HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Maman Fa’iz????

[9:05PM, 5/7/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

 

0⃣4⃣

Fitowa hajia tayi daga motar ta zagayo inda fatu take, bude murfin kofan tayi ta kamo hannun fatu suka shigo cikin gida ta zaunar sa ita kan kujera a palour. Fatu ta cigaba da kukanta. “Dija dija” dija ta fito dga kitchen ta ce “gani hajia” hajia tace “taimaka min da ruwa pls” komawa kitchen tayi ta fito da tray an daura swan water da cup. Ta ajiye ta koma tana tunanin wace yarinya ce haka hajia ta samu? Daga kafada tayi tace hala yar aiki ce. Hajia ta tsiyayi ruwa ta miqa ma fatu wacce kukanta ya tsaya sai sheshsheka takeyi tace “kisha ruwa” ba musu ta karba ta sha, tayi ajiyar zuciya. Hajia ta numfasa ta fara magana “fatu a yanda na lura da yanayinki kina cikin matsala, kuma kinyi yarinya a barki ki fito daga kauyenku ke kadai ba tare da wani dan uwanki ba. Tambaya nake son miki, ki fadi tsakaninki da Allah, gurin waye kika zo anan garin? Fatu da tunda hajia ta fara magana kanta na qasa tace “gurin dan’uwa na nazo”  ” a ina yake?  Fatu tace “na manta sunan unguwan amma yana cikin jakata. “Farouq farouq hajia ta kira shi yana room dinshi yana buga game, tun 12:30 y dawo daga skul. “Gani mummy” “jeka room dina ka dauko min wani skul bag akan bedside drower. Yace “to, amm mummy wannan ba itace ta mutu dazu ba? A cikin motarki. Hajia tayi daria tace a’a suma tayi not mutuwa, now get d bag. Ya juya da gudu ya dauko ya miqawa hajia ita kuma ta miqawa fatu, gurin fatu yaje da take kallonsa tun farkon shigowarsa. Yace daxu mum ta bugeki, kinji ciwone? Tace “a’a tana murmushi, amma kin suma ko? Tace ehh. Zai qara wata tambayar hajia ta katse shi tace ” farouq jeka fara shirin islamiyya. In ka dawo she wll answer all ur questions. Ya haura sama da gudu yana cewa to mummy kar ta tafi, ta jirani fa.

Aljihun gefe na skul bag din fatu ta bude ta ciro wani pic hade da guntun paper ta miqawa hajia kulsum. Mamakine ya bayyana qarara a fuskar hajia data kalli pic din, paper ta bude ta qara gaskata abunda ta gani. Ba komai ta gani ba illa pic din sultan gefenshi kuma fatu ce, a kauye aka dauki pic din,don ga irin bukkan rumbun nan da ake ajiye amfanin gona. A cikin paper kuma adress na gidansu sultan ne,  wato gida mai kallon gidanta.

Hajia ta dubi fatu tace “wannan dan’uwanki ne? Fatu tace ehhh, “ya dangantakar ku take? Fatu ta numfasa tace hajia zan fada miki ko zaki taimaka min in shiga cikin gidan, don naga kamar sai da mota ake shiga irin gidajenku.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

 

ASALIN LABARIN

Taku

Maman Fa’iz????????

[4:57PM, 5/8/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

 

0⃣5⃣

ASALIN LABARIN

Kamar yadda na fada miki sunana fatima. Dangin mahaifina yan asalin garin modibbo ne, fulanine usul. Dangin mahaifiya ta kuma yan dukku ne, suma fulani.

