FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

[10:09AM, 5/18/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣0⃣
Idan na gaji inyi alwala inyi sallah in kai kukana gurin Allah.
Sati daya daya wuce na cika shekara daya da aure, a cikin shekaran kuma dan aika yana kan zuwa kowanne month. Idan muka tambayeshi labarin sultan sai yace bai dawo bane. Hankalin kaka ya fara tashi ya fara dana sanin daura auren, akwai lokacin da ya kirani ya ke cemin ko zamuje kotu a raba auren? Nace mishi a’a, don nasan gwanda zamana da igiyar sultan akaina akan in zama bazawara hankalin kaka zai fi tashi. A ranar da zan cika shekara da aure muke tsammanin zuwan dan aika, a ranar na shirya plan dina don sanin matsayina. Yawanci bayan azahar dan aika yake kawo kudi, kaka na samu a kofar gida karfe 12:30 nace zan shiga jeji debo ganyen lalle, yace in aika yara mana, nace ina son zuwa da kaina ne, bai kawo komai a ransa ba ya mini izini. Already na gama shiri na fito, hanya kawai na yanka na shiga jeji inda nan ne hanyar shigowa cikin gari. Sai da na debo ganyen lallen na fito bakin hanya na tsaya a gindin bishiya ina jiran dan aika.
Nafi minti 30 na hangoshi yana tahowa kamar kullum a kan machine dinshi. Fitowa nayi ina tafiya nayi kamar ban ganshi ba, yazo dab dani na juya ya ganni ya ce ahh fatu me kikeyi anan? Yana kokarin tsayar da machine din, nace laa nazo tsinkar ganyen lalle ne yanxuma gida na nufa. Yace in hau ya isar dani, nace a’a nagode. Yace to ga aikan tunda na hadu dake a hanya, ki gaishe min da mallam Ameenu. Na karba nayi godia ya juya ya koma. Sai dana tabbatar yayi nisa sannan na bude envelope din, yau ma kamar kullum kudine babu wasiqa. Na fito da yar takarda daga cikin ledan da tun fitowana daga gida yana cikin hijabi na, hade da dan kunu a farar leda takardan na tura cikin envelope din na shapa kunu na liqe kamar ba’a budeba nayi hanyar gida ina mai farin cikin hukuncin dana yanke.
Jama’a menene fatu ta rubuta? ????????????????
Ina mai bawa masoya hakuri na rashin jina kwana biyu, phone dina ne ya samu matsala.
Luv u ol
Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[1:33PM, 5/19/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣1⃣
Dawowa na gida na iske kaka na yana masallaci, don haka kai tsaye dakina na fada na ajiye kayan na fito nayi alwala nayi sallah. Ina idar wa naji kakana ya dawo, goggo asabe ta kirani in kai mishi abinci, naje na karba, har zan juya ta kirani na jiyo, “amm fatu yau ba’a kawo miki saqo bane, wallahi rance nake so ki bani na dubu uku, masifaffiyar goggon kin nan innani na ara a gurinta, don tsiya jiya har da aiko sadiqa tayi tamin rashin mutunci” nan ta fara matsar kwalla, kar ki manta hajia duk randa aka aiko kudi rabashi akeyi duk abunda aka bani ita ke amshe wa da wayo, wani tace zata biya bashi wani kuma tace zata karbo min maganin bakin mutane, Wani kashin na abincin gida, don wani abincin da muke ci ba’a cinsa a gidan maigari, kinga kamar taliya da dan waken fulawa, wallahi wataran harda macaro muke ci (inji jawaheer????????). Hajia tace “Macaroni kike nufi? Fatu tace “ehh, sauran a ajiye saboda bukatun yau da kullum. Nace “an kawo in kaka ya bani zan kawo miki” na fita a zuciyana ina cewa anji kanku. Dakina na fara bi na dauko envelope din na wuce dakin kaka. A daki na iske shi yana kishingide, na masa sallama ya amsa, ajiye abincin na miqa mishi saqon nace a hanya na hadu dashi ya bani. Ya karba jikinshi a sanyaye yace zai kirani anjima. Ina fita naga goggo asabe a kofar dakinta tana jirana, sai da na isa tace ina kudin? Nace ” sai yaci abinci