HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

[7:16PM, 8/23/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣3⃣

 

Hararanshi mammi tayi cikin wasa tace “bribe me” tsananin sonjin menene yasa yadauki wayarshi ya bata, mammi tace “a’a riqe kayanka, an sami matar sultan, fatu ‘yar qanwata rahmatu, tana tare damu kusan shekara amma bamu ganeta ba” abba yace “tana ina kenan” mammi ta bashi labarin komai. Abba cikin mamaki yace “ikon Allah, ranar dana fara ganinta a gida na dauka ‘yan uwa ne daga yola, ku dai mata sai a hankali, ai sai ku sanar damu, hakan da kukayi kun nuna bazaku umurci ‘yayanku akan abunda kuke so ba, sai dai ku biyo musu ta yanda suke so, munada iko akansu tunda mu muka haifesu, Allah ya kyauta, ni zan tafi gidan commissioner in sanar dashi an samu yarinyar” mammi dai tana shiru har ya dasa aya tace “Ameen, a dawo lafiya” murmushi ya mata yace “ameen, na tayaki murnan ganinta” tace “nagode, sannunka da wahala kaima” bai bata amsa ba yace “sai na dawo” ya tafi gurin ajiye motoci. Mammi ta tashi ta shiga cikin asibitin.

Su fatu na shiga lubna tace “kin fada mata ne? Fatu ta goge hawayen fuskarta tace “na fada mata, yanzu ji nakeyi kamar an dauke min wani nauyi a kaina, saura sultan shima da kaina zan fada masa insha Allah, amma lubna ina tsoron kar mammi taqi yafemin don na sanya danta kwanciya a gadon asibity” lubna ta dafa kafadarta tace “karki damu, mammi ta riga da ta yafe miki na sani, ke dai sultan ne ya rage, shima baza’a samu matsala dashi ba” anan suka iso gurinsu jameel lubna tace “DJ ya labarin matar sultan? Yace “kayya, madugu uban tafiyan ma ya kasa controlling kanshi kin gamshi a kwance, yanzu inaga gurin abba zanje muyi proceeding kafin sultan ya farfado” murmushi lubna tayi tace “u dnt have to” cikin rashin gane inda maganarta ya dosa yace “ban fahimceki ba! Tace “ga fatun nan da kuke nema” ya kalli fatu yayi yaqe yace “lubby u must be joking, ke a wannan halinda muke ciki har kinada lokacin wasa” ya gama maganarshi cikin bata fuska. Amrah da tunda suka fara magana tana binsu da ido cikin rashin fahimtan akan su waye ake magana tace “waye ya bata? Wane sultan? Kallonta sukayi dukansu sukayi shiru, fatu ta isa gurinta tace “ni cousin sis dinki ne, da mammi da mamana mahaifiyarsu daya” Ta cigaba “yayanki yaje nema na aka aura masa ni, to ni yar kauye ce ba ajinsa bane yasa ya tafi ya barni 4 a year bai qara waiwayana ba, ganin haka yasa na fito nemanshi, anan mummyn farouq ta kadeni a bakin tashan nan garin, lokacin da na bata story na tace I should stay with her har randa mai bayyana ta bayyana” fatu ta kalli lubna alamar labarinta yayi daidai yanda za’a fadawa amrah? Lubna ta mata ???? yayi dai dai, fatu ta maida dubanta ga amrah wacce ta sake baki tana mamakin wannan labari, tace “to meyasa yayana ya kwanta rashin lafiya? Lubna ta karba tace “ya fara sonta, da yaje can garinsu sai ya tarar bata can, shine hankalinshi ya tashi yazo ya fadawa mammi, mammi kuma ranta ya baci, so kinsan yanda sultan baya son bacin ran mammi, dats why he end up here” amrah ta fara tunani tana kada kai, no wonder jiya sultan da yamma yace ta tafi dakinta zasuyi magana da mammi, kuma taga mammi cikin damuwa don ita kanta tasan yanda mammi take son ganin auntyn nasu, ehh lallai biri yayi kama da mutum. Jameel ya miqe ranshi a bace yace “lubna for how long kika san cewa fateema fatu ce? Lubna ta fara inda inda yace “tell me” tace “tun ranarda suka hadu suka fara hira” cikin bacin rai yace “kin kyauta, yanzu idan mutuwa yayi ma babu ruwanki, a dalilin ki tayata ramawa kika qi fada min ina? Weldone, banga laifin fateema ba sai naki don ita sultan ya mata laifi nima shaida ne” yana gama fadan haka yayi ficewarsa, a bakin kofa ya taradda mummy na shigowa yace ina abba? Tace “yana tare da mammi” lubna ta iso gurinsu cikin sauri sau haki takeyi jameel na ganinta yace “mammi bari in dan fita, zan dawo yanzu” ya fice lubna tayiwa mummy yaqe ta bi bayan mijinta, har suka wuce su mammi basu ankara dasu ba, keke napep ya tara a bakin asibitin ya shiga itama ta shiga tana bashi hakuri. Kamar na bisu nace ‘kai labarin fatu nake bi ba nasu ba”

