HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

A kitchen khadija ta sameta ta dauki ice cream tana neman qaramin spoon, tace “fateema kiyi hakuri da abunda na miki, I was a victim too, lokacinda nayi aure kafin na haihu sai da nayi 2yrs, irin haka in dangin mijina na qauye sukaje hutu gurinmu sukan fada min irin maganganun nan and bana jin dadinsu, duk abunda baka so a maka kar ka yiwa dan uwanka, kiyi hakuri don Allah” fatu ta dafa kafadarta tana murmushi tace “ni baki bata mini rai ba maman sabeer, don a raina na dauka hakan yana faruwa ga irina, so kinga in nace zan dinga bata rai zan hadu da matsala, haihuwa na Allah ne da kudi ko matsayi basa bawa mutum” Khadija tace “hakane kiyi hakuri” fatu tayi daria tace “c’mon ki daina bani hakuri, nifa ban dauka da wani manufa ba” khadija tayi murmushi tace “nagode” a haka sukayi ta tadi har bayan la’asar sakaliya ta koma gidan mammi. Ana isha sultan yazo suka wuce gida.

 

*Bayan Sati daya*

 

Fatu ne zaune a palourn lubna tana shan kankana yayinda lubna ke kitchen tana aiki take cewa “kayan nan suna ta tafiya fateema, hajia nazifa ta kirani tana son swiss guda 24, dozen biyu kenan” fatu zatayi magana taji muryan jameel a waje yana cewa “kana nufin har yanzu baka fada mata ba? Sultan yake cewa “ka santa da sa abu a rai, kuma ma me zance mata? Dai dai nan suka shigo fatu tayi saurin amsawa lubna maganarta da cewa “idan na koma gida zan aiko miki sai ki tura mata” amma can qasan ranta ta fara tunanin akwai wani abu da yake tafiya, ‘something is fishy’ kwanan nan ta lura da wani extra care da sultan yake bata haka ma mammi koyaushe saita kirata tana wani lallabata. A ranta tace she has to find out. Zama sukayi suna hira sai bayan isha suka koma gida. Qarfe 9:55pm agogon wayan fatu ya nuna, fitowanta daga wanka kenan tasa kayan baccinta ta feshe jikinta da turare ta nufi palourn qasa inda sultan ke aiki da laptop dinshi lokaci daya kuma yana waya. A gefenshi ta zauna ta canja tasha zuwa zee world, kallonta yakeyi kamar ya cinyeta don wani irin kyau da take qara masa koyaushe, a daddafe ya qarisa abunda yakeyi ya jayota jikinshi yana shinshina wuyanta yace “kin hanani aiki” tayi murmushi tace “dama already ka gaji” ganin abubuwan da yake mata yana yawa yasa ta dan zare jikinta tace “can we talk? Gyara zamansa yayi lazily yace “why now? Meyasa yanzu? Tace “sorry jannah” yace “ina jinki” tace “me yake faruwa ne? Naji dazu kuna magana da ya jameel” ta kalleshi tana son karantan yanayinshi. Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace “a ina? Tace “dazu bayan maghrib da kuka shigo gida” murmushi yayi yace “me kika ji? Juya idanunta tayi irin questions din sunyi yawa tace “yana tambayanka dalilin da yasa baka fada min wani abu ba” ta gyara zama ta fuskanceshi sosai tace “mene kake boye min? Yau kam ka fada min, kafin mu tafi mauritius naga kayi waya wanda magananka baiyi tsawo ba kace zaka kira, kamar baka son yin wayar a gabana, ina lura da kai. Ko abokiya zaka kawo min ne? Ta qarisa maganan yayinda wani irin abu ya tokare mata maqoshinta yana qoqarin sata kuka. A hankali sultan yake kallonta da dan murmushi a fuskarsa yace “tunda kinyi smelling ya kamata in sanar dake” ya kamo hannunta duka biyu yana murzasu a hankali yace “fatuhhh…..”

 

Maman Fateey????????

[10:24PM, 9/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

7⃣5⃣

 

