HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Maman Fateey????????

[10:14PM, 8/7/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣2⃣

 

Sultan a room dinshi ya kasa samun sukuni, ya kai gauro yakai mari, tunaninshi ina fatu zata iya zuwa a nan garin, tuno maganar jameel yayi ranar da aka daura musu aure suna hanyan dawowa…. jameel ya miqa mishi pic yace “ga pic dinka” ko kallonshi baiyi ba yace “don Allah mallam ka barni, duk kai ka jawo min, ka wani saurin amsawa kamar kai za’a aurawa ita, gaskia ni baka min dai dai ba” girgiza kai jameel yayi yace “yarinyar nan tana da nutsuwa ga hankali, baka san alkhairin da ke tattare da auren nan ba, nine kai daukanta zanyi ta zauna a matsayin matata har lokacin da naji na fara sonta, koda ban sota ba zan zauna da ita saboda yar’uwata ce kuma zan iya qara aure nan gaba, ni dai na bata address na gidanku idan baka zo ka dauketa ba zata biyoka” yana tunawa a lokacin haurawa sukayi sosai akan wai jameel yana masa katsalandan a rayuwa “don meyasa zaka bata address dina? Baka taba bata min rai irin haka ba jameel” dawowa daga tunanin yayi yace “may be tazo nan” da sauri ya fita gurin maigadi yana kwala masa kira Iliya ya fito daga bandaki da gudu yace “yallabai gani” yace “wata takwas da suka wuce wata mace tazo nan gidan tana nemana?  Daga kai iliya yayi yace “babu wacce tazo nemanka sai wannan yarinyar sharipa da kace kar in kuskura in barta ta shigo, ita ce take zuwa lokaci lokaci nemanka, wallahi yalla…. sultan ya katse shi yace “ba ita na tambayeka ba, babu wacce tazo kamar yar kauye kauye haka? Iliya yace “a’a yallabai, sai dai yar aiki da hajiyayya ta kawo kwanaki, naji ita ke share maka daki. Juyawa sultan yayi da sauri cikin gida, a palour ya tarar da mammi da amrah na hira, lokacin yamma yayi liss, mammi ta kalleshi tace “sultan ya kaji jikin? Yace “da sauki” don shi har ya fara tunanin ko larai mai gyara masa daki itace fatu, yace “mammi ina larai mai gyara mini daki? Mammi tace “amrah kira min ita” da sauri amrah ta tafi kiranta. Mammi ta dawo da dubanta gurin sultan tace “manga wani abu ta maka? Girgiza kai yayi yace “a’a tambaya zan mata” mammi tace “to” nan amrah ta shigo larai na binta a baya a tsorice Allah yasa ba laifi tayi ba, kallonta yayi, yayinda ita kuma ta durkusa a gabansa jiki na bari tace “gani ranka shi dade” alama ya mata data miqe, da sauri ta miqe amma kanta na kasa, kallonta yayi yana tuno kamannin fatu, fatu fara ce wannan kum baqa, fatu kyakkyawa ce wannan kuma masha Allah????, fatu yarinya ce wannan kuma da alama ta haihu 7, sai dai rashin jiki da tsayi wanda in baka ganta da kyau ba zaka ce yarinya ce. Tsaki yaja yace “jeki kawai” zama yayi a kujera yayi shiru Mammi da take kallon show din tun daga farko tace “sultan lafita kuwa? Ka kira mata kuma baka ce mata komai ba, me yake damunka ne yau din nan? Kallon amrah yayi yace “kije dakinki zanyi magana da mammi” ba musu ta wuce dakinta. Zamowa yayi ya zauna a kasa kusa da kafafun mammi yace “mammi ki yafe mini, na miki laifi”

 

Maman Fateey????????

