HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Ayi hakuri da rashin jin FATU kwana biu, qanwata aka yiwa aiki a tayamu addu’a Allah ya bata lafiya da duk marasa lafiya Ameen. Masu jaje ta group, ta private har masu kira a waya nagode muku da nuna kulawa, Allah ya saka da Alkhairi????????????????. Luv u all????????

 

Maman Fateey????????

[8:48PM, 8/19/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣7⃣

 

Da sauri jameel ya shiga gidan kai tsaye ya shiga falo, a zaune ya samu mammi ta qurawa tv ido wanda daga gani hankalinta baya kan kallon. Sallama yayi ta amsa da guntun murmushin ta, ganin yanayin fuskar sa yasa tasha jinin jikinta tace “jameel lafiya? Sai da ya zauna ya gaisheta a gurguje ta amsa tace “ya na ganka haka? Baka jin dadi ne? Girgiza kai yayi yace “mammi sultan ya fita cikin wani yanayi, na kira layukanshi duk a kashe, kin tsananta fushi a gareshi, ina gudun kar ayi biyu babu mammi” tashi tayi tsaye tana “innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ta dauki wayarta da yake kan kujera a gefenta ta dialing number abba, sanar dashi tayi ta qarisa maganan tana hawaye Abba bai ce komai ba ya katse wayar, gwada layukan sultan yayi duk a kashe, baiyi wata wata ya dawo gida, a palour ya tarar da jameel zaune ya zuba uban tagumi, mammi kuma sai safa da marwa takeyi tana ta kiran sultan a waya amma baya shiga,

Tana ganinshi tayi saurin zuwa gurinshi gaba daya hankalinta a tashe, tace “ka sameshi? Bai mata magana ba ya maida dubansa gurin jameel daya cire tagumin yana gaishe sa, abba ya amsa shima fuskarsa cike da damuwa yace “jameel me yake faruwa ne? Jameel ya kalli mammi tukun abba yace “fada min komai ba matsala” jameel ya kwashe duk yanda akayi har abunda mammi ta yiwa sultan da safe ya fada masa, “kinga irinta ko? Yanzu kam kinji dadi ai, meyasa ku mata bakwa tunani kafin ku aikata abu?” Abba ya fadawa mammi yayinda takaici ya gama rufesa, ganin haka yasa jameel ya musu sallama ya dauki motarsa ya fice a gidan ya shiga gidansu.

“Sadia na miki magana akan yaron nan, kina ganin halinda yake ciki amma kika qara masa akan hakan! Na samu ya fara walwala, dazu gidan commissioner muka je don a nemo matar tashi, mun gama tsara komai, lokaci daya kin bata komai, sai ki fada min waye za’a fara nema” mummy da ta fara hawaye tun dazu tace “kayi hakuri, wallahi naso danne zuciyata amma laifin da sultan ya mini yayi nauyin da bazan iya boye fushi na ba” abba yace “idan wani abu ya samu sultan…..” nan wayarshi ta fara ringin ya dauka.

 

Maman Fateey????????

[10:37PM, 8/20/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣8⃣

 

Gaisawa sukayi da wanda yayi masa wayan, mutumin yace “don Allah da ahaji rufa’I nake magana? Abba yace “ehh, shine” gefe daya akace “idan kanada spare key na motar danka kazo nan ebele road its an emergency” abba bai tsaya tambayan meya faruba yace “gamu nan zuwa” don yasan bai wuce ace sultan yayi hatsari kuma motar taqi buduwa ba, ya dubi mammi ta cikinta ya gama kullewa tana kallonshi a tsorice tace “alhaji lafiya? Qin fada mata yayi yace “ana nemana a office ne” bai saurari me zata ce ba yayi fita. Zama tayi a kan kujera gabadaya hawayen ma ta nemesu ta rasa, idan wani abu ya samu tilon danta sultan ya zatayi? Sultan da amrah kadai suka rage mata cikin ‘yayanta duk sauran daga tayi miscarriage ko kuma suna jarirai su rasu, gashi Allah ya saka mata son ‘yaya, shi yasa take neman zuriyar mahaifiyarta itama tace ga nasu sun tara ‘yaya masu yawa. Zufa ne yaketa keto mata ta ko’ina, tana son tashi tabi bayan abba amma ji takeyi kafafunta bazasu dauketa ba, anan ta samu hawaye ya fara zuba, a haka amrah tazo ta sameta tace “mammi, mammi meya sameki? Share hawayen mammi tayi tace “babu komai amrah, kaina ke ciwo” a sanyaye ta tashi ta shige dakinta, amrah tayi zugum tana tunanin me yake faruwa ne a gidan daga jiya zuwa yau, don daga mammi har sultan yanayinsu ya sauya sosai, akwai abunda yake faruwa amma kowa yaqi ya fada mata. (Kai fatu, kinsa mutane da yawa a cikin damuwa) Mammi na shiga daki ta kira layin abba amma bai dauka ba, tayita kiransa shiru, hakuri tayi ta zauna kawai tana addu’a Allah ya dawo mata da danta lafiya. Abba na fita ya wuce dakinsa ya dauko key din, bai ko saurari driver ba yayi driving da kansa zuwa ebele road, kiran layin mutumin yayi ya masa kwatancen inda suke, nan da nan ya isa gurin amma baiga alaman anyi hatsari ba, asalima motar a parkee take a gefen hanya ga mutane sun zagayeta, da sauri abba ya isa gurin zuciyarsa na fada masa ciwo yayiwa sultan yawa ya mutu, duk dauriyansa sai da zuciyarsa ta karye ganin danshi sultan cikin mota kanshi akan steering babu alaman numfashi a tattare dashi bai kula mutanen da suke masa magana ba ya bude motan gaba daya jikinshi a mace, ya jayo sultan, taimaka mishi wani mutum yayi suka maida shi baya yayinda abba ya shiga driver sit ya kalli mutumin daya tayashi yace “kaine ka min waya? Mutumin yace “ehh nine alhaji” abba yace “shiga muje” suka wuce asibiti dama already ya locking motarsa daya taho da ita.

