HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Fatu tana gama Taya dija aiki ta wuce dakinta, tama rasa me zatayi, gashi ba makaranta balle karatu ya debe mata kewa, chattin ta fara tana karanta novels anan taci karo da sabuwar littafin BEBEELO ‘HANNE ????’ daria takeyi tace ‘lallae hanne kin cika bomb’ kiran sallahn maghrib yasa ta tsaya da chattin ta wuce tayi sallah, farouq ya shigo dakinta yace “anty fateema ki bani laptop dinki inyi game” ya rausayar da kanshi, linke sallaya da hijabin tayi ta ajiye akan bedside drawer ta kamo hannunshi suka zauna akan gado tace “baka ce please ba” kama kunnenshi yayi yace “ok please kinji? Murmushi tayi tace “zan baka amma sai munci abinci tukun” washe baki yayi yace “nagode” taja hancinsa tace “u ar wlcm” hira suka yi har aka kira sallah isha, farouq ya tafi mosque ita kuma ta kabbara nata, bayan ta idar ta sauko palour ta tarar da mummy a palour da alama itama bata jima da fitowa ba, fatu ta mata sannu mummy tace “Yau kuma kin zama matar daki” murmushi tayi tace “na fito dazu kina daki ne” sallama farouq da mahmud sukayi suka shigo, fatu ta fadada fara’ar tace “oyoyo mutan abuja” daria yayi yace “inda wata bata taba zuwa ba” fushin wasa fatu tayi tace “anji, nima watarana zanje” mummy tace “kyale shi, kuje kuci abinci, dadynku ya dawo daga mosque ne? Ta tambayi mahmud, yace “nidai tahowan mu mun barshi da abban amrah a haraban masallacin” “ok” mummy tace ta tashi ta wuce side din daddy. Fatu suka wuce dinnin tayi serving dinsu sai wasa da daria sukeyi ita da mahmud, yana ce mata yar qauye. Bayan sun gama ne ta tattara takai kitchen ta dawo palour suka qara bude babin wani hiran, farouq ya tuna mata alqawarinta tace yaje ya dauko laptop din a daki, bayan ya dauko ta cire masa password din ya fara game suka cigaba da hiransu. Kusan 10 mummy ta shigo tace “farouq kaje ka kwanta” dama ya fara gyangyadi, ya tashi ya tafi dakinsa, su fatu suka mata saida safe ta wuce side din daddy. Sabon hira suka bude anan fatu tace “yau baka ga sultan ba? Yace “na ganshi, ana idar da sallah ya fice a motarsa, kamar ma bashida lafiya” daria fatu tace “yaje garin modibbo ne ya samu bana can shine ya shiga tashin hankali harda suma” zaro ido mahmud yayi yace “yaushe? Murmushi qarfin hali tayi tace “yau” gyara zama yayi yace “kin sanar dashi ne? Girgiza kai tayi alamar a’a. Mahmud yace “karki dau alhakinsa fa madam” tace “bazai kai har can ba” dauko wani zancen sukayi na case din da ya gama abun daria abun haushi yana bata labari, su ne basu tashi ba sai 11, bayan ya fita ta kulle kofa ta haura upstairs zuwa dakinta, wanka tayi tasa kayan bacci ta dauki wayarta ta bude data mssgs suka shigo, updates din sultan ne ya bata daria da tausayi, tace ya kamata in masa jaje, typing ta fara masa.

 

Maman Fateey????????

[10:14AM, 8/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣5⃣

 

_Allah ya yasa a ganta cikin sauqi, ya kuma kare na gaba._

 

Abunda ta tura mishi kenan, yana cikin ganin comments din mutane yaga na Fateemah Mahmud da sauri ya karanta, yaji dadin jajen da ta masa, a zuciyarsa yace she loves me.

 

_Thanks alot baby_

 

Murmushi tayi tace duk randa ka gane nice fatunka akwai drama.

Kashe data tayi ta kwanta amma ta kasa bacci, tunanin mijinta kawai takeyi ko a wane hali yake ciki sai Allah, rungume pillow tayi tana aukin tunanin sultan dinta har bacci barawo ya saceta.

Sultan yaga bata qara masa reply ba a ranshi yace da sauran aiki kenan, ganin dare ya tsala yasa ya shiga toilet ya daura alwala ya fara nafilfili, Allah yasa a ga matarshi fatu.

 

Washe gari haka ya tashi duk jikinshi na mishi ciwo saboda rashin bacci da bai samu ba jiya, hatta idonshi sai da suka kumbura. Misalin 8:12am ya shiga palourn abban nashi, samu yayi mummy na jera abinci akan dinning table duk jikinta a sanyaye, ganin yanayin danta yasa ta tausaya mishi, gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, tace “sultan kayi bacci kuwa jiya? Shiru yayi tace “magana nake maka” ya dago da kanshi yayi yaqe yace “nayi mammi” bata yarda ba don daga ganinshi bashida kwanciyar hankali. A daidai nan abba ya fito yana daura agogo a hannunsa, mammi ta isa ta tayashi, sultan ya gaishesa, abba yace “kaci abinci kuwa? “A’a, na koshi ne” ya bashi amsa, “kaji mini shiririta, rashin cin abincinka zai warware maka matsala ne, zo nan ka zauna kaci abinci, hajia zuba masa” Zama sukayi duka akan dinning table din mammi ta zuba masa dankali da kwai ne sai ferfesun zabuwa wadda yaji kayan hadi, ga ruwan lipton a gefe, mammi ta tashi zata tafi abba yace “kefa? Tace “ba yanzu zanci ba” dukansu suka bita da ido yayinda ta fice daga falon, sultan kamar yayi kuka, abba ya girgiza kai ya fara cin nasa amma sultan sai jujjuya fork din yakeyi cikin abincin, ganin haka yasa abba yace “idan kaci akwai good news” sultan ya kalli abban nashi, shi kuma ya masa murmushi, cin abincin ya fara don yasan good news a yanzu bai wuce ace an fara tracing inda fatu take ba, yaci abinci sosai.

