MUTUM DA DUNIYARSA 29 – 30

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[29➖30]_*
………..Shirye-Shiryen biki dai ya kankama, dukda aure kawai za’a d’aura biki sai satin sama, dangima mazane kawai zasuzo d’aurin aure, mata kuma sai ranar tariya.
A wannan Karon kam dolene ka fahinci ana biki gidansu Jiddah, dukkan tanadin da Umma keyi Na kayan d’akin y’ay’anta ta fiddo Na Jiddah fili, abinda babu kuma ta had’a y’an kud’ad’enta Aunty Nafisa da Maman Sadiq ɖa Balu suka shiga kasuwa.
Uncle yahya ma yanata shirinsa akan kayan gado, dan baimayi tunanin Neman Abba ba balle ya tunkareshi.
A 6angaren Jiddah kam tanajin k’aunar Sheikh Aliyu, amma kuma batajin son auren kwata-kwata, duk d’okin da y’an uwanta keyi kallonsu kawai take, babban ma abinda ke damun ranta da akace yanada Mata, tana tsoron komawa Y’ar gidan jiya gaskiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Duk suna a tsakar gida, Umma da Balu suna kan tabarma, Balu na yima Umma kitso suna hirarsu ta zuminci, sai Jiddah dake yankan alayyahun da zasuyi miyar taushe, Zarah Nata aikin tuwo daga can k’ofar kicin.
Da sallama Walida ta shigo hannunta rik’e da madaidaiciyar bak’ar leda data sayo kifin miya, kallo d’aya zakai Mata ka fahimci tagaji.
Duk sannu sukai Mata bayan sun amsa Mata sallama, ta ajiye ledar a gaban Jiddah tana fige hijjabinta ta jefe saman igiya sannan taje kusa da su Umma ta zauna tana fad’in “Wash ALLAH k’afafuna”.
Balu tai Y’ar dariya “Sannu Walida, kona goyakine? Naga kin gaji”.
“kai Aunty A’a na hutashsheki, kawai gajiya nai da tafiya, ga wani shegen Mai naci daya nanuk’emin tundaga titi har k’ofar gidannan”.
“Tofa, auta kice dai Umma tayi suruki”.
“Kai Yaya Jiddah dan ALLAH, ni wlhy ban fad’aba”.
Dariya Zarah dake k’ok’arin tuk’a tuwo takeyi tace, “O su walidatu an kusa aure ashe”.
Umma ta zubama Zarah harara tana fad’in “Ya isheku hakanan malamai, yanzu zaku tasomin yarinya gaba ko huce gajiyar wahalar da kuka sata batayiba, tama dawo kod’an ruwa baku bataba”.
“To Umma naga ai da ita za’aci?”.
“Yo Yaya Jiddah tamafi kowa lauma ai”.
“Gaskiyarki kuwa Zarah”.
Dariya itadai Balu take musu, dan tsarin yayarta da y’ay’anta Na matuk’ar birgeta, idan sun Mata laifi zata tsawatar musu tamkar bata sansuba, amma hakan bazai hanata ta Saki jiki dasuba tamkar k’awarsu, hakanne yasa take saurin gano matsalarsu, suma kuma basa iya 6oye Mata komai nasu.
“Yaya Jiddah Ku tsaya, nifa dukma ba wannanba, Naga matar Alhaji garba a kasuwa yanzunan, sannan tare Na ganta dawata Y’ar budurwa, amma alamun yarinyar baimin Kama da y’artaba kamar mai aiki”.
Jiddah dake kallon Walida itadasu Umma tace, “A kwarai akwai mai aiki agidan Bilki”.
“Kai Yaya Jiddah, amma shine baki fad’aba, duk wannan kullawa da kwancewar da mukeyi kullum akan yanda za’a zak’ulo abinda ta binne a kanki”.
“Humm Zarah kenan, ni nama manta da Bilkin wlhy, sannan kuma ma munada tabbacin bilkisun zata taimakemu”.
Umma tace, “Wannan gaskiyane Jiddah, tunda dai kunga tare muka gansu, kamar dai yanda Uncle d’inku yace mubi komai a sannu to mubi d’in, insha ALLAH komai yanada iyaka, yanzuma mungode ALLAH tunda abubuwa sun dai-daita sosai”.
“Hakane Umma, ALLAH ya datar damu dai”.
Balu zatayi magana sukaji sallamar Uncle yahya, hijjab Umma tajawo ta saka sannan tace, “Uncle d’insu ka shigo”.
