FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

[11:06PM, 7/20/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣9⃣
Fatu na isa gidan jameel ta shiga gabanta na dukan uku uku, a palour ta tarar da lubna na zaune “kin iso? Tace da ita, sai da ta zauna tukun tace “ehh, Allah yasa lafiya” hoton ta ajiye akan cinyar fatu wanda lokaci qanqane dan walwalar da yake fuskarta ya bace ya koma matsanancin damuwa, ido ta kurawa hoton kamar yau taba kallon irinsa, lubna da ta kafe ta da ido tana nazarinta tace “explain please” hawaye naga yana zarya a kumatun fatu tana girgiza kai tace “its over, d charade” lubna ta matso kusa da ita ta dafa kafadunta tace “its not over yet, yanxu aka fara, trust me” tiryan tiryan fatu ta fara bata labarin har zuwanta gombe da yanda hajia ta taimaketa ta sakata a skul ta maida ita *FATUN BIRNI* ta kuma dauketa tamkar ‘yar cikinta da ta haifa. Ajiyar zuciya lubna tayi tace “one last question, do u love sultan” dago idonta tayi da sukayi dan jaa don kuka tace “anty lubna……a life without sultan, even an immortal life would be empty, I wish to stay on earth with him” murmushi mai bayyana 32 lubna tayi tace “kamar yanda na fada miki its not over, to hakan ne” magana suka fara wanda nayi nayi inji amma fateey na ta dameni da kuka, naga dai lubna na zazzago magana yayinda fatu ke ta maida hankali 100% tana ji, can naji tace “he’ll love her too” fatu da ta kasa boye farincikinta ta ruqunqume lubna tana daria kamar ance yau za’a kaita gidan sultan. Sai da suka natsa tace “anty lubna tnx alot Allah ya bar mini ke” “Ameen” ta bata amsa tana murmushi. Kiran sallah la’asar yasa suka farga dat its time. Lubna ta shiga bandakinta ta hadawa fatu ruwa a bathtub turarukan wanka naga ta diga a ciki, tayi alwala ta fito, ta bawa fatu towel ta shiga bathroom din yayinda ita kuma ta fara sallah. 15mins ta dauka tana dirja jikinta kamar yau aka haifeta???? kana tayi alwala ta fito, zani da hijab lubna ta bata tasa tayi sallah, daga nan ta feshe jikinta da body spray ta shafa humra da kulacca duk na lubna, nan da nan dakin ya dau asirtaccen kamshin da komin gulmanka bazaka gane me da me aka hada ba. Wani swiss lace red nd black naga lubna ta dauko ta bawa fatu ta saka, fatu tace “na taho da kayana fa” “ban taba saka shiba, ko DJ bai san da zaman shiba, jst ki saka” ba musu ta karba ta saka, kamar a jikinta aka dinka, figure 8 dinta ya fito tarr, zaunar da ita lubna tayi akan kujera ta fara tsara mata make up, dauri ta kafa mata wanda yasa gashinta ya fito ta tsakiya ya kwanta a bayanta, Qara feshe ta tayi da wani turare mai sanyin kamshi, tace “done! Kallon kanta tayi a mirrow, ita kanta tasan tayi kyau bana wasa ba, kamar wata amaryan da za’aje dinner, qaran phone dinta ya katse kallon qurilla da take yiwa kanta, sultan nagani a screen din, dauka tayi ta kashe murya tace “Hello” sultan da yake kusa da motarsa yayin saurin dafawa don yanda muryan ya kashe masa jijiyoyin jikinsa, “hey” ya fada a sanyaye, ya cigaba “gani zan fito yanzu, kina gida ne in biya mu tafi tare? Sai data ja aji tace “nop, ina gidan yanzu haka” yace “ok gani zuwa” ya kashe wayan. Tsayawa nayi na qare masa kallo yau, dogo ne amma ba can ba, kuma da alama yana motsa jiki, fuskarsa irin na fulani sak, dogon fuska, manyan idanuwa, dogon hanci da bakinsa dan daidai, ga saje daya zagaye fuskar da quarter million suka qara qawata shi, gashin kansa kamar na fulani Aww ashe fulanin ne, black ga santsi a kwance. Fatar jikinsa Brownie ne kuma ba chocolate ba, daka ganshi kasan hutu da kudi sun zauna hade da kwanciyar hankali. Half jumfa ne a jikinsa na dakakkiyar shadda mai launin blue, takalmin shi da agogon shi black, ya hadu ne iya haduwa Dan Fulanin. Motarsa ya shige sai gidan jameel.
Maman Fateey????????
[10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣0⃣
Fatu ta kalli lubna tace “he’s on his way” jinjina kai lubna tayi ta fara magana “ki kula kiyi duk abunda ya dace, zan fita in nemo mijina nima” daria suka sanya dukansu, hijabi ta sanya ta fice a gidan a yar qaramar motarta, a waje ta hadu da sultan sukayi gaisuwan light ta harba titi shi kuma ya shige gidan maigadi ya rufe gate.
