FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Fateey????????????
[10:39PM, 9/26/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
7⃣6⃣
Washe gari qarfe 10 suna gidan mammi wai daga nan zasu wuce hospital don fara anti natal, a palour suka samu amrah tana breakfast, da murnanta ta gaishesu, sultan yace “ina mammi? Tace “tana dakinta” yace “dear mu shiga” fatu ta noqe kafada tace “a’a nikam ina jin kunya” murmushi yayi ya shiga dakin mammi, bai jima ba suka fito tare da mammi, fuskarta annuri kamar wacce akayiwa bushara, fatu tayi sauri sauqowa daga kan kujera zata gaisheta, dagota mammi tayi ta zaunar da ita a kujeran tace “a’a fateema, ki daina aikin wahala, Allah ya miki albarka ‘yan nan yasa ki sauka lafiya” amrah tace “mammi tafiya zatayi? Mammi tace “amrah abun farinciki ne ya samemu, fateema zata kawo mana d’a” amrah tayo gurin fatu da gudu zata rungumeta mammi tace “ke amrah me haka? Zaki bugeta ai, bana son irin haka” sultan da yake gefe yana kallon show din a ranshi yace ‘an gamu da mammi yanzu kam’ a fili kuma yace “fateema tashi mu tafi asibityn. Mammi tace “A’a ka barta ta huta, zuwa anjima zan kaita da kaina, tukunna ma wani asibity? Wani asibity ne suka fi bada kulawa? Da kyar sultan ya bari mammi ta hakura yakai fatu don yasan fatun bazata sake tare da mammin ba. Private hospital mai kyau ya kaita, doc ya mata tambayoyi ta bashi amsa yace za’a mata scanning. A gurin scanning dinne likitan ya kasa gane ‘ya’ya nawa ne a cikinta, don clearly biyu ya gani amma ta gefensu yaga wani kaman babyn, yace “a bisa scanning da mukayi cikinta wata uku ne da sati daya da kwana 3, kuma ‘yan biyu ne a cikin nata amma zata fara zuwa anti natal daga jibi thats kowanne wednesday don duba lafiyanta da abunda ke cikinta” sultan da fatu da suka kasa magana don tsananin mamaki don basu tsammaci cewa zasu sami ‘yan biyu ba. Suna komawa gida aka fadawa mammi Again murna tayi kamar me, anan ta kira mummy ta sanar mata, ko minti biyar ba’a qara ba mummy ta shigo tana barka barka. Dangi aka kira ana fada musu fatu har abun ya fara bata kunya kamar a kanta aka fara haihuwa.
*4months 2weeks later*
2:12am na dare, sultan ne zaune ya qurawa fatu wacce ke kan gado ido da goran faro babba cike da madaran shanu a hannunshi yana dan jijjigawa don saboda ya dan huce, a hankali fatu take motsawa, idonta ta bude ta shafo rusheshen cikinta wanda girmanshi har abun kallo ne. Da sauri sultan ya isa gurinta ya taimaka mata ta zauna, ruwa ya fara bata ta kukure bakinta ta zuba a wani container da ya kawo daidai bakinta, straw ya saka a cikin goran kana ya bata tana zuqa a hankali har ta shanye tass,???? nace kaii!!! Ta dago ido ta kalleshi ya mata murmushi tace “nagode” yace “nine da godia, don yarana suna wahalar min dake, ga ci kamar me” daria tayi tace “lafiya kenan” sai daya tabbatar tayi 30 mins sannan ya gyara mata kwanciya yace “kiyi bacci” shafa gashin kanta ya fara tana lumshe ido ko minti biyu bata qara ba kuwa ta soma bacci. A hankali ya tashi ya koma dayan side din yana tunano irin wahalan da suke sha aka cikin nan, fatansu dai Allah ya sauqeta lafiya……. tun daga ranar da suka fara zuwa anti natal ake mata scanning koyaushe ana cewa ‘yan biyu, da cikinta ya cika wata shida aka turasu wani hospital a mata scanning don doc din da yake dubata he’s confused yana ganin kamar babies uku ne, thats why ya tura su wani asibitin. A can da aka mata cewa sukayi ‘yan uku ne kuma kosassu lafiyansu kalau, wani abun mamaki shine fatu batayi laulayi ba sai na ciye ciye, abinci kam tana ganin damarsa, kuma