Uncle yahya ya shigo, zama yay inda Walida ta saka masa tabarma, bayan duksun gaidashi har Balu suka gaisa da Umma ma.
Kallonsa ya maida ga Jiddah dake bakin rijiya tana wankin Alayahu da kifi. “Jiddah ki shirya Sheikh Aliyu zaizo anjima kad’an, dan yacemin bayan la’asar idan ALLAH ya kaimu”.
Kai Jiddah ta duk’ar alamar jin kunya, sai Balu ce ta amsa da “ALLAH ya kaimu”. Amma Jiddah ta kasa.
Shima bai damu da rashin amsawar tataba, dan yasan duk y’a mai tarbiyya za’a sameta da kunya.
Mik’ewa yay yana kallon tuwon da Zarah ke gyarawa bayan ta tuk’a, “Fati a ajiyemin tuwonan Zan dawo naci”.
Zarah tace, “To Uncle, kamar kasan kuwa miyar taushece dama kanaso”.
“A’a lallai yau saina kasa tashi kenan ashe, Walida kidafa zo6o saboda bak’oma, kar6a wannan”. Yay maganar yana mik’a mata dubu d’aya.
Zuwa tai ta kar6a hannu biyu tai godiya, shima yaymusu sallama yafita suna masa addu’ar dawowa lafiya.
★★★★★★
Balu da kanta ta tsare Jiddah tayi wanka gab da la’asar, sai zum6ure-zum6ure takeyi su Walida namata dariya, da Zarah tace zata Mata kwalliya saita sanya musu kuka.
Umma ma dai har dariya tayi, “Wlhy Jiddah kinji haushi, ke komai abin kukane a wajenki? Humm gidan dai kishiya zakije, saikije da miji yamiki Abu ko abokiyar zamanki kihau kuka”.
“A’a wlhy bazatayiba, yanzuma su Zarah d’inne suncika takura, tunda tace bataso basai subartaba”.
“Yo Balu ayi mace babu kwalliyane a rayuwa?”.
“Ai zata ringayi insha ALLAH”.
★★
Anayin Sallar la’asar Uncle yakira Umma akan ta turo Jiddah gidansa.
Hijjabinta ta zabga har k’asa da nik’af, walida taimata rakiya hannunta d’auke da k’aramin basket da aka saka zo6o.
Gidan babu kowa sai Uncle yahya dan Maman Sadiq tafita gidan suna tunda safe, gaidashi sukayi, walida tafita kicin ta shirya zo6on akan tire ta had’a da ruwa.
Zamansu baifi Na minti 5 ba Sheikh Aliyu da malam mustafa suka Iso. Uncle yahya yafita yashiga dasu seatroom d’insa dayasha gyara yanata tashin k’amshi.
Gaban Jiddah babu abinda yakeyi sai fad’uwa, har Walida taje takai musu ruwa ta dawo tace taje suna jiranta.
Idonta cike da kwalla ta fita, dan Walida ta kwace Mata nik’af, gabanta na dukan tara-tara ta isa, saidai kuma takalmi d’aya tagani bak’i, abin yabata mamaki, dan walida tace Mata su biyune, kuma Uncle yahya ma yana can.
Ganin batada mai bata amsa saita danne zuciyarta tashiga da sallama.
Sheikh Aliy dake zaune cikin kujera sanye da wani lallausan farin yadi daya d’au guga ya kwanta luf, sai hularsa Zanna, k’amshin turarirrikansu dukya mamaye falon. Cikin sassanyar muryarsa ya amsa mata sallamar yana d’ago fararen idanunsa akanta.
Kanta a duk’e yake, dan haka baya ganin fuskarta sai kad’an. Daga can farkon k’ofar ta zauna a k’asan kafet, muryarta nad’an rawa tace, “Sannu da zuwa ina yini”.
Numfashi yad’an sauke yana gyara zamansa, “Lfy lau, kina lafiya?”.
“Alhmdllh”.
“To Masha ALLAH” ya fad’a idonsa a kanta, komi yake kallo oho. Shiru sukayi Na wani lokaci kafin yad’anyi gyaran murya.
Ba tareda jiddah ta shiryaba ta d’ago kanta ta kalleshi, caraf suka had’a Ido, saurin janyewa tayi ta maida kanta k’asa.
Murmushi yayi yana fad’in “Ahaka ake za6en miji dama?”.
