HAUSA NOVEL

FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

Shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa a ransa, farouq ne ya dawo yana mummy oyoyo, hajia ta shafa kanshi tace “Ka dawo” yace “ehh, yauwa mummy kika ce dama baza ta tafi ba, to yanzu in mata questions din? Hajia tace “gata a gabanka ai” zuwa gurin fatu yayi yace “dama tambaya daya ya rage, ina ne gidanku? Kai tsaye fatu tace “a kauyen kumo, ka taba zuwa kumo? Yace “aa’aa” tace “kana kama min da wani sunan shi jameel” yayi caraf yace ” ya jameel yayi aure rannan ya tafi da matarsa south africa wai yana aiki, amma naji dady na cewa ya kusa dawowa” kafin ya qara bude baki hajia ta katse shi tace “aje a canja kaya ayi shirin zuwa sallah magrib” ba musu ya haura sama da gudu. Hajia ta juyo ta kalli fatu da kanta na qasa tace ” jameel dana ne yana da kanne 4, mahmud ne mai binsa sai khadija da Aisha da autana umar farouq. Mahmud yana karatu a cyprus lawyer ne, insha Allah nan da 4 months zai kammala ya dawo gida. Khadija da Aisha sunyi aure inda khadija ke Abuja Aisha ke kano. Jameel abokin sultan ne tun suna yara, daa ba’a unguwan nan muke ba, muna jeka da fari ne, Allah cikin ikonsa ya budawa mahaifansu inda suka sayi fili anan GRA, In kin lura yanayin ginin gidajen iri daya ne amma kowanne da design dinshi. Skul daya sukayi tun daga primary har sec, inda a university kowa da zabinsa, don sultan fita waje yayi ya karanci Business ad, while jameel yana gwags karantan likita. Alhamdulillah sun kammala with flying colors. 8months da suka wuce jameel yayi aure ya tafi da matarsa south africa akan karatunsa. Mahaifiyar sultan qawatace sosai, hakama dads dinsu suke abokai.

Kiran sallah da aka fara ya tsayar da hajia, sai da aka idar tacewa fatu ta isa daki tayi sallah, ita kuma hajia ta nufi kitchen don duba me aka girka.

 

 

Nima na fita daga gidan don inje in daura nawa sanwar kar oga ya dawo babu abinci, kunsan bature yace “Hungry man is an Angry man”????????????????????????????????????????

Taku a kullum

Maman Fa’iz????????

[12:32PM, 5/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣3⃣

Sun idar da sallah suka ci abinci, dija mai aiki ta tattare gurin fatu ta taya ta suka kai kitchen ta fito palour, farouq sai zuba surutu yakeyi fatu tana biye mishi har aka kira sallan isha ya tafi mosque suma suka tashi don yin sallah. Bayan sun idar da sallah ne suka dawo palour hajia ke tambayar fatu “sultan din bai baku number wayarshi ba? Fatu tace “hajia ai address din ma ya jameel ne ya bani bashi ba” kuma ni ban taba yin waya bama, to da waye zanyi? Ta karasa tana daria. “Babangida da kawu muntari ne kadai masu waya a gidanmu sai goggo asabe da ta taba siya tayi wata hudu ba’a kirata ba shine ta sayar????????. Murmushi hajia tayi tace “to yanxu fatu ya za’ayi ki tunkari sultan har kice ya sauwaqe miki? Fatu tayi dan jimm sannan tace “hajia tunda innar tawa qawarki ce sai ki fada mata ita tayi mishi magana” hajia tace “ke bakya dokin ganin innar taki ce”? Fatu tace “hajia inaga abunda sultan ya mini itama shi zata min, mahaifiyata suka zo nema bani ba, kinga ko baza su damu dani ba, nima kuma bazan tura kaina cikinsu ba” Haajia tace “fatu mahaifiyar sultan zata so ki sosai, don tun muna jeka da fari ta je dukku gurin mamanta wato kakarki, sunje aka ce musu ta rasu, ‘yarta rahmatu kuma tayi aure a wani gari. Hajia sadiya (maman sultan) ba yanda ba tayi su fada mata sunan garin ba amma suka ce sun manta, zuwanta na biyu bana mantawa bamu dade da dawowa nan gidan ba ta qara zuwa, wannan karon  Cewa sukayi karta qara zuwa gurinsu, don basu hada dangi da ita ba, wacce suka hadan ma sun yafe ta. Duk maganganun nan daga bakin yayan kakan ki yake fitowa, wai sunan shi mal jauro, ina mamakin yanda akayi sultan ya nemo ku”. Fatu tayi shiru tana tunanin ya auntyn ta hajia sadiya zata karbeta, taji dadin jin ance tana son su. Hajia ta cigaba da cewa “ni a nawa shawaran ki zauna anan har lokacin da kike tunanin zaki iya samunshi ki masa magana, batun hajia sadiya kuma baza ta taba yarda sultan ya sake ki ba, don haka ki zauna anan ki fara makaranta har zuwa lokacin da naga ya dace ki tunkareshi. Fatu tayi shiru tana tunanin maganan hajia, hala in taje gurinshi yanzu yace bazai saketa ba ya korata kauye, amma in ta zama ‘YAR BIRNI bazai wulakanta ta ba zai bata abunda take nema cikin salama tunda yasan tana da ilimi.

