HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

An kusan tashi ya jawo hannunta ya rada mata a hankali “daga nan gidanmu zamu tafi ko? Ta harareshi qasa qasa tace “a’a nikam, ka maida ni gurin mammi na” murmushi yayi yace “kina wasa yarinya” qarfe 10:10 suma suka tashi, mahmud sai lilliqewa salma yake yi tana basarwa, da za’a koma gida ma shi ya daukesu dasu bizzy, jameel ya tattari matarsa da qaton cikinta shima.

Sultan ke drivin yayinda fatu ke gefenshi tayi miqa tace “waashhh, na gaji wallahi” kallonta yayi ta gefen ido yace “dats y nace mu tafi gidanmu zaki fi watstsakewa” da sauri ta girgiza kanta tace “um um nikam, gida zan tafi” yanda tayi magana ya bashi daria yace “nayi hakurin 1 month kinga zan iya yin na kwana daya, inace gobe za’a kawoki? Daga gobe shykenan”

 

Maman fateey????????

[9:12PM, 9/20/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

6⃣9⃣

 

Jikinta yayi sanyi tayi shiru, bai qara cewa komai ba har suka iso gida, ta bude kofa ta fita a hankali yana kallonta ta juyi tace “good night” yace “Ahaa” ta rufe motar, jin shiru bai kirata ba har ta kusa shiga gida yasa ta juyo ta tsaya a gurin window dinshi tace “na bata maka rai ne? Ya girgiza kai yace “a’a me kika gani? Tayi shiru kanta na qasa yace “ki shiga gida dare nayi, kinga mune last din shigowa” a sanyaye tayi hanyar gida tana jin jikinta ba dadi, sai data kusan shiga gida yace “heyyy” ta juyo yace “kinyi kyau” murmushine ya subuce a fuskarta tana kallonshi har ya fice daga gidan. Washe gari hka ta tashi jikinta kamar wacce aka yiwa duka, haka dai ta lallaba har bayan isha, tayi wanka aka bata kaya fitted gown na lace green, aka kafa mata dauri tasha make up, jikinta da kayanta sai qamshi yakeyi. Wani abu a gora kamar madara falmata ta miqa mata tace “gashi kisha inji mummy” fatu ta bata fuska tace “nikam abubuwan nan bazasu qare bane? Lubna da take gefenta ta dafa kafadarta tace “kisha fa” fatu ta karba ta kafa kai ta shanye tass ta ajiye goran tace ‘Alhamdulillah” daria su salma suka saka. Anan mammi ta shigo da wani babban mayafi white mai adon stones kala kala ta daurawa fatu a kanta tace “muje gurin abbanku” ta riqo hannunta har palourn abba, sukayi sallama suka shigo, mammi ta zauna a kujera fatu kuma ta zauna a qasa gurin kafafuwanta. Fatu ta gaishe da abba, ya amsa yana mai fara’a dai dai nan sultan ya shigo shima sanye yake da green shadda jamfa da hularsa itama green, sai zuba qamshi yakeyi ya samu guri kusa da abba shima ya zauna yana satar kallon fatu wacce ta sunkuyar da kanta qasa sosai har baka kallon fuskarta. Abba ne yayi gyaran murya ya fara musu nasiha dukansu, sosai nasihar sa ya ratsa zuqatansu bayan ya gama sultan ne yayi magana yace “abba mun gode” anan mammi ma ta fara nata, a lokacin fatu ta fara kuka harda shesheka, idon sultan na kanta. Sai da mammi ta gama nata nasihar ta kalli sultan tace “ga amanar fateema, marainiyace gaba da baya, qanwarka ce yar uwa, kuma mata a gareka, don Allah idan tayi laifi a gyara mata ta hanya mai kyau, Allah ya baku zaman lafiya” fatu bata samu damar magana ba don irin kukan daya kwace mata tunowa da iyayenta da tayi, anan ta bawa kowa tausayi, abba yayi addu’a aka shafa. mammi ta dauketa zuwa gurinsu inna asabe, suma nasihan dai suka maimaita aka shigar da fatu mota mummy a gefenta da goggo innani, har aka iso gidanta dake New GRA bata bar kuka ba. Gida ne madaidaici hawa daya, zagaye yake da flowers masu ban sha’awa ciki da waje, ana shigowa zaka iske parkin space wanda a kalla zai dau motoci 5 zuwa 6, sai ta bayan gidan lambu ne shima madaidaici, babban palour ne