HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Abba na dawowa ya gida kai tsaye dakin mammi ya nufa don yasan hankalinta a tashe yake tana ganinsa kuwa ta taso yayi saurin zaunar da ita yace “ki kwantar da hankakinki, an samu danki” mammi wacce muryanta ya dashe don kuka tace “ya rasu ko alhaji? Abba yace “yana nan da ranshi sai dai tension da ya masa yawa yasa jininsa ya hau, yanxu yana asibiti zai farka nan da awa 48, tace “Alhamdulillahi, Allah nagode maka, alhaji muje in ganshi” abba yace “a’a kiyi sallah azahar tukun zai muje” ba yanda ta iya tace “to” abba ya fita daga dakin zuwa side dinsa, sai a sannan ya dauko wayarsa ya duba missed calls ciki harda na cmmssnr da jameel, a ranshi yace ‘Allah sarki duk inda yake hankalinshi shima a tashe yake, kiran jameel din abba yayi, yace “jameel an samu sultan, yanzu haka yana asibiti” jameel ya miqe tsaye yace “abba a ina aka sameshi, ya aka sameshi? Abba ya fada masa jameel yace “Alhamdulillah, gani nan zuwa nima” fatu da take labe tana jiran jameel ya fita itama ta fita neman mijinta tayi saurin sauqowa qasa har tana tuntube tace “an same shi? Jameel wanda murna ya sakashi murmushi yace “an sameshi, Allah abun godia” itama murmushin tayi idanunta cike taff da hawayen murna ta sharce tace “muje in ganshi” jameel yace “too”

 

Maman Fateey????????

[9:05PM, 8/21/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣0⃣

 

Motar jameel suka shiga, ya kunna suka fita daga gidan zuwa gidansu sultan don abba ya fada mishi cewa sai sunyi sallah azahar suma zasu je. A haraban gidan suka sami abba na magana da driver yace “ka hau achaba na bar motana a ebele road gurin *FA’IZ PLAZA*” Abba ya miqa mishi key din driver ya karba ya fita, har qasa fatu ta tsugunna ta gaishe da abba, ita kunyan hada ido dashi takeyi don a dalilinta danshi ya shiga wani hali, shiga cikin gida tayi tabar abba da jameel zasu je masallaci.

Tana shiga falo babu kowa, zama tayi kirjinta na dukan uku uku, tana son ta bayyanawa mammi cewa itace fatu amma tana tsoron abunda zai biyo baya, don yanda mammi take son sultan baza taji dadin abunda fatun ta musu ba, kusan minti biyar tana zaune gashi har an kira sallah, amrah ta fito daga dakinta zata shiga dakin mammi, nan taga fatu zaune a falo da uban tagumi, amrah ta kira sunan ta amma inaa! Hankalinta ya gama tafiya, sai da ta matso sannan fatu ta juyo a tsorice, ganin amrah ne yasa ta kwaqulo murmushi wanda iyakacin shi fatar baki tace “amrah” tace “anty fateema lafiya” tace “lafiya lau” amrah tace “mammi tasan kinzo kuwa? girgiza kai fatu tayi tace “a’a, nima ban jima da shigowa ba” amrah tace “ki shiga dakinta mana” fatu tace “a’a, kaini dakinki inyi sallah” amrah tace “to muje” a dakin amrah tayi sallah tayi addu’a Allah ya tashi kafadun mijinta, tana gamawa ta share hawaye a fuskarta ta koma falo, bata dade da zama ba mammi ta fito tare da amrah kowa da shirin zuwa asibiti, fatu ta sunkuyar da kanta qasa ta tsugunna ta gaishe da mammi, mammi tace “sai kika ji abunda ya faru ko? Kasa cewa komai fatu tayi mammi tacigaba da magana “qaddara baya wuce ranar sa, sai addu’a zamuyi Allah ya tashi kafadunshi” kuka fatu ta fara har da sheksheqa, takaicinta daya, meyasa taqi bayyana kanta tun ranar da sultan yaje ya samu bata nan? Gashi yanzu a dalilin ramuwarta mijinta da take matuqar so yana kan gadon asibiti, muryanta a sarqe tace “ban kyauta ba” mammi tausayin fatu ya gama cikata, tana son yarinyar sosai tana son sultan ya aureta ko da an samu fatu, daga mammi har amrah bbu wanda ya gane abunda ta fada, mammi ta isa gurinta ta dago ta daga tsugunon da tayi, ta kama hannunta suka fito haraban gidan suka shiga mota, jameel yana driving yayinda abba na gefenshi, mammi da fatu na baya amrah a tsakiyarsu. Fatu Hawayen dai bai daina zuba ba, ta juya kanta gurin window tana cewa a ranta ‘a yau kowa zai san wacece ni! yau zan dawo fatu! Share hawayen tayi tana mai fatan ganin mijinta ta bayyana masa kanta!!!

 

Maman Fateey????????

