HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Maman Fateey????????

[10:05PM, 8/30/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣0⃣

 

Kallonta yayi yace “fateema please banda joke a wannan time din” Ta dago idanta tace “ba joke bane, gaskia nake fada maka” sultan ya gyara tsayuwarshi yace “ina fatun? Tace “I said nice fatu, nice matarka, na fito nemanka mummy na hadu da mummy” kan sultan ya dau zafi yana kallonta kamar wacce take masa tatsuniya, wani lokacin tana masa dan kama da fatu especially in tana kuka. yace “ban gane ba, ban fahimceki ba, shin rikida kikeyi from fatu to fateema ko me kike so ki fada min? What do you mean? Fatu tace “please muje garden, not here” yace “noo, nan din ma is ok” tace “please” yace “ok muje” a garden suka zauna akan kujerun da suka qawata gurin, ya dafa table din dake tsakaninsu yace “ina sauraronki” Fatu tace “ka min alqawari duk abunda na fada maka baza ka yi fushi ba” sultan daya qagu yaji maganan yace “ba komai, ina jinki” Fatu ta fara bashi labari tun daga zuwanshi garin modibbo har yau, tashi yayi tsaye yana nunata da yatsa jikinshi har rawa yake yi yace “a hakan ne kike sona? Ko kunyar fada bakya yi? Kinada tausayi kuwa? Ya harde hannayensa a qirjinsa yana tsaye a kanta, ranshi a bace, fatu ta miqe tsaye itama ta share hawayen fuskarta ta turo baki tace “ai bani kadai bace mara tausayin, kuma naga abunda kamini na rama” ta murguda baki ita ala dole ta masa masifa. Taci gaba da magana wanda ita a ganinta masifa takeyi, shi dai ya tsaya yana kallonta bacin ran da yake ji zuciyarsa yana raguwa a hankali, Yanda take maganan tana juya idanu ya mishi kyau har baisan lokacin da ya saki murmushi ba, ita kuma kallon gefe tayi ta riqe qugu tana wani girgiza, sauke hannayensa yayi tareda yin nannauyan ajiyar zuciya yace “naji na miki laifi amma bai kamata kimin horo da wannan hanyar ba, kina gani fa yanda na rikice amma ko a jikinki” ta kalleshi taga yana murmushi, a ranta tace ‘bari muja ajii’ ta qara hade fuska tace “kaima haka kamin, bayan an sanar da kai halinda nake ciki amma hakan bai sa ka tausaya min ba” ta qara murguda baki, ya ciji lips dinsa Yace “wa kike murgudawa  baki? Kallonshi tayi taga ita yake kallo ta kawar da kanta tace “ni ba da kai nakeyi ba” ta qara murguda baki, qoqarin zagayawa gurinta ya fara yi, ita kuma ganin haka yasa ta matsa, Suka fara zagaye table din, shi burinshi ya kamata ko rankwashi ya mata na wahalar dashi da tayi, ita kuma taqi hakan ya faru, ganin yana qoqarin kamata yasa ta kwasa da gudu cikin gida, tsayawa yayi yana kallon yanda take gudun kamar wata small girl, murmushi yayi ya kalli gabas yayi SUJUD SHUKR yayiwa Allah godia da ya bayyana masa fatu ta inda baya tsammani, a hankali ya furta “Allahu Akbar, Alhamdulillah” Ya dauki basket din yayi cikin gida.

 

Maman Fateey????????

[2:02PM, 9/2/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣1⃣

 

