FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tazo daidai bakin main falo zata shiga taji ance “fatu” waigowan da zatayi taji an fincikota tayi masauqi a kirjin mutum, tana daga ido ta kalli fuskar sultan wanda yake mata murmushi wanda daga gani murmushin mugunta ne, rufe mata baki yayi da hannunsa ya fara janta zuwa side dinsa.
Maman Fateey????????
[9:40AM, 9/3/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
6⃣3⃣
Tirjewa tafara tana qoqarin cire hannunsa daga bakinta amma hakan bai samu ba don wani irin kyakkyawan riqo daya mata, ganin zata bata masa lokaci yasa ya dagata cidok har dakinsa, bai direta a ko’ina ba sai kan kujera, ya juya fatu ta bishi tana magiya yana tattareta yayi locking kofar, key din ya cilla sama ya cafe ya kashe mata ido yace “baby nah, yaya dai? Ji dan rainin hankali ta fada a ranta a fili kuma tace “don Allah ya sultan ka bude mini kofa, don Allah kar kamini komai” tsayawa yayi da karkada key din da yake yi yace “oohh kin dauka wani abu zan miki? Okey wato har kinsan abunda ake yi? Ya qarisa yana daga mata gira, sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya ta fara wasa da yatsunta, kallonta yakeyi kamar zai cinyeta, yace “don mugunta ina kika bi shawaran mammi? Shiru tayi yace “answer me” tace “nifa ba haka bane” yace “to mene? Tace “dama ina son zuwa garin modibbo ne” yace “okey, don kina son zuwa garin modibbo shine zai sa ki qi tarewa a gidan mijinki? Shin nace miki baza kije bane ko mene? Shiru tayi yace “da alama yau zaki kwana anan, da nayi niyyan barinki amma shirunki zai sa ki kwana mini” ta dago da kai tace “don Allah…a’a…. to kayi hakuri” matsowa yayi kusa da ita, taja baya, kyakkyawan runguma ya mata sannan ya ajiye nannauyan ajiyan zuciya, batayi qoqarin kwatar kanta ba saboda yanda jijiyoyin jikinta suka mutu lakasss! Sai da suka kusan minti uku a haka sannan ya saketa ya bata key yace “sai da safe” ba musu karba ta bude kofan jiki a sanyaye ta fita ta mayar da kofan ta rufe, wani irin sanyi ne ya bugeta wanda har tsikar jikinta sai da suka tashi, ta kankame jikinta ta fara tafiya, a ranta tace ‘anya bazan koma ba? Irin wannan sanyi’ murmushi tayi tunowa da cewa ko giyan wake tasha bazata kai kafarta gurinshi ba. A haka ta iso part dinsu ta rufe kofa bayan ta shiga, ta wuce dakin da take kwana.
Sultan kuma da kyar ya saita kanshi ya samu salama, amma tunanin fateema kawai yakeyi, da kyar bacci ya debe shi cike da dreaming dinta.
Shirye shirye aka fara tun
washe garin ranar, events 5 mammi ta lissafawa abba wanda za’ayi yace ta rage bidi’an yayi yawa, daga baya aka maida shi 3. Bayan kwana 4 sultan, fateema da mammi suka je garin modibbo, kaka ya rasa inda zaisa kanshi don dadi, koda aka ce masa ga fatu da farko kasa gaskatawa yayi, fatu harda guntun hawayenta ta rungumi kakanta, su goggo asabe suka zubar da makamai don ganin fatu ta musu nisa, dolenta ta dawo ta nan nan dasu, ganin haka yayiwa fatu dadi ta godewa Allah, kawu muntari ma yayi murna inda ya aika aka siyo musu fura da nono mai dadin gaske aka kuma yanka kaji biyu aka musu miya, bayan azahar naga mammi da kaka zaune a cikin zaure, mammi ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar dashi tace “daa nace ko baza a sanar daku ba sai abban sultan yace lallai a fada muku kar ranku ya baci kuma kusa shakku a zuciyanku idan magana ta fito waje, nasan ‘dana yayi kuskure amma yayi nadama, ina mai baka hakuri a matsayina na mahaifiyarsa” kaka yayi shiru a cikin ranshi baiji dadin abunda ya faru ba, ashe shiyasa ranar da sukazo sultan ya rikice don sanin bata tare dasu? Biri yayi kama da mutum, tun ranar zuciyarsa take raya mishi abubuwa daban daban, in bai manta ba yau sati kenan da faruwan al’amarin. Yace “babu komai hajia, yanzu kam ya zama tarihi” mammi taji dadin yanda bai tsawaita maganan ba ta sako musu hiran bikin fatu da take shirin yi, nan da nan fuskar kaka ta washe yana murmushi yace “diyar ku ce, sai yanda kukayi, fatanmu Allah ya hada kansu ya basu zaman lafiya” sultan da fatu sun tafi gona inda yake ganin yanda ake shuka domin damina ta fara, Basu jima ba suka dawo dalilin kiran da mammi ta musu kan su dawo su tafi gida, tsaraba sosai kaka ya tara musu, goggo asabe ma harda garin kuka, daddawa da man shanu, mammi bata barsu ba sai da ta cikawa kowa aljihunsa ta kuma roqi alfarman cewa idan lokacin biki yayi suzo, kaka yace insha Allah za’a zo. Fatu bata so tafiya ba amma haka suka tafi tana mai kewan su kaka, a wajen fita daga gari ne suka hadu da hafizu dan ladan da alama daga gona yake, fatu tace “ga hafizu” qasa qasa yanda sultan zaiji, yace “waye shi? Tayi murmushi tace “kaka bai baka labarinshi bane? Sai a sannan sultan ya tuno ya murtuqe fuska yace “shine kike kallonshi kina murmushi ko? Tayi tsit, don yanzu tana tankawa qari zai zama kababa. A yanda ta lura dashi yana da kishi sosai Murmushi tayi tace “sorry” daga nan kuma ta dauko musu wani hiran, mammi dai tana baya ko ta kula su, hasalima waya takeyi da wata qawarta yar borno wacce zata hadawa fatu humra, kulacca dasu turaren wuta. Woo mammi????. A haka har suka iso gida.