Kaka na mallam Aminu malami ne sosae wanda yake koyarda almajirai da manya, yana da matarsa binta wacce tun auren saurayi da budurwa suke tare, auren dangi aka hadasu. Yayansu biyar amma biyu ba rai, uku ne suka rayu har girma, goggo innani itace babba, sai sama’ila da kaninshi jamilu sune suka rasu, sai babana mamuda da kaninshi muntari. Tun kafin a haifi muntari goggo innani tayi aure. Tun tasowan babana Allah y yishi mai kokari ta fannin karatu da neman na kanshi, baiyi boko ba amma yyi arabi sosae. Tun yana saurayi ya fara kasuwanci, inda yake bin kasuwannin kauyuka yana sayar da busheshen kubewa. In damina tazo kuma ya taya bbanshi noma. A yawonsa na bin kauyuka ya hadu da mamata a Dukku, tazo siyan kubewa ya ganta yace yana so, itama ta nuna ra’ayin hakan, bai bata lokaci ba ya samu babanta ya masa bayanin inda ya fito da sana’ar sa kuma yaga diyarsa yana so. Babanta yayi murna da jin haka, don akoyaushe addu’arsa bai wuce Rahmatu ta samu miji tayi aure ba, don tun tana karama mahaifiyarta ta rasu anan zamanta ya dawo gurin kishiyar mamanta, ba irin duka zagi da wahala rahmatu bata dandana ba, babanta kuma bashi da bakin magana kamar an asirce shi. Bukatarsa kullum ta samu miji tayi aure ko zata huta. Ya sami yayansa da maganan inda yaqi amincewa, wai tunda gida bai koshi ba baza a bawa bare ba. Kuma ai zatayi nisa da gida. Shi a sonsa a hada ta aure da dansa wanda duk garin bbu wanda baisan yana dauke dauke ba, bashi da takamaimen sana’a. Babanta ya nuna rashin amincewarsa shima, a haka suka tashi ba tare da tsayayyem magana ba. Babana kuma yana komawa gida ya sanar da iyayenshi inda sukayi murna da fatan alkhairi.

Sati daya da maganan babana ya koma dukku don jin amsarsa, Inda ya tafi da kakana wato malam Aminu. mallam sirajo (baban mamana) ya musu iso yasa aka shimfida musu tabarma a zaure, fura da nono aka kawo musu hade da ruwa suka sha sukayi hamdala, sannan aka fara magana. Yayan babana na aka kira yazo, koda aka koro masa bayani yace shi sam bai san zancen ba, fada yakeyi sosai ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, wai sai da baki suka zo sannan za’a kirashi, kuma sai da sirajo ya amince? To me  zaice? Ai yarsa ce yayi abunda yaga dama. Don anga danshi bashida abun hannu amma da mai kudi yazo shine xa’a bata? Karshe ma cewa yayi bbu ruwansa akanta yayi tafiyarsa. Zuciyar fulani ta tashi na mallam sirajo ya cewa mallam Aminu a yau za’a daura auren, karshen iko kenan. A ranar aka daura auren a masallacin garin bayan an idar da sallahn azahar. Sai shigowa da akayi da goro da cingam cikin gida yara na cewa an daura auren rahmatu da mamuda. Da farko ta aza wasane sai da taga inna haule (kishiyar mamanta) na watso mata kayanta waje tana cewa ta hada ta kulle yau zata tafi gidan mijinta. Tana hawaye tana hada kayanta inna haule bata daina masifa ba da yake bakinta daya da su yayan mallam sirajo da matarsa. Wasu na cewa bakin cikinsu ne ya kashe maman rahmatun. Babanta ya mata nasiha ya miqa amanarta gurin kakana. Tana kuka yana hawaye suka rabu. Basu dawo ba sai bayan isha. Kakata tana jiran isowansu sai kawai taga har da amaryan aka taho. Bayan sun huta sunci abinci mallam Amenu yake sanar da ita komai. Ta jinjina lamarin inda ta tausayawa mamata. Dakin babana aka gyara musu inda ya siyo mata duk kayan daki da ake sayawa amarya na wannan lokacin.

 

Hajia kulsum ta numfasa tace fatu ki tsaya anan. Lokacin sallar la’asar yayi. Dakin hajia suka shiga anan ta nuna mata yanda zatayi amfani da toilet din taa barta a ciki ta sauko kasa tana kiran farouq yazo driver ya kaishi islamiyah time yayi. Bayan ta shigo daki ne ta samu fatu har tayi alwala ta fito, sallaya ta miqa mata ta nuna alkiblah sannan ta shiga toilet din don gabatar da alwala. Fatu sake baki tayi tana kallon duniya tun a toilet din take kauyanci taba nan taba can da kyar ta yi alwalan ta fito, a dakin ma sai da taga kamar hajia zata fito ne ta tada kabbara.

 

Taku

Maman Fa’iz????????

[12:26PM, 5/10/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button