FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[10:15PM, 5/27/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣5⃣
Bangaren hajia kuwa wautan fatu take gani, ace miji kamar sultan kaso rabuwa dashi? Ita dai bazata bari hakan ta faru ba shiyasa take son fatun tayi karatu ta kuma waye yanda shi sultan bazai so koda kuda ya gifta tsakaninsu ba. Duk da sultan bai kyauta ba amma ba taga laifin shi sosai ba don rayuwar turai yayi, ya saba ganin mata masu class da wayewa zai so matar sa ta kasance kamar su.
Don haka hajia tayiwa kanta alkawarin kai fatu gidan sultan cikin so da kaunar junansu.
Tun asuba fatu ta tashi tayi sallah ta dan jima tana addu’o’inta sannan ta shafa. Ta kusan minti 30 a zaune tana tunanin ko ta fita ne ta taya mutanen gidan aiki ko ta zauna ne oho. A haka har gari ya fara haske Knocking kofarta taji anayi da sauri ta tashi ta bude. Hajia ta gani ta durkusa har kasa ta gaisheta, hajia ta amsa tana murmushi tace “ya kwanan baqunta” fatu tace “Alhamdulillah” hajia ta miqo mata wata doguwar riga tace “idan kinyi wanka ki saka, sai ki sauqo kasa breakfast ni zan je in shirya farouq zuwa skul” fatu ta karba tayi godia ta ajiye kan gado Sannan tayi hanyar fita daga dakin hajia tace “ina zaki je” fatu tace “zanje in shirya farouq dinne” bata jira me hajia zata ce ba ta fita ta shiga dakin farouq don kusa da nata yake, tattausan murmushi hajia tayi sannan itama ta fice zuwa dakinta. Fatu tana shiga dakin ta samu shi baccinshi ma yakeyi, a hankali da wayo ta tashe shi ya shiga wanka bayan ta hada mishi ruwan wankan. Da ya fito ta tsane mishi jikinshi ta shafa mishi mai hade da sanya mishi uniform dinshi, gurin sa neck tie ne suka kai ruwa rana, don daga ita har farouq din babu wanda ya iya. Daria yake ta mata yace “mummy ta iya, muje ta saka min” daukan skul bag dinshi tayi suka sauqo zuwa palour anan suka sami hajia tana rufe lunch box din farouq. Tace “iyee har kun gama ne?” Cikin daria farouq yake bata labarin yanda fatu ta rinqa kokawa da neck tie wai bata iya ba, hajia ta dara kadan ta kirashi tana saka masa duk fatu tana gani. Dinning hajia ta kaishi aka hada mishi tea ga hadedden indomie dinshi a gefe, cikin nitsuwa ya cinye ba tareda ya bata kayansa ba, kana ya tashi yace “mum yau ma kece zaki kaini skul” hajia tace “noo, driver zai kaika, jiya ma don yayi asubancin tafiya garinsu ne” Farouq ya hade rai hajia na lallashinshi don kar ya makara. Fatu ce ta jawo shi jikinta ta rada masa magana a kunne, duk iya gulma na banji me ta fada masa ba, kawai naga suna daria ta riqo hannunshi tace “muje in raka ka mota” hajia da ta tsaya kallonsu tace “ohh wariya za’a min kenan? Farouq yayi saurin hugging dinta tace “a’a mummy kema zan fada miki in na dawo, bye” har mota fatu ta rakashi ya shiga suna dagawa juna hannu, baba maigadi ne ya bude gate suka fita, yana kokarin rufe gate din fatu ta kalleshi da kyau.
O M G ???? mai kawo mata aika ne. Da gudu ta koma palour shi bai ma ganta ba.
Taku a kullum
Maman Fai’iz????????
[10:26AM, 5/28/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣6⃣
A guje fatu ta shigo palour, hajia dake qoqarin haurawa sama ta dakata tace “lafiya fatu? Fatu tace “mummy wallahi mal usman na gani, mai kawo min saqo din nan, yana tura gate” hajia tace “mal usman ne yake kai miki saqo dama? No wonder kowanne month yakance zaije kumo kai saqo, kuma ban taba tambayarshi ba, da yake shi dan garin kumon ne” fatu dai bata ce komai ba sai zare eyes da take yi. Hajia tace “karki damu, nasan abun yi, kije ki shirya ki sauqo muyi breakfast” fatu tace “to” kana ta miqe ta haura zuwa dakinta.
