HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Maman Fateey????????

[9:28PM, 8/3/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

3⃣9⃣

 

Ba fatu kadai ba har lubna da xahra mamakine a fuskarsu, tsintan  pieces na pic din sultan ya fara yana ajiyewa a gefe, jameel ne ya shigo ya tsaya a kanshi yayinda su fatu ma suka matso suna ganin ikon Allah. Sai daya gama tarawa ya kwashe, yazo zai wuce ta kusa da fatu, tsayawa yayi yana kallonta itama ta tsura masa ido, har ta fara tausaya masa ganin a yini daya har ya fara susucewa, kawar da kanta tayi shima ya wuce bai ce mata komai ba, zama yayi a kujera ya jawo centre table ya baza pieces din ya fara jerawa, jameel ne ya zauna kusa dashi ya dafa kafadarshi yace “sultan” bai kalleshi ba yaci gaba da jerawa amma ko kadan basu jeru ba don kuci kuci suke, gumin da yake hadawa ya diga akan wani piece yayi saurin gogewa hakan yasa abunda yayi qoqarin hadawa kusan minti 10 ya wargaje, watsa nakan table din yayi a qasa ya dafe kanshi, ya kwantar da kanshi akan kujera, jameel da yake gefenshi yace “kayi addu’a sultan” addu’o’I ya fara idonshi a rufe yana dafe da kanshi. Jameel ne ya fara basu labarin abunda ya faru tun zuwansu, yana qarisawa sultan ya tashi zai fita, jameel ya tareshi yace “ina zaka je? Ka huta tukun” girgiza kanshi yayi yace “zanje gida ne, ka kai hoton gidan tv a fara cikiyanta don Allah, da gidan radio please” yana gama maganarshi ya fice, jameel yabi bayanshi. Lubna ta juyo da dubanta gurin fatu wacce take danna wayarta alamar bata da matsala tace “fateey ya kamata ki fada mishi kece, kiga fa yanda yake qoqarin zaucewa” tsayawa tayi da danne dannen tace “dadina daya da basu bayyana wa kakana ba” xahra tace “u have to talk to him” tashi tayi ta tsaya tace “a’a ba yanzu ba” murmushi tayi tacigaba “na zauna tsawon shekara daya cikin zullumin inda mijina yake, nayi kuka, nayi addu’a, duk inda nabi mutane magana sukeyi anacewa ga bazar bazar, wato mace mai aure amma ba miji, kaka ya hana ni fita, haka na zama tamkar mujiya, cikin gidan ma ba’a barni ba, goggo asabe cikin gaya min baqaqen maganganu take” juyo da dubanta tayi kan su xahra tacigaba “duk akan waye na sha wannan bakin ciki? Akan sultan, dalilin cewa ni baqauyiya ce, wacce bata waye ba, ban dace dashi ba” lubna tayi ajiyar xuciya tace “bawai na raina halin dakika shiga bane, a’a kinaji yanda DJ ya fadi abunda ya faru, har suma fa yayi” murmushi fatu tayi tace “babu abunda zai sameshi, xahra mu tafi” sallama sukayi wa lubna suka wuce gida, ita lubna har ta fara tausayawa sultan, fatun ma ta tausaya mishi amma tayi alqawarin saiya horu tukun, tana son nuna mushi dan adam ba abun wulakantawa bane, kuma cewa “kare ma yanada rana, balle mutum dan adam mai tunani da hankali”

 

Maman Fateey????????

[4:13PM, 8/5/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣0⃣

 

Fitansu suka wuce gidan tv bayar da cikiyan, ba qaramin daru sultan ya tayar musu ba kan sunce bazasu karbi hoton a matsayin wanda zasuyi cikiyar ba, A cewarsu suna buqatan hoton ta na yanzu, yanda jama’a zasu ganeta, da kyar suka karba ganin yana neman daga musu hankali, suka ce zasu saka amma ba dole bane jama’a su gane ba. A gidan radio ma hakan ya faru sun buqaci a fada musu kamanninta da shekarunta, kamannin Jameel ne yayi guessing ya fada shekaru kuma sultan yace “17 noo 18” kallon mamaki ma’aikatan suke binsu dashi, ace yazo a masa cikiya amma bashida  cikekken details.