Maman Fateey????????
[11:56AM, 9/3/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
6⃣4⃣
Fatu ta koma gidan mummy da zama, mammi ta lura da yanda sultan ya takura mata, hakan ba qaramin dadi yayiwa fatu ba domin in har ta bari suka zauna su kadai to sai yasan yanda zaiyi ya sata kuka da irin abunda yake mata. Shi kuma baiji dadi ba amma ya nuna musu ko a jikinshi, qarshe ma tafiya yayi dubai kan cewa shi zai hado kayan lefe da kayan daki, mummy ta mammi suka rubuta masa duk abunda suke buqata. A ranar da zai tafi ya shigo gidan mummy, a falo ya tarar da mummy tana zaune, ya gaisheta tace “sai tafiya ko? Yace “ehh” tace “fateema tana kitchen, ka shiga kuyi sallama” kamar bazai shiga ba amma yayi missing dinta, a kitchen ya sameta ita da dija suna aiki, dija ta gaishe shi ta fice daga kitchen din, fatu ta gaishe shi tace “ya na ganka haka? Yace “kamar ya? Tace “kamar bakada lafiya” ya shafa sajensa yace “lafiyana kalau, zanyi tafiya ne” zare ido tayi ta matso kusa dashi tace “yaushe? Ina zaka je? Murmushi yayi ganin reaction dinta alaman bata so ba, yace “yau, dubai daga nan in wuce china, sai ana saura kwana biyu biki zan dawo” fatu da idanunta suka fara tara kwalla tace “don na dawo nan shiyasa zakayi nesa dani ko? To zan koma gidan mammi, kaji? “A,a kiyi zamanki, dama kema bakya son ganina, kuma ina takura miki, so kinga inna tafi zaki fi sakewa ayi shagalin biki dake” girgiza kai tayi tace “ni baka takura min ba, don Allah ka zauna, kayi hakuri, bazan iya jure rashin ganinka ba har tsawon kwanakin nan, ban saba da rashinka ba” tausayi ta bashi sosai, amma shima abun tausayawan ne, kuka ta fara ya jawota jikinshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta “its ok dear, nima ba’a son raina zan tafi ba, 10 days zanyi kawai in dawo, u happy? Girgiza kai tayi tace “shima yayi yawa” ya dago da kanta ya share mata hawaye yace “kamar yau ne zakiga 10dys din yayi” wayarshi ce ta fara qara ya dauka jameel yace “ina jiranka a waje, kar kayi missin flight naka” yace “ok ganin nan fitowa” jin haka yasa fatu tara wani kwallan ya kalleta yace “in tafi? Tayi shiru, peck ya bata a kumatu yayi ficewarsa don shima daurewa kawai yakeyi, mahmud ya samu a palour, mummy kuma da alama ta shige dakinta, ya tsaya suka gaisa, mahmud ya hango fatu a bakin kitchen tana kuka yace “dukanta kayi ne sultan” sultan ya juyo ya kalleta yace “wai don zanyi tafiya ne, dadi ne ya mata yawa” mahmud ya kwashe da daria yace “dan tsaya don Allah” …..’ashe sabo yana da dadi, amma in za’ai rabo da zafi’….. waqan ‘sai wata rana’ ya saka musu, sultan yaja tsaki ya fita daga falon, fatu kuma ta fito tayi hanyar dakinta tana matsar kwalla, mahmud sai kwasar daria yakeyi, dai dai nan mummy ta fito tace “me haka mahmud? Ya tsagaita darianshi yace “sultan zaiyi tafiya shine ‘yar kauyen nan take ta kuka” mummy ta bata fuska tace “kai kuma qaton banza shine kake mata daria? A haka wai kai yayanta ne? Shiru yayi fatu kuma tasa daria mummy tace “sannu mai kuka da daria” fatu ta haura sama tana murmushi. Sultan ya sauqa lafiya, kai tsaye ya wuce hotel din da yake zama, fatu ya fara kira yace mata ya iso, ta mishi barka da hanya. Yana wanka ya fita zuwa gidan wani abokinshi Ahmad, balarabe ne amma yayi zaman naija, sosai yake jin hausa, matarsa Nihal ta kawo wa sultan abinci ya zauna yaci anan yake bashi labarin aurenshi. Ahmad ya masa murna, sultan yace “ina gayyatarku kaida madam ku tayani sayayya” ahmad yace “karka damu, a shirye muke” daga nan suka dunguma zuwa kasuwan deirah dubai, matar ahmad nihal ita tayita zaban kayan lefe su sultan na tayata, gurin kayan bacci sultan yace “ni zan zabi wannan kam” daria suka mishi ya fara kwasa, a gajiye likis suka dawo gida, shi kuma ya wuce hotel din daya kama.