[10:25PM, 8/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣1⃣

 

Suna isowa asibitin suka fito suka shiga ciki har kofar dakin da sultan yake, anan suka tsatstsaya suna lekanshi ta window don ance ba’a son a shiga, fatu ta leqa ta ganshi kwance ga drip an daura mishi, ya wani haske ya rame, kuka ne yazo mata tayi saurin toshe bakinta ta fita da gudu, mammi ta bi bayanta tana kiranta, abba ya girgiza kai ya nufi office din dr, jameel da amrah kuma suka samu guri suka zauna cikin jimamin abunda yake faruwa. A haraban hospital din mammi ta samu fatu akan bench a karkashin wata bishiya tana zaune tana kuka, mammi ta zauna kusa da ita ta jawo ta jikinta tana jijjiga ta, fatu tace “mammi kiyi hakuri na miki laifi, nice na jawo halinda sultan yake ciki” ta qara fashewa da kuka, mammi ta dagata tace “kul! Kar kice haka, bakida laifi ko kadan, nice mai laifi fateema” fatu ta zamo daga kan bench din tayi knelling hannayenta nakan cinyan mammi tace “mammi” mammi ta tace “na’am fateema, ki tashi ki zauna, bana son ganin kina kukan nan, ki tashi” fatu ta girgiza kai tace “mammi kinsan inda fatu ‘yar qanwar ki take? Tuno da fatu yasa mammi hawaye ta share tace “a’a fateema, kema kinsan abunda ya faru ko? Muna kan nemanta” Fatu ta kama hannun mammi tace “nice fatu mammi, nice yar qanwar ki rahmatu wacce kike nema mammi, gani gabanki ki mini duk hukuncin daya dace dani” shock mammi ta shiga ta miqe tsaye tana nuna fatu da yatsa, tace “kece fatu? Fatima yar qanwata? Yar mahmud da rahmatu? Fatu dake still a durqushe ta daga kanta alamar ehh hawaye shabe shabe a fuskarta tace “nice mammi, nice wallahi” tsayawa mammi tayi cikin tsananin mamaki tana kallon fatu, wacce sai yanzu take ganin kamanninta dasu sultan da amrah, “ashe ke dama jinina ce, shiyasa nake jinki har cikin raina, nake ganinki tamkar yar dana haifa, Alhamdulillah” mammi ta fada yayinda take hawayen farinciki, lokaci daya kuma ta canja, fuskarta ba alamar annuri tace “meyasa kika kasa sanar dani tun baya??? Dago da kai fatu tayi ganin fuskar mammi yasa ta firgita bakinta na rawa tace “m…mam…mi walla..hi…” mummy ne ta qaraso ita da lubna cikin sauri don tun dazu jameel ya kirasu ya fada musu, ganin yanayin fatu da mammi ya tabbatar musu an bayyana wacece FATU A BIRNI….

 

Maman Fateey????????

[11:22AM, 8/23/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣2⃣

 

Mummy na qarisowa ta daga fatu ta dora kanta akan kafadar mummy tana hawaye abun tausayi mummy tace “its ok daughter, its ok, ki daina kukan nan haka kar ya jawo miki matsala” mammi da take kallonsu cikin mamaki kanta ya kulle, yaya akayi fatu tazo gidan hajia kulsum? tace “hajia how comes fatu ta kasance a gidanki? Please ku cireni a duhu, anya itace fatuna? Mummy tace “itace fatunki hajia, kar kiga laifinta na qin sanar dake da tayi, lubna ku shiga ciki keda fateema zanyi magana da hajia sadia” lubna taja hannun fatu suka shiga cikin hospital din, mammi da mummy suka zauna akan bench din mummy tace “fateema bata da laifi ko kadan mammin amrah, in har hakan laifi ne to nice da laifi, hasalima hakan da nayi shi ya kawo kusancin da yake tsakaninta da sultan, wanda adaa babu wanda yake son dan’uwansa” Mammi tace “naso in fahimceki hajia, ni ba don halinda sultan yake ciki bane, a’a Ina matsayin mahaifiyarta tana kusa dani amma ta kasa fada min? Nifa uwace, kuma nasan kin fada mata yanda nake son ganinsu, sultan kuma shi ya jawowa kanshi, banga laifinta ba, ai ya fada min yanda aka yi har aka daura mishi aure da ita” anan mummy ta fada mata yanda akayi ta kadeta da mota ta kawota gidanta har yau da take bata labari, mummy ta qarasa da cewa “ban san sultan yaje neman ta ba, da nazo na warware komai, fateeman ma inaga bata da labarin cewa yaje can garin midibbon” Murmushi mammi tayi ta daga hannu sama tace “Allah na gode maka, Alhamdulillah, Allah ka bawa sultan lafiya ya tashi yaga fatun shi” “Ameen Ameen” mummy amsa itama tana murmushin jindadin yau ta kusan cika burinta, saura haduwan FATU DA SULTAN. Suna zaune a gurin abba yazo zai wuce commssnr yana nemansa ya kallesu yace “hajia zan wuce gidan cmmsnr yana nemana, inaga akan matar sultan ne” da mamakinshi sai yaga dukansu suna murmushi a ransa yace ‘mata dai akwai matsala’ yasha mur da yake suna wasa da mummy yace “kun tasa ni a gaba kamar qaramin yaro kuna min daria, hala kun shaqi laughing gas ne” ya qarisa maganar da dan murmushin sa. Mummy tace “gashi kaima ka shaqa ai, hajia bari in shiga ciki ki mishi albishir” tana gama fadan haka ta shige cikin hospital din, abba na ganin ta qule yazo ya zauna yana mamakin wani albishir za’a masa, shi dai yasan ba akan sultan bane don yanzu ya baroshi kwance, to kodai an samu matar sultan ne? Noo bazai yiwu ba don basuda link da inda za’a ji labarinta. to menene haka? Kallon mammi yayi yace “bazaki fada min bane sai kinja raina?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button