FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna fita lubna tace “mutumiyata ya akayi” labarin yanda akayi fatu ta bata duka. Kallon sama lubna tayi tana murmushi tace “sai nan da 4 days zamuyi move din mu na biyu” fatu tace “na fara tsoro anty lubna, anya bazai….. “noo insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi, mu hada da addu’a” Daga nan suka shiga daki sukayi sallah suka girka simple abinci mara nauyi, ana kiran isha sukayi sallah bayan sun idar ne su sultan suka dawo. Lubna tasa fatu ta qara gyara fuskarta sai dai wannan karon da gyalenta suka fito falo, abinci suka fara ci wanda fatu duk a takure take yayinda lubna, Jameel da sultan ko a jikinsu, suna qare cin abincin Jameel da lubna suka rako su bakin mota, inka gansu sai sun burge ka, a gaba ta zauna suka tafi.
Suna isowa gida tana kokarin budewa ya sa lock tayi tayi ta bude ta kasa, kallonshi tayi ya zuba mata sexy eyes dinshi yana murmushi, anan ta gane shi yasa lock, da shagwaba tace “amma ka wahalar dani, Allah na dauka yaqi buduwa ne” kwaikwayanta yayi yace “ai ban gaji da kallonki bane” daria tayi tace “kai ko? Bude mata yayi yace “sai na kiraki, kar kiyi bacci” “ok” tace yayinda ta fita ta maida marfin motar, daga mishi hannu tayi alamar bye amma bawan Allah yaqi tafiya, har cikin zuciyarta take jinjina irin son da sultan ke yiwa fateema. “Allah ka barmin mijina” ta furta a hankali ta shige cikin gida, shima sai daya ga kulewarta yayi ajiyan zuciya yace “Allah ka taimakeni” kana ya wuce gidansu.
Maman Fateey????????
[4:05PM, 7/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣2⃣
Fatu na shiga gida ta samu farouq na kallo ya mata oyoyo tace “har yanzu bakayi bacci ba? Yace “yau saturday, remember? Ba skul gobe” tace “yess hakane, ina mummy? Yace “tana falon daddy” tace “ok, bari in shiga in watsa ruwa”.
Wanka tayi ta sa sleeping dress ta dora hijab kana ta fito palour, ganin mahmud a zaune kusa da farouq wanda har yayi bacci yasa kirjinta dukan uku uku! Tun dawowan shi yake tsare ta da tambayoyi yana so yasan daga cikin wani gida take a familyn nasu, answers da take bashi basa gamsar dashi kuma akwai alamun rashin gaskia a tattare a ita, _real lawyer_ ????. Rufin asirinta daya shine after walima na gama karatunshi ya fara aiki a abuja, ba kowanne weekend yake dawowa ba, duk randa ya dawo kuma bata bari su zauna su kadai, in kuma suka zauna zai fara tambayoyi, in mummy na kusa sai tace “mamuda nan fa ba kotu bane da zaka dame yarinya da questions, distant relative ce baza ka ganeta ba” To yau kam qaryanta ya qare tunda ba mummy mai rufe bakinsa. Murmushi ta qaqalo tace “ahh mutan abuja sauqar yaushe” murmushin shima yayi yace “dazu da yamma, kina fita na shigo, naje gidan jameel din ma na samu kuna maganarku ke da matarsa, so bana son katse muku sai na tsaya, da naji bamai qarewa bane yasa na tafi” cikinta ne ya bada sautin qulululu… kirjinta na bugawa da sauri da sauri tace “m..me..me.. kaji? Murmushin cin nasara yayi ya qara narkewa a cikin kujeran yace “abunda kuka gama magana akai” Shiru tayi fuskarta na qasa tace “can u kip a secret?” bai motsa daga kwanciyar ba yace “yess, amma ina son details” briefly ta fada masa abunda ya dace, ta qarisa maganar da cewa “promise me babu wanda zaka fada wa” daria yayi yace “ni banida gulma, bincike na iya” daria sukayi dukansu hkan yayi daidai da shigowan mummy tana cewa “oya farouq kallon ya isa haka kaje ka kwanta” ganin su fatu yasa ta yin shiru Tace “fateema kin dawo? Fatu tace “eeh mummy, anty lubna tace a gaisheki kuma tana godia da kunun aya” da murmushi a fuskar hajia tace “madallah, mahmud dauki farouq ka kaishi dakinsa” Mahmud na haurawa tace “fateema akwai matsala ne? Naga mahmuda yana damunki da tambayoyi” murmushi fatu tayi tace “babu komai mummy, munyi magana dashi” hakan yayi daidai da dawowan mahmud mummy tace “to asuba ta gari, fateema ki locking kofa ki kashe wuta, na tafi” suka mata sai da safe ta wuce side din daddy.