Suna gama karyawa abba da sultan suka fice daga gidan, driver ne yayi driving dinsu a motar abban nashi, a hanya abba yake fada masa zasu je gidan commissioner ne a watsa masu nemo fatu saqo saqo na gombe a binciko inda take, hatta local govs sai an bincika, dadi ne ya cika sultan, don yana mai fatan Allah ya karbi addu’arshi ya takaita mishi wahalan nemo fatu, gidan suka je aka musu iso nan da nan don abban nashi sananne ne, kuma commssnr abokin shi ne. Bayan sun gama gaishe gaishe abba ya masa bayanin abunda ke tafe dasu, cmmssnr yace “alhaji za’a sa a nemota, kuma ya kamata a fadawa su iyayen yarinyar don watakila ta gurinsu a samu wani haske” abba yace “tashin hankalin da zasu shiga muke tunani, basu da kowa anan garin da zata iya zuwa can” magana suka cigaba dayi ta yanda za’a bullowa al’amarin. Basu tashi ba sai da suka gama tsara yanda za’ayi komai, Sukayi sallama driver ya ajiye abba a office, sultan kuma ya koma gida.

Fatu ta tashi washegari wasai abunta, bayan sun karya ne farouq ya fita wasanshi a cikin gida, suka zauna a palour da mummy suna kallon wani indian series jefi jefi suna hira.

 

Maman Fateey????????

[10:21AM, 8/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣6⃣

 

Sultan na dawowa gida ya tarar da mummy a dakinta ta zuba uban tagumi yayi sallama ta amsa, yace “mammi….” daga mishi hannu tayi tace “bana son jin komai daga gareka sultan, idan kana son kaga farinciki na ka kawo min fatu, ban taba tunanin bakada tausayi irin haka ba, yar uwarka ta jini ka barta cikin wahala da uquba don kawai an aura maka ita? Ka tashi ka bar mini daki” tashi yayi ya fita yana share hawaye ashe mammi ba yafe masa tayiba?

Gefen mammi tana tausayin danta amma kowanne second ta tuno bacewar fatu wanda ta dalilin sultan ne sai taji bakin ciki mara misaltuwa, share siririn hawayen daya zubo mata tayi tace “Allah ka bayyana fatu a duk inda take”

Yana fita kai tsaye ya shiga motarshi maigadi ya bude masa gate ya fita, motar jameel ya hango ta nufo shi parking yayi a bakin hanya jameel ya qara gaba kadan shima yayi, tare suka fito jameel ya nufo shi yayinda sultan ya jingina da motarshi, gaisawa sukayi jameel yana lura da shi yace “sultan yaya dai” yace “na fadawa mammi komai” Da sauri jameel ya kalleshi cikin tashin hankali yace “why? Meyasa baka bari har sai mun nemo fatu ba? Baka tunanin mammi zata shiga wani yanayi? Yanzu mebya faru? Sultan ya fada masa yanda akayi jameel ya girgiza kai yace “daa ka nemi shawarata tun farko bazaka fara fada mata ba, yanzu abun ya zame maka biyu, ga neman fatu ga tunanin halinda mammi take ciki” sultan yace “gani nakeyi kowanne daqiqa laifina qaruwa yakeyi, gani nakeyi rashin fada mata da wuri zaisa ta tsaneni, gani nak…….” “its ok” jameel ya tareshi yana bubbuga kafadunshi Qoqarin shiga motarshi ya fara jameel yace “ina zaka je? Shiga yayi ya kunna motar yace gidan tv and radio” jameel yace “kace min abba yayi magana da cmmsnr” yace “ehh, bamusan ta ina za’a ganta ba, yafi a bawa ko’ina muhimmanci” jameel yace “ka jirani in ajiye motata a gidanku in fito” kallonshi sultan yayi yace “jameel kar in daura maka wahala” yace “damuwarka tawa ce, what are frnds for? Shigar da motarsa yayi gidansu sultan kana suka tafi. Sunje amma babu alaman nasara haka suka dawo gida jiki a sanyaye nan ma jameel na kwantar masa da hankali, hannayensa ya dora akan steering yace “ka fadawa mammi zan nemo mata fatu, zan zo tare da fatunta, da daina fushi dani” jameel da bai gane nufinshi ba ya fita daga motan yana qoqarin zagayawa ya budewa sultan, kafin ya ankara har sultan yayi reverse ya fice a gidan da gudu. Yayi Saurin shiga motarsa yabi bayanshi amma ko alamarsa bai gani ba, ya nema sa duk inda yake zaton zai samesa amma babu labarinsa, hankalinshi yayi mugun tashi don za’a yi biyu babu yanda ya fita da gudun nan komai kan iya faruwa dashi, naushin steering yayi ya furzar da iska, ji yakeyi kaman shima yayi kukan, da sauri ya lalubo wayarshi ya dialing number sultan amma ‘switch off’ sauran numbers din ya gwada suma duk a kashe, cikin tashin hankali ya nufi gidansu sultan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button