HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata jima ba ta dawo da alama tayi alwala, sai data shigo ta manta bata dauko hijab ba ta juya zata koma, ya tsayar da ita yace “ina zakije? Tace “zan dauko hijab ne” yace “me zakiyi da hijab din? Tace “zan saka muyi sallah mana” yace “sallahn me? Tayi shiru murmushi yayi irin na???? yace “oohh wato kinsan ana sallah kenan, ashe ba sai nasha wahalan koyar dake komai ba” bata kulashi ba ta qara niyyar juyawa yace “wait” yaje gaban makeken wardrobe dinshi ya bude ya dauko mata wani white hijab ya bata. Mamakine a fuskarta don this is the second time da yake bata hijabi daga wardrobe dinshi kuma duk nata ne. Tace “a ina ka samu? daga kafada yayi yace “nima ganinsu nakeyi a gurina” tace “serious dai” yace “a gurin shanya kaya nake gani sai in dauka” daria tayi tace “to a dalilin me? Me kakeyi dasu? Yace “ohoo, yanzu ba gashi sun miki amfani ba? Lets pray” Ba musu ta bishi yaja su raka’a biyu suka sallame. Ya juyo ya dafa kanta tare da kwararo addu’o’I da musulunci ya tanadar domin samun zaman lafiya da zuria dayyiba. bayan ya gama, ya qara wasu addu’o’in suka shafa. Ya miqe tareda da fita daga dakin, a hankali ta tashi ta linke darduman sallah tareda hijab dinta ta adana su, ta rasa me zatayi gashi gabanta sai dukan uku uku yakeyi, bata qara 2mins ba ya shigo da ledoji a hannunshi, ya ajiye a lallausan carpet din dake tsakiyar dakin ya zauna yace “kizo” ba musu tazo itama ta zauna dan nesa dashi. Murmushi yayi ya kada kai ya ciro kazar dake cikin ledan ya daura ta a kan plate din da ya shigo dashi, fresh milk ya saka a glass cup ya miqa mata, ta girgiza kai yace “what? Tace “na qoshi” bai ajiye hannunsa ba yace “gashi” ta karba, ya qara tsiyaya wani a cup, hankali ya yanko tsokar kazar tare da kaiwa bakinta ta juya fuska, murmushi yayi ya gyara zama yace “kinsan me? Ta juyo tace “a’a” yace “ranar dinner saura kadan in shaqe, cake din da kika bani ya mini qato” daria tayi tace “sorry dear” yace “noo, naqi hakurin” wasa wasa ya rinqa janta da hira har ya miqa mata kazar ta karba ta fara ci tana korawa da fresh milk din, da na hannunta ya qare da kanta ta qara yanko wata tsokar, shima a haka yana ci sai da sukayi nakk! Ya cire hannunshi yace “Alhamdulillah, anaso ana kaiwa kasuwa, gashi ke kadai kin yiwa kazar illah” ta sunkuyar da kanta kasa tana juya empty glass cup din dake hannunta tace “ba wayo ka mini ba, kana ta jaana da surutu” yace “ba wani dama jira kikeyi” ya fada yana murmushi, itama murmushin tayi ta fara tattara gurin ta kai kitchen. Dakinta ta wuce ta cire kayan jikinta ta fada wanka, bata jima ba ta fito ta shafa humran ta mai dadin qamshi saqo saqo na jikinta, ta shafa cream dinta mai kulacca, tana tsaye a bakin wardrobe ta rasa wani night wear zata saka don gaba dayansu basuda M????. Tana tsaye taji mutum a bayanta ya rungumota a hankali ya daura habarshi a shoulder dinta ya zagayo hannunsa ta kan tummy nata yace “in tayaki zaba?

