FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

11:00 ta farka, bandaki ta shiga ta kama ruwa sannan ta sauqo palour, babu kowa sai kamshin girki da yake tashi a kitchen, ta shiga kitchen din ta samu dija tana girka abincin rana, fatu ta mata sannu da aiki ta kama sunayi tare. Fatu tace “maman isya (dija) mummy bata fito bane? Dija tace “ta fito dazu ta fadi abinda za’a girka” Fried rice wanda yaji hanta da kayan lambu sukayi sai coslow, fatu tace “akwai zobo ne?” Dija ta kawo mata, tace “mman isya a ina zan samu bawon abarba? Dija tace “sai dai a aika habu driver ya karbo, akwai masu sayar da fruits a bakin hanya” dija ta fita ta bawa habu driver aika, minti goma ya dawo da bawon abarba mai yawa, fatu ta karba ta daura akan wuta tasa ginger, kanunfari da zobon, suka ci gaba da hiransu suna gyara inda suka bata har zobon yayi, ta sauke dija ta tace shi a wani bokitin roba ya dan huce suka sa sugar sukayi blending cucumber suka saka. Dija ne ta fara tabawa tace “zuwaiiitt kenan, hajia zata ji dadin wannan zobo dama bata cika son na kwalin nan ba” fatu tayi murmushi itama ta taba tabbas yayi dadi don bata taba yi ba, time din da take secondary tayi food and nutrition to anan ta dan iya wasu girke girken sai dai ba kowanne ta gwada saboda yanayin gidansu. Freezer suka kai don yayi sanyi da wuri, barin dija tayi a kitchen Din ta fito palour, hakan yayi dai dai da shigowan farouq 12:40 da sauri ta rungumeshi tana masa oyoyo, peck ya mata a kumatu tayi murmushi itama ta masa duk suka sa daria, wa yaga FATU A BIRNI har an fara wayewa????. Duk abunda sukeyi hajia na kallonsu tana jindadin shakuwarsu na kwana 1. Da gudu yaje gurin hajia itama ya mata peck ta masa oyoyo.
[9:56PM, 6/3/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
1⃣9⃣
Hajia tace yaje yayi wanka ya sauqo yin lunch, fatu ta riqe hannunsa suka tafi dakinsa tana tambayarshi labarin skul. Yayi wanka fatu ta wuce dakinta don gabatar da sallah, shima farouq wucewa mosque yayi. Bayan ya dawo ne suka hallara a dinning don cin abinci, suna kan ci fatu ta dauko musu zobo, ta tsiyayawa kowa kana ta zauna. Farouq ne ya fara tabawa yace “mummy wannan Ribena ne? Mummy tace ” kamar zobo ne lemme taste it” hajia ta dan kurba tace “natural” kana ta kira dija tazo “haba dija, dama kin iya irin wannan zobon amma baki taba mana ba? Dija tace “hajia bani bane fa, fatu ce tayi” nan hajia ta maida dubanta ga fatu wacce cin abincinta take hankali kwance, tace “fateema a ina kika koyi wannan zobon? Fatu tace “mummy a skul ne, nayi food nd nut ai” fatu ta fada mata yanda sukayi. hajia tayi smile tace “zaki koya min nima, gashi babu wani flavour ko color, komai natural sai qarin lafiya ba abun cutarwa” duk sukayi daria, in banyi qarya ba kowa yasha zobo cup 5????.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, yau fatu ta cika 3 weeks a gidan, tayi fresh tayi kyau abunta, hajia tana nuna mata gata ba qarya, don kaya kala kala naga fatu na sawa ita da tazo da kala 3, shoes and bags ma gasu nan kamar na wata yar gwamna, make up kuwa takanas hajia ta kaita PRETTY AYSHA PALOUR ta koya mata kwalliya na zamani.
Sanye take cikin wani swiss lace mai pink nd blue, tayi simple make up amma tayi matuqar kyau, kayan sun amshe ta kamar ka sace ka gudu, gyalenta ta dauka ta yafa a kafada ta fito palour ta samu hajia na kallo manara tv. “Sannu da hutawa mummy” hajia ta juyo tace “yauwa yar mummy, gurin mal usman zaki je kice kafin ya wuce kumo ina son ganinsa” fatu tace “to mummy” ta fita daga palourn ta nufi bakin gate. Turuss ta tsaya ganin sultan na magana da mal usman din. Rabon da ta ganshi tun ranar shigowanta gombe. Zuciyarta ne yake dukan uku uku, kar fa ya ganeta ya korata kauye ko kuma yaci mutuncinta, wayyo Allah! A zuciyarta tana ina ma bata fito yanzu ba. Yana gama maganansa ya miqa wa mal usman envelope yana cewa “bari in gaisa da mummy” juyowan da zaiyi yayi arba da ita, dumm gabansa ya fadi, “tsarki ya tabbata ga Allah da ya tsara wannan halitta” sultan ya fada a zuciyarsa yana mai qarewa fatu kallo ita ma din shi take kallo, sunfi 1 min a haka, fatu ce tayi qarfin halin fara tafiya ta nufi gurinsa.
Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[9:27PM, 6/4/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣0⃣
Tafiya take yi a hankali zuwa gurinsa don ita duk a tunaninta ya ganeta, tazo dab dashi ya aika mata da murmushi yace “sannu yan mata” tsayawa tayi cakk, a ranta tace ashe bai ganeta ba, don haka ta fuske tace “sannunka” kana ta cigaba da tafiyanta zuwa gurin mal usman. Ta gaishe shi tace “mummy tace tana son ganinka kafin ka tafi” yace “to” kana yayi qasa da muryansa yace “fatu yallabai ya ganeki kuwa? (Mal usman gulma????) shiru tayi tana kallon gefe, sannan tace “ka manta abunda hajia tace ne? Duqawa yayi kamar me neman gafara yace cikin karamin murya “ahh yi hakuri, wallahi mantawa nayi fateema, bakin nawa ne ba sakata” murmushi tayi tace “ba komai” wuce wa tazo ta sake yi ta gaban sultan wanda tun tafiyanta gurin mal usman ya tsaya ya zuba musu ido, sai dai bai san me suke cewa ba. Tana shiga palour ta isar wa hajia saqonta tayi saurin haurawa sama, hakan yayi dai dai da shigowan sultan ya zuba ma bayanta ido, sai yake ganin duk duniya babu wanda hawan step ya masa kyau irin wannan babe din. Sai da ta shige ya juyo da kallonsa palourn ganin idon???? mummy qurrr a kansa yasa yaji kunya. Daya daga cikin kujeran ya samu ya zauna yace “sannu mummy” tace “kaima sannunka” dariya yayi don duk a tsarge yake kamashi da mummy tayi yana kalla mata baquwa. Suka gaisa, mummy ke jajensa tace “wato don jameel baya nan shine ko kafanka ba’a gani ko” murmushi yayi yana sosa qeya yace “wallahi mummy ban zauna bane, last wik ma dawowana daga china, kuma nazo farouq yace kina bacci” hajia tace “ba komai in abokin naka ya dawo ai zamu na ganinka, Kaga shikam yayi iyali, kai kuma naga alama so kake azumin nan a fara kada maka gangan tuzuru” daria yayi sosai yace “mummy ki shirya bayan sallah zakuyi bikina, na samu mata sai dai bamu daidaita ba” Mummy ta kallesa tace “a ina” sultan yace “kin santa ma mummy, ki tayani addu’a kawai” da jin haka mummy ta gane fateeman ta yake nufi, sai ta fuske tace “nidai ban gane wacece ba, Allah ya baka sa’a” ganin bai samu fuska ba yasa ya maida kallonshi kan tv, yafi kusan 30 mins xaune da hajia suna hira sai dai ko kadan bata kawo masa tadin baquwarta ba, fatu kuwa qin fitowa tayi. Ya gaji da jiran fitowan ta yayiwa hajia sallama ya fita.
Taku a kullum
Maman Fa’iz????????
[10:36PM, 6/5/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
2⃣1⃣
Sultan na fita ya hadu da farouq ya dawo daga skul, tafawa sukayi yace “big boy, ka dawo? Ya skul” yace “lafiya kalau, yau muka yi games, mukayi gudu muna waqan soldiers” sultan yace “Ai ana ganinka anga sojaa, give me five” suka qara tafawa, kana sultan yace “amm sojaa, nikam wacece baquwar mummyn nan? Farouq yace “anty fateema ce, tazo karatu ne” da yake hajia ta gargade shi kan duk wanda ya tambayeshi fateema ya fadi haka nan. Yace “ok good boy, maza in ka shiga gida kace ina gaisheta” yace to. “Fateema” sunan ta mai dadi, murmushi yyi ya shafi face dinsa kana ya dan bugi kirjinsa saitin heart dinsa, (ko me hakan ke nufi oho????) fita yayi daga gidan, a bakin gate ya hango mal ahmadu yazo karban mal usman guard tunda zaije aika. Suka gaisa ya wuce gidansu.