Kuma k’asa tayi da kanta jikinta na wata tsuma. Tsaf ya lura da halin da take ciki, sai tausayinta ya k’ara kamashi, har tunani yake Yaya zasu kwashe idan ya tuno matsalarta……
Tunaninsa ya katse sabodajin tarinta, Wanda da alama yawune ya sark’eta. Ruwan da walida ta zuba masa yasha rabi ya d’auki sauran da hanzari yamatso kusada ita yana jera mata sannu.
Ansa tayi Tasha, idanunta harsunyi jajir sun cika da kwalla, sai kuma jera Mata sannu yake tana d’aga masa kai, saida tarin yalafa sannan yakoma wajen zamansa ganin jikinta na rawa.
“Ki daure kina k’arfafa zuciyarki dan ALLAH”.
Kanta tad’an d’aga tana share hawayen da suka cika Mata ido.
“Magana kuka, karatu kuka, Anya kuwa ked’in jarumace?”.
Batareda ta saniba tad’an turo bakinta, dan taji haushin maganarsa.
“Yi hak’uri Malam, maida bakin nagani, Bari sai nan da kwana uku amma ba yanzuba”.
Bata fahimci ina ya dosaba, amma hakan bai hanata jin kunyar maganarsaba.
Murmushi yasakeyi yana kallon agogonsa silver dake d’aure a tsintsiyar hannunsa, “Bara nayi abinda ya kawoni, dan wannan hajiyar bata shan inuwa d’aya da jinsina. Malam Jiddah nasan zakiyi mamakin shigowar maganar aurenmu da wuri, gashi kuma maganar so bata had’ani dakeba, wannan hukuncine Na ALLAH dakuma cika burin mahaifina dayay tunkan aurenki na farko, cikin Amincin Ubangiji nima dana ganki sainaga kin cancanci zama matata, wannan yasaka iyayena suka shigo da zafi-zafi, dan hausawa kance da safe ake Kama Fara, anzo nema min izinin neman so a gareki saikuma akamace an bani, na jinjinama dattako da halin girma irin Na iyayenki, dan sun tabbatar mana sud’in iyayene nagari, yanzu dai fatan da zanyi shine ALLAH yasa Na kar6u, karna zama macen shige, Ku mata kunce bata kwarjini”.
K’asa Jiddah tai da kanta takasa magana.
“Ki daure kice wani Abu, dan ayanzu kinada ikon za6arma kanki miji a matsayinki na wadda ta ta6a aure”.
Nanma bata iya cemasa komaiba, amma yanayinta yabashi amsar tambayarsa.
Numfashi ya sauke, “To koba’a amsamin a bakiba nasamu sak’on zuciya, ALLAH yay miki albarka, kunya adone na d’iya mace, hakama jan aji mayafine Na kimarku, kin kuma tabbatarmin kinada banbanci da zawarawa na yanzu, wad’anda suke ganin sunsan komai idonsu abud’e yake akan namiji, Abu nabiyu shine inada Mata, kuma maganar gaskiya inasonta sosai, saboda tanada halaye Na kwarai da tarbiyya, sannan bata gazamin a komaiba Na rayuwar zamantakewa da hak’k’ok’ina na aure, hasalima har yanzu amarci muke dan aurenmu bazai gaza watanni shida ba zuwa bakwai, to ban saniba ko malama Jiddah zataso tsoho mai mata”.
Kan jiddah a k’asa, ko kad’an kalamansa basu Sosa rantaba, dan duk jarumin namiji Na kwarai bazai tozarta uwargidansa agaban ta wajeba, hakannema yakuma saka Mata kwanciyar hankali akan aurensa, ko anan gaba bazataji shakkaba idan zai k’ara ta uku akan itama zai tozartata. Cikin sanyinta tace, “Duk namijin kwarai shike mutunta matarsa ga macen waje, halayen matarka sun birgeni, kuma ina addu’ar ALLAH yabani ikon yin koyi da ita, dakuma girmama ta amatsayin wadda take a gaba dani”.
“Masha ALLAH, Alhamdllh, ALLAH yay miki albarka, yanzukam hankalina yasake kwanciya, ina kuma miki albishir da samun soyayya tsaftatacciya agareni inhar kika girmama zaman lafiya tsakaninki da matata insha ALLAH, sannan Zan kasance mai adalci a tsakaninku da yardar ALLAH, fatana muyi koyi da rayuwar aure irinta gidan MANZON ALLAH (S.A.W)”.
“Insha ALLAHU”.
