HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

 

Maman Fa’izz????????

[7:41PM, 7/17/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣6⃣

 

Yau kimanin wata biu da sati biu kenan da haduwan sultan da fatu a a gidan jameel, shakuwa mai tsanani ya shiga tsakaninsu, wanda yawanci in sultan na qasar shi yake kaita school, waya kuma kowanne dare sai sunyi b4 bacci, no love jst qanwa da yaya. Chattin babu wanda fatu batayi da taimakon qawarta xahra levels. fatu har sunyi exams na second semester suna hutu. Yau saturday sunyi da levels zasu je saloon, Karfe 11 na safe tana gidansu levels daga nan suka rankaya gurin saloon din da yake ba nisa tsakaninsu.

 

A gidan jameel naga sultan da abokin nashi a palour suna magana, jameel yace “its time ka furtawa fateema cewa kana sonta, don kun saba wanda nasan lokacin da kuka dauka kuna tare itama ta fara sonka” sosa kai sultan yayi yace “kana ganin ta fara sona? “Kwarai insha Allah” Jameel ya bashi amsa. Sunkuyar da kai sultan yayi kana ya dago yana kallon gefe. Muryan jameel yaji yace “FATU FA?? Da sauri sultan ya juyo da kanshi gurin jameel zuciyarsa na dukan uku uku, don shi ya manta ma da wata fatu, yau kimanin wata uku kenan ko aika da yake mata ya daina, fateema ta mantar dashi cewa yana da mata ajiyayya. Jameel ya qura masa ido yana jiran yaji mai zai ce, shi dai fatu ta masa tun ranan har yanxu kuma yana tausaya mata a matsayinta na marainiya abar tausayi, “baka yi magana ba” jameel yace dashi, sultan da har yanzu bai gama saita kanshi ba yace “ni fateema nake so, bani da ra’ayin zama da mata biu kuma. Inaga its time itama da zan furta mata abunda ya dace da ita” jameel zaiyi magana sultan yace “jameel u knw yanda aka hada auren, sam babu yarda ta. I cnt live with her” Shiru jameel yayi, sultan sai da ji hankalinshi ya dawo jikinshi ya dauki wayarsa yayi dialing numbern fatu.

Bayan an gama musu suka rankayo gida. Fatu ne da xahra ke hira kan sultan levels na cewa “wallahi qawa har yanzu ina mamakin wai sultan mijinki ne amma kuma bai ganeki ba, kuma wai he’s in love with new fateema” murmushin daya fi kuka ciwo fatu tayi tace “labarin rayuwata kamar a movie, bansan nan gaba ya zaya kasance ba, zan rabu dashi ne ko zamu kasance a inuwa daya a matsayin mata da miji, levels ki tayani addu’a kawai. Allah ne kadai abun dogaro na” siririn hawaye ta goge hakan yayi dai dai da ringing din da wayarta ya fara “dan halal, yaqi ambato” cewar fatu yayin da murmushi ya bayyana a fuskarta, xahra ta bita da kallon tausayi. “Assalam alaika yayan fateey” “wa’alaiku mussalam qanwata, ya kike? Tace “lafiya lau, ya aiki? Yace “da godia, jiya kince zaki je saloon kinje ne? Tace “ehh, yanzu muka dawo ina gidansu levels ne” Yace “ok, in baza ki damuba anjima da yamma inason ganinki” tace “ok yayana, zaka zo gidane? Yace “noo, mu hadu a gidan jameel” sukayi sallama sukayi hanging. Fatu ta kalli levels tace “I gotta go, zanyi wa mummy kunun aya nd sultan yana son ganina” levels kada kai tayi kawai ta rakata haraban gidansu tasa drivernsu ya maida fatu gida.

Sultan na ajiye waya yace “jameel insha Allah nan da 1 week zamu je Garin Modibbo gurin FATU”

 

Maman Fateey????????

[9:44PM, 7/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣7⃣

 

Jameel yace “I am sorry to say bazan iya raka ka ba, I cnt face da dattijo” yana gama fadan haka ya fice daga palourn, sultan ya bi bayansa amma yana fita jameel already yaja motarsa ya bar gidan, shima ya fita.

Lubna dake kitchen ta fito jiki a sanyaye da alama taji duk hiransu, jameel ya bata labarin fatu tun ba yau ba, haka kawai itama take kaunar sultan da fatu, ko ba komai ‘yar uwarsa ce, marainiya mai neman taimako, kuma a yanda taji jameel ya fada fatun tayi karatu har zuwa secondary, so why not ya maida ta skul in educated wife din yake so, tunani barkatai lubna tayi akan fatu, tana tausayawa yarinyar. Tashi tayi ta shige dakin jameel ta bude drawer da yake ajiye pictures, da kyar ta samo pic din sultan da matarsa fatu. *WHAT*? naji ta furta da karfi hade da miqewa tsaye harta manta cikin 6months da yake jikinta.

