HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da yaji he’s okey ya tashi ya shiga bandaki. Bayan ya fito ya kwaye bargon data lulluba dashi yace “taso kinji, sorry dear” da kyar ta miqe don wani irin ciwo da bayanta ya fara tun dazun. Zai bita bathroom din tace “ba komai zan iya” ganin yanda take cize baki tana riqe da bayanta yace “ko dai nayi hurting dinki ne? Tace “a’a” tare da shigewa bandakin. Da kyar ta samu tayi wanka don irin ciwon da mararta kuma ya fara. Tana fitowa ta samu ya gama shiri har yasa kaya ya ganta wani iri yace “na sani na ji miki ciwo, I am so sorry, ya Allah” ya dafe goshi, tausayinshi taji don haka tadan fuske duk da irin ciwon da takeji tace “kadan ne fa, kuma ya fara tafiya ma” bai saurareta ba don yanda yaga take hada gumi yasan tana jin jiki,  daguwar riga ya zura mata yace “mu tafi hospital” Magiya ta fara mishi wai ita bazata je hospital kar suce haihuwa ne, tana tsoron haihuwa balle ita da aka ce yan uku ne. Kafin ma su isa asibiti abu ya qara jiqa, don yarfe hannu takeyi tana dafe mararta. A gaggauce nurses suka karbeta aka shiga da ita labour room, doctor da take dubata ya kira a waya ya fada mata ya kawo fatu asibity, ko minti biyar bata yi ba ta iso bakin labour room din don dama tana cikin asibitin. Safa da marwa ta samu sultan yakeyi yana kiran sunan Allah sai kace shine mai labourn. Da dan murmushi ta gaisheshi ko amsawa bai yiba yace ” ki shiga ki dubata, inaga ba haihuwa bane doctor, coz nine na jawo” da dan mamaki a fuskarta tace “kamar ya? Kamar bazai fada mata amma yaga no need da boye boye shi dai fatanshi a Magance halinda fatu take ciki don haka yace “I…I have.. I have se* with her” doc tace “ba matsala ai hakan, kar ka damu” da hanzarinta ta shiga labour room din yayinda sultan ya cigaba da safa da marwa, anan ya kira mammi ya shaida mata suna asibiti. Minti goma doc ta fito tace “haihuwa ce coz har ta kai 5cm” cikin rashin fahimta yace “me 5cm?  yanzu haihuwa zatayi? Zan iya shiga? Ganin yanda ya rude yasa doc din ta fara kwantar masa da hankali, sai anan ya tuno cewa ai EDD dinta bai cika ba, yace “doc edd dinta next week ne” tace “wasu suna rage kwanaki wasu kuma suna qarawa. So yau Allah yayi zata haihu” Anan mammi ta shigo itama daka ganta zaka san hankalinta a tashe yake.

 

Maman Fateey????????

[12:56PM, 10/1/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

7⃣8⃣

 

Gaishe da mammi yayi ta amsa tace “ba dai tun jiya abun ya fara mata ba? Yace “a’a yau da safe har mun shirya zan kawota gida” harara mammi ta watsa masa kana ta dubi doc din ta bata wani ruwa bottle din Faro tace “ga wannan ruwan addu’a ne a bata tasha” da sauri sultan ya karba yace “doc zan iya shiga? Tace “ehh zaka iya” mammi da mamaki ya gama rufeta tace “ya zaka shiga gurin haihuwa? Kafin ma ta qarisa sun qule shida doc. A kan gado suka samu fatu tana jijjiga kai tana yarfe hannu, ganin sultan ba qaramin qwarin guiwa tajiba, ya isa gurinta ya kamo hannunta yace “INA TARE DA KE, ki dinga addu’a kinji? So sorry dear” Gyada mishi kai tayi cikin baqar wahalan da take ji, ruwan ya bata, ta girgiza kai yace “na addu’a ne mammi ta kawo miki,  kisha kinji? Jin ance na addu’a ne ta karba tare da bismillah ta shanye. Shiru shiru kusan 20mins.

Ganin fatu har ta fara nishi nishi doc tace a gwada mata cm nawa take. Daya daga cikin nurse dinne tazo gwada fatu sultan ya tareta yace “what are you doing? Me haka? Da kyar doc ta fahimtar dashi sannan ya yadda. Fatu ko ta kansu bata bi. Nurse din tana gwadawa ta fadawa doc, tace “ina kayan haihuwa? Don mun muku list din abunda muke buqata” sultan yace “yana mota” da sauri yaje ya dauko ya kawo mammi na kallonshi yazo ya qara shigewa. 30mins da haka ta haiho babies dinta hudu duk maza, fatu ta wahala sosai. Murna gurinsu ba’a cewa komai. Su da akace musu uku sai ga hudu. Mammi kam ta rasa inda zata sa kanta don murna, dukansu sai hamdala sukeyi tayi (wani jinkirin ma Alkhairi ne) Awa hudu da haka aka sallamesu bayan an tabbatar da lafiyan maijego da babies. Kafin suna ‘yan uwa da abokan arziki sunzo barka. Yara tubarkalla kyawawa dasu tula tula, kama sukeyi da babansu sosai. A ranar suna suka ci sunan Abu-bakr, Aliyu, Usman da Umar. Anyi shagalin suna na gani na fada, mai jego da babies sunyi kyau cikin shiga ta alfarma. Mutanen garin modibbo suma sunzo suna.