Da sallamansa ya shigo falon fatu data bashi keya ta juyo a kasalance ta amsa sallaman, daskarewa yayi a gurin yayinda ita kuma take jefanshi da malalacin murmushi tace “ka shigo mana” samun kanshi yayi da bin umarninta, a 1sitter ya zauna yayinda ita kuma take 2sitter suna fuskantar juna, bai taba ganinta haka ba gyale ko hijab ba sai yau, manyan idanunshi sexy ya zuba mata kamar yau ya taba kallonta, kunya ce ta rufe ta ta dago ido tace “kai yayana wannan kallon” bai sani ba bakinshi ya furta “u luk gorgeous” “tnx” ta furta mishi. Tashi tayi tace “mutanen gidan basa nan bari in dauko maka ruwa” a hankali take tafiya wanda ya bawa sultan daman kare ma bayanta kallo, tana shigewa kitchen ya jijjiga kanshi yace “control sultan, control” saisaita kanshi yayi ya gyara zama yana tunanin ta ina zai fara mata magana, bai gama shawara ba ta fito da tire a hannunta ruwa ne da cups sai juice, nan dinma kura mata ido yayi har ta iso ta jawo centre table kusa dashi ta ajiye kana ta sunkuyo yanda dole ya shaqi kamshin jikinta, tace “wanne za’a zuba maka? Sultan da ya lula shaqar kamshinta ya kuma shagala da kallon kirjinta yace “na’am” sarai tasan abunda yake kallo amma ta nuna bata ganeba cikin ranta kuma tace ka kalla halalinka ne. Miqewa tayi tsaye ta qara maimaita masa tambayar da sauri yace “juice” don yasan dole ta tsaya shaking dinsa kafin ta zuba masa hakan kuma na nufin shaking din abunda yake son kallo Murmushi tayi ta dauki juice din ta shaking dinsa daga tsaye ta sunkuya tana saka masa a cup, tana gama sawa ta koma gurin zamanta shi kuma ji yayi inama tayita tsiyaya masa har gobe, kodai yace ta saka mishi ruwa ne? “Control sultan” ya fada a sanyaye ya dauki kofin yasha kadan ya ajiye. “As u said kana son ganina” fatu tace dashi yayinda take harde kafuwanta, yace “ehh” tace “gani to”.
Maman Fateey????????
[10:38PM, 7/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣1⃣
Sunanta ya kira “Fateema” tsikar jikinta ne ya tashi tace “na’am” yace “magana ce tafe dani very important” yayi shiru tace “ehen i’m ol ears” yace “fateey tun ranar da na fara ganinki nake jinki cikin raina _love at first sight_ da tunaninki nake kwana dashi nake tashi, nayi amfani da lokacin da muka dauka tare don mu shaqu nd to knw more about each other” fatu da tun daya fara magana kanta na qasa naga murmushi ya subuce a fuskarta, “fateey” ya kira sunanta a hnkali, dago idanunta tayi suka sarqe cikin nashi “I’m really madly deeply in love with you fateema” Da sauri ta sauqe kwayar idonta yayinda wani siririn hawaye ya biyo kuncinta, na rasa gane na farinciki ne ko ko! Shiru tayi, zufa ne ya fara keto masa ba dai tana da wanda take so ba! “Fateema ko kinada wanda kike so ne? Ya fada cikin tashin hankali. Kada mishi kai tayi alamar a’a. “Bakya so na ne? Talk to me fateema, idan bakya sona zan iya jiran har lokacin da kikaji kin fara sona, shirunki kan iya sa jinina ya hau pls talk to me” ya qarasa maganar yana dafe kanshi da yaji yana barazanar tsagewa. Lura da yanayinsa yasa tace “Ina buqatar time nayi tunani” yace “zuwa yaushe? Tace “ko nan da 2 weeks” yaqe yyi ‘wanda masu iya magana suka ce mugun kuka’ yace “kiyi hakuri na baki 5 hours, zan kiraki anjima in d nyt” zatayi magana ya tari numfashinta yace “kiji tausayina please” ya langabar da kai kaman qaramin yaro dolenta yasa tace “to Allah ya kaimu” yace “Ameen matata” daria tayi tace “tun kafin inyi tunanin? Kana gaggawa” shima darian yayi ya mance ciwon kan daya fara damunshi dazu yace “I knw tunaninki zai kasance positively” daga nan suka bige da hira yana sako maganan soyayyarshi tana basarwa. Kiran sallan da aka fara ne yayi daidai da shigowan lubna da jameel sai darawa sukeyi, ganin fatu ta sultan yasa sukayi kasaqe suna kallonsu, sultan tadi yayi tadi ya dawo 2sitter inda fatu take sai hiransu suke. Gyaran muryan jameel yasa suka farga yace “sannunku” fatu tayi saurin daukan gyalenta ta yane jikinta sultan kuma ya miqe yace “ai sai muje sallah ko, tunda kaji ana kira” bai kula darian da jameel ke mishi ba ya fita daga falon shima jameel ya bishi suka wuce masallaci yana tsokanarshi wai akan yarinya ya dawo parrot.