HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Maman Fateey????????

[8:28AM, 8/27/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣7⃣

 

“Shhh” tace dashi, “ba inda yake maka ciwo? Ido ya tsura mata, tuno da cewa doctor yace a kirasa yasa ta fita da sauri, shi tsoro ma ta bashi, wacece ita? Shin an samu fatu? To ina su mammi? Tukunna ma waya kawoshi nan?? Qoqarin tashi ya farayi daidai nan aka bude kofa, fatu ne da doctor sai nurse tana riqe da kayan aiki, fatu tazo gefenshi ta tsaya doc ya mishi gwaje gwaje yace “can u talk? Sultan yaqi ya kulashi, ya qara cewa “me kake ji a jikinka? Nan ma shiru yayi, Fatu tace “baby kayi magana kaji? Sai yanzu ya qare mata kallo ya gane muryanta, ya fara qoqarin tashi da sauri ta taimaka mishi ya tashi zaune, kallonta yayi yace “fateema what ar u doing here? Tace “ka amsa tambayar likita tukun” ya maida dubansa kan doctor yace “just headache sai jikina da yake ciwo” doc yayi ‘yan rubuce rubuce yace “ki bashi abinci in yaci a bashi magungunan shi, nurse ki basu sai ki fada musu yanda zai sha” tace “ok doctor” ya fita, nurse ta gwadawa fatu yanda zata bashi itama ta fita. Fatu tace ka sauqo kaje kayi brush sai kaci abinci, yace “baki bani amsa ba” tayi murmushi ta cire hijabinta ta ninke, dogon rigan atamfa ne a jikinta wanda daga sama ya kamata, ta qasa kuma ya dan budu, babu make up ko kadan a fuskarta, ta isa gurinshi da murmushinta ta jawo kafafunshi tace “nazo jinyar ka ne, ka sauqo in raka ka bandaki” ba musu ya sauqo yana mamakin meyasa su mammi suka bari fateema na jinyarsa alhali sun san cewa ba muharraman sa bane. Ya shiga bandaki ta tsaya daga kofa yace “ki shigo mana” da sauri ta juya shi kuma yayi murmushi ya rufe kofar, yayi wanka yayi brush ya leqo yace “akwai kaya ne? Tace ehh ta miqo masa t-shirt white da dogon jeans baqi, ya karba ya saka sannan ya fito, jiri jiri yake ji hakan yasa ya nufi gado da sauri ya zauna. Fatu da take nazarinsa tace “jiri kake ji ko? Yace “ehh” tace “rashin qarfin jiki ne gashi kuma akwai yunwa tattare dakai” kada mata kai yayi ta miqe tana zuba mishi abinci, gwaten dankali wanda yaji kayan lambu da kifi, sai kunun gyadan cous cous mai madara ta tsiyaya masa a cup, ta nufo gurinshi, gaba daya shi tunani yakeyi tana isowa yace “kinada waya a hanunki” tace “ehh, akwai” yace “dan bani inyi kira” ta miqa mishi, numbern abba yayi dialing ya dauka yace “Assalamu alaikum abba, sultan ne” abba yana zaune ya miqe  tsaye yace “sultan ka tashi? Baka jin komai ko? Ya jikin naka? Yace “da sauqi Alhamdulillah, an samu fatu abba? “An samu fatu ka kwantar da hankalinka, amm fateema bata fada maka bane? Sultan da mamaki ya kamashi kan a ina abba ya san fateema, kuma me hadinta da fatu? Yace “abba me zata fada min? Nan fatu ta mai alama daya miqa mata wayan, yayi kamar ya hanata amma sai ya miqa mata yaga iya gudun ruwanta, sallama tayi tace “abba yanzu ya farka, yanzu zai ci abinci yasha magani” abba yace “to ki saka yaci abinci kinji, yanzu muna zuwa” tace “to abba, Allah ya kawoku lafiya” sukayi sallama.

