HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Taku a kullum

 

Maman fa’iz????????

[9:27AM, 5/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

0⃣8⃣

 

Sallama sukayi ya amsa, kana ya dubi yaran da sukayi dandazo suna kallon samarin yace su tafi wasan su, kan kace me kowa ya watse don basu da rashin kunya. daya daga cikin samarin  yace

“Don Allah baba nan ne gidan mallam mahmudu? Duk’ar da kai kaka yayi sannan yace “ehh” still wanda yayi tambaya na farkon yace “gurinshi muka zo shi da matarshi, daga gombe muke” kaka yayi dan jimm sannan yace “Allah ya musu rasuwa dukansu” “sun rasu” saurayi na biyu ya fada cikin firgici, sannan ya nemi guri ya tsuguna yana “innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya jikanku”.

Saurayi na farkon ya dubi kaka da tarin damuwa a fuskarsa yace “Allah ya jikansu yasa sun huta” “Amin Amin” kaka ya furta yana goge hawayen da ya zubo mishi ba shiri. Saurayi na tsugunne yace “jameel mu tafi” ya miqe jikinshi a sanyaye ya nufi mota. Kaka ne yace “zaku tafi baku sanar dani alakar ku ba” jameel yace “wancan abokina nane, sunanshi sultan, matar mallam mamudu wato aunty rahmatu qanwar mamanshi ce, uwarsu daya. “Allahu Akbar Alhamdulillah” kaka ya fada cikin tsananin mamaki don baiyi tsammanin za’a ga dangin mahaifiyar rahmatu ba cikin ruwan sanyi haka. “ai akwai rabo tsakaninsu sun sami ‘ya mace fatu, tana nan, ni mahaifin mahmudu ne” farinciki ne kwance a fuskar kaka yana murmushi. Jameel ne ya kwalawa sultan kira ya fito daga mota still jikinshi a sanyaye, jameel yace “akwai cousin dinka fatu, ‘yar aunty rahmatun ce” cikin doki yace “ina take? Yana kallon zauren gidan. Kaka yace “tana ciki, amma in bazaku damu ba ina son magana daku.

Tabarma kaka ya shimfida musu a zaure suka zauna, shiga gida yayi ya sameni  tsakar gida ina karanta wani  littafi, yace “uwargida ki samin ruwa a kofi nayi baki” nace “to”. Miqa mishi kofin nayi ya karba ya wuce cikin zauren. Bayan sun qara gaisawa ne kaka ya fara basu labarin mamata har zuwa kaina, bai rage komai ba harda wahalan da nake sha gurin asabe idan taga kaka baya nan. Kaka ya qarasa magananshi da cewa “idan baza ka damu ba kai sultanu ka auri qanwarka zata fi jin dadi cikin ku, nasan dana fadi na mutu fatu bata da gata sai Allah, don wadannan ba riqeta da gaskia zasuyi ba” kaka ya cigaba da maganarsa duk akan sultan ya aureni ya taimaka min. Kan sultan ne yadau zafi yayi dana sanin nemo su, gaskia bazata sabu ba. Shiru yayi kansa a qasa ko motsi mai kyau bayayi, ya bude baki zaiyi magana kenan Jameel yayi caraf yace “hakan yayi kyau, Allah ya tabbatar da alheri” Amin. Kallon mamaki sultan yake bin jameel dashi don ya wargaza mishi plan, wata dabara ce tazo mishi in akayi sa’a zai fita.

Yace “mallam zamu koma gida sai daga baya inshaAllah magabata su zo. Kaka yace “mutum bai san ranar mutuwanshi ba, watakila bazan kai zuwa gobe ba har zuwa lokacin da zaka turo magabatanka, kamar yadda na fada maka nine ke riqe da fatu, ayau nabar dunia zasu iya aura mata wanda ransu yake so, inda zata cigaba da shan wahala. Nafi aminta dakai shiyasa nake so ayau a daura muku aure, “Shikenan” abunda sultan ya iya fadi kenan don tsohon ya cika kwarjini bazai iya mishi musu ba.