“ALLAH yay muku albarka, bara na barki haka kije ki huta, inaga sai bayan an d’aura aure kuma insha ALLAH zaki kuma ganina saboda sabgogina yawane dasu, mikike da buk’ata na shagalin biki?”.
“Bana buk’atar komai, dan babu abinda zanyi”.
“Haba dai malama Jiddah, kod’an rawan coge d’innan Na Mata bazakuyi a cikin gidaba”.
Dariya yabata wai coge, amma saita danne batayiba, sai murmushi datayi Wanda harya bayyana fararen hak’oranta a fili.
“Kin iya murmushi haka ashe amaryar Aliy? amma jan aji yasa ba’a ta6amin naganiba tunda muke had’uwa?”..
Da sauri Jiddah ta kudundune kanta a hijjab, shima ya mik’e yana fad’ad’a murmushinsa. “Tunda rowa akemin bara nayi gida matana tamin”.
Ita dai Jiddah takasa d’agowa, takula yanada yawan tsokana, amma a fuska saikaga tamkar baya magana ma.
Kujerar dake d’an kusa da ita kad’an ya sake zama, addu’a yaymusu kafin ya kuma mik’ewa yana fad’in “Na barki lafiya”.
Batare data d’agoba tace, “ALLAH ya tsare, ka gaidamin auntyna”.
Yaji dad’in maganarta, dan haka ya amsa da amin ngd, auntynki kuma zataji, kafin ranar juma’a kuma kid’an canja dan ranar babu y’ar nesa-nesa..”.
Ya k’are maganar ahankali bayan yad’an duk’o kusa da ita kad’an.
Sosai jikinta yake tsuma saboda jinsa kusa da ita, ga k’amshinsa yakuma mamaye hancinta, ta takure jikin kujera sosai har saida ya fita sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gidan Malam Aliyu kam da yamma saiga Aminatu k’anwarsa dasuke uba d’aya, d’iyar iya habi mai ruk’on Maimunatu, sai kuma yayar maimunatun Hassana.
Tarbar mutunci tai musu, bayan takawomusu ruwa ta zauna suka gaisa.
Aminatu ta kalli maimuna baki a ta6e tana fad’in “Miya samu idonki nagansa jajur kuma a kumbure?”.
Dariyar yak’e maimuna tayi, sannan tace, “Babu komai Aunty Amina, kawai dai kinsan bajin dad’in jikin nakeba”.
Kallon juna Amina da Hassana sukayi suka ta6e baki, Hassana ta maida kallonta kan maimuna, “To Uwar y’an zurfin ciki, auren na Mijin nakima 6oyewa zakiyi? To ai kin makaro, dan kowa yasani, yanzunan maimuna sabodake wawuyace zama kikai kina kwad’a kuka saboda za’ai miki kishiya?, kishiyarma bazawara, to wlhy idan zaki mik’e ki mik’e, kuka babu maganin ubanda zai miki, ni bammasan sanda zakiyi hankaliba kekam…..”
“Ke wlhy da hankalinta, son mijine kawai, kinsanfa ita batason laifin Yaya Aliyu saboda shine autan maza”. Amina takatse Hassana tana huci.
Maimuna ta share hawayen da suka zubo Mata, wad’anda dama suta yini yi, bayan fitar Aliyu dayace mata zaije wajen amaryane Yakuma tunzura kukanta, shinema suka iske tanayi, jin sallamarsu tai saurin zuwa ta wanke fuska ta shafo fauda, “Haba Aunty Amina yakikeson nayi, Zan hanashi yayi aurene?”.
“Bakuwa zaki hanashiba wawuya kawai, yoke banda kin rako Mata duniya wata shida da aurenku kacal kizauna a dank’aro miki kishiya? Wato ya Danna miki ciki amfaninki yak’are shine zai auro wata ko? To wlhy kibud’e kunne kiji bayani, idan zaki mik’e kitada masa hankali ki haukace masa, duk yanda ya taroki kice bakisan zancenba…..”