Sultan da yake binta da kallo yace “fateema Can you tell me whats going on here?

 

Maman Fateey????????

[8:43AM, 8/27/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣8⃣

 

Tashi yayi yana cewa “zan tafi gida….” jiri ne ya debeshi kanshi na juyawa da sauri fatu ta zaunar dashi akan gadon fuskarta dauke da damuwa tace “pls kaci abinci kasha magani, nd I promise zan fada maka duk abunda kake buqata”

Shiru yayi can yace “ok, qarfe nawa yanzu? Ta duba phone dinta tace “2:01pm” yace ” Ya kamata inyi sallahn azahar” fatu tayi daria tace “dear salloli da yawa akanka, azahar, asr, maghrib, isha, asuba, azahar” yace “ban gane ba” kallonshi tayi ta debo abinci a spoon ta kawo dai dai bakinshi tace “tun jiya kake kwance baby” bude bakinshi yayi ta saka mishi, a haka yaci abincin sosai tana masa hiran barkwanci, tuni ya manta damuwarsa harda daria, yasha kunun sosai da yake yana son kunu, bayan ya gama cin abuncinne yasha magani ya tashi tsaye,  yaji baya jin ciwon kan, gashi jiri jirin ma babu, kallon fatu yayi wacce take saka magungunan cikin leda, yaji kaman ya jawota jikinshi (ehhh lallai ka qoshi????) yana nan tsaye har ta gama ta dauki used plate da cup din ta saka a basket, ta dauki hijabinta ta saka, juyowan da zatayi ta ganshi tsaye, tace “har ka fito? Murmushi yayi yace “ban ma shiga ba” tace “kana jin jirin ne har yanzu? Yace “a’a” dai dai nan abba, mammi da jameel suka shigo, ganin dansu tsaye yana murmushi kamar ba wanda ya tashi daga gadon rashin lafiyaba ya saka su farin ciki, mammi harda dan guntun hawayenta, jameel ya isa gurin sultan ya rungume shi yace “wellcome back dude, fatu ta wahalar mun da kai, amma naga alama she’s taking good care of you” sultan yace “ban gane ba” abba yazo ya dafa kafadan shi yace “ya kake jin jikin naka? Yace “da sauqi abba” mammi tace “baka jin komai ko? Kaci abinci? Yace “bana jin komai, naci abinci” abba yace “bari inyi magana da doctor” ya fita daga room din, jameel da mammi suka samu guri suka zauna sultan ya shige bandaki, fatu kuma ta fara kimtsa musu kayansu, sultan ya dade a bandakin yana tunanin maganan abba da sultan …abba “an samu fatu… fateema bata fada maka bane?  …..jameel “fatu ta wahalar mun da kai, amma naga alama shes taking good care of you” ya dafa kan sink din bandakin maganansu na mishi yawo akai, to Yaushe fatu tazo har tayi jinyar shi? Ganin yana bata lokaci yasa yayi alwala ya fito a ranshi yana cewa tunda dai an sameta shykenan, wani farin ciki ne ya lullube shi

daya tuno da fatun shi yana ayyana irin kyakkyawan qaunar da zai gwada mata. Ganin ba mammi da abba a room din yasa sultan yace “jameel abban bai dawo bane? Jameel da yake danne danne da waya yace “sun tafi gida, zamu tarad dasu a can, an sallameka” sultan ya maida dubanshi kan fatu wacce ta dale kan gadon nashi itama tana danne dannen phone dinta, yace “fateema ina sallaya? Ta shimfida mishi ya fara rama sallolin da ake binshi fatu da jameel na jiranshi ya gama su tafi gida.

 

Maman Fateey????????

