FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Fateey????????
[10:51AM, 7/31/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣4⃣
Fatu ta juyo da kallonta gurin sultan tace “matarka? Pls kace wasa ne” bai dago ya kalleta ba zuciyarsa na tafarfasa, ya dafe kanshi yayi shiru, lubna ta miqe tayi daki dama jameel yana gurin aiki. “alama ya nuna gaskia ne kenan, ya Allah” juyi tayi ta cigaba “ashe yaudarata kakeyi? Na dauka kai mutumin kirki ne ashe ba haka ba ne, why me sultan? Jin muryanta kaman tana kuka yasa ya dago da kanshi, hawaye ne ke sintiri a fuskarta, ji yyi bazai iya ganin su suna zuba ba, kamo hannunta yyi ya zaunar da ita a 2sitter shima ya zauna, still hannun su na cikin na juna, yace “aure aka min amma bada son raina ba, ke kanki kinsan ke kadai nake so, ki fahimceni” juya masa baya tayi tana share hawaye tace “na fahimta amma ka sani ni bazan zauna da kishiya ba, kaje ka zauna da matarka, Allah ya baku zaman lafiya” cikin kidimewa ya juyo da fuskarta yace “what? Yanzu fateema zaki iya rabuwa dani? Wallahi bana sonta ko kadan kuma nakusa zuwa in bata takardar ta, nima bazan iya zama da villager irinta ba” wasu zafafan hawayene suka sauqo wa fatu yayinda wani baqin ciki ya turnuqe ta, wato itace villagern!!! daukan hoton tayi ta yayyaga kuci kuci, ta zubar a palourn tace “maza duk halinku daya, jiki da kwalliyan mace kuke bi, baku damu da kamala ba, karka qara taka inda nake” ficewa tayi a gidan ta barshi zaune a gun yana jin radadin maganarta. Shi a iya saninshi mace bata taba hararansa balle ta gaya masa magana. Me take nufi da kalamanta? Tattara pieces na pic din yyi yasa a small dustbin din da yake falon, shima ya fita daga gidan.
Fatu kuma tana fita ta tari keke napep ya kaita gida, tana shigowa palour Allah yaso ba kowa ta haura upstairs zuwa dakin ta, zaman yan bori tayi a tsakiyar room din tacigaba da kukanta. Meyasa mazan ynzu basu damu da addinin mace da kamun kanta ba? Sunfi son wayayya yar boko wacce ta dace ta zauna a gaban mota kuma ta nunawa duniya? Meyasa taimako da tausayi yayi qaranci wanda har ana raba zumunci don son zuciya da kyale kyalen duniya? Tayi alqawari muddin ya saki fatu to bashi ba ita har abada, kallon kanta tayi a mirrow, me ya qaru a jikinta kuma me ya ragu? Gayu da gogewan da tayi yake so ba ba ita ba. “Villager” ta furta ta qara rushewa da kuka, ita tayi setting din draman amma ya dawo mata real life, a tunaninta zai so matarsa fatu ita kuma ta fada masa gaskian wacece ita! But sai hakan bai faru ba, miqewa tayi kaman wanda aka tsikara tace “yanzu inya sakeni ya zanyi? Ni fatu ya zanyi” zuciyar ta taji na mata quna, hakan yasa ta kwanciya akan gado tana aukin zubar da hawaye har bacci yayi gaba da ita.
Maman Fateey????????
[10:54AM, 7/31/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣5⃣
Sultan gidansu ya nufa kai tsaye yayi hanyar garden a can ya zauna. Maganar gaskia yana son fateema amma wani gefe guda kuma yana jin bazai iya sakin fatu ba, don da zai iya da tuntuni ya aikata hakan tun bayan aurensu da 1month, a lokacin ya fara mata aika mata kudi, yaso ya rubuta amma zuciyarsa ta haneshi da aikata hakan, a baki kawai yake fada amma shi kanshi yasan ko yaya zaiyi bazai iya ba. “Shes quit nd innocent” daukan wayarsa yayi ya turawa fateema text….
