FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Fateey????????
[10:00PM, 9/24/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
7⃣3⃣
Ya gyada mata kai yace “dayar fateema mahmud dayar kuma fatu mamuda” ya qarisa yana daria, duka ta kai mishi a kirji kana ta juya mishi baya tana kallon window, share hawayenta takeyi tana murmushi, Allah ne kadai yasan yanda zuciyarta tayi pounding jin cewa sultan dinta yayi aure, ya jayota tana qoqarin kwacewa ita ala dole tayi fushi, matseta yayi sosai ya juyo da fuskarta har suna shaqan numfashin juna yace “u ar d only one I need, kece fateema kece fatu so ke kadai kin isheni” ya dan sassauta riqon daya mata yacigaba “amma saidai bamusan abunda Allah ya tanadar mana gaba, amma in dai nine u ar d one nd only” murmushi ya subuce a fuskarta tace “abunda yasa kaga nayi haka bawai tsantsan kishi ba ne, nooop tunanina cewa kayi aure baka sanar mini ba wanda hakan ya nuna rashin matsayina kenan a gurinka, babu macen da zata ji dadin cewa mijinta
Yayi aure ba tare da saninta ba. Naji dadin maganarka na cewa I am d one nd only kuma daga baya ka fada min gaskia cewa bamusan abunda Allah ya tanadar ba, yana daya daga cikin abunda yasa nake qara sonka fadin gaskiarka, Ban taba addu’an zama ni daya ba don nasan kai *mijin mace hudu* ne littafin eeshmal. Sai dai koyaushe addu’ana Allah ya kawo abokiyar zama tagari” shafa kanta yayi yana murmushi yace “Ameen, in kuma ni mijin mace daya ce Allah ya qara mana zaman lafiya da zuria masu albarka” tace “Ameen Jannah”…… kwankwasa kofan bandakin da akeyi yasa ta dawo daga tunanin da takeyi. Tayi gyaran murya, bude bandakin yayi yace “lemme join u” ta karkada mishi kai alamar a’a, bata fuska yayi yace “please” Tace “ok” wankansu sukayi suka shirya cikin qananan kaya, zama sukayi a palour suna kallo suna hira, wayar sultan ne ya fara ringing ya dauka yace “hello” magana aka fada mishi, ya dan kalli fatu kamar mara gaskia yace “zan kira anjima please, bye” fatu bata ma jishi ba don kallonta take yi. Washe gari da asuba bayan sunyi sallah sunyi karatu dama wannan qa’ida ce har sai rana ta fito, fatu tayi addu’a ta shafa ta miqe ta niyyar kwanciya a gado ya tareta yace “sai ina? Tace “bacci jannah” yace “noop ba yanzu ba, muje in tayaki shirya kaya, tafiya zamuyi” Tace “ok” wankansu sukayi suka shirya cikin qananan kaya, zama sukayi a palour suna kallo suna hira, wayar sultan ne ya fara ringing ya dauka yace “hello” magana aka fada mishi, ya dan kalli fatu kamar mara gaskia yace “zan kira anjima please, bye” fatu bata ma jishi ba don kallonta take yi. Washe gari da asuba bayan sunyi sallah sunyi karatu dama wannan qa’ida ce har sai rana ta fito, fatu tayi addu’a ta shafa ta miqe da niyyar kwanciya a gado ya tareta yace “sai ina? Tace “bacci jannah” yace “noop ba yanzu ba, muje in tayaki shirya kaya, tafiya zamuyi” Ta ware eyes tace “ina? Yace “around da world” aiko da gudu ta dane kanshi tana daria shima tayata yayi. Dama ya mata alqawarin in ta gama skul zasu fita yawon bude ido.
