FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ruwan zafi ta qara hadawa ta shiga tayi sitbath duk da cewa jiya sultan ya gasata, tafi 15 mins a ciki sannan tayi wanka da ruwan dumi tayi brush ta fito, ba laifi ta daina jin ciwon da jikinta yake mata sai abunda ba’a rasa ba. Cream dinta ta shafa tayi light make up, riga da siket na wani super wax mai yellow nd blue ta saka, dinkin ya amshe ta kamar a jikinta aka dinka, dauri ta kafa kamar mai shirin zuwa liyafa, bin jikinta tayi da turare ta ko’ina. Tana ajiye kwalban turaren sultan ya shigo shima da alama yayi wanka don ya canja kaya, brown three quarter ne a jikinshi da black t-shirt an rubuta _special you_ a jiki, sai zuba qamshi yake yi sajenshi da gashin kanshi ya kwanta luff luff yana kyalli. Sunkuyar da kanta tayi don irin kallon da yake aiko mata ta mirrow bazata iya juraba. A hankali ya qaraso gurinta ya rungumeta ta baya tace “ina kwana” yace “lafiya lau, kin tashi lafiya? Tace “lafiya” yace “ya jikin kuma? Shiru tayi ya juyo da ita suna fuskantan juna fuskarsa so serious yace “har yanzu kina jin zafi, sorry habebteey. Ok dauko gyalen ki mu tafi hospital” Ta marairaice fuska tare da dago fararen idanunta tace “nifa lafiyata kalau, bari in sauka in mana breakfast”
Ya kama hannunta yana kallon cikin kwayar idonta yace “are sure bakijin komai? Ta daga kai yace “um um fa” tace “Allah naji sauqi” murmushi yayi yace “ok Allah ya qara lafiya, kinyi kyau dear” murmushi tayi tace “thanks” yace “shi kadai kika ji? Baki amsa addu’an da na miki ba” kwace hannunta tayi a hankali ta fara tafiya tace “zan hada mana break fast” binta yayi yana cewa “mammi ta aiko mana” a dinnin ta tarar da food flasks din zata wuce kitchen ta dauko plates da cups ya tsayar da ita yace “ki huta, don naga baki dawo normal ba” ya zaunar da ita kan daya daga cikin chairs din dinning table din shi kuma ya wuce kitchen. Bai jima ba ya fito riqe da plates da cups a hannunsa ya ajiyesu akan table din ya fara servin dinsu, ferfesun kifi ne sai masa da miyan ganye wacce tasha tsokokin nama, kunun gyada ya saka musu a cups din ya turawa fatu gabanta, anan ya kalleta yaga ta zuba masa ido tun shigowansa take kallonsa tana jin wani irin sonshi na fisgarta, dan fulani kyakkyawa wai mijinta ne ita dayanta, gaskia na taki sa’a…. iskan daya hura mata ne yasa ta farka daga kogin tunanin da ta fada, murmushi ne a fuskar sa yace “what are u thinking? Ko na miki kyau ne? Murmushi tayi ta kalli abincin gabanta tace “nagode” A hankali suke cin abincin suna hira jefi-jefi har suka kammala, ya dauki used plates din ya kai kitchen fatu ta bishi da cups din, anan suka wanke hannu, zatayi
wanke-wanke yace “noo, ki bari akwai masu aiki, zasu zo suyi” zatayi magana ya daura yatsansa a kan lips dinsa yace “shhhh, muje muyi bacci”
*AFTER 3yrs*
Maman Fateey????????