[7:30PM, 8/8/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣3⃣

 

Kallonshi mammi tayi cikin rashin gane me yake nufi, tace “me ka mini sultan? Ina jinka” qara sunkuyar da kansa yayi ya fara bata labarin tun daga farko har karshe, anan yace “ki gafarce ni mammi wallahi son zuciya ne ya kaini da aikata haka, nasan nine silan bacewarta, zan nemo miki ita a duk inda take mammi” ya qarisa maganan yayinda yake riqe da kafafuwanta, shock mammi ta shiga, Kasa magana tayi don ranta yayi mugun baci, hawaye ne ya gangaro daga idonta, ‘wannan wani irin rashin hankali sultan yayi? tashi tayi zata tafi, sultan da yake riqe da kafanta ya dago ya kalleta, hawayen daya gani a fuskarta yasa hankalinshi qara tashi, magiya ya fara yana kuka yana bawa mammi hakuri, kwatar kafanta tayi bata ce dashi komai ba ta shige dakinta, shirun mammi yayi yawa, shi da dukansa tayi ko ta masa fada amma shirunta na nufin abubuwa da yawa har da ‘kar in qara kallon fuskar ka’ tashi yayi ya fita yana share hawayen da baisan lokacin da suke ambaliyan fitowa ba, in ka ganshi sai kace yayi sati a kwance, duniyar gaba daya yaji ya fita a kansa, idan yau akace an samu fatu to duk soyayyar duniyan nan zai dora a kanta, “where are you fatu” ya furta yayinda ya fice daga gidan zuwa masallaci sallan maghrib. Yana idar da sallah ya shige motarshi ya dinga bin unguwa unguwa ko Allah zaisa yaga fatu, a wata unguwa yayi sallahn isha, ya samu limamin mosque din yace a tayashi da addu’a matar shi ta bata, Limamin ya mishi alqawarin tayashi addu’a, yawo ya cigaba dayi, idan yaga masu neman taimako sai ya taimaka misu, bai dawo gida ba sai kusan 11, abunda bai taba yi ba. Yana shigowa yaga kiran abbanshi ya dauka yayi sallama aka amsa mishi, abba yace “kazo palour na ina son ganinka” cikin girmamawa yace “too abba, gani nan”. Da sallama ya shiga ya samu mammi ce da abba zaune, kallon mammi yayi ta dauke kai, daka ganta zaka san tana cikin bacin rai. Gaishe su yayi mammi taqi ta amsa, abba ne ya fara magana “Mahaifiyarka ta sameni da magana wanda banji dadinsa ba ko kadan, hakan da kayi ka nuna cewa kayi girman da mu iyayenka babu ruwanmu da sha’anin rayuwarka, abunda kayi niyya shi zakayi, kusan shekara biyu da aura maka mata amma mu iyayenka bamu da masaniya, baka kyauta ba ko kadan” sultan da kanshi ke qasa tun da abba ya fara magana ya samu bakin cewa “nayi kuskure abba, kasa baki mammi ta yafemin”

[9:09PM, 8/8/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣4⃣

 

Nasiha sosai abba ya mishi kana ya kalli mammi yace “hajia sadia kinsan sha’anin yara da rashin hankali, kiyi hakuri yayi nadama” kasa furta komai tayi, alama abba ya mata da ido yasa tace “naji, wani mataki ka kai na nemo ta? Sultan da yaji sanyi a ranshi yace “na bayar da cikiyanta a gidan Tv da radio, insha Allah za’a sameta” jinjina kai mammi tayi tace “Allah yasa” tambayoyi abba ya mishi ya bashi amsa sannan yace “kaje ka kwanta, zan nemeka gobe akwai abunda za’ayi” da farinciki sultan ya musu sai da safe ya fita. Abba ne ya fara bawa mammi baki sai daya tabbatar ta rage damuwa sannan suka kwanta.

Sultan na shiga dakinshi ya shiga wanka, bayan ya fito ne ya saka kayan bacci daukan wayanshi yayi, ya lalumi aljihun rigan daya cire ya fito da pic din fatu tana 3yrs, inka ganta kaman baby doll, taci kaya masu ado an mata jagira ga jan farce an mata diqo dashi a goshi, tasha kwalli rambadadau, bakinta ne da alama ba’a mishi kwalliya ba don pink ne, zura mata ido yayi yace “sweet matata yar rigima, kina bani wahala” nan take ya tuno da fateema yace “sai na samu fatu zan dawo kanki” daukan pic din yayi a hoto ya postin a facebook, twitter, da duk wani chat da yakeyi yace “duk wanda ya ga mai kama da ita yar 18yrs ya fada masa, akwai kyauta ga duk wanda ya sameta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button