Yace “fatuhhh” tayi shiru ta qura masa ido kirjinta na bugawa da sauri da sauri, yace “fateema” tace “na’am ina jinka” don ta qagu taji menene don zuciyarta na gab da tarwatsewa. Ya cigaba da murza hannunta yana cewa “ranar da jones nake magana don shi ya mana visa, so bana son kiji a lokacin ne” Tace “uhum” yace “fateey wai u ar pregnant” ya qura mata ido yana kallonta. Ta girgiza kai tace “wai? Kuma… oh god!! Don Allah ka fada min abunda yake faruwa,  nasan ba maganar ba kenan” wani siririn hawaye ya gangaro fuskarta ta share. Yayi ajiyan zuciya yace “wallahi maganan kenan, ranar da muka dawo su lubna ai sunzo, so anan jameel daya ganki yaga alamun masu ciki tare dake, so mun fita sallah yake gaya min, in kin lura muna cin abinci inata kallonki amma banga alamun komai ba” da sauri fatu ta shafa cikinta tana lalumawa kamar mai neman abu, tana cewa “da gaske inada ciki? To tayaya zan gane? ganin hakan bazai nuna mata komai ba ta kwaye rigarta tana dubawa, sultan ya zuba mata ido yayi tagumi, yace “kinga dalilin da yasa naqi fada miki kenan, don kar kizo ki sa rai alhali ba cikin gareki ba ki qara tada hankalinki” Ta dago ido tace “muje chemist mu siyo PT strip” yace “me kenan? Tace “abun gwada ciki ne” tashi muje” Ta miqe ta haura sama da gudu harda harhada steps, tana kulewa sultan ya dafe kanshi yace “ya Allah ka taimakeni, Yanzu in ba ciki bane sai tayi wata daya mood dinta bai dawo dai dai ba” fitowanta yasa ya juya yana kallonta, tasa zani da hijab, ta iso gurinshi tana wani dafe ciki tace “muje to” Ba musu ya dauki key din motarsa da yake kan kujeran suka fita. Da yake dare yayi wasu chemist din har sun rufe,  A.A Aliyu chemist suka samu a bude, ya barta a mota ya shiga, yace “ina son PT strip, abun gwada ciki” mutumin yace “guda nawa? Sultan yace “da guda nawa akeyi? Yace “da guda daya akeyi alhaji” Sultan yace “ok, a bani 5” aka bashi ya ciro kudi ya bayar ya koma mota. Fatu tana can tana jiranshi sai addu’a takeyi a zuciyarta Allah yasa ciki take dashi, sai a sannan ta tuno rabonta da tayi period tun tafiyansu mauritius, kuma cikinta ya dan tashi, amma ta danganta hakan da irin ciye ciye da cin abincin da takeyi kwanan nan, kuma dama tayi dan qiba.

Ya miqa mata ledan suka koma gida, kafin ya fito daga mota har ta shige gida, tayi fitsari a wani dan qaramin roba ta saka strips din duka tana ajiyewa, anan ya shigo bandakin yace “fateema ki nitsu fa” ta matso gurinshi tana kallon agogon hannunshi tace “nan da minti 5 zamu ga result” Zaiyi magana tace “shhh, muyi addu’a jannah, zuciyata tana ta bugawa, kaji” ta daura hannunsa akan kirjinta tace “kaji? Yace “ehh” fatu ta bata fuska tace “kamar kai baka damu ba” yace “ya zanyi? Kin kasa fahimta ta, banso fada miki ba, to yanzu tunda na fada miki dole in biye miki” kallon agogon hannunshi tayi tace “saura 3mins” shiru shiru har 5miins din suka cika. Ta kalleshi tace “ina tsoro, kaje ka duba” yayi ajiyar zuciya ya fara tafiya zuwa gurin ta riqo shi idonta taff da hawaye data kasa tantance na menene tace “zanje” ya matsa mata taje ta dauka bakinta sai addu’a take kwararowa, ta rufe ido ta bude a hankali… “P…popp…POSITIVE” wani irin tsalle ta daka sai akan sultan yace “what? Menene? Gabadaya ya kidime, kukan farincikine ya hanata magana, ya sauketa yaje ya duba, dukansu sun nuna lines biyu red, ya dauki pack din strip din ya karanta, “Alhamdulillah” ya dinga maimaitawa har ya iso gurin fatu wacce take daria ga hawaye shabe shabe a fuskarta yace “its true fateema, kinada ciki, Masha Allah, Alhamdulillah” Gaba dayansu sun kasa controlling farincikin da suka tsinci kansu ciki. (Shekara uku ba wasa ba, d’a kuma da dadi, Allah ka bawa wanda basuda shi Ameen) A bakin gado suka zauna kowa da murmushi a fuskarsa tace “jannah har yanzu na kasa gaskatawa, gani nake kamar mafarki nakeyi” yace “ba mafarki kikeyi ba, yau Allah ya nufe mu da samun abunda muka dade muna addu’an samu” sultan ya kira jameel a cikin daren ya fada mishi, fatu tana hanashi akan ya bari sai gobe amma yaqi don d’oki, har zai kira mammi ma fatu tayita roqonsa sannan ya bari, bude cikin yayi yana ta shafawa can kuma sai ya daura kansa wai zaiji heart beat din babynshi, da kyar ranar sukayi bacci don fatu gani takeyi ma sultan ya fita farincikin samun cikin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button