lubna da fatu suna ta tadinsu, sallama sukayi suka shigo, Lubna tace “ba dai har anyi sallah isha ba? Jameel ya zauna kusa da ita yace “ina zaki sani tunda kin samu abokiar hira” lubna ne ta canja tasha zuwa cartoon wa farouq tace “fateema ki shiga daki kiyi sallah, bari inyi serving dinsu abinci” shigan fatu keda wuya suma suka wuce kan dinning jameel yace “mutumina ka tafi da yawa fa, irin wannan kallon haka” cike da tsokana ya karasa maganar. Lubna tace “ba dai fateema yake kallo ba? Sultan yace “dadina dake yawan tambaya, ni kawai ki tayani campaign” Jameel yace “ni dai kaman na taba ganinta a bauchi, amma inaga mahmud zai fi saninta don ya fini shiga ziyara, ko hutu yazo sai yaje bauchi ya zaga dangi” nan dai sukayi ta tattaunawa har suka samu solution, fitowan fatu yasa sukayi shiru, ganin haka ta gane maganarta sukeyi kawai ta wayance ta zauna kusa da farouq. Bata dade da zama ba suka kammala jameel yace “muje ko fateey” sun fito haraban gidan jameel yace “ohh ashee ba mai da yawa a mota na, pls sultan ka sauqesu mana” sai da yayi dan jimm kana yace “ok” jameel ya tura farouq baya, lubna kuma ta budewa fatu gaba tace “ki zauna a gaba ke” ba musu ta shiga, lubna ta miqo mata leda tace “ga tsaraba ba yawa” godia fatu tayi sultan yaja su suka tafi.
Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[10:40PM, 7/16/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣5⃣
Tun shiganta motan kamshin jikinsu ya gauraya ya bada wani ni’imantaccen scent mai kwantar da hankali, ga a’c ya sanyaya ko ina. Ba sultan kadai ba har fatu taso inama suyi ta zama haka har abada *what? Fatu ar u in love?* tsohuwar cool music na celin dion mai taken _TITANIC_ ya saka musu (in d nyt in my dreams I see u, I feel u….) yana bi a hankali, fatu da ta gama narkewa ta juya kanta gurin window tana jin kalaman waqar har cikin zuciyarta yana ratsa ta. Maimakon taga anyi hanyar gida sai ya biya wani guri, basu tsaya a ko”ina ba sai katafaren gurin sayar da phones. Ya juya zaiyiwa farouq magana yaga yayi bacci. Fatu ta juyo tace “baka ce zaka yi branching ba, srry mun takuraka” yace “no wahala, abu zan saya kuma gashi farouq yayi bacci banida dan rakiya, muje ki rakani” tace “no, in kai alone ne zaka fi sauri” Yace “noo, to ki biyani rakiyan dana miki dazu” yanda yyi maganar kamar yaro yasa fatu daria tace “muje to”. Suka shiga tana binshi a baya, yace “pls ki tayani zabe, amrah nake son sayawa waya” tasan dai amrah nada waya koda yake abunka da masu shi, tara wayoyi a hannu qaramin aikinsu ne. Iphone latest ta nuna tace “wannan yayi” Yace “irin nawa” tace “sai kuyi anko” yace “hakan za’ayi” Qaramin Nokia ya qara dauka ya biya kudinsu, anan ya qara sayan sim cards 2 dfffrnt layi suka fita. Har komawansu mota farouq na baccinsa, basu zame ko ina ba sai *eman* ya saya musu ice cream da snacks, daga nan suka yoo gida wajen tara saura. Har cikin gidan ya shiga yayi parking suka fito daga motan, fatu na qoqarin daukan farouq yace “lemme help” ba musu ta matsa masa ya dauke sa suka shige gidan, a palour ya kwantar dashi mummy kuma da alama tana dakinta, Fatu tace “thanks” yace kinyi mantuwa a mota, tace “ni? Ok tsaraban da anty lubna ta bani” fita sukayi ya bude motar ya dauko ledojin da sukayi shoppin ya miqa mata, tace “wannan ne nawa” ta karba yace “dan tsaya pls” tayi juyi irin ta gajin nan, yace “srry” bude ledan wayoyin yayi ya saka musu layi duk tana tsaye ya kunna ya miqa mata, yace “bari in gwada kira” ita duk bata dauka wani abu ba ta karba, wayarshi ya ciro sak irin na hannunta ya kira sai ga numbern shi ya bayyana a screen din, miqa mishi tayi tace “yayi” yace “kip it, naki ne” cikin zaro ido tace “what? Noo kayi hakuri…. kafin ta qara magana ya rufe motarsa yayi reverse tana tsaye har aka wangale masa gate ya fita, ta jima kana ta koma gida jiki a sanyaye, a palour ta tarar har mummy ta shigar da farouq dakinsa, tana sauqowa qasa, fatu tace “mummy mun dawo” hajia tace “sai yanzu kenan? Jameel din ne yadawo daku? Fatu tace “a’a amm…. yayan amrah ne” sarai hajia tasan sultan ne ya dawo dasu don tana ganin shigowarsu duka, tace “bari in duba kullin masan nan, gobe da safe dadynku zai sauqo yace shi yake sha’awa” har hajia ta dubo ta fito fatu na tsaye a gun, hajia tace “auu baki haura bane? Kaman zatayi kuka tace “mummy wayoyi ya bani fa” da fara’a hajia tace “a ina” fatu ta labarta mata komai, hajia taga wayoyin tace “amma sunyi kyau Allah ya amfana” fatu da mamaki ya gama lullubeta tace “mummy gobe zan mayar masa dai ko? bata fuska hajia tayi tace “maganar gaskia fateema ki nemi soyayyar mijinki, abunda zan iya fada miki kenan, kibi komai a hankali da nutsuwa” har zata juya fatu tace “mummy ga tsaraba anty lubna ta bani” mummy ta gani tayi Allah ya amfana tayi upstairs. Zama jugum fatu tayi tana aukin tunani, ita ta rasa a wani yanayi take, shin tana son mijinta ne ko bata sonshi? Kodai kawai son yan’uwantaka ne? Amma deep inside her heart tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba. Da taga tunani bazai fishhe ta ba tace “Allah ka shige min gaba” tashi tayi ta dauki roban ice cream daya da snack iya wanda zata ci sauran tasa a fridge, kashe wuta tayi ta kulle kofa tayi dakinta, bayan ta gama ci ne tayi wanka ta fito taga leda akan mirrow nata, murmushi tayi tace tsaraban mummy ne. Ta duba takalma ne yan ubansu guda uku kowanne da jakansa, na lubna kuma turaruka ne da cosmetics, adana su tayi ta kwanta. Qarar wayanta ne yasa ta tashi zaune a tsorice (sabon shiga????????) a hankali tasa hannu ta dauka, number ta gani wanda tasan na sultan ne tace “hello” can gefe akace “hii” shiru ya biyo baya, can a gefe yace “sultan ne ya gajia? Tace “lafiya, nagode fa Allah ya saka” har cikin ranshi yaji dadin addu’anta yace “ameen, sai da safe, karki shanye ice cream din ki ragewa farouq nashi” daria dukansu sukayi kana sukayi hanging, daga ita har shi da murmushi a fuskarsu bacci ya dauke su. Hmm _lovebirds_????