_ban yaudareki ba kuma bana fatan hakan ya taba faruwa, duk da bana sonta ‘yar uwata ce kuma marainiya, I dunno what to do, bana jin zan iya sakinta, amma please ki daina batun rabuwa dani, I cnt take it fateema_
Tsawon minti goma da turawa ba’a masa reply ba, hakan yasa yace “bata huce ba har yanzu, ya kamata na bata lokaci”
Fatu na tashi daga bacci kusan bayan la’asar tayi wanka da sallah, yanzu kam ta daina jin qunar da zuciyarta yake mata, wayoyinta ta dauko ta fito palour, ba kowa kamar mummy ta fita unguwa farouq kuma yana islamiyya, a kitchen ta tarar da dija na yankan kayan miya suka gaisa dija tace “ya na ganki kamar bakida lafiya? Fatu tace “kaina ke ciwo, ina mummy? Tace “tana gidan hajia sadia, a zubo miki abinci ne? Fatu tace “a’a kiyi aikinki zan zuba” daukan plate tayi ta zuba tuwon shinkafa ne miyar ugwu yasha kifi da nama sai kamshi yakeyi, spoon ta dauka ta fito daga kitchen din, a dinning ta zauna tafara cin abicinta, wayarta ta dauka sai a sannan taga text din sultan, fuskarta ba yabo ba fallasa ta ajiye, tana gama cin abinci takai kitchen ta dawo falo ta kunna data wayarta, mssgs na sultan ta gani duk na ban hakuri, ta karancesu tsaf ta kashe data ta kunna kallo amma hankalinta baya kai sai tunani, a haka mummy ta shigo tayi sallama bata jita ba, sai da ta taba ta sannan ta juyo a dan tsorice, ganin mummy ne ya sata fara’a tace “sannu da dawowa mummy” Mummy ta kalle ta fuskarta da damuwa, zama tayi tace “fateema lafiyanki kuwa? Idan akwai abunda ke damunki ki fada min, karki boyemin komai I’m ur mum” kanta ta kwantar akan kafadan mummy yayinda hawaye masu dumi suka biyo fuskarta tace “mummy nayi missing din gida ne, tunda nazo banje ba haka kuma banji daga garesu ba” shafa kanta mummy tayi tace “karki damu, in kin kusa komawa skul zakije musu, saboda akwai abunda nake so in aiwatar kafin kije”
Maman Fateey????????
[12:04PM, 7/31/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
3⃣6⃣
Yau saturday ya kama ranar da sultan zaije garin modibbo, da kyar da lallami yasa jameel ya shirya ya rakashi, wayarsa ya dauka ya turawa fatu text,
_yau zan tafi garin modibbo, pray for me_
Sai daya tura kuma yaji haushin kansa, yau kusan kwana uku bata daukan wayarshi bata amsa text dinshi, ko yazo ya aika ta fito bata zuwa, rabon daya ganta tun ranar da lubna ta kopsa masa, amma hala kawai ko abinci zaici sai ya mata text, zuwa unguwa da sauransu, amma bata kula shi. Shiga mota yayi ya zauna yana jiran jameel ya fito daga gidansa. Fitowa jameel yyi tare da lubna sai wani mannewa juna sukeyi suna I miss u, I miss u, haushi ne ya cika sultan ya danna horn da karfi wanda yasa suka dawo cikin hayyacinsu, tsaki jameel yaja yace “mallam zaka kashe min kunnen yaro” ko kulashi baiyiba, yanashiga yaja motar suka fara tafiya. Tittitititi alamar shigowan saqo da sauri sultan yaja birki wanda yasa jameel tsorita shi ya aza ma sun buge wani ne, da sauri Ya dauki wayan ya duba saqone daga fatu
_ka gaisheta_
Shine abunda ya gani, wato duk mssgs dinshi tana gani wannan ne kawai taji zata amsa? Jameel wanda har yanzu zuciyarsa bai daina bugu ba yace “amma kai dan iska ne sultan, wannan wani irin ganganci ne zaka tsayar da mota cikin sauri haka? Kuma akan wata kake qoqarin kashe mu duka? Da mamakin shi sultan murmushi yake yi yace “srry dude, na love” jameel bai iya qara cewa komai ba don tsananin mamaki, shi ko ada da yake cewa in soyayya ya kama sultan zaisha wahala to bai taba zaton abun zai kai haka ba. “This is madness” sultan ya kunna motar yace “indeed”. A haka suka kama hanyan kumo, jefi jefi sultan na bude saqon yana dubawa, da jameel yaga abun yayi yawa yasa ya karbi driving din, sultan yayi ta gwada calling fatu ko zata dauka amma taqi dauka, daya gaji ya hakura. Fatu kuma yau levels ta kawo mata ziyara, a daki na gansu suna zaune akan gado, fatu tayi wani _silent_ kamar marainiya xahra na bata baki “bai kamata kisa damuwa a ranki, duk da nasan its hardly ace baki damun ba amma gaskia ki sassautawa zuciyanki, addu’a zaki cigaba dayi, ki barwa Allah komai, kinji kam? Fatu da alama bata jin abunda xahra k fadi don wayarta take dannawa a hankali, kwace wayar xahra tayi pics din sultan take kallo, ido xahra ta bita dashi yayinda fatu ta gyara kwanciyarta ta bawa xahra baya, “ehh lallai babyn nan wato ni na zauna ina baki shawara kin maida ni bi ta can ko? Kinata kallon mijinki” tashi xahra tayi ta dauko laptop din fatu da sultan ya saya mata wai na karatu tace “me ma pasaword din? Sarai tasani amma ta tambaya _”SULTAN”_ fatu ta bata amsa, daria xahra tayi tace “soyayya ko wahala” ta cigaba da danne dannen ta har ta samu film din da take so ta fara kallo. Fatu kuma tunani ne fall a ranta na abunda zai faru in sultan ya isa ya tarar fatu ta fita nemansa months back!!!