”Hummm, aunty Hassana kenan, da hauka Na hana namiji k’aro aure da mata da yawa sun tsira daga kishiya, da asiri Na Hana maza aure da wasu matan ba’ai musuba, yakamata muringama kammu adalci kafin ai mana, idan mun hana mazajenmu aure yazamuyi da y’ay’an da muka Haifa?, Kituna yanzu haka mamanmu yara hud’e kannenmu Mata agabanta, idan munce mazanmu bazasu auro mana wasuba, su wanene zai auresu?, dukma ba wannanba, shin munada tabbacin kaiwa darene dahar mukeda kwarin gwiwar Hana abinda ALLAH ya halatta?, kuyi hak’uri inason mijina, kuma ina matuk’ar kishinsa, amma hakan bazaisakani bijire masaba Na lalata alak’ata da Ubangijina akan son zuciya, kishi gaskiyane amma bata mummunar hanya yakamata mu Mata mu jagoranceshiba, kamata yayi Ku koyamin yanda Zan kuma damk’e zuciyarsa, Na zama tauraruwa a garesa ba yanda Zan tsinke igiyar aurenaba, iyayenmu babu wadda bataje ta tadda kishiyaba, miyasa su iyayensu basu k’i aurar dasuba saboda zasu iske wata? Saimu da za’azo a iskene zamuce bazai yuwuba?…….”.
“Kinga Amina taso mukama gabanmu kafin tace mana y’an wuta”, Hassana tafad’a tana mik’ewa.
”Wa’iyazubillahi aunty Hassana, mak’iyinama bazan dangantashi da wutaba balle ku”.
Basu tanka mataba suka fice, duk kiransu datake ta biyosu har gate basu sauraretaba.
Kuka tayi sosai akan hakan, a ganinta bai cancanci manya dasu su kawo mata rabuwar hankaliba.
Koda Aliyu ya dawo bata fad’a masaba, shima bai tambayeta ba dukda yakula ranta a 6ace yake, yanayinta kuma ya nuna masa tayi kuka. Kulawa yayta bata yanda hankalinta zai sake kwanciya da sake rarrashinta, dan tunda yaymata zancen aurennan duk sai ta susuce, dukda dai tana dannewa a gabansa.
Hakan saiya k’ara dasa masa k’aunarta da tausayinta, koba komai ya yarda da son da take masa mai nagartane, kamar yanda shima ayanzu yakejin sonta tun bayan aurensu, sokuma Na gaskiya mai gauraye da zallar k’auna.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A 6angaren Jiddah ma ranar kwana tai da tunanin Aliyu, hardasu mafarki.
Komai nasa yamata yanda take addu’a da fatan mijinta ya kasance, fatanta ALLAH yasa matarsa ba irin hajia Deluwa baceba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_RANA BATA K’ARYA_*
Yau take juma’atu babbar Rana, duk tarone Na maza kawai hakan bai hana su Maman Sadiq yin abinci ba dai-dai misali saboda y’an Adamawa maza su kusan goma da y’an barno biyar da sukazo d’aurin auren, a Mata kam gajiram da yaruwaiya ne kawai sukazo (Yayar Umma, da k’anwarsu wadda Balu ke bimawa).
Abba zakari dai baisan hidimar da akeba, amma har gida Uncle yahya yaje yacemasa yashiryo suje d’aurin auren wani yaron malam Abdul-ra’uff, da farko cayay akwai inda zaije, amma Hajia Hindu ta saka baki harya amince.
A babban masallacin juma’ar dake anguwar gwammaja sukaje sallah, mamaki ya Kama Abba ganin Kawunansa, Kawu Surajo da bashida 6oye-6oye yafito yasanarma Abba auren Jiddah za’a d’aura yau d’innan, kafin Abba yasamu zarafin magana tawagar malam Abdul-ra’uff data ango suka Iso.
Su Kawu Surajo basubi takansaba suka shiga hidimar tarbarsu, babu yanda ya iya dole yabi ayari dan karyaji kunya, dan manyan malaman sun cika masa idanu, amma daka gansa kasan a birkice yake gaba d’aya, kuma hankainsa baya jikinsa.
Ana idar da sallar juma’a wadda su malam sukayi anan suma aka d’aura Auren *Sheikh Aliyu Abdul-ra’uff Maina da Jiddah Zakari Yaro* akan sadaki dubu d’ari biyu ciff????????…………..✍????
*_Munga idi, ya za’ayi da Abba zakari da Alhaji Garba kenan?????????????._*
*_⛹♀????kayana a shirye suke nayin hijira walla, kad’an daga aikin Abba ya lallasa gayu????????????_*
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d’in na sama sisters, Abban dausayi YouTube channel tv????????????_*
*_Ubangiji yabama d’an uwan momin khairi malam Adamu lafiya, bisaga had’arin mota da yayi, muna barar addu’arku. Dama dukkan y’an uwa musulmi dake kwance sanadin ciyo????????????_*.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*