Fatu sai data saisaita kanta kafin ta shiga falo, mammi ne kadai zaune tana jiran isowarsu, fatu ta mata sannu mammi tace “ina sultan din? Fatu tace “yana shigowa” tana rufe baki ya shigo yayinda ita kuma ta shige room din amrah,  zama yayi kusa da mammi ya riqe hannunta yace “mammina kin yafe min abunda na miki? Ta kalleshi cike da qauna tana murmushi tace “na yafe maka manga na” shima murmushin yayi yace “nagode, duk dana saba alqawari ayau burina ya cika, na samo miki fatu” tace “Alhamdulillah komai yazo da sauqi, yanzu kaje ka huta zamuyi magana anjima da dare” yace “to” mammi ta tashi ta shiga dakinta, sultan na ganin haka yayi sanda ya shiga dakin da fatu take, da alama ta shiga wanka, don ga kayanta data cire, kwafa yayi yace ‘Allah ya taimakeki, zamu hadu ne’ sosa kai yayi yana murmushi, wani irin farinciki yakeji mara misaltuwa, wai fateema da yake so itace fatun shi da yake nema!! Yayi tunanin ya rama wahalar dashi da tayi amma wata zuciyar ta haneshi da aikata hakan, don a dalilin rama abunda ya mata ya kwanta a asibiti. Ya fita daga room din zuwa part dinshi. Da dare bayan isha anci abinci abba ya tara familyn gaba daya a palour nshi, yace “Alhamdulillah ala kulli halin, komai ya faru ga dan adam muqaddari ne daga Allah, anan nake so naja hankalinku dukan ku cewa kar a bawa kowanne shashe laifi kan abunda ya faru, abunda ya faru ya wuce, kuma ina mai qara jawo hankalinku kan cewa ku kasance masu jin maganan iyayenku, sannan ku daina wulakanta mutum duk inda kuka ganshi, kowanne bawa da baiwar da Allah ya masa, and lastly kuji tsoron Allah, ku kiyaye hakkokin junan ku, duk wani abun da akace hakki ne rataye a wuyanku kuyi iya qoqarin ku wajen sauqe shi don saboda gujewa fushin Allah, ba tone tone ba, kai sultan tun farko daka dauki aurenka a matsayin qaddara ka kuma yi imanin cewa ‘matar mutum kabarinsa’ da duk wani tashin hankali bai faru ba, zaka iya cewa ai shima qaddara ne, yess qaddara ne amma anbi don zuciya, wanda son zuciya kan kai mutum ga ga halaka, Allah ya kare”  a hankali kowa yace “ameen” jikin kowannensu yayi sanyi da alama nasihar abba na shiga dai dai “sai ke fateema, duk da bakida laifi amma nasan kinyi hakan ne don ki hora shi kan abunda ya miki, shi  hakuri maganin zaman duniya ne, kar ku rama sharri da sharri, ku kasance masu aikata alkhairi ga kowanne mahaluqi, hakan zaisa ku sami babban rabo a gurin Allah, ku kasance masu yafiya wa junanku don gudun nadama nan gaba, Allah ya shige mana gaba a duk al’amuran mu” “ameen” suka qara amsawa. Anan sultan ya kalli fatu wacce kanta na qasa tun shigowanta taqi su hada ido a zuciyarshi yace ‘she’s now fatu’ karaf idanunsu suka hadu, murmushi ya sakar mata yayinda itama ta mayar mishi da murmushin ta sunkuyar da kanta, sosai abba yayi nasiha har amrah an tabo ita kuma akan karatunta, gyaran murya abba yayi yace “sultan yaushe zaka dauki matarka?? Dumm gaban fatu ya buga, don ita duk lissafinta bata taba zaton za’ayi maganar tarewanta nan kusa ba, da sauri ta dago ta kalli sultan shima ita din yake kallo, wannan karon murmushin mugunta ya mata ya kanne mata ido daya yace “…….

 

Maman Fateey????????

[2:04PM, 9/2/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣2⃣

 

Yace “abba nan da sati daya” kallonshi fatu tayi kamar zatayi kuka ya qara narka mata murmushi har hakoranshi na bayyana, abba yace “to sultan bakayi gaggawa ba? Mammi ta amshe “ehh gaskia sati daya yayi kadan, ina laifin wata daya? Sultan ya kalli mammi a natse yace “mammi har wata daya? An daure auren fa, kawai ku dauketa ku kaita shine zai dau wata daya? Haba mammi” daria abba yayi yace “kuyi shawara to, amm fateema kefa wanne kike so? Sati daya ko wata daya? Fatu ta kasa magana, ta daga ido ta kalli sultan murtuqe fuska yayi alaman ki zabi nawa, mammi kuma tace “fateema kiyi magana babu mai takura miki” fatu ta nisa tace “abba yanda mammi ta fada yafi” murmushi abba yayi sultan kuma ya bata rai, shi gaskia ba’a masa adalci ba, wata daya ai yayi yawa, mammi ko tausayin shi batayi. Abba yace “sultan sati daya yayi kadan a gama shirye shirye duk da an daura aure kasan mata akwai su da son biki, da sati da wata dayan duk daya ne, hajia sadia ku fada min duk abunda kuke buqata na hidiman da za’ayi, komai da komai” mammi tace “to Alhaji mun gode” sultan dai yana shiru don shi a ganinshi sam ba’a kyauta mishi ba, shi farko ma da cewa zaiyi a bashi matarsa su tafi yanzu tunda yana da gurin zama, amma sai yayi kulaku yace sati daya, kenan sati dayan ma a gurinsu yayi kadan, “wata daya, ina zaman jira?” ya furta a zuciyarsa amma baisan har ya fito fili ba, amrah da take kusa dashi ta tuntsire da daria harda riqe ciki, mammi tace “amrah lafiyanki kuwa? Sultan yana mata ido amma ina bata ma ganshi ba tace “wai cewa yayi ‘wata daya, yana zaman jira” duka ya kai mata a baya wanda yasa ta saki kuka mammi tace “kiyi hakuri, kije ki kwanta” tashi tayi tana kukanta ta fita, mammi ta maida dubanta kan sultan wanda yanzu kam kowa yaga yanda ya hade rai tace “to sannunka da cin zali, in kayi wasa sai in qara wata biyu akan dayan, sati daya kamar auren yar tsana za’ayi? Wannan ne karo na farko da zan aurar, kuma ‘yaya biyu, haka kawai in sungumi ‘yata in baka ba wani biki? Kamar zaiyi magana sai ya fasa ya tashi yace “sai da safenku abba” abba yace “mu kwana lafiya, ka tabbata kasha maganinka kafin ka kwanta” yace “to” yasa kai ya fita. Fatu da tunda aka fara draman nan kanta na qasa ta dago tabi bayanshi da kallo, mammi tace “fateema kema kije ki kwanta, ki huta gajiyanki, Allah ya miki albarka” “ameen” fatu ta amsa ta musu sai da safe ta fita. A hankali take tafiya tana waige waige don bata son haduwa da sultan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button