 

An daura aurena da sultan a masallaci bayan an idar da sallah. Inda kaka ya zame min waliyyi liman kuma waliyyin sultan. (Tarihi ya maimaita kansa). Gida suka dawo inda kaka yace ya tafi dani, amma sultan yace zai tafi wani course na wata biyu inya dawo zaizo ya daukeni, kaka bai kawo komai ransa ba ya yarda. Shiga cikin gida yayi ya barsu a zaure inda ya aika in kai musu abinci don ranar ni nayi girki. Har lokacin banida labari don kawu muntari yayi tafiya, asabe kuma taje ganin gida. ‘yayansu kuma ba zuwa masallaci suke ba. Na fita na kai musu, durkusawa har kasa nayi na gaishesu mutum daya ne ya amsa yana min murmushi, amma dayan ko dago kai baiyi ba. Mai murmushin yace “me sunanki” nace “fatu” yace “masha Allah abokina yayi sa’ar mata” fita nayi ina mamakin maganarsa, to a ina hafizu ya sami abokai yan birni haka.

Shiga na keda wuya kaka ya kirani dakinsa, da farko nasiha ya fara min kan ya bani labarin abunda ya faru. Babu abinda na iyacewa illah hawaye da ya dinga bin fuskata, na rasa hawayen menene, ta wani gurin ina farincikin samun dangin mamata, while ta wani gurin ina tausayawa kaina don wanda aka aura min ko kallona bai yi ba. Na dade a dakin kaka sanna ya fita dubo bakinshi ko sun gama cin abinci. Ya fita ya samu jameel yaci amma sultan ko ruwa bai sha ba, jameel ne yake cewa wai sultan din azumi yakeyi.

Kaka ya musu iso cikin gida aka shimfida musu tabarma ta bayan dakunan mu gurin akwai bishiiya gefenta kuma rumbun ajiye abinci ne. Kaka ya wuce yana cewa bari ya kira fatun. Gefen su kadan na zauna akan wani dutse na sunkuyar dakai ina wasa da yatsuna. Mijin nawa dai har yanzu kansa na kasa bazaka game yanayin da yake ciki ba. Jameel ne ya fara magana.

[9:28AM, 5/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

 

0⃣9⃣

 

