FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣6⃣
Sunyi sallah inda fatu taci gaba da labarinta..
Zaman lafiya akeyi tsakanin mamata da surkunanta, abu daya ya ke damun mahaifiyata rashin haihuwa. Duk lokacin da goggo innani tazo sai ta samu bakar magana ta yaba mata, nan ma kakata na mata fada. Ta shekara biyu ne ta shirya zuwa ganin gida. Tana isa ta tarar babanta ba lafiya sosai sai dai a kwantar a tayar, tayi kukan halin da yake ciki shi kuma yayi murnar ganinta, don tayi kyau tayi kiba. Ta bawa kowa tsarabar sa bbu wanda ta manta, bayan kwana biu tace a kaishi asibiti, mallam jauro (yayan babanta) yace ba za’a kaishi ba, ai rubutu da maganin gargajiyan da ta raina shi ya kawo shi har yau, yayi ta mita. Satin ta uku tana jinyarsa Allah ya amshi abunsa. Tayi kuka sosai bbu wanda bai tausaya mata ba. Bayan sadakan arba’insa akace azo ayi rabiyan gado, aka raba da yake ita mace ce bata tashi da komai ba sai budurwar akuya. Tun suna bata abinci har rannan mallam jauro yace shi ya gaji da ciyar da ita, hala wani mugun abun tayi acan mijin ya korota shine zata zo tace wai tazo ganin gida, ai wata biun ya cika mijin baizo ba, tana kuka tana bashi hakuri amma ko a jikinsa, hasalima inna haule da matarsa ce suke zugashi, a cewarsu zata cinyesu in suna bata abinci, Akuyarta ta sayar take cin abinci. Ranar sai ga babana ya zo inda ya tarar da rasuwan surikinsa, ya musu ta’aziyya yace zai dauki matarsa su tafi. Budan bakin mallam jauro cewa yayi kar rahmatu ta sake zuwa garin don wanda ya hada ya raba, (kuji rashin tunani da imani) in kuma tazo ta nemi inda zata sauka badai gidansa ba. Mamata tayi kuka kamar ranta zai fita haka babana ya jata suka tafi. Anan yake tambayanta yan’uwan mahaifiyarta. Tace fulani masu yawo ne, sunzo dukku babanta mallam sirajo ya ga mahaifiyar ta wacce ta taba aure a cikin yan’uwansu amma zaman baiyi dadi ba, ‘yarsu daya suka rabu da mijin, aka daura musu aure, bayan wata 2 sauran kuma suka kara gaba. Daga nan basu kara yowa ta dukku ba. Sun dawo gida ta samu muntari yayi amarya. Shekararsu 9 Allah bai basu haihuwa ba, inda amarya asabe ta haifi ‘yaya 4, goggo innani ta hada kai da asaben muntari suna kuntata wa mamata kakata na tsawatar musu. Ana haka har ta samu cikina sunyi murna sosai amma cikin yazo da laulayi ta wahala sosai inda tana haihuwata tace ga garinku. Babana yayi kukan rashin matarsa mai hakuri da juriya ga sanin dattako. Ran suna naci sunan kakata (mamar babana) wato Fatima inda ake ce mini fatu. Na taso cikin kulawan mutum uku, kakannina da babana. Don yanzu kawu muntari ya fara bin hudubar su goggo innani wai an fi sona akan yayansu. Na yi primary anan kauyen mu. Inda duk garinmu bbu wanda ya kaini kokari, sannan na shiga secondry ina jss 2 babana ya hadu da accident akan hanyarshi ta zuwa kasuwanci. Bamu da labari sai gawarsa da aka kawo. Fadin irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne. Nayi kuka har na rasa inda zan tsoma raina. Anan nake tunanin kodai gaskiansu goggo asabe cewa dangin mu akwai mayu masu cinye duk wanda suka rabe su. Kakata kuma tun daga lokacin ta fara kananun rashin lafiya. Na cigaba da karatuna inda kakana ya jajirce sai na gama secondry skul, duk sa’annina sunyi aure daga mai ‘ya’ya biu sai mai uku. Na kuma faranta masa nayi candy daga nan kuma samari suka min caaa! Don duk wanda yazo gurina kakana kance mishi sai na gama karatu. A cikinsu kuwa harda dan kawu muntari da dan goggo innani. Ni kuma wallahi duk cikinsu bbu wanda nake so.
Rannan ina bacci da dare naji ana shafani, bude idon da zanyi naga babangida dan kawu muntari ne. Zan yi ihu ya toshe bakina, na takarkare na dankara mushi cizo sannan nayi ihu. Mutanen gida suka fito ana haskawa. Fitowa nayi da gudu cikin gida ina haki, kaka yace “mene fatu me ya sameki? Nace “babangida ne ya shiga dakina kuma yana tabani” na fada ina matsar kwalla wanda har lokacin jikina bai daina rawa ba. Inna asabe ta cabe “munafuka, sharri zaki yiwa yayan naki? Me zaiyi da ke jiki kamar na aljanu” kaka ya dakatar da ita yace “ina babangidan? Ya ce gani nan, “kaji abunda fatu tace? Yace “wallahi karya take min, na fito zaga bayan gida ne naji kamar nishin mutum a daki, nayi zaton batada lafiya ne da na haskata sai naga mafarki takeyi tana wannan nishin. Shine na bugi hannunta tana tashi tasa ihu. Salallamai goggo asabe tasa wai nayiwa danta sharri. Shi kuma ya fita zaure inda dakinsu yake yana mita wai dama ba’a sonsu a gidan. Ni kuma sai rantse rantse nake, kakanina da kawu muntari sun yarda don zai aikata. Kakatace ta jawoni dakinta na karasa kwana anan. Daga ranan na dawo dakinta kwana. Sati da faruwar lamarin kakata ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzabi ga jiri da yake dibanta, anyi magani na gida har asibiti aka je inda suka ce jininta ne yahau sosai.