[10:12AM, 9/23/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
7⃣2⃣
*AFTER 3YRS*
Gurin cike yake da mutane, ko’ina ka duba group group ne na family sunzo taya ‘yan uwansu murnan gama university. A cikin su na hango familyn su fatu, mammi, mummy, lubna da jameel da ‘yarsu yar shekara 2 da rabi, mai sunan mummy ce wato kulsum amma ana kiranta khairy, amrah ce a gefe ta zama budurwa tana bawa al’ameen ruwa a baki, yarone dan shekara da wani abu, yana gama shan ruwan ya wuce gurin mamanshi salma matar mahmud yana cewa “ummii give me cake” dan gaba dasu naga fatu tareda sultan suna zaune abinci take zuba masa a plate yayinda yake qoqarin bude Qaton cooler da sukayi guxurin drinks a ciki, coke ya dauko ya balla marfin ya fara sha, tana gama saka masa ta miqa mishi ya karba ya koma gurin su jameel da mahmud wanda suma abincin ne a gabansu. Anan suke labarin yanda graduation din ya qayatar, fatu ta fito da flying colors wanda hakan ba qaramin dadi kowa yaji ba, mammi harda hawaye. Bayan an gama shagali suka kama hanyar gida. Kai tsaye kowa ya wuce gidansa don irin gajiyar da suka kwaso, tun safe suke cikin GSU sai yanzu bayan la’asar suka koma gida. A falo fatu ta yada zango ta dafe kanta tana tunani. Shigowan sultan yasa tayi saurin sauqe tagumin ta qaqaro murmushi, fuskarsa da damuwa yazo ya zauna kusa da ita yace “what again, nikam bakya tausaya min ne? Ya kike so inyi ne? Tace “babu komai fa, kawai gajiya na debo ga ciwon kai da yake damuna” Hugging dinta yayi tsam a jikinshi yana buga bayanta, a hankali wasu siraran hawaye suka gangaro daga idanunta, da wayo ta gogesu don kar sultan ya gani. Mintuna kadan suka yi upstairs. Dakinta ta shiga shima ya wuce nashi, ta kwabe kayan jikinta ta shiga wanka. Ruwan mai dumi ta hada a bathtub din ta diga turaren wankanta wanda bata rabuwa dashi tun aurenta yau shekara uku. Shiga ciki tayi ta zauna tareda sauke nannauyan ajiyar zuciya. A haka ta fara tunani….. tun bayan aurensu suke dokin samun haihuwa amma har yau Allah bai basu ba, shekara da aurensu mammi ta kira fatu gida take tambayanta “fateema kinyi planning ne? kina school may be kina tsoron wahala, ga karatu ga yaro ko? Don Allah Ki bari ki haihu in yaso ni zan karbi babyn” fatu tace “mammi wallahi babu abunda nayi, har asibity naje a dubani ko inada matsala ne suka ce a’a, mammi ban san ya zanyi ba” ta qarisa maganan tana hawaye. Anan kuma mammin ta shiga lallashinta tana bata baki, tace “ki kwantar da hankali, Allah zai baki a lokacin da ya dace, kinga mahaifiyarki ma sai data shekara 9 kafin ta haifeki a labarin da naji, ni kuma kinga daga nayi miscarriage sai su rasu suna jarirai, mu kuma haka Allah yaso ya ganmu. Muyi tawakkali” fatu ta jinjina kai tana share hawayen fuskarta. Daga ranan mammi bata qara mata magana akai ba sai qoqarin ganin ta kwantar mata da hankali takeyi. Shima sultan ya taba mata kwatankwacin haka still shekaransu biyu da aure lokacin mahmud da salma sunyi aure, salma ta haihu ana gobe suna, sun fita shopping din kayan suna yaga wani feeding bottle dan qarami mai kyau, ya dauka yana juyawa a hannunsa, anan ta dauko wani riga na jarirai tana nuna masa amma hankalinshi nakan feedern, tabashi tayi ya juyo da dan murmushi a fuskarsa yace “wannan ya miki kyau” itama murmushin tayi tace “yayi kyau” yace “zan ajiyewa babyn mu da zamu haifa” daga kanshi yayi kamar mai tunani can yace “yau 2yrs da aurenmu harda wata uku, anya fateema banida matsala kuwa? Ya sauqe Idanunshi a kanta yaga har ta fara kuka, kafin yayi magana ta fita daga gurin, ranshi a dagule yaje ya biya abubuwan da suka siya ya kai mota, a motar ya sameta tana kuka ya ajiye ledojin shopping din a backsit ya zagayo zuwa mazauninsa, yana shiga ya jawota jikinshi yace “na bata miki rai ne? Ta girgiza kai yace “to meyasa kike kuka? Tayi shiru yace “fateema talk to me” share hawayen fuskarta tayi tace “babu komai” yace “don kawai nace ko inada matsala? Last year mammi ta mini magana akan ko munyi planning nace mata a’a, amma ta tambayeki may be kinyi ban sani ba, wanda kuma nasan hakan zaiyi wuya, bayan ta kiraki ne take sanar dani cewa babu abunda kikayi lokaci ne kawai baiyi ba, ta fada min cewa kinje asibity wanda a sanina baki fada min zaki je test ba, amma sanin irin halinda kike ciki yasa kwata kwaata banji raina ya baci ba kuma na nunawa mammi cewa da sanina kikaje” ya dago fuskarta yace “damuwarki daya: mammi tana son jikoki nd ni kadai ne danta kina tunanin ko hakan zaisa in qara aure! Ni mata biyu nake da niyyan yi kuma already na auresu” a firgice ta miqe daga jikinshi lokaci daya kuma tace “aure?? Mata????