HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Bayan su xahra sun gama cin abinci sukayi wanka, sukayi shirin fita rabon iv, anan suka shiga cikin gida sukayi yiwa mammi sallama tace “da fatan ba da fateema zaku tafi ba? Salma tace “mammi ai ta shigo cikin gida ma” mammi ta kada kai, su kuma suka fita a motar xahra bixxy na driving. Can bayan la’asar sakaliya suka dawo, a bakin gate suka hango dandazon yan biki kowa hankali a tashe wai ba’aga amarya ba!! Mammi tafi kowa rudewa sai kiran numbern fatun akeyi yaqi shiga, ta kira abba shi kuma bai dauka ba da alama yana gurin meeting, dawowansu xahra yasa aka fara tambayansu inda fatu take, anan suka ce rabonsu da ita tun suna cin abinci sultan ya kirata a waya, amma basu san meya fada mata ba ta tashi ta fita a dakin, da sauri mammi ta kira numbern sultan na china, ‘is switch off’ aka fada mata, ta kara kiran numbern abba shiru, anan ta kira jameel ya dauka yana gaisheta bata saurareshi ba tace “jameel ba’a ga fateema ba, ka kira sultan in kana da numbern hotel din da yake” jameel da mamaki ya kamashi yace “mammi ai sultan yana gida, yau da safe karfe 9 naje na daukoshi a airport” kafin ya karisa maganar mammi ta kashe wayan tayi hanyar part din sultan ranta a bace, ganin haka yasa kowa binta cikin kidimewa kan me yake faruwa????

 

 

Yanzu labari ya fara????

 

 

Maman Fateey????????

[2:07PM, 9/8/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣7⃣

A bakin falon mammi ta tsaya tana knocking, shiru shiru ba’a bude ba yasa ta bude door din ta shiga, a ranta tana ayyana irin bacin ranta da zata nunawa sultan, ganin ba kowa a falon yasa ta tabbatar lalle suna daki, kasa motsi tayi ga jama’a a can a bakin kofa, ga sultan nason sakata kunya, knockin din dakin tayi shiru ba’a bude ba, ta dauki wayarta ta kira sultan din da number nasa na Nigeria.

 

A bacci fatu take jin kamar ana bugun kofa, ta bude idonta tare da zare jikinta daga na sultan wanda baccinsa yakeyi hankali kwance, barin jikinshi da tayi yasa shi farkawa yana mutsike ido, da muryansa ta masu bacci yace “fateey yadai? Fatu data kasa bude kofan don yanda zuciyarta ke bugawa, kuma bata ji an qara knocking ba tace “ana knockin ne” ya tashi a hankali ya bude kofan, wayamm ba kowa, ya leqa falon nan ma ba kowa ya juyo yace “babu kowa fateema” ya qarisa bakin gado ya dauki wayarsa its 4:02pm, yace “lokacin sallah yayi, ki shiga kiyi alwala muyi sallah” tace “a’a nikam zan tafi, wallahi mammi zata neme ni” ya tsaya ya riqe qugu yace “ki shiga kiyi alwala nace” kallonshi tayi ganin ba wasa a fuskarsa yasa ta shiga bathroom din ranta bai so ba, tana fitowa shima ya shiga yayi alwala, kafin ya fito har ta gyara masa shimfidin gadonsa ta kimtsa gurin, sallaya ya dauko musu ta karba ta shimfida, sai a sannan ta tuno bata da hijab, ta kalleshi tace “banida hijab fa” ya bude wardrobe dinshi ya ciro wani pink hijab wanda daga gani ta gane nata ne, zata yi magana yayi kabbara ta saka hijabin ta bishi, bayan sun idar da sallahn sukayi addu’a ta ninke sallayun ta adana, anan ya mata umurnin su fita, daukan cake dinta tayi suka fito, zatayi cikin gida ya jawo hijabinta yace “um um, yau tare dani zaki wuni, muje garden” kallonshi tayi tana murmushi tace “jannah, mammi fa!! Yace “idan kina son mu shirya ki daina kira mini mammi, gutsureki zanyi ne? Ko ni ba mijinki bane? A hankali yayi maganan amma da alama ranshi a bace ne, tace “srry, muje to” qin tafiya yayi, ta jawo hannunshi da kyar ya bita suka tafi. Hira sukeyi cikin kwanciyar hankali har yamma sakaliya. Anan wayarshi ta fara ringing ya dauka yace “Hello mammi” tace “ina fateema? yace “gata nan” tace “ka bude kofan ka bani ‘yata” yace “wani kofa? tace “tambaya na kakeyi? Yace “mammi mufa muna garden tun dazu” hamdala tayi zuciyarta yayi fess, ta fito daga dakin tana murmushi ganin haka yasa aka fara tambayan ina fatun?? Tace “suna lambu” su bizzy da salma ne akan gaba harda gudu gudu, suna isa kuwa salma ta hango cake din kan table bata bi ta kansu ba ta qarisa zata dauka sultan ya aza mata rankwashi, “wayyo innata” ta furta a wahale, dai dai nan su mammi suka iso, tana cewa “ka kyauta, kaji? nace ka kyauta” murmushi yayi yace “ina wuni mammi” tace “lafiya, yaushe ka dawo? Yace “dazu ne da safe” tace “shine baka sanar mana ba? Shiru yayi yana kallon bizzy da take qoqarin daukan cake din itama don taga mammi na kusa, ya make hannunta da qarfi, ta cire da sauri tana yarfe hannun don ta bugu, anan ya fara gaisawa da sauran ‘yan uwa suna tsokanarsa, sai da kowa ya watse ya rage daga su salma sai mammi, mammi ta cewa fatu “ki shiga gida fateema” ta tashi ta dauki cake dinta su salma suka rufa mata baya (kwadayi????) Guri ya rage daga mammi sai sultan tace “manga” yace “na’am” tayi shiru can cikin tsigar rarrashi tace “kaga yanzu ka dawo ko? Kuma saura sati a gama biki, to please kar inji wata magana ta taso kaji?” Daria yayi yace “to” da sauri tabar gurin tana cewa “anjima after isha ka sameni a falon abbanku”

 

Maman Fateey????????