sannan zai bani. Shiga dakinta tayi bata kulani ba ni kuma nayi shigewata daki ina jiran kiran kaka don karanta wasiqa. Bayan Minti sha biyar lamido dan goggo asabe ya zo ya kirani hijabi nasa na fita. Shiga nayi na samu guri na zauna nace “kaka gani” yace “takarda na gani a cikin kudin Allah yasa ba abunda nake zato bane, ya fada yana mai girgixa kai cikin damuwa. Nace “ba komai kaka Allah ya zaba mana mafi alkairi. Yace “ameen” hade da mikomin paper. “Hajia kinsan abunda na rubuta? Hajia tace “a’aa” fatu tacigaba “rubuta ban hakuri nayi na jimawan da sultan yayi bai zo ba, hakan ya samu asali ne ga riqeshin da akayi a kasar wajen, kuma kaka ya bari inzo gombe gidansu yana so yayi wa mamarsa suprise”
[10:17PM, 5/19/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣2⃣
Tunda na fara kaka murmushi yakeyi cikin jindadi, har bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba, na share ba tareda ya gani ba. Sai dana gama yace ” fatu Allah ya amsa addu’a na, kullum burina mijinki yazo ya dauke ki, ayau Allah ya nuna min ranar” kwalla taff a idon kaka na farinciki. Hajia nayi dana sanin rubuta wannan wasiqar don bawai inason zuwa gurin sultan don ya karbe ni a matsayin matarsa bane, a’a don ya sauwaqe min ne nima in samu dai dai ni in aura. Kuma hakan zaisa kaka ya samu kwanciyar hankali. To amma tsananin farincikin dana hango shimfide fuskarsa sai tausayinsa ya kamani, ban kyauta masa ba. Kaka yace in shirya gobe in tafi. Kuka na fara Nace a’a sai shi sultan din yazo, zanyi ta zama da igiyarsa a kaina har ranar da Allah ya kawo shi. Ban taba yiwa kaka musu ba sai ranar. Bai ce min komai ba har na tashi na tafi dakina na cigaba da kukana, ina tausayin kaina da kaka. Da kawu muntari ya dawo aka fada masa abunda mijina ya rubuta shima ya bada goyon baya in tafi, goggo asabe kuwa hankalinta ne ya tashi don bata son taga abu mai kyau ya rabe ni. Ana gobe zan taho na fara shirin tafiya gombe don inje ayita ta qare, na kasance koyaushe ina tunani da addu’ar Allah yasa zuwana ya kasance alkhairi. Hajia har abinci nake kasa ci, ace an daura mini aure yau shekara amma mijin bai ko waiwayeni ba. Abunda kaka ya fada min ne ya girgiza ni, wai da kawu muntari zanyi tafiyan!!! Tirkashi????????
Nace masa ai a wasiqar sultan yace inzo ni daya, na nuna masa tunda nayi karatun boko ai bazan bata ba koda a kano ne????, Kaka ya amince. Da dare kasa cin abinci nayi don ina da tabbacin in naje sultan zai sake ni kamar yadda zan bukata. Da kyar kaka yasa na sha fura da daddare a dakinsa, mun kusan kai karfe goma yana min nasiha gameda inda zan koma wato gidan mijina, jinshi kawai nake yi ina mai tausaya mana.
Tun da asuba na gama shiri kaka yana dawowa daga masallaci naje na gaishe shi, ya miqo min 15k wai in riqe zai min amfani a can din. 5 din saman na dauka nace zai ishe ni, ya qara min nasiha ya bani addu’o’I. A lokacin gari ya fara haske, machine din abokin baba ne mukaji yana diri a kofar gida. Har daki na sami goggo asabe na Mata sallama, duk ‘yan gida aka fito domin ganin tafiyana. Ban dauki komai ba sai ‘yar jakana na skull da kudin sadakina 20k sai kayana kala 3 don nasan ba jimawa zanyi ba. Kudin kuma bashi kayanshi zanyi. Na haye machine din ina hawaye haka muka kama hanya suna daga min hannu. 6:22 muka iso kumo, direct tasha muka isa ya sakani a motar gombe, shi ya biyamin kudin motan ma, yayi tafiyarsa don anan kumon yake aiki. Bakwai saura motar mu ta tashi mune bamu shigo garin gombe ba sai 7:30. Anan na sauka na sayi abinci, fitowana kuwa tsautsayi ya afka dani. Wannan shine takaitaccen tarihina.