FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan fitan farouq fatu ta musu saida safe ta shiga daki, mammi na lura da fatu tana cikin damuwa, wanda itama daurewa kawai takeyi don hakan bai taba faruwa da danta sultan ba, mammi ta kalli amrah tace “ki bar mata dakinki, ki kwana a nawa, ni zanje side din abbanku” amrah tace “to” kana mammi ta tafi.
Maman Fateey????????
[11:01AM, 8/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
5⃣5⃣
Fatu na shiga daki ta bude jakan, phones dinta ne a sama sai kayan sawanta kala biyu da night gown, brush da undies sai dan abunda baza’a rasa ba. Wanka ta shiga ta fito, tana tunawa jiya sultan lafiyanshi kalau amma yau a gadon asibity zai kwana, ‘mutum ba’a bakin komai yake ba’
Hakan ta ayyana a ranta, tasa kayanta, bayan ta gama ne amrah ta shigo ta dauki kayan baccinta ta mata saida safe, fatu ta lockin kofar ta zauna a gado ta dauki wayarta ta bude, sai yanzu ta tuno jefar dasu da tayi dazu a falo, daidai nan calling din xahra ya shigo fatu ta dauka a sanyaye tayi sallama xahra tace “fateema kin daga min hankali wallahi, kina lafiya kam? Fatu tace “lafiya” xahra tace “na dauka wani abu ya faru dake, u said yanzu zaki shiga mota, after 15mins inda yaci kin iso sai na jiki shiru, I clld ba’a dauka ba, me ya faru ne? Fatu sai lokacin abun ya dawo mata sabo ta fara hawaye tace “xahra sultan na gadon asibity, zuciyarsa saura kadan ta buga bcos of me” “innalillahi wa inna ilaihir rajiun, garin yaya? Xahra ta tambaya cikin tashin hankali. Fatu ta fada mata yanda akayi, xahra ta mata jaje sukayi sallama akan itama gobe zataje dubashi.
Budo pics din sultan tayi tana kallo a hankali hawaye kuma na wanke mata fuska, wani pic dinshi ne ta tsurawa ido, inda daga gani ba’a nan qasar ya dauka ba, yana sanye ne da suite dark blue tayi matuqar karbanshi, fuskar nan tashi kaman na baralabe don tsaban walwali da kwarjini, murmushi yakeyi wanda har hakan ya sanya idanun shi kyalli da haske, ta cigaba da kallonshi tana shafa fuskar shi ta screen din wayarta, tana ayyana irin farin cikin da zatayi in yau akace sultan dinta ya tashi. A haka bacci barawo ya saceta, karfe 1:30 ta farka dalilin alarm da ta saka ta tashi tayi alwala ta fara sallah tana mai roqon Allah ya bawa mijinta lafiya.
Washe gari tun asuba ta gama shirinta ta zauna tana duba agogo lokaci lokaci, qarfe 6 amrah ta shigo ta gaisheta ta dauki uniform dinta, zata fita ne fatu tace “amrah mammi ta fada miki yaushe ne zuwa asibitin? Amrah tace “ehh, wai sai kun karya” fatu tace “ok” Tana nan zaune har amrah ta gama shirin school ta tafi, karfe 7 mammi ta shigo dakin, fatu ta durqusa ta gaisheta mammi ta amsa cikin sakewar fuska, tace “ki fito mu karya sai mu tafi” fatu tace “ina azumi mammi” tace “wani irin azumi keda ko sahur bakiyi ba! Fatu tace “nasha ruwa da asuba” mammi tace “wannan azumin naki fatu baiyi ba, jiya ma haka baki ci abinci da dare ba” shiru fatu tayi kanta na qasa tana wasa da yatsunta, ganin haka yasa mammi tace “to shykenan, bari inna gama zan kiraki, ko zaki fito falo ki zauna? fatu ta kada kai alamar a’a, mammi tasa kai ta fita. Itama mammin kasa cin abincin tayi ta zuba masa ido, tunanin abba takeyi wanda shima a tsatstsaye yayi breakfast ya fita tun da sassafe ya tafi hospital, jiya ma bai dawo ba sai 11 na dare.
Ganin tana bata lokaci yasa tacewa dija tazo ta kwashe gurin, mammi kuma ta saka hijabinta ta kira fatu suka tafi hospital.
[12:54PM, 8/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
5⃣6⃣
Suna isa suka tarar abba na cikin dakin da sultan yake shi da doctor suna magana, mammi suka zauna a chairs din kofar dakin suna jiran su abba. Doc dinne ya fara fita kana abba shima ya fito, fatu ta gaishe shi, ya amsa da sakewar fuska, ya dubi mammi yace “zaku iya shiga ku ganshi, amma ba’a son yawan surutu” mammi tace “ya jikin nashi? Abba yace “to da sauqi dai, likita yace jinin shi ya sauka yanzu, zai iya farkawa any moment from now” Mammi tayi hamdala abba yace “zan leqa office akwai meeting da muke dashi” mammi tace “Allah ya kiyaye” yace “Ameen” ya fita. Shiga dakin sukayi kowannensu jiki a sanyaye, fatu tsayawa tayi a bakin kofa tana kallonshi cikin tausayawa, mammi kuma ta isa gurin shi ta masa addu’a kana ta fita daga dakin, aka bar fatu da sultan su kadai.