saboda irin yanda jikinta ya mutu yasa ta kasa koda kwakkwaran numfashi, ya daga ido ya kalleta yaga yanda tayi kasa da kanta dan mitsitsin bakinta a bude tana numfashi, saketa yayi ya shiga duba kayan, ya dauko daya ya manna a jikinta ya dan dubeta, tana nan tsaye kamar statue da dan qaramin towel dinta, ya ajiyeshi ya dauko wani purple dan guntu silky one, gaban rigan anyi ado da pink flowers, hannun rigan irin na bra, ya manna a jikinta yace “wannan zai miki kyau” ta dago ido ta kalli rigan tace “nifa ba irinsu nake sakawa a gida ba” murmushi yayi ya cire rigan daga hanger ya bata yace “banbancin gida da gidan miji kenan, idan kin gama ki sameni a dakina akwai abunda zan nuna miki” ya shafa sajenshi ya fita daga dakin, binshi tayi da ido yana fita ta murguda baki hakan yayi dai dai da juyowanshi yace “ni kika murgudawa baki? Ehhh lallai zaki gane” ya fita. Murmushi tayi ta dauki rigan tana kallo, ganin ba sarki sai Allah yasa ta saka, ba qaramin kyau rigan ya mata ba, ta zamo kamar wata baby doll, kallon kanta tayi a madubi, ta juya ta qara juyawa, qarar wayanta ne yasa ta tsaya da juye-juyen kafin ta dauka ya zama missed call, body spray ta fesa ta saka dogon hijabinta ta kashe light din dakin ta fita tareda rufe kofan.

 

Maman Fateey????????

[7:10PM, 9/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

7⃣1⃣

 

A hankali ta murda handle din kofar sultan ta kutsa kai tareda sallama a bakinta, yana zaune a bakin gado yana danne-danne da laptop dinshi, dago da kai yayi ya amsa mata, tsayawa tayi a bakin kofar tace “kace zaka nuna min abu” yace “yeah, zo ki gani” yayinda ya mai da kanshi kan laptop din yana dannawa. Dan nesa dashi kadan ta tsaya tace “gani” hannunsa ya miqa mata alamar ta taho, kamar bazata je ba amma ta miqa nata hannun, jawota yayi jikinshi tareda cire hijab din jikinta, hakan yayi daidai da mutuwar laptop din, ya rufe ya ajiye a bedside yace “labari zan baki, amma first ki saki jikinki kuma karki tsorita!!!

 

Washe gari misalin 8:45am yaji ana buga kofa, bude idonshi yayi a hankali ya sauqe akan kyakkyawar fuskar matarshi fatu, wacce baccinta takeyi hani’an, murmushine ya subuce a fuskarsa, lokaci daya kuma tausayinta ya mamaye zuciyarsa tuno da irin wahalan da tasha jiya, “she’s special” ya furta qasa-qasa yayi kissing goshinta tareda zare jikinshi a hankali daga jikinta. Jallabiyarsa ya zura tareda fita daga dakin zuwa palourn qasa inda ake bugu har yanzu. Salma da bizzy ya gani bayan ya bude qofar kowacce bakinta a washe da food warmers a hannunsu, bizzy tace “sannu ya sultan” salma tace “ina kwana, an tashi lafiya? Bizzy tace “ya gajiya? Kallonsu yakeyi ya zura musu ido kuma bai amsa duk gaisuwan da suke masa ba. Ganin haka yasa suka rage fara’a salma tace “mammi ce tace mu kawo muku breakfast” Tokare qofar yayi yace “da sanyin safiyar nan? Kallon juna sukayi salma ta zaro ido tace “ya sultan yanzu fa karfe 9, ai ko na goye yasan rana ta fito” ya harde hannayensa yace “magana zaki fada min ne? Salma tace “wane ni? Sorry. To bari mu shiga mana” ta fara qoqarin yin step gaba. Ya sauqe hannayensa yace “ba matsala, kawo abincin, mungode” Baki suka sake yayinda ya karbi na hannun bizzy ya ajiye a falon, ya qara karban na hannun salma shima ya ajiye yace “ku huta gajiya” Ruff ya rufe kofar ya barsu tsaye a gurin, mahmud da yake cikin mota don shi ya kawo su ya tuntsire da daria harda riqe ciki, ganin sun juyo yasa ya masge ya fuske. Jiki a sanyaye suka qaraso gurin motar salma kamar ta nitse don kunya don mahmud da take yiwa big time yaga an mata ajii down. Babu wanda yayi magana har suka shiga motar, maigadi ya bude musu gate suka fita bizzy tace “ohhh yanzu karfi da yaji ya hanamu shiga? Daria ne ya subucewa mahmud, yanayi a hankali salma ta harareshi ganin haka yasa bizzy itama tayi daria tace “ba laifinshi bane” anan abun ya zama na tsokana suka dinga darawa har suka iso gida.

Sultan na komawa daki yaga ba fatu akan gadon, dakinta ya nufa anan ya samu ta shiga bathroom. Komawa dakinshi yayi yana sosa kai shi daya yana murmushi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button