FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Fateey????????
[1:18PM, 9/7/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
6⃣5⃣
Washe garima haka suka fita, sukayi ta siyayya, sultan na duba list din su mammi, a ranar suka gama hada lefe, akwatuna 12, kowanne shaqe da kaya na gani na fada, Wani set din sarqa, dan kunne, rings da bracelet na gold ya siya mata, wanda fadin tsadarsa ma bata lokaci ne, Shoes nd bags designers, kayan cosmetics gasu nan birjik, undies, dogayen riguna kala kala, kai zan muku video kawai kowa ya gani????.
Kwanan shi uku a Dubai ya gama siyayyar da zaiyi har da furnitures da kayan kitchen, a rana ta hudu ne ya tura kayan nigeria shi kuma ya wuce china business trip dinshi. Yau saura sati biyu a fara shagalin biki, amarya fatu ta fara shan gyara, takanas qawar mammi yar borno ta aiko matar da zata yiwa fatu dilka da turaren jiki, mummy ta hado “SINADARAI”???? ingantattu marasa illah. Sultan kuma waya kan waya suke da fatu, don wani irin qaunarta da yake fisgar sa har yakan ji kamar wani zai kwace masa ita. Ita din ma hakan ne, wani zazzafan sonshi take ji a zuciyarta, gashi tayi missing dinshi sosai.
Dangi yan uwa na kusa har sun fara zuwa, mammi ta fadawa dangi an samu fatu, wato dangin mahaifiyarta, murna a gurinsu ba’a cewa komai, kowa yana marmarin yazo yaga fateema nan da mammi take nema. Akwai wata qanwar kakar fatu wacce take kaman uwa a gurin mammi, don itama tasha neman addarta wato maman rahmatu mahaifiyar fatu, ana kiranta inna habiba, tana ganin fatu ta fashe da kuka wai taga yayarta zainabu, kowa ya ganta sai yayi mamaki don kamanni da takeyi da kakarta sosai, duk da basu san rahmatu ba sunyi kewarta a matsayinta na yar uwarsu, fatu taga dangi, tayi murna ta kuma godewa Allah da ya nuna mata dangin mahaifiyarta masu sonta. Ranar sunday ana saura sati biki, ana yiwa fatu dilka tana wani tutturo baki wai ta gaji da murje murjen nan, salma cousin din sultan tayi daria tace “murje murje ko? Wannan kadan kika gani” xahra da bizzy (itama cousin din su sultan ne, duk sa’anni suke da fatu) suka fashe da daria, fatu da bata san inda maganan su ya dosa ba tace “ohh nan gaba murjewan zaifi haka? Bizzy tace “sosai ma, kuma wanda za’a miki nan gaba in bakida dauria har kuka zakiyi” suka qara fashewa da daria, fatu tayi shiru tana kallonsu one by one, jikinta yayi matuqar sanyi tace “baku da kunya” falmata matar da take yiwa fatu dilke wacce bazata wuce 28yrs ba tace “rabu dasu fateema, suma suna hanya ai, ba’a yiwa motar gawa daria” murmushi fatu tayi kawai su salma kuma suka ci gaba da yiwa fatu tsiya falmata na kare ta. Maman dota ne ta shigo dakin tace “wai har yanzu baku gama ba? Kusan azahar, xahra ba kunce zaku je rabon Iv ba? Xahra da take shafe shafe da mirrow a hannunta tace “zamuje, amma sai anjima da yamma” maman dota tace “to shykenan bari a kawo muku abincin ku” tasa kai ta fita, salma tace “haba bizzy ki shafa a hankali mana, zaki sa mu rasa ai, irin wannan makkalawan da kikeyi” bizzy kota kulata ta cigaba da shafawa, salma ta kwace robar dilkan taje bakin kofa ta tsaya, itama tana shafawa, bizzy tace “ai wallahi baki isa ba, ban shafa a wuyana ba fa” zagaye dakin suka fara su xahra na musu daria, da yake dakin babba ne, takanas mammi tasa aka gyara wai wajen gyaran amarya, carpet ne shimfide a dakin sai katifa guda daya da kujeru one one sitter biyu, sai da suka gaji suka zauna suna shafawa tsakani da Allah.