bata jimawa zata nemi wani. Da mammi taji haka tace to scanning din ya isa, Allah shi yasan komai. Fatu bata wasa da maganin da ake rubuta mata a wurin awo, sam bata skipping, sultan har tausaya mata yakeyi in yaga ta ajiye abinci a gabanta tana ci, watarana haka zata bude mishi tumbin yana ganin yanda babies din suke naushinta har abun mamaki. Da cikin ya cika wata 7 kuwa tashin dare ta fara wai yunwa takeji, haka zai tashi ya hada mata tea tasha amma baza’a jima ba zata qara tashi tace Yunwa, ana haka rannan kaka ya ziyarceta ya kawo mata maganin shawara da ake bawa masu ciki, anan ya kawo musu madaran shanu mai yawa a gallon jarka, a ranar da dare fatu ta tashi tace a bata madaran, sultan ya kawo mata, da yake an saka shi a fridge yayi sanyi tace a dumama mata, dolenshi ya sauka ya duma mata ya juye a gora ya bata, to a ranar bata qara tashi neman abinci ba, daga ranar yake aika mata nonon shanun daga kumo. Marking din lokacin tashinta yayi, kafin ta tashi zaije ya dumama ya dawo ya zauna yana jiranta har ta farka ya bata tasha. Mammi tayi tayi ya dawo da fatu gida amma sai yayita mata kwana-kwana. Yau dai EDD din fatu saura kwana 8, yayi niyyar maida ita gida gobe don kar abu ya tashi baya gida. Dauke wutan da akayi ne yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi, da sauri ya dauki handa fan ya fara mata fifita don bata son zafi ko kadan, ba’a yi minti 3 ba maigadi ya kunna generator, anan sultan ya ajiye handfan din ya shige toilet ya dauro alwala, ya gyara mata pillow yayi kissing goshinta kana ya fara nafilfili Allah ya sauqeta lafiya.
Maman Fateey????????
[7:39PM, 9/29/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
7⃣7⃣
Washe gari da safe Tana zaune akan gado tana shan Apple shikuma yana hada mata kayanta da zata buqata. Kallonshi takeyi cike da tausayi don ba qaramin qoqari yake yiba, tunda cikinta ya girma ya hanata girki duk da ma sunada mai wanke wanke da shara, Haka kuma koda zai bukaceta ya dinga tambayarta kenan cewa “bazan takuraki ba? A’a “are u in d mood? Da ire irensu, tana mugun respecting dinshi akan hakan. Sultan mutum ne wanda take alfaharin samun shi a matsayin miji, yana tausaya mata kuma bashida saurin fushi. Gashi baya gajiya da mata hidima, takanas ya fita waje ya musu siyayyan haihuwa wanda kwanan shi uku ya dawo wai tunaninta ya hanashi zama. Laluma plate apple dinta takeyi taji wayam, wato har ta shanye apples 8, dai dai nan ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace “a yanko miki wani ne? Ta girgiza kai tace “a’a, na koshi” yace “to ki tashi in miki wanka mu tafi” tace “to” A hankali ta miqe yayinda shi kuma ya dauko mata towel ya tayata cire kaya yana daura mata towel din. Tace “jannah” ya dago ido yace “maman uku yadai? Murmushi tayi tace “thank u” bai ce komai ba ya jata zuwa bathroom. Don ya saba da irin hakan, koyaushe tana cikin nuna jindadin ta ga yanda yake nuna mata kulawa, hakan shi kuma kan qara masa qwarin guiwa wajen kyautata mata. Wanka sukayi amma fatu na lura da sultan akwai abunda yake damunshi. Bayan sun fito ne take tambayarshi lafiya yace ba komai. Bata fuska tayi tace “ka fada min don Allah” zaunar da ita yayi a bakin gado yace “can u help me? Anan ta gano bakin zaren, don yau kusan 3wiks rabon daya nemeta wanda tasan duk a dalilin tausaya mata da yakeyi ne, lallai tana da sonkai, tasan yanayinshi ba mai juriya bane amma ta mance dashi tana enjoying sangartata da yakeyi. Murmushi tayi tace “I am sorry jannah, nayi sonkai da yawa….” bata qarasa magana ba taji an rufe mata baki da lips nasa……..