Saai da suka nitsu tace “thanks jannah, Allah ya saka da alkhairi” yace “Ameen, oyaa dauki abunda kike buqata don qarfe 9 jirginmu zai tashi” a qaramin akwati ta hada abubuwan da take buqata don ya hanata daukan kayan sawa wai zasu sayi new ones, dan sinadaranta, undies da turarukanta sai dan abunda zata buqata, kafin 8 sun gama shirinsu tsaff, suka rufe ko’ina suka fito, doguwar riga ce a jikinta indian design mai purple nd pink, sai baby hijab dinta black, takalmi da jakanta ma black, tayi dan make up tayi kyau abunta kamar sweet 16 kai kace bata yi shekara 22 ba. Shi kuma jeans da riganshi t-shirt ya saka yana riqe da jakan laptop dinshi sai dan qaramin trolley dinshi yana ja, a palourn qasa suka hadu yace “kinyi kyau habeebtey” tace “thanks jannah, kaima kayi kyau kamar wani dan saurayi” daria yayi yace “me banbancina da saurayi? Itama ta dara ta nuna kanta da yatsa tace “gani kuwa, idan aka ganmu tare ansan lallai ka ajiye iyali” Kayansu suka saka a bayan mota tayi driving dinsu zuwa gidan mammi suka mata sallama ta bisu da addu’a, tana jin dadin irin yanda suke zaman lafiya, dadi fall a ranta ta koma gida yayinda drivern abba yayi drivin dinsu zuwa gidan mummy. Itama suka mata sallama farouq yake cewa “da ana hutun school dana biku” fatu tace “next time da kai zamu tafi”.
A airport driver ya ajiyesu su kuma sukayi proceeding jirginsu ya daga zuwa abuja, daga nan suka qara shiga wani zuwa Mauritius, daki suka kama a wani 5star hotel, sun zaga cikin gari sun bude ido, kwanansu 5 suka daga zuwa india, shima basu jima ba suka wuce london, paris, china, daga nan suka wuce saudi arabia sukayi umrah, satinsu biyu a qasa mai tsarki sannan suka wuto dubai, anan sukayi masauqi a wani apartment da sultan ya siya, da yake fatu tana zuwa dubai in anyi hutu, kuma harkan business dinsa yafi yawa anan dubai din. Fatu ta cika tayi bul bul abunta ga wani haske data qara. Satinsu biyu sukayo haramar dawowa gida, tsaraba kam sun kwaso shi, da safe jirginsu ya tashi zuwa Abuja Nigeria, daga nan suka hau na gombe, kusan la’asar suka sauqa airport, driver ne yazo ya dauke su ya kaisu gidansu. Kamar koyaushe an gyara musu gida an share ko’ina kamar dama masu gidan suna ciki, bayan sunyi wanka sun shirya suka fito palourn qasa, Amrah suka tarar a xaune da food flasks a gefenta. Ta tashi da dan tsallenta ta rungumesu tana cewa “I miss u guys” sai da suka gaggaisa amrah tace “kai anty fateey wallahi kin qara kyau, ya sultan kaima kayi kyau” fatu tayi murmushi tace “amma cikinmu wa yafi kyau? Na fishi ko? Tafada tana winking din amrah. Daria sultan yayi yace “aiko makaho ya laluma yasan na fiki” buga kofan da aka fara yasa amrah ta miqe tare da budewa, khairy yar jameel ce ta shigo da gudu amrah ta dagata suna daria tace “ina mom dinki? Sallama jameel da lubna sukayi aka amsa musu fatu ta tashi ta tari lubna cikin dokin ganin juna, lubna ta ajiye basket din hannunta sukayi hugging juna, jameel ya zauna kusa da sultan ya bugi kafadanshi yace “ka gansu kamar basa waya koyaushe” daria sultan yayi sukayi hand shake yace “zaka fara ko?
Maman Fateey????????