Bayan dilkan ya bushe falmata ta shiga bathroom din dakin don hadawa fatu ruwan wanka wanda shima yasha hadin turarukan wanka masu dadin qamshi, anan fatu tace kallesu tace “nifa banga amfanin shafe shafenkun nan ba, ni kunga mijina nake yiwa, kufa? Harara suka watsa mata, bizzy da aka fi jin muryanta saboda surutu baya mata wahala tace “aikin banza, idan yazo yabon kwalliyan naki mummurje ki zaiyi” suka kwashe da daria da yake sun san bata son kalman “murjewa’ Itama daria tayi alamar ko a jikinta tace “wa yaga taliyar hausa ta murji” anan falmata ta fito tace “fateema ki shiga wanka, bari in je in debo garwashin yin turare” ta fita, fatu ta shige bathroom tana kada musu duwawu, salma tace “hhh yarinya zaki gane” bayan ta fito tayi sallah aka mata turaren jiki, Ta saka wani maroon doguwar riga cotton mai guntun hannu, fatarta ta qara haske, santsi da taushi, jikinta na fitar da wani daddadan qamshi mai sanyi, tayi wani fresh da ita, cream dinta mai hade da kulacca ta shafa a jikinta, ta murza farar powder ta saka lip balm, da yake ance ta daina kwalliya mai yawa, abinci suka fara ci suna hiransu duk akan yanda bikin zai kasance, suna tsakar ci wayar fatu ta fara ringing ta dauka, sunan sultan ne akan screen din, ta daga ta kashe murya tace “Jannah” gyara zamanshi yayi a kan kujeran da yake yana murmushi yace “Habibteey ya kike” ta rausayar da ido kaman yana gabanta tace “lafiya lau” su salma suka sa ihu har bizzy na kwarewa, yace “su waye haka? Ta kalli su xahra da suke dukan bayan bizzy wacce ta kware suna dura mata ruwa, tace “yara ne suke wasa” hararan da suke watsa mata ne yasa ta juya musu baya taci gaba da wayanta, sultan yace “please kije dakina akan gado zakiga wasu papers a cikin envelope ki bawa mammi” tace “dakin naka a bude ne? Yace “ehh a bude ne” tace “ok” ya kashe wayan ta miqe ta dauki gyalen rigar ta fita zuwa shashen sultan.
Maman Fateey????????
[10:02PM, 9/7/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
6⃣6⃣
A hankali ta murda handle din dakin ta shiga da sallamanta duk da tasan babu kowa a ciki, qaramin palourn nashi tsaf tsaf kamar baiyi tafiya ba, ta bude kofar dakin ma tayi sallama tareda kutsa kai ciki, ganin duhu a dakin yasa ta fara lalube gashi bata san inda switch din yake ba, kafarta ne ya bugi gado, ta daga kafar ta riqe tana wayyo Allah na. Tuno da cewa tana da waya hannunta yasa ta kunna light din wayar ta duba qafarta gurin har yayi jaa, ta shafa gurin ta ajiye kafar ta haska dakin, dummm gabanta ya fadi ganin mutum kwance a kan gadon yana kallon ceiling, tare fuskarsa yayi yace ‘kina haska min ido” fatu ta kasa motsi don tayi matuqar razana lallai yau tayi gamo da aljani a dakin sultan. Ganin ya tashi yana qoqarin zuwa gurinta ne yasa ta fasa ihu tace “wayyo mammi….na shiga uku” tayi hanyar qofa da gudu har tana jefar da wayarta, nan da nan hasken dakin ya mutu sakamakon mutuwar wayarta da yasha qasa, addu’a takeyi tana kokawa da kofar yayinda kuma tana juyawa tana ganin inda aljanin yake, ji tayi an tuntsire da daria hade da kunna hasken dakin, Balloons pink nd white ta gani ko ina, an qawata dakin dasu, can kuma gefe cake ne madaidaici an rubuta ‘fateema is 19’ ta dawo da kallonta kan sultan wanda ta tabbatar ba aljani bane tace “jannah” qarisowa yayi gurinta yana murmushi ya kamo hannunta har gurin cake din, kallon mamaki take binshi dashi yayinda tana gani ya dauko lighter ya kunna 3 candles din da suke kan cake din ya juyo gurinta yace “bismillah” a raina nace Karfa ta kashe candle din da ruwa????, itama murmushine a fuskarta tace “with u dear” Rage tsayi sukayi a tare suka ce one…two….huuuuuhhh suka hure candle din wutan ya mutu, Yana clapping itama tanayi harda guntun tsallenta, a tare suka yanka cake din yana “happy birthday to you, happy birthday to you” ya bata a baki itama ta bashi, sai a sannan suka zauna a bakin gado yace “washhh na gaji” ta juyo tana kallonshi tana cin cake tace “amma guy din nan ka tsorita ni wallahi, tukunna ma yaushe ka dawo? Ba sanarwa haka” Kallonta yakeyi yaga ta qara masa kyau tayi wani bul bul da ita, yace “kinyi kyau” ajiye sauran cake din hannunta tayi murmushi tace “nagode, nd thanks for everything” Murmushin shima yayi yace “u ar welcome dear, now selfie” ai kuwa ta turo baki suka dauka, na biyun kuma tayi murmushi, a haka suka yita daukan pics kala kala, sai da suka tsagaita ya dauko wani qaramin akwatin ring daga aljihunsa yace “ga gift dinki” ya bude wani hadedden zobe ne wanda daga gani na pure azurfa ne, ya saka mata a yatsanta, fatu ta murna yasa ta kasa rufe baki tace “thank u so so so much, Allah ya bar mini kai” daria yayi yace “ke daya? Tace “yesss ofcos” yace “towww” tace “amma kasan na manta cewa yaune birthday na, ya akayi ka tuna ne? Yace “dama ina tune kuma nasa reminder a phone dina, jiya a china na ga remindern, so already na gama abunda nakeyi kawai nayi bookin flight na dawo, tun safe nake gida amma abba ne kawai ya sani” Fatu da take kallonshi tana qare masa kallo don shima yayi dan haske ya mata kyau bata san sanda bakinta ya furta “kayi kyau” ya shafa sajensa yace “godia nake, amma na rame ko? Ta dan hararashi tace “me zai ramar da kai? Yace “rashinki kusa dani” kafin tayi magana ya jawo ta suka fada gado ya kashe light din dakin yace “muyi bacci”