[10:12PM, 9/19/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣8⃣

 

Tun daga ranar bai qara kiran fatu gurinshi ba, hasalima qaura yayi zuwa sabon gidansu da zasu tare, anyi fenti an saka furnitures da komai an gyara ko’ina das das, gida yayi ready yana jiran amarya. Ranar wednesday aka yiwa fatu lalle jaa da baqi ya amshi fatarta, Anan ta fito amarya sak, ga yanda jikinta yasha dilke tana kyalli, Kitso kanana falmata ta yarfa mata wanda suka zubo bayanta suka qara haska ta, mammi bakinta ya kasa rufuwa don farinciki, qawayen amarya su xahra, bizzy, salma, sai shiga da fita sukeyi. Su kaka sunzo tare da jagorancin kawu muntari, da inna asabe da goggo innani, ba yanda mammi batayi ba kaka ya kwana yace inaa!!! Zasu ga gida daga baya, a ranar suka koma  shida kawu muntari bayan mammi ta cika su da abun biki, aka bar su inna asabe suna santin gida da daular da fatu take ciki.

Ranar thursday akayi KAMU inda amarya da ango suka fito kamar taurari, gashi suna kama, anyi pictures kala kala, abun ya qayatar ba laifi, ranar fariday akayi WALIMA Inda amarya tasha laffaya fara sol mai adon golden, ansha wa’azi sosai kuma anyi rabon kaya irinsu hijabs, paper bags masu hoton amarya da ango, atamfofi,  da sauran kayan da ake rabawa a bikin ‘yayan manya. Washe gari saturday aka shirya dinner qarfe takwas na dare no african time, saboda ba’ayi daurin aure ba yasa dinner ya zama big event, abokanan abba, frnds din sultan, abokan kasuwanci duk za’a hallara. Jameel babban abokin ango shi ya shirya komai, babban hall makeke aka kama inda aka qawata shi da ado masu kyau da ban sha’awa, a can step din sama na hall din Royal kujeru biu ne na amarya da ango, a qasa kuma tables ne kowanne da kujeru 4, gurin yasha decoration ba laifi. 8:08 kowa ya hallara amarya da ango kadai ake jira, ko ina ka duba mutane ne kowa yayi shiga ta alfarma, manyan yan kasuwa da qososin gwamnati da sauran jama’a, abba na hango cikin frnds dinsa ana raha hatta daddyn jameel wanda bai cika zaman qasan ba ya hallara. Mammi da mummy ma ba’a barsu a baya ba,  sunyi shiga ta mutunci suna zaune cikin qawayensu ana jiran shigowan amarya da ango, su inna asabe ma sunje. Anan abokin su jameel Naseer ya tashi da mike a hannunsa yadan bubbuga yace “hello” aka ce “hiiii” ya gabatar da shigowan couple, kowa ya qura ido yana jira, a hankali aka saka kida mai sanyin sauti, farouq da wata yarinya ce wacce zasuyi sa’anni suka fara shigowa, yana sanye da coat brown ita kuma gown pink an gyara mata gashinta ya zubo bayanta, farouq na riqe da hannunta sunyi kyau, anan sultan da fatu suka shigo suma hannunsu a hade sai doka murmushi sukeyi, tafi aka fara raff! rafff! raffff! Sanye take cikin riga sa siket na hadedden code lace milk color, sai head da shoe dinta red, veil dinta mai walwali da kyau shima red ta saka a kafadanta daya ya zagayo ta qugunta an riqe shi, sultan kuma jamfa da gare ne milk color sai hularsa zanna brown, takalminsa da agogonsa brown, tafiya suke yi da murmushi a fuskar su, sunyi kyau iya kyau, hasken flashes din camera na masu daukan hoto da kuma phones din mutane ya qarawa gurin haske da walwali, bayansu kuma qawayen amarya sanye da ankon pink gown da head milk, abokan ango suna sanye da brown jamfas, har suka iso gurin zaman su suka zauna suma qawaye da abokai suka zauna a inda aka tanadar musu. Aka bude taro da addu’a, aka fara shagali, jameel ya bada tarihin ango, xahra kuma ta bayar dana amarya, kowa cikin harshen turanci, Mammi, abba da ango suma sun fito sun miqa godiarsu ga baqin da suka halarci wannan taro, sultan da fatu suka yanka cake, ya yanko qarami ya bata a baki ita kuma ta yanko dan babba ta bashi aka saka tafi, An kira amarya da ango su fito yin rawa, abokanan abba suka fita ana musu barin kudi, bayan sun gama qawayen su mammi ma suka fito suka yi nasu liqin, komai ya tafi yanda ake buqata ba hayaniya da cunkusowa, karfe 9:14pm abokan abba suka fice bayan sun cika couple da gifts, su mammi da qawayenta ma suka rufa musu baya, guri ya rage daga abokan ango sai qawayen amarya, sunyi shagalinsu son ransu amma sultan ya hana fatu rawa wai bbu wanda zai gane mishi jikin matarshi na karkaduwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button