[9:09PM, 9/25/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
7⃣4⃣
Hiran yaushe gamo sukeyi har aka kira sallarn
Maghrib, bayan sunyi sallah suka hadu a dinning table, tuwon shinkafa miyar egusin da amrah ta kawo sukayi serving, snacks da kunun aya lubna ta kawo. Sultan sai kallon fatu yakeyi, in sun hada ido sai yayi murmushi, jameel ne ya bugi kafadarshi a hankali yace “ya? Sultan shima yayi qasa da murya yace “I am confused! To ta yaya zan….” wayar amrah ce data fara ringing ne yasa ya dakata da maganan da yakeyi, har wayan ta katse bata dauka ba, sultan yace “bakiji ana kiranki bane? Ta bata fuska tace “yaya ka bari kawai” bai qara cewa komai ba har suka gama cin abincin ita kuma tasa wayar a silent. 8:19pm su lubna sukayi haraman tafiya, fatu ta kwaso musu tsarabansu ta basu, amrah ma aka bata nata, suna tafiya amrah tace “nima fa zan tafi, bari in kira driver” sultan yayi saurin katseta yace “ki barshi kawai, kizo in kaiki” fatu ta kawo tsaraban su mammi da abba tace a kai musu. Suna isa gida suka sami mammi a falon abba, sultan ya gaishe su, sunyi murnan ganinshi, mammi tace “manga kun dade kam gaskia, har na fara zaton ko kun koma can da zama ne” ya sosa kai yana murmushi yace ” a’a mammi” tace “ina fateeman? Tana lafiya? Yace “lafiyanta kalau, tace a gaisheku, gobe itama zata zo” mammi taji dadi tace “to Allah ya kaimu, in banda ita ai da ta huta tukunna” sultan yace “ita ta matsu mu dawo, wai tayi kewan gida” mammi tace “ayya fateema na” bai jima ba ya musu sallama mammi ta fito ta rakashi har gurin motanshi suna hiran tsakanin d’a da uwa, yace “mammi akwai maganan da zamuyi” ya fada wani sunkuyar da kai, tace “wani abune manga? Magana naga yake fada mata tayi shiru tana sauraronsa can tace “amma kunyi bincike ne? Yace “a’a zamuyi dai, amma kar a fadawa abba. Ba yanzu ba” mammi tayi murmushi tace “ai abun farin ciki ne, ya kamata ya sani tun wuri” sultan yace “a’a mammi, to ki bari ni zan fada masa da kaina” daria mammi tayi tace “kai kadai dinka, Allah ya tabbatar da alkhairi” yace “Ameen” shima yana daria, tace “mara kunya, mun gode da tsaraba” ya shige motarsa yana daria. Kafin ya isa gida sai da ya biya ya sayawa fatu chocolates da ice cream sannan ya koma. A dakinta ya tarar da ita ta fito daga wanka tana shafa mai, ya lallaba zai dan tsorita ta sai kuma ya fasa, yayi sallama ta amsa ya shigo tace “ya ka sami su mammin? Yace “lafiyansu sunce ma a gaisheki” tace “ina amsawa, na qagu ai gobe tayi inje inga mammi na” ta qarisa magana tana murmushi. Fita daga dakin yayi yana zolayarta wai goben ma bazata je ba, tana gama shiri cikin kayan baccinta ta mulka humranta ta fito, a falon sama ta hango leda akan kujera ta bude, ice cream ne da chocolates ai da murnanta ta hau sha, kafin sultan ya fito ta cinye tasss, Ya fito shima da kayan baccinsa ya ganta yace “ina nawa” ta ware ido tace “dama baka ci bane? Ya harde hannayensa yace “tukunna ma wayace naki ne? Shiru tayi tana mai murmushi can tace “sorry” yace “zanga wazai siyo miki gobe” ta marairaice fuska ta turo baki tace “bana baka hakuri ba? Yace “its ok, ai bakya laifi, muje mu kwanta” Washe gari fatu ta shirya tun 11 sultan ya sauqeta a gidan mammi shi kuma ya wuce, mammi ba qaramin dadi taji ba ganin fatunta tayi kyau tayi fresh, tana azahar ta wuce gidan mummy itama taji dadin ganinta, ta basu tsarabansu duk na farouq yafi yawa, anan ta hadu da khadija qanwar jameel tazo da yaranta biyu, khadija ke cewa ” Madam ya kamata yanzu kam muga baby” fatu tayi shiru kaman ruwa ya cinyeta, khadija ta qara cewa “kinyi shiru ko har yanzu baku gama amarcin bane? Fatu ta dago kai fuskarta ba yabo ba fallasa tace “kinsan komai sai lokacinsa yayi, kuma mutum bashi yake bawa kansa ba, Allah ne zai kawo a lokacinda ya dace” tana gama fadan haka ta tashi tace “bari in dauko abu a kitchen”.