a qasa mai dauke da set din kujeru da tangamemen tv sai sauran kayan kallo, an qawata falon ba laifi, a palon akwai kitchen sai wasu dakuna biyu, dayan kusa da kitchen daya kuma kusa da toilet in palour, still a palourn akwai wata kofa wacce ba’a bude take ba. Upstairs aka haura da ita, nan ma zaka iske wani qaramin palour ne shima da kayan kallonsa,sai dakuna hudu, A cikin dakunan aka bude daya aka shigar da fatu, har kan qaron royal bed dinta mummy ta zaunar da ita tareda dan daga lullubin kan fatun tace “fateema kukan nan ya isa haka, ki share hawayenki” anan ta ciro hanky daga jakarta ta sharewa fatu fuska ta gyara mata shi, tace “karki qara bata fuskan ki kinji? Fatu ta daga kai tana ajiyar zuciya, lokacin qarfe 8:43pm mummy sukayi haraman tafiya fatu ta riqe gyalenta  tace “mummy zan biku” murmushi mummy tayi tace “kiyi hakuri ki zauna gidan mijinki fateema, ai gasu xahra zasu kwana miki” jin haka yasa fatu murmushi tace “to shykenan mummy” su goggo innani suka mata sallama kan gobe zasu koma kumo, ta musu sallama tace su gaishe mata da kaka” gida ya rage daga amarya sai qawayenta, salma da bizzy na waya da alama da samarinsu ne yayinda lubna da xahra da fatu kuma suke hira, fatu tsakaninta da Allah ta yarda zasu kwana bata san wayo mummy ta mata ba. Goma saura wayar lubna ya fara qara ta dauka ganin sunan mijinta, yace ta sauko su tafi. Bayan ta kashe ne ta kalli su bizzy ta musu ido, nan da nan suka fahimta. Xahra ce ta fara tashi tace “nifa banga gidan nan da kyau ba, bizzy kuzo muje mu gani” aiko nan suka miqe suka fita, lubna da take murmushi ta juyo tace “kinsan nikam bazan kwana ba, bari in tafi DJ yazo” fatu ta marairaice fuska tace “shi yaya jameel dan kwana daya bazai bar mana ke ba? Lubna tayi daria yayinda take yafa gyalenta tace “nima bazan iya ba, sai da safenki amarya” fatu ta tashi zata rakata lubna tace “a’a yi zamanki, ba komai, bari in kira miki su bizzy” Tana fita fatu ta koma ta zauna harda cire mayafi, tana zaune shiru har kusan 15mins kuma bata ji motsin su ba, tsoro ne ya shige ta a take tace badai tafiya sukayi ba. Da sauri ta fito daga dakin, ganin basa palourn sama yasa ta sauko qasa nan ma basa nan, cikinta ne ya fara bada stars tabbas guduwa sukayi, a’a ta haura sama da gudu tana bubbude dakunan tana leqawa, kowanne ta bude basa ciki, room din qarshen ne taga hatta door din daban ne, nan ta murda handle din ta shiga dai dai lokacin da sultan ya fito daga wanka da jallabiya fara sol a jikinshi yana taje gashin kansa, jin an bude kofa yasa ya juyo yana kallonta yana mata murmushi, akan mirrow ya ajiye comb din ya dauki wani remote ya danna saitin kofa, nan take kofar ta rufe, fatu ta juya tana qoqarin budewa da taga bazai budu ba ta juyo fuskarta kamar wacce zatayi kuka tace “inasu xahra? Sultan daya harde hannu yana kallonta sama da qasa yace “jameel ya maida su gida” Ido ta zaro ya gyada mata kai hade da kashe mata ido ya nufo gurinta yana cewa “WELCOME HOME HONEY”

 

Maman fateey????????

[2:13PM, 9/21/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

7⃣0⃣

 

Tsayawa yayi daff da ita har suna shaqan qamshin jikin juna yace “me zaki yiwa su xahran? Ta dake tace “mummy tace zasu kwana ai” yayi daria yace “wayo ta miki, babu wanda zai kwana miki sai ni kadai” ta turo baki kamar zatayi kuka tace “nifa… nifa..gaskia ka kiramin su xahrah” murmushi yayi ya juya ya dauki remote din ya danna kofar ta bude yace “kije kiyi alwala ki dawo yanzu” tace “nayi salla fa” yace “I know, ko zakiyi anan? Tace “a’a” tare da ficewa daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button