Hajia kuma hijabinta ta saka ta nufi bakin gate gurin mal usman. Yana ganinta ya taso da sauri har yana duqawa ya gaishe ta, ta amsa masa cikin fara’a kana tace “mal usman saqo da kake kaiwa kumo gurin waye kake kaiwa” mal usman yace “gurin wata yarinya da kakanta ne, shekara kenan ina kaiwa, inaga na taimako ne ko kuma yar uwarsu yallabai sultanun ne” harda abunda ba’a tambayeshi ba ya fada. Hajia ta nisa tace “Yarinyar tana nan gidana amma shi sultan bai sani ba, idan ya baka saqon next month ka kai can garin modibbon, idan kakan ya tambayeka labarin fatu kace tana nan lafiya kalau, kar ka nuna masa ba’a gidan su sultan din take ba, zaka min wannan alfarmar? Kai tsaye mal usman yace “hajia duk yanda kika ce haka za’ayi” hajia tace “nagode kuma shima sultan din kar ka nuna mishi komai” hajia ta fada sannan ta shige cikin gida. Shi kuma ya koma bakin aikinsa don ta daure masa kai, amma dai yasan duk rintsi hajia baza ta taba cutan wani ba, kuma in ba kwanan nan ba basu san cewa Iyalai biyun ba dangin juna bane.
Sake curtain din window fatu tayi bayan taga hajia ta koma palour tayi ajiyar zuciya ta fada toilet tana mai addu’an Allah yasa mal usman ya bada hadin kai.
[10:44AM, 5/28/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣7⃣
Wankanta ta tsala ta fito ta shafa mai da dan pop powder dinta na 100, sai kwallinta data sawa idonta, ta lakuti vaseline ta shafawa lips dinta. Doguwar rigan da hajia ta bata ta saka black ne mai adon sky blue a gaban rigan, kana ta dauki gyalensa shima sky blue ta yane kanta Wahoho jama’a sai yau na qarewa fatu kallo. Fara ce amma ba tass ba, tana da matsakaicin tsayi, figure 8 ce don rigan anyi shaping dinta, idanunta ba manya bane kuma ba kanana ba, tana da dogon hanci ba laifi, bakinta dan tsurut kamar bakin bottle, tana da gashin gira dai dai, fuskarta mai yawan murmushi. Itama kallon kanta ta tsaya yi a jikin mirrow tana smilling, sannan ta nufi kofa ta fita. Tun daga kan steps hajia ta ganta a ranta tace “masha Allah” don sultan yayi sa’ar mata, ga kyau ga ilimi both arabi da boko ga nutsuwa ga kuma ladabi da biyayya. Fatu ta iso ta dan duqa tace “mummy sannu da aiki” har ranta hajia taji dadin yanda fatu ta saki jikinta tana kiranta da mummy. Dinning suka nufa fatu tayi serving dinsu indomie da dankali da kwai sai tea. Suna ci suna hira duk akan yanda skul din fatu zai kasance. Bayan sun gama ne hajia tace zata yi bacci kadan kana ta haura sama. Fatu ta tattare gurin ta kai kitchen ta samu dija na wanke wanke,;ta tayata suka qarisa cikin tadi da raha, suka gyara kitchen din. Anan ne dija take tambayar fatu dangantakarta da hajia fatu tace “zan fada miki amma ba yanzu ba” dija tayi daria tace “to Allah ya kaimu ranar” fatu tace ameen ta haura sama itama ko zata runtsa.
Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[12:16PM, 5/28/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣8⃣
Shigan fatu daki ta kwanta a gado tana tunanin rayuwarta, ita kanta mamakin yanda ta sake a gidan takeyi, amma da ta tuna da yanda hajia ta karramata sai take ganin ko me hajia tace tayi zatayi in dai bai kauce shari’a ba. Duba agogo tayi 8:34, kakanta ne ya fado mata a rai, yanzu haka yana can yana kewanta, Allah sarki, hawaye ne ya fara sintiri a beautifull face dinta idonta a rufe, a haka har bacci ya dauketa.