A hankali ta isa gurinshi, ta jawo kujera ta zauna daidai fuskar shi, hannunshi ta riqo ta kawo dai dai bakinta tayi kissing dinshi hawayen da ya taru a idonta ya samu damar gangarowa a fuskarta har kan hannun sultan, rungume hannun tayi tana kallon fuskarshi, a hankali ta fara shafa kwantaccen gashin kanshi fuskarta bai daina zubar hawayen ba, magana ta fara a hankali kamar mai rada tace “ka tashi gani nan kusa dakai JANNAH nah, ka tashi ga fatunka da kake nema, ka tashi baby nah, kaji? Wake up” kuka ne ya kwace mata tayi mai isar ta tana kallon sultan wanda har yanzu yana nan kwance bai motsa ba, dora kanta tayi a gefen gadon kusa da kirjinsa, hannunshi na cikin nata ta riqe gamm! Jefi jefi tana daga kai tana kallonshi ko ya farka. A haka su mummy suka zo suka sameta, ta gaishe da mummy tace “fateema ya mai jiki? Fatu tace “da sauqi mummy” tace “Allah ya qara sauqi” bayan fitan mummy ne jameel da lubna suka shigo wanda da alama sun shirya, suma suka mata ya mai jiki suka fita, dangi da abokan arziki sai zuwa dubiya sukeyi amma ganin ana yawan shiga da fice yasa likita yace a daina shiga, mai son ganinshi ya leqa window, kowa ya leqa sai yaga fatu zaune kusa dashi, suna mamakin wacece ita, marasa hakuri sukanyi tambaya sai mammi tace ‘yar uwace, ba daman yawan tambaye tambaye haka suke tafiya da dunbin questions a kansu. Dai dai azahar likita ya shigo yace “bai farfado ba? Fatu tace “ehh” ya qarasa shigowa ya duba shi ya
Bude idon sultan ya rufe yace “ya kamata ya farka yanzu” ya dubi fatu yace “ke qanwarshi ce? Fatu tace “ehh” yace “make sure kun kirani idan ya farka, kin gane? Tace “yeah ok” ya fita, Tana nan zaune abba ya shigo ya duba shi yace “ki fito ku tafi, anjima da yamma sai ku dawo” fatu na jin haka tasa kuka harda sheshsheka, abba yace “ki zauna to, shykenan? Ta daga kai ya fice yana murmushi. Daukan su mammi yayi suka koma gida akan sai yamma zasu dawo, aka bar fatu ita kadai. Bayan da idar da sallah ne ta daga hannunta sama tana addu’a, sultan ya fara motsa yatsun shi, a hankali a hankali komai yake dawo mishi kamar a flash yayinda yake qoqarin bude idonshi, haske ya gani yayi saurin rufewa, ya qara budewa ya rufe, a haka har ya saba da hasken, a hankali ya juya kanshi gefen da yake jin motsi, wata ya gani zaune akan sallaya tana addu’a, fuskarta hawaye na bin wasu, ganinta yayi kamar fateema amma lokaci daya yaga kamanninta kamar na wata…..kamar a flash ya tuno kamannin fatu, da sauri ya runtse idonshi idonshi ya fara recalling…….. “Kinyi makaranta? Tace “ehh” yace “a ina kika tsaya? Tace “secondary” yace “shekarunki nawa? Tace “17” yana tunawa dai dai nan ya kalleta 4 d first time, kallon na kan sallayan yayi yaga ta shafa addu’an kanta na qasa tana kuka a hankali, ya tuno fatu wacce ita ma a lokaci kuka take son hadiyewa, yayi saurin kai kallonshi kanta yana tuna fatu tanada wani jijiya a tsakiyar goshinta, wannan din ma hakane tana dashi, kallonta ya cigaba dayi yana ganin fuskar fatu, fuskar fateema a fuskar wacce take kan sallayan nan!! Wacece ita??? Dago hannunshi yayi wanda aka saka mashi drip hakan yasa qarfen da aka dora drip din yayi qara, fatu da take kuka ta dago kanta da sauri, lokaci daya kuma ta miqe kamar wacce aka tsikara, nan da nan fuskarta ta washe da murmushi yayinda idanunta na tsiyayan hawayen farin ciki, ta nufo gurinshi ta kamo hannunshi yace *”FATUUUUUHHH”*