5mins ya qara shima ya mata sai da safe, kopa ta kulle ta kashe wuta ta wuce dakinta. Tana hawa gado ta lalubo wayarta ta kira xahra “badai kinyi bacci ba? Fatu tace da ita xahra wacce da alama tayi nisa da baccinta tace “8:30 ma ina kan gado” fatu tace “ok dama labari zan baki amma tunda kin fara bacci sai da safe” da sauri xahra ta miqe zaune harda kunne bedside lamp tace “bani in sha, wallahi na tashi” daria sosai fatu tayi tace “shegen son labari”
Maman Fateey????????
[9:37PM, 7/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣3⃣
Labarta mata yanda akayi duka tayi. Shiruu xahra tayi can tace “anya wannan plan din babu hatsari a ciki, kar garin neman gira a rasa ido fa” itama fatun shiru tayi xahra ce tace “are you there? “Yess” fatu ta bata amsa ta cigaba da cewa “insha Allah ba matsala, ki tayani da addu’a, Allah ya zaba mana mafi alkhairi” “Ameen” xahra tace suka cigaba da tattaunawa daga baya sukayi hanging.
Missed calls din sultan ta gani kusan goma a screen din wayarta tace yaushe ya kirani? (Har yanzu dai sabin shiga ne) Wani kiran ne ya qara shigowa ta dauka tace “hello” bai amsa ba ya watso mata tambaya “da waye kike waya? Ina kiranki ana cewa call waiting” murmushi tayi kaman yana kusa da ita tace “levels ne fa, ka koma lafiya? Shima murmushin yayi yace “lafiya lau, ya maganar mu? Tace “wacce kenan? Shiru yayi kaman bazaiyi magana ba, a kalla babes sun kai goma shima yana musu irin tambayan nan cikin jin kai, amma reshe ya juye da mujiya yau shi ake yiwa! “Answer na dazu, u said zakiyi tunani” fatu tace “ok, na tuna” yace “ina jinki” shiru tayi yayinda shi kuma ya qagu yaji matsayinsa a gurinta, gani yakeyi in ya rasa fateema duk matar da ya aura baza ta samu soyayyar da yake yiwa fateema ba. Sunanta ya kira “fateey, kinyi shiru” sai da ta dauki 5seconds kana tace “yess, Allah ya zaba mana mafi alkhairi” farinciki fal a fuskarsa yace “u mean kin amince? Tace “yeah”. Hira suka yi cikin wayewa da natsuwa, sai da sukayi 30mins yace “ya kamata in barki haka kiyi bacci, amma ban gaji da jin sweet voice naki ba” qanqame wayar tayi a kunnenta tana lumshe ido ta qara qasa da murya tace “okay, gud nyt” yace “nyt dear, karki manta kiyi addu’an bacci” tace “ok tnx” sallama sukayi. Suna kashe wayan fatu ta tashi ta dauko pic dinsu tare da kudin sadakinta ta qura musu ido, kuka ne ya kwace mata tayi mai isarta har bacci ya dauketa. Sultan kuma yana ajiye wayan yace “saura fatu” murmushi yayi ya fara danne dannen laptop akan business dinshi. Yau kimanin 4days da fara soyayyarsu, in kaga yanda suke love sai ka aza sun shekara, wani zazzafan soyayya sultan yake nunawa fatu, yayinda itama take nuna masa bata da kowa like him. Haka da yamma zaizo ya dauketa suje yawon shaqatawa su sha hiransu ya dawo da ita, ga shopping niki niki. Wata rana kuma a gidan jameel zasu yi hiran, sai dare ya dawo da ita, nan ma sai an qara bata time kafin ta shiga gida. *love kenan* Mummy ta lura da hakan ta kira fatu tace “meke faruwa tsakaninki da sultan? Cikin jin kunya tace “wai mummy sona yakeyi” murmushi mummy tayi tace “kefa? Kina sonshi? Rufe fuska fatu tayi hakan yasa mummy ta gano answer dinta, “Alhamdulillah” mummy ta furta a hankali, tace “kin fada mishi matsayinki a gurinshi? Da sauri fatu tace “a’a mummy ba yanzu ba, kuma zan fada mishi da kaina in lokaci yayi” mummy taso ta gane wani abu amma ta basar a cewarta tunda suna son junansu shykenan. Ranar da suka cika 5 days suka hadu a gidan jameel. Hiransu sukeyi gwanin ban sha’awa, lubna ne ta fito da pics ta rarraba musu suna kallo, na daria suyi daria, na a bada labari a labarta, caraf a cikin pics din dake hannun fatu taga hotonsu itada sultan, turo baki tayi tace “honey wacece kusa da kai haka? Ta wani manne maka! Ta qarisa maganan tana miqawa lubna pic din, lubna na karba tace “laa fatu ce, uwargidan sultan” sultan da tunda fatu ta fara magana notinan kanshi ya sunce, ji yakeyi kaman ya rusa ihu, shikam fatu ta cuce shi, a ‘yan kwanakin da yayi da fateema ya lura tana da kishi, yanzu in tasan fatu matarsa ce ya zaiyi. “Innalillahi” yayinda fatu ta miqe tsaye tana dafe kirji “lubna matarsa fa kika ce”…….