Jameel ne ya fara magana “Amaryanmu kina lafiya” nace “lafiya kalau” ya kara cewa “sai kika ji an daura aure babu wani taro babu al’adu irinsu zance, bayarwa, kayan aure da sauransu. “Uhmm” na iya cewa. “Komai da kika gani muqaddari ne daga Allah, wannan aure naku insha Allah baza kuyi dana sani ba. Ya cigaba da maganan shi inda yake nuna mana mu riqe junan mu cikin amana duk da ba auren soyayya bane, ya karasa magananshi cikin nasiha. Duk abunda yake cewa sultan bai ce uffan ba, don wayarsa ya dauka yana dannawa. Mikewa yayi sannan yace “bari in barku kuyi magana, kar in takuraku da yawa” ya fada cikin tsokana. Mun fi minti biyar b wanda yayi magana can yace “kinyi makaranta? Nace “ehh” “ina kika tsaya” “secondry” yace “shekarunki nawa? Nace “17” sai lokacin ya dago kai ya kalleni 4 d first time nayi saurin sunkuyar da kaina. Can ya kara cewa “kin taba shiga birni” nace “Aa’aa” yace cikin bata rai “kin min yarinta da yawa, kuma karatunki baiyi zurfi ba, bana jin zan iya rayuwa da irinki” dai dai nan jameel ya dawo yace “times up, kar muyi yamma a hanya” hope kun daidata? Ya fada yana murmushi. Babu wanda ya kula shi don ni ina kokarin mayar da hawayen da yake son zubo min ne, jameel ne yace in matso kusa da sultan zai daukemu hoto. Shiru nayi sai da ya kara maimaitawa na taso na tsaya nesa dashi, turo sultan yayi gurina wanda yake aika masa harara ta ko’ina, baya yayi yace mu dago fuskokin mu, still kowa kansa na qasa, yace to bari in kira kaka, may be zaku fi jin  magiyarsa. Saurin dago da kanmu mukayi yace “smile” sannan ya daukemu a hoto. Abun mamaki yana daukan hoton wani abu ya fito daga cikin camera, ya kara daukan mu abun ya qara fitowa. Miqa min na farkon yayi na karba ban duba ba. Sultan har ya fita waje, ciro kati yayi daga aljihunshi ya bani, yace “wannan shine address na gidansu sultan, abokina yana da wuyar sha’ani amma in kika yi hakuri komai zaiyi karshe, ki ajiye address din don bamusan gaba me zata haifar ba” ya karashe maganarsa cikin tausayawa. Nace “Nagode Allah ya kiyaye hanya” shima fitan yayi inda ya iske kaka da sultan suna hira kamar bashi ne yake bata rai dazu ba. Tafiya sukayi kaka ya shigo cikin gida yana mai farincikin fatu tayi sa’ar miji. Ni kuma tun tafiyan jameel na nade tabarman na shige dakina ina kuka mai tsuma zuciya, daa kaka yasan wa ya aura min da bazaiyi farin ciki ba. Kiran da kaka yake min yasa nayi saurin goge fuskata na fita ina murmushi yace in sameshi a dakinsa. A dakinsa na samu guri na zauna ya miqo min kudi yace “sadakin ki ne dubu ashirin” nace ya dauka ni bana so, yace ai hakkina ne maza in karba. Na karba na wuce dakina na cigaba da kukana har bacci ya daukeni. Bugun kafa na naji anayi na tashi ya firgice goggo asabe na gani tsaye a kaina fuskar nan a tamke, tace “wani jita-jita nake ji a gari wai an daura miki aure hka ne? Nace “ehh” nan ta fara masifa ai dama dangin mu haka suke sai sunga mai kudi suke aura, ga babangida yana sona amma kaka ya hana shi. Allah yasa mijin nawa ma dan yankan kai ne, kallonta nayi ido cikin ido nace “ba kudin shi muka bi ba, sultan dan’uwana ne, mahaifiyarsa addar mamata ce” cikin mamaki tace ‘eeeyeee’ nace  “kwarai” fita tayi daga dakin tana jin bakin cikin auren, don yadda aka fada musu mijin nawa dan birni ne kuma ga kudi akace da mota irin ta sarkin Kumo yazo. Sadakina na boye don nasan ko ita ki ‘yayanta wani zai biyo dare. An koma baya don goggo asabe tana ganin kaka ya fita zata fara cin zalina, girki kuma da shara wanke wanke nice keyi da kaka yayi maganan a rage min koda daya  ne cewa tayi horar dani takeyi, gidan wani zanje don haka ya kamata in saba da aiki, kaka kuwa ya yarda da magananta.  Bayan wata da daurin aure na wani mutum yazo da envelope ya bani yace aikoshi akayi daga gombe. Na aza wasika ce amma sai naga kudi ne 30k. Kakana na kaiwa yayi godia yana cewa sultan bai mance dani ba tunda har yana kokarin sauke wasu hakkina. Bayan wata daya muna tsammaninshi sai muka ga dan aikan rannan. Yace sultan yace a fada mana zai qara yin wata uku. Kowanne karshen wata sai dan aiken yazo da envelope kudine a ciki wataran 50k watarana 30k. Koyaushe aka kawo zanyi tsammanin akwai wasiqar sultan a ciki amma babu. Har wata 3 ya wuce babu labarinsa daga nan su goggo asabe suka fara habaici “ai nasan za’a rina, hala kakaba mishi ita akayi, yoo dama me zaiyi da kucakar yarinyar nan; shi dan birni. A haka zakiyi ta zama har ki tsufe, dama kudi kuke so to ai gashi ana turo muku” idan ta fara maganganun nan nakan shiga daki inyi ta kuka ina kallon hoton da jameel ya dauke mu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button