Jameel na shiga gida ya samu ba kowa a falo, ya zauna jagabb a kujera Fatu ce take sauqowa daga steps tana waya, taci makeup ga kayan jikinta sun amshe ta, da qaramin jakanta yayi matching da takalminta tana cewa “ke dallah yanzu ma haka ina qoqarin shiga mota ne” tana sauqowa suka gaisa da jameel a ranshi yace ‘bakisan halinda masoyinki yake ciki ba’ yace “ina mummy? Tace “ta fita unguwa dazu” Yace “kefa” tayi murmushi tace “wollah zanje birthday party na qawata ne xahra levels” yace “hala bakida labarin am nemi sultan an rasa ko” miqewa yayi zai tafi fatu da ta zama statue ta yi saurin qarisa gurinshi kamar zata shige jikinshi tace “yaa jameel meya samu sultan dina? Ina yake? Tana maganar ne yayinda hawaye ke sintiri a fuskarta kamar famfo, jikinta har rawa yake gaba daya ta fita a hayyacinta kowanne pore na gashin jikinta gumi yake fitarwa “kamin magana yaa jameel” ganin bashida niyyan magana yasa ta fita da gudu, ya kwala mata kira yayi saurin bin bayanta.

 

Maman Fateey????????

[1:04PM, 8/21/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

4⃣9⃣

 

A haraban gidan ya sameta tana kokawa da kuban gate, (ta manta akwai qaramar kofan fita), yayi saurin qarasawa gurinta yana kiran sunanta “fateema, fateema! Ta juyo tana kallonshi amma bata fasa kokawar ba, yace “ki nitsu, idan har kina son jin inda yake.

 

Abba na isa asibiti aka gangara sultan emergency, likitoci uku ne a kansa suna faman nemo numfashinsa, abba ya zauna akan chair yayi tagumi, bakinsa na motsi a hankali alama addu’a yakeyi, wayarshi ce ta qara ringing bai duba ba don yasan mammi ce, bai san me zaice mata ba. mutumin da abba yazo dashi yace “alhaji ayita addu’a insha Allah babu abunda zai sameshi, zai fito lafiya” abba yace “Ameen, Ameen” mutumin yace “ai muna zaune a shagon bakin hanya muka ganshi yazo da gudu lokaci daya kuma yaja birki ya tsaya, shiru shiru bai fito kusan awa daya, ganin haka yasa na tashi in duba ko lafiya, don na shaida motar, ai nima ta unguwar taku nake amma a pantami, da naje na duba sai na kwankwasa glass din motar, shiru shiru bai dago ba har yan majalisan mu suka taso suma suka zo, anan dai suka tabbatar da cewa ba bacci yake yi ba, Shine na kira masinjanka makwabcina ne, ya turo min numbern ka. Abba yace “nagode kwarai mal dahiru” doctors minti 30 suka dauka akan sultan kafin suka samu daidaituwar numfashin sa, dakin hutu aka kaishi don sunce yana bukatan hutu sosai don jininsa ya hau, zai iya farkawa in da next 48hrs. Abba ya dade tsaye a kansa yana tofa masa addu’a, kana ya fito bayan ya shaidawa family doctor nasu ya kula mishi da danshi sultan sosai, mal dahiru yabi bayanshi yana cewa “alhaji ya mai jikin? Yace “da sauqi Alhamdulillah” a haraban hospital din abba yacewa mal dahiru ya shigo motarsa ya ajiyeshi a shago amma yaqi, yace “alhaji zan hau mashin wallahi, iyalinka na jiranka a gida” abba yace “to shykenan” ya dauko kudi mai dan tsoka yabashi, mal dahiru sai godiya yakeyi har abba ya shiga mota ya fita daga hospital din. Sai da jameel ya tabbatar ta nutsu kafin ya fada mata yanda ake ciki, durkushewa tayi a gurin tana kuka mai tsuma zuciya, “duk ni na jawo, nine na jawo” tashi tayi tana kuka make up din zuwa party ya cabe, ta fita daga gidan, jameel ya dauka akan sabanin da suka samu tsakaninta da sultan ne, jikinta ba kwari ta nufi hanyar fita, jameel ya tsayar da ita yace “bazaki fita a cikin state din nan ba” komawa gida tayi ta zauna tana rabzan kuka, ta rasa me zatayi? Tukunna ma ina sultan dinta??? Tashi tayi ta leqa falo ganin jameel yasa ta tsaya, shi kuma qin tafiya yayi don kar a kuma baro wani aikin, ba’aga fatu ba, ba’a san inda sultan yake ba, to in fateema ma ta fita wayasan inda zata je? Layukan sultan ya qara kira amma shiru, ya kira na abba shi kuma bai dauka ba, (Allah sarki, abba bai ma duba ba don ya dauka mammi ke kiransa) yana son fita nemo abokinshi amma yana tsoron barin fateema ita kadai. Ya kusan 1hr kafin wayarsa ta fara ringin ya dauka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button