Fatu kuma tun fitansu kirjinta yake dukan uku uku, to wannan reaction din jameel ne, yaa na sultan kuma zai kasance a kanta? Zufa ya keto mata tace “kar fa yace bazaiyi accepting dina ba tunda ban tausaya mishi ba” amrah da take gefenta tace “me kika ce anty fateema? Yaqe fatu tayi tace “babu komai amrah, maganar zuci ne” dai dai nan mummy ta qaraso ta fara bawa fatu baki kan ta kwantar da hankalinta, batada matsala da mammi, fatu dai kada mata kai kawai takeyi amma tunaninta nakan irin draman da za’ayi in sultan ya farfado.

 

Maman Fateey????????

[8:55PM, 8/25/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣4⃣

 

Suna cikin haka mammi ta shigo itama, fatu sai sunkuyar da kai takeyi bata son hada ido da ita, ganin haka yasa mammi ta isa gurinta ta kamo hannunta suka zauna tace “karki damu kanki, laifinki daya fateema na qin sanar dani wacece ke, mummy ta fada min dalilinki, have no worry dear, uwa bata fushi da danta” rungume fatu mammi tayi tana jin tsantsar sonta cikin ranta, taso ace mahaifiyar fatu tana da rai itama taga wannan rana, hawayen farin ciki ne ya gangarowa mammi ta share ta dago fatu wacce itama fuskarta ya cabe da hawayen, mammi ta ciro hanky a dan qaramin bag din da ta taho dashi tana gogewa fatu fuska, abun ya bawa mummy daria tace “hajia surkuwa ce fa”

Mammi ta dago fuskar fatu tana mata murmushi yayinda fatun ma murmushi takeyi amma idanunta na qasa tace “wannan ba suruka bace, ‘yata ce hajia kulsum” mummy ta kada kai tace “hakane hajia sadia”

Amrah tace “nice show????”

A mosque din hospital din sukayi sallah Daga nan suka dawo suka duba jikin sultan, yana nan kwance kamar yanda suka barshi, abba ya shigo yace “ya kamata ku tafi gida tunda ance zaiyi 48hrs b4 ya farka, zan zauna dashi” mammi bata so ba haka ma fatu, dolensu suka fita. Mummy tayi drivin dinsu a motarta da suka zo ita da lubna a ciki, cikin gidan mammi suka fara sauqa suna maida zance fatu ta kule dakin amrah, basu jima ba mummy tace “hajia zan tafi gida, sai gobe insha Allah zamuje mu duba shi, ina fateema taxo mu tafi” mammi tace “to ba komai Allah ya kaimu, hajia baza ki barmini yar taki bane? Ta fada cikin barkwanci, mummy tace “na bar miki yanzu amma zanzo in dauki diyata” mammi ta kira fatu tace “mummynki tace ki dan zauna a nan, me kike buqata a kawo miki daga gida? Fatu tace “mummy kayan sakawa na” sukayi sallama ta tafi. Anan fatu taji ta wani iri, tafi sabawa da mummy kuma ita kunyan maman sultan din take, komawa tayi dakin amrah ta zuba tagumi tana tunanin mijinta koyaushe zai farka? Sa’I sa’I amrah na mata magana tana bata amsa. Bayan sallah isha farouq yayi sallama ya shigo da dan madaidaicin travelling bag ya kawowa fatu, ta karba yace “mummy tace a gaisheki” ta shafa kanshi tace “ina amsawa” bai jima ba ya koma don dare ne, yana komawa gida ya turnuqe fuska yace “mummy ni a dawo min da anty fateema na, kar ta kwana a gidansu sis amrah” mummy tace “to farouq, gobe zata dawo”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button