 

Fatu na isa gida tayiwa mummy kunun aya tasa mata a fridge, fitowanta daga kitchen din yayi dai dai da shigowan mummy gidan, fatu tace “sannu da dawowa mummy” tace “yauwa fateema” fatu tace “farouq daya dawo daga skul yace zai biki gidan mammi, yaje ne” hajia tace “dan rigima yaje, ynxuma na barsu zasu je unguwa da amrah ne” fatu tace “ayya, nima inason zuwa gidan anty lubna anjima” mummy tace “Allah ya kaimu” fatu tace “Ameen, na gama kunun ayan, yana fridge” da murmushi a fuskar hajia tace “nagode ‘yata Allah ya miki albarka” “Ameen mummy” fatu tace ta bar mummy a palour ta shige dakinta don tadan huta zuwa yamma, ko meyasa sultan yake nemanta oho. Wayarta ta dauka don tayi chattin amma sai taga missed calls din lubna 4, da sauri ta kirata don ita ta dauka ma ba lafiya ne. Ringing daya biyu ta dauka tace “Hello fateema kina gidana ne? Tace “ina gida, naga missed calls dinki ne, lafiya kam? Lubna tace “sai alkhairi, don Allah ina son ganinki yanzu yanzu” fatu tace “ai anjima ina zuwa da yamma” lubna tace “a’a its urgent pls ko minti biyar karki qara” fatu tace “to pls bari inyi wanka” “ohhh fateema kiyi hakuri ki dauko kayan da zakisa in kinzo kiyi anan” fatu tace “to gani nan zuwa” kashe wayan tayi zuciyarta na dukan uku uku. Anya ba ganeta sultan da jameel sukayi ba? Saisaita kanta tayi ta dauki abubuwan da take bukata taje dakin mummy tace “mummy bari inje yanxu anty lubna ta kirani” mummy tace “to shykenan Allah ya kiyaye hanya, ki dauka mata kunun ayan nan naga itama tana so” murmushi fatu tayi tace “to mummy” bayan ta dauka ne ta fita mal habu ya drivin dinta sai gidan jameel.

 

Maman Fateey????????

[9:45PM, 7/19/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

2⃣8⃣

 

Sultan na fita gidansu ya nufa, kai tsaye room dinsa ya nufa ya zauna akan daya daga cikin kujerun da suke room din. Shi gabadaya jin haushin fatu yakeyi, ta bata mishi plan din rayuwarsa, gashi akanta har sun sami matsala da abokinshi wanda tun suna yara rabon da hakan ya faru, shi fa bazai iya ba, never!! Zai saketa ya kawota gurin mammi ya kuma gargadeta tayi kipp da bakinta. Laifinshi ne ma daya qarfafa bincike wajen nemo innar tashi. Tunani ya fara shekara biyu da suka wuce yana tare da mammin shi a dakinta suna hira lokaci daya tayi shiru yace “mammi lafiya” tace “tunanin ‘yar uwata nakeyi, ko ya take? A ina take? ita kadai ce ‘yar uwata da muke uwa daya, sai kannena da muke uba daya, shekarana 6 a lokacin aurensu ya mutu, ba yanda ba’ayiba a maida auren abun ya faskara, a haka aka barsu amma kuma ana tare don rabuwansu bai raba zumuncin dake tsakanin babanta da babanshi wanda suke yan uwan juna ba. Ina shekara 7 muka je dukku anan wani da ake cewa mal sirajo ya ganta yace yana so, a lokacin yana da mata da ‘yayansa 4, da kyar aka bashi aurenta don ma tace itama tana sonshi ne, saboda bakin cikin hakan dangin mu suka tattara suka bar garin a cewarsu ta zabi bare akan dan’uwanta, duk da shi din ma bafulatanin ne, amma wai su fulanin yawo ne. Na sha kuka dana rabu da ita, bamu wuce ko ina ba sai yola dama can ne asalin garin mu, anan muka zauna har babana ya fara shiga birni yana kasuwanci anan yaga yara na zuwa skul ya saka ni, har Allah ya buda masa sosai yayi aure, kamar yanda ka sani kannena biu, rufa’I da musa. Mahaifinka shima auren dangi aka hada ni dashi, a can na haifeku duka muka dawo nan gombe lokacin ina goyon amrah. Na tashi cikin dangi amma ina kewar mahaifiyata Muna dawowa gombe na je dukku ganin mahaifiyata amma aka ce ta rasu, kanwata kuma tayi aure, nayi nayi su fada min inda tayi auren amma suka ce sun manta, sultan ina kaunar naga wani tsatso daga mahaifiyata” kwallan daya taru a idonta ne ya saurin zubowa ta share. Tun daga wannan lokacin sultan ya qudura aniyar nemowa mahaifiyarsa ‘yar uwarta, yaje sau daya shima suka fada masa haka, zuwansa na biyu shigan dare yayi da wasu soldiers da yayi hayansu, tsoro sosai suka bawa mal jauro wanda ya fadi inda take aure har da sunan mijin nata. Yanzu a dalilin haka ya jawo wa kanshi damuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button