[11:02AM, 8/30/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

5⃣9⃣

 

Yana gama sallolin aka kira asr, jameel yace “mu tafi mosque mubi jam’I” hakan kuwa akayi, sultan a hanyar fitansu yaga fateema sai masa magana takeyi a ranshi yace ‘kodai na bata tausayi ne yasa ta ajiye kishinta a gefe? A mota suka barta suka shige mosque din asibitin, a lokacin fatu ta fara tunanin ya zata fara fadawa sultan cewa itace fatu!! Duk irin abubuwan da takeyi daurewa kawai takeyi don zuciyarta har yanzu yana bugawa da sauri idan ta tuno kalan draman da zasu kwashe ita da sultan, ta rafka tagumi, wayarta ya fara qara, xahra ce “sai yanzu zaki kirani? Cewar fatu, xahra tace “tunda safe naso inzo, kakana ne ba lafiya muka kaishi hospital shima, kuna wani ward ne? Fatu tace “ayyah Allah ya bashi lafiya, ai an sallame mu” xahra tace “what? Gani nan fa cikin asibitin! Fatu tace “don Allah? Kizo parkin space ‘B’ ina gurin a motar ya jameel, bamu tafi ba, sun shiga sallah ne” xahra ta iso a motarta fatu ta fito sukayi huggin juna, xahra tace “ya? Kin fada mishi komai? Fatu tace “not yet, ban samu chance ba” xahra tace “ki fada mishi da kanki don zaifi jin zafi in wani ne ya fada mishi” Fatu tace “hakane, bazan bari wani ya fara fada masa ba” dai dai nan sultan da jameel suka iso fuskar sultan kamar wanda aka aikowa saqon mutuwa, ya hade giran sama da qasa, fuskar sa sai da tayi wani jaa, ya shiga mota next to driver, ganin yanayinsa yasa fatu da xahra suka sha jinin jikinsu, tabbas jameel ya labarta masa, fatu ma tayi sauri ta shiga baya jikinta har rawa yakeyi, xahra da jameel suka gaisa, ta leqo ta window tace wa sultan “ya jiki” yayi yaqe yace “da sauqi, nagode” itama ta nufi motar ta bayan tayi wa fatu kallon tausayi. A hanya babu wanda yayi magana, sautin qira’ar da jameel ya sanya kawai ke tashi a motar, jameel yace “daa baka kulashi ba wallahi, irinsu ne masu tayar da hatsaniya” ya cigaba da cewa “fateema angonki akwai zuciya, an idar da sallah ana fita sultan ya dan bugi wani saurayi bai sani ba, shine saurayin ya hayayyaqo mishi harda barazanan wai zai kulle sultan, to shine gogan naki yaso ya nuna qarfinsa mutane suka shiga tsakanin su” sultan yayi tsaki yace “to fadi ba’a tambayeka ba, parrot, jameel ka koyi surutu wallahi” jameel yayi murmushi ya shafa kanshi yace “zama da madaukin kanwa……” anan suka iso gida, fatu ta sultan suka fito jameel yace “ka huta gajiya, zan zo anjima da dare” ya kalli fatu yace “amarya a kula min da abokina” maigadi ya bude masa gate ya fita. Qaramin basket din hannun fatu wanda suka dawo dashi daga asibiti sultan ya karba yace “kawo in tayaki” ya fara tafiya, tace “ina son magana da kai” ya tsaya yace “mu shiga gida to” tace “noo, anan nake so muyi” ya kalleta a diririce yace “fateema hope ba’a kan matata fatu bane, please ki janye wancan maganan” ta kalle shi da idanunta da suka fara tara hawaye tace “ba shi bane” yace “ina jinki ki fada min” shi ya qagu ya shiga gida ya tarar da fatunshi, ya tambayi jameel ya fada mishi inda aka samu fatunshi da yanda aka sameta amma jameel yaqi sanar dashi, wai fateema ce zata fada mishi, whats so special in fateema ta fada mishi? Anyway tunda ance fatun shi lafiyanta kalau, nd babu abunda ya sameta he can wait fateema ta gama maganarta. Kallonta yayi yace “ina jinki” shiru tayi kanta na qasa, yayinda hawaye ke bin kuncinta tace “NICE FATU”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button