[12:42PM, 5/10/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣7⃣
Inda sukace jininta ne ya hau sosai, bata jima a asibitin ba ta koma ga mahaliccinta. Damuwa goma da ashirin.
Anan fatu ta fara hawaye, hajia kulsum cikin tausayawa ta miqa mata tissue paper ta goge fuskarta sannan taci gaba.
Na shaku da kakata sosai, a matsayin mahaifiya na dauke ta. Bana jin rasuwar mahaifiyata kamar nata. Bayan rasuwan kakatace zamana ya dawo gurin goggo asabe, nine wankinta dana ‘yayanta da yake duk maza ne sai autar ta zainab yar shekara 4. Shara, wanke wanke da girki ya zama daily work dina, duka zagi da tsangwama kuma har na saba dasu. Duk abunda yake faruwa kakana bai sani ba, da yake baya zaman gida yana can masallaci tare da tsofi irinsa suna karatu. Idan ya ganni ina kuka sai yayita lallashina da inyi hakuri komai zai wuce inyi ta musu addu’a, Tunaninshi mutuwar iyayena yake damuna, bai san harda wahalan da nakesha yanxu bane. Kwatsam ranar wata friday bayan an dawo daga sallahn juma’a goggo ta sameni da duka wai ban gama abincin rana da wuri ba, na tsaya wasa, tace “shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya ki gama abincin sannan kixo kiyi wanki, kuma wallahi kika kai la’asar sai naci uwarki. Ta aza mini rankwashi a kaina wanda ya sani sakin wani wahalallen qara, “kina jina ina miki magana kina daga min kai kamar wata kadangaruwa don ubanki” da sauri nace “goggo kiyi hakuri” na cigaba da sheshshekar kuka, na tashi da sauri na fada kitchen. Kakana ne ya shigo da sallamarsa ta amsa tana muzurai, Allah yasa baiji abunda tayiwa fatu ba, don batayi tsammaninsa yanzu ba, baya dawowa a wannan lokacin. Ya shige dakinsa ya jima sannan ya kwala min kira, ina sauri zanje ta yafuto ni, naje, murde min kunne tayi tace “saura ki fada masa wani abu sai na ballaki, bulaliya kawai” ta sake ni hade hankada ni har ina cin tuntube na shiga dakin kakana. Cewa yayi inje inyi wanka zan rakashi unguwa. Na fito na fada mata ta harareni tayi kitchen. Da sauri na watsa ruwa na fito, kaya nasa da hijabi na cewa kakana na shirya muka fita. Maimakon naga mun shiga gari sai naga munyi hanyar gona. A cikin gonarshi a karkashin wata bishiyar dorawa muka zauna. Yace “fatu me asabe take miki a gida? Don yau naji wasu maganganu sabanin hankalina” ban yi jayayyaba na fada mishi komai. Idonshi yayi jawur yace ” mahaifiyarki rahmatu amanace a gurina haka kema amanace, bazan bari ta maida ke baiwa ba insha Allah zan nema miki mijin aure kwanan nan inda zaki sami yancinki. Nayi farin ciki da haka sosai. Yayita bani baki hade da nasiha sai yamma liss muka koma gida. Muna zuwa yace in shimfida mishi tabarma a kofar dakinshi ya zauna. Daga ranar ya dawo wuni a gida yana waje tare da mutane, zai aika a kirani sau goma shi ma zai shiga gida sau goma. Abun yana damun goggo asabe sai dai bbu yanda ta iya. Na murmure na fara samun kwanciyan hankali, kaka ya sama min miji dan ladanin garinmu. Hafizu yarone mai hankali da nutsuwa, ga karatun addini baiyi boko ba amma yana da sana’arsa ta dinki, Yana samu ba laifi. Kaka yace “ga zabina wato hafizu dan ladan, idan kin amince inje in sami babansa muyi magana” gaskia bana jin sonshi a raina amma hankali da nitsuwarshi sun kwanta min. Nace “kaka duk wanda ka zaba shine zabina, fatana Allah yasa in samu zaman lafiya da kwanciyar hankali” kaka yaji dadin furucina yace “Allah ya miki albarka uwargidana” daria nayi nace “Ameen tsoho na” carbinsa ya dauka da niyyan min dukan wasa nayi saurin shigewa gida ina daria shima yana daria. Daga kan da zaiyi ya hango wata mota tana tahowa ta layin unguwanmu ga yara rudududu suna binta da gudu, parking tayi a jikin katangar gidanmu. Samari biyu ne suka fito suka nufo kakana da har yanzu yake zaune a kofar gida bai motsa ba. Kallo ya dawo kansu aka manta da mota. Sun fi kama da turawa ko aljanu.