[12:43PM, 5/22/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????

????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????

Na Mrs Aslam Haidar✍

1⃣4⃣

Da wannan tunanin tace “hajia na amince in har zaki yarda ki dauke ni, wanke wanke da shara ko girki zan dinga yi? Hajia tace “ban gane ba” fatu tace “kince zan zauna anan inyi karatu to kuma banida kudi kuma ai bazan zauna hakanan ba tareda ina muku aiki ba” murmushi hajia tayi sannan tace “ni babu abunda zaki min, kudin makaranta kuma nice zan biya, dake dasu jameel duk daya na dauke ku” fatu harda hawayen farinciki tana kwararawa hajia kulsum addu’a sai da ta dakatar da ita. Fatu tace “hajia to kakana fa? Don yace in sanar dasu in na isa” hajia tace “karki damu nasan abunyi” farouq ne ya shigo da sallaman shi ya nemi guri kusa da fatu ya zauna hajia tace ” farouq a ina ka zauna tun tafiyanka sallah isha? Yanzu gashi har 8:42″ yace “mummy gurin baba mai gadi na tsaya, yana bani labarin sojoji ne, kinsan ina son zama soja” hajia tace “kai kam da son soja, shima mal amadu da yake biye maka kana sa shi surutu” daria sukayi dukansu, farouq yaje ya dauko home work dinshi ya kaiwa fatu wai ta tayashi. Yanda take nuna mai komai dalla dallah yasa hajia cikin mamaki, don ta english take masa bayanin wanda in bai gane ba sai ta masa da hausa, sun gama ya dauki bag dinshi ya musu sai da safe ya wuce dakinshi. Hajia ta dubi fatu wacce tafiyan farouq bai mata dadi ba, don har ta fara takura kana tace “fatu kince a kauyenku kikayi primary, to sec fa? Fatu tace ” a garin kumo nayi scndry skul dina, abokin babana ne wanda ya kawo ni tasha yake zuwa da sassafe ya kaini, in an tashi ni kuma in hau acaba ya mayar dani kauye, anan na fara tun daga jss1 har nayi waec da neco, na samu kyautuka da dama ranar speech and prize giving day din mu. After months result ya fito na samu both waec and neco, sai dai banyi jamb a shekarar ba. Bayan aure na ne nayi jamb ina tunanin in sultan ya yarda sai inyi university dina. To da yake bai zo ba sai abun ya mulmulce” hajia tace “kinci jamb dinne? Fatu tace “eeh naci, ina da 220 points” hajia tace “ahh lalle kinyi kokari, last year ne kikayi ko this year? Fatu tace “nayi last year kuma nayi this year” hajia tace “ashe bazamu sha wahalan sama miki admission ba, yanzu dare yayi muje ki kwanta ki huta, gobe in Allah ya kaimu zamu qarasa magana” kashe komai na wuta sukayi suka haura sama hajia ta kaita wani daki kusa da na farouq, daki ne madaidaici da toilet dinshi a ciki, komai na dakin pink nd white ne, gadon Mai dan girma, sai wardrobe dinshi da mirrow duka pink, can gefe kuma gurin karatu ne desk da chair white, labulayen pink nd white sai paint na dakin sky blue mai oily sai sheqi yakeyi. Sana’ar dai fatu ta sake yi wato sake baki, hajia tace “nan dakin aisha ne yanzu kuma ya dawo naki” fatu tace “hajia duka wannan, nikam ko da mai aikin ki zan dinga kwana” hajia tace “a’a anan zaki zauna na fada miki bana son kina banbanta kanki dasu farouq, duk daya kuke, ki saki jikinki tamkar nan ne gidanku, abunda nake bukata daga gareki kenan in har zan samu” fatu tayi saurin riqo hannun hajia tace “kinfi karfin bukatar abu a gurina sai dai ki bani umarni, insha Allah zaki sameni mai miki biyayya, wallahi ban taba tsammanin akwai masu kudi da son jama’a irinku ba hajia. Nagode Allah ya biyaki da Aljannah ya kuma raya miki ‘yayanki” “Ameen Ameen” hajia ta fada sannan ta mata sai da safe ta wuce dakinta, rufe kofar fatu tayi ta ajiye jakanta a gado, ta hau kan gadon tana daddannawa, can ta miqe ta shiga toilet din sai da ta gama qare masa kallo tana daria sannan ta fito ta cire hijabinta ta bude jakanta ta dauko soso da sabulu hade da brush da tootpaste ta ajiye a gefe. Cire kayanta tayi ta dauki Wani extra zani da alama na wankanta ne tasa ta shiga wanka, bata dade ba ta fito ta sane jikinta ta shafa mai, tazo daukan wani kaya ne taga wasu night wears riga da wando orange colour masu laushi akan gadon, taga kuma an saka bedsheet an lailaye gadon wahoho fatu tace “Alhamdulillah” tasa kayan ta jera kayanta kala uku a cikin wadrobe din jakan ma tasa shi a ciki wanda akwai kudinta a ciki. Ta kashe wuta ta haye kan gadon tayi addua ta rufe idonta tana tunani har bacci ya dauketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button