 

Maman Fateey????????

[11:09AM, 10/2/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

7⃣9⃣

 

Su xahra amarya, bizzy mai ciki, (suma sunyi aure) lubna da salma qawayen mai jego sun entertaining baqi sam barka,’YAN MUMBARI tare da MUM FATEEY FANS suma sun halarci wannan bikin suna. Da yamma akayi walima inda Malama Asma’u (maman Al’ameen) ta gabatar da wa’azi kan tarbiyatan da yara bisa yanda addinin musulunci ya tanadar. An ci, ansha anyi guzuri, su Mrs umar, Autar hajia, ummi Aisha, Jabo, da jegal sunfi kowa kwasar abun suna. An raba soveniers kamar ba gobe, taro yayi ansha pictures kala-kala.

 

*11 years later*

 

Fatu na gani da dan jaririn cikinta wanda bazai wuce 5 months ba, a kan cinyanta plate ne cike da gyada dafaffe tana barewa tana ci. Gefenta kadan sultan ne shima zaune suna kallon wani indian film mai suna “SULTAN” inda SALMAN KHAN ya fito a wrestler. Da alama dukansu hankalinsu ya tafi ga kallon don fatu ko kallon gyadar batayi take barewa tana turawa a baki. Sai ta bare goma tasa a baki, kana ta baro daya ta bawa sultan. Gama film din yayi daidai da Qarewan gyadan fatu ta laluma taji wayam sai bawon gyada kawai. Sultan ya juyo yace “film dinnan ya hadu….” ganin plate ba komai yasa ya waro ido yace “ba dai kin cinye ba? Ta turo baki tace “mun cinye dai” ya lalumi bakinshi da harshen shi yace “kin cinye dai, don nikam banji alaman gyada a bakina ba, matar nan zanyi maganinki, daga yau na siyo abu sai na ci nawa a hanya before na kawo Gida, ko samarin gidan nan baki ragewa ba” daria tayi sosai tace “in kana kiransu samari abun har daria yake bani” tashi yayi ya nufi door inda ake bugawa yace “naga haka kike kiran waleedah (mai sunan mammi, shekaranta 8, mammi ta dauketa tun da amrah tayi aure) fatu tace “waye ne? murmushi yayi yace “inaga sun dawo” a hankali ya bude ya leqa, wasu kyawawan yara yan kimanin 11yrs su hudu na gani bayansu karamar yarinya da bazata wuce 4yrs ba tana matsar  kwalla, sultan yace “kun dauko ta ko? Tare da basu hanya suka wuce, daukan ta yayi ya saba a kafada yace “Ameera munyi missin dinki” ta turo baki Abu-bakr yace “bata jin magana sam, boarding school zamu kaita, da kyar muka banbareta a jikin Al’ameen din aunty salma shima yaje gidan granny” fatu ta tashi tace “wa za’a kai boarding school? Katti daku ba’a kaiku ba sai yar yarinyar nan? To akul dinku naji kun takurata mata, yarinya yar qarama da ita kunbi kun sa mata ido…..” karban ‘yar tayi taja hannunta suka shige daki tana fadanta. Sultan dai baice komai ba ya samu guri a kan kujeran ya zauna kana ya dubi zaratan samarinsa wanda inka gansu zaka dauka sun kai 13 ko 14, Aliyu wanda duk cikinsu yafi zafi yace “mommah tana sangarta Ameera” Usman yayi murmushi yace “mai sunan mamanta ne ai” zama sukayi dukansu a kan kujera sultan yana binsu da ido cikin tsantsar qauna yace “ba sangartata take yi ba, shekarunta 4 ne, wanda komai a yanzu cikin lallami da wayo za’a nuna mata ba by force ba, kuma haka mommah dinku ta raine ku har  girman ku. And gashi kun tashi a nitse da ilimi both Arabi da boko. Sons I am proud of your mom and i trust yanda take tarbiyantar da yara” Jinjina kai sukayi cikin amincewa anan suka fara maida zance. Gurin driver taje tace ya kaita gidan granny inji momma, shi kuma without bincike ya dauketa ya kaita. Dawowanshi yayi dai dai da dawowan sultan yake tambayrsa inda yaje, driver ya fada mishi, anan sultan ya mishi warning kar a qara daukanta in ba babba yayi magana ba. Shiganshi gida yasamu samarinshi suna taya mamansu hira, ya fada musu suka tafi dauko ta don washegari monday akwai skul. Shine suma suka yi zamansu sai yanzu suka dawo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button