A hanyansu ta dawowa sultan yayi shiru yana tunanin abunda zai faru gaba, don shi gani yakeyi fatu ta mutu ko kuma an sace ta, gani yakeyi baza a taba ganinta badon wata takwas ba wasa ba, yanzu me zai cewa mammin sa, yanda take muradin ganin qanwarta da zuriyarta, akan son kai irin nashi ya saka mafarkin mahaifiyarshi bazai taba zama gaskia ba. Hawaye naga ya gangaro a fuskar sa, yayi saurin gogewa don kar jameel ya gani, Yace “jameel nayi kuskure kuma nayi nadama, daa na yarda da qaddaran auren yarinyar nan daa haka sam bai faru ba, nayi wa mammi alqawarin nemo mata qanwarta, amma sai gashi ta dalilina da selfish mind dina nayi sanadiyyar bacewar the one nd only blood din aunty na. Ban san a wani hali yarinyar take ciki ba, ko tana raye ko ta fada hannu mara kyau I dunno, jameel Allah zai kamani akan hakkin fatu, tana matsayin matata shekara da wata takwas ban waiwayeta ba” muryan shi ya fara rawa hawayen da yake qoqarin boyewa ne ya silalo, jameel ya kalleshi ya girgiza kai cikin tausayawa, sultan ya cigaba da magana bayan ya share hawayen “jameel da na dauki shawararka tun bayan auren da ban shiga matsala yanzu ba, yarinya ce fa, she’s just 17 a lokacin, tana kuka ina fada mata maganganu marasa dadi, kamar qanwata take fa, qanwata ce kuma matata” gyara zamanshi yayi idonshi na hawaye yacigaba “ban san wani hali kakanta da mummy zasu shiga ba in har ba’a samu yarinyar nan ba, ban san da wani ido zan kalle su in musu bayani ba” Zai qara magana jameel ya dafa kafadarshi yace “its ok, ka rage damuwa sultan, za’a sameta da yardar Allah”

[9:17PM, 8/5/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣1⃣

 

Sun shigo unguwan jameel yace “mu wuce gidana muci abinci ne? Sultan yace “ka kaini gida kawai, nikam na koshi” gidan su sultan ya nufa, a haraban gidan yayi parking ya fito amma sultan yaqi fitowa, gani yake yana shiga mammi zata karanci abunda ya faru! Jameel ya bude masa kofa ya jawo hannunshi ya fito dashi kamar mara lafiya, a palour gidan ya zaunar dashi ya fara kwalawa amrah kira, amrah da take dakinta ta amsa ta fito ta gaishe shi ta dubi sultan da ya wani sanyi dashi kamar maraya tace “ya sultan bashida lafiya ne? “Ehh, ki kawo mishi abinci” tace “too” ta wuce kitchen, dai dai nan mammi ta fito daga dakinta tana waya, ganin sultan cikin wani yanayi da bata saba ganinshi ciki ba yasa tace da wanda take wayan “zan kiraki anjima” ta kashe, jameel ya gaisheta hankalinta na kan sultan da yake binta da ido kamar yau ya taba kallonta (yayi laifi yana tsoron duka????) Tace “meya sameka _manga_? Runtse idonshi yayi, ji yakeyi kamar ya fada mata laifin daya aikata na wasa da rayuwar abunda take muradin gani. Jameel ya ari bakinshi yace “kanshi ke ciwo mammi kuma bai ci abinciba, a bashi paracetamol in yaci” amrah ta fito da tray a hannunta ta ajiye a qasa tace “inyi serving ne? Mammi tayi saurin cewa “ehh” jameel ya musu sallama ya tafi gidanshi cike da tausayin halin da abokinshi yake ciki, Amrah ta zuba masa a plate jalof na spaghetti da irish potato yaji kifi, da kyar ya yadda yaci don sai da mammi ta bata rai tukun, magani ta ballo masa ta bashi dolenshi yasha ba don zai yaye mishi matsalan da yake ciki ba. Yana gamawa mammi tace ya tafi dakinshi ya kwanta ko na 30mins ne.

Su fatu na isa gida suka wuce dakinta, tunanin fatu daya yanzu kuma, kar magana ta fito mummy taga laifinta, shiru tayi tana tunano halin da tabar mijin nata ciki, xahra ta buge ta tace “kinyi abu yana damunki, ko a yanzu sultan ya jijjiga, abeg karki sashi kwanciyar asibiti, kinsan ajeebo ne bai saba da damuwa ba” harara fatu ta watsa mata tace “eeyee tunda ni kuma ajeebako ce na saba da damuwa sai in tausaya mishi ba? Levels tace “ba haka bane qawas, lamarin duniyan nan in kowa yace zai rama abunda aka masa fa baza’a zauna lafiya ba, kuma hakuri yana da kyau, ko yanzu ya gane kuskurenshi kuma yayi nadama, shawara nake baki” tana gama fada ta shige toilet. Kogin tunani fatu ta fada  ‘tana son mijinta sosai, tana son kasancewa tare dashi, amma yini daya yayi kadan a cikin horon laifin daya aikata’ ajiyar zuciya ta sauqe ta rafka uban tagumi, alamar an bude kofa yasa tayi saurin sauqe tagumin, xahra na fitow tace “ni zan tafi gida” rakata tayi mal habu ya maida ita, fatu ta dawo gida cikin damuwa, kitchen ta nufa tana taya dija aiki don rage yawan tunani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button