GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Teemah dake tsaye saboda tsabar takaicin abinda Zaid yayi mata ta kasa koda kwakwkwarar motsi ne balle tayi yunk’urin barin wajen, mutanen dake wajen suka shiga nuna ta suna magana k’asa-k’asa, har suka gaji suka watse suka barta tsaye ita kad’ai, sai da ta gaji dan kanta sannan ta nufi motar ta, ta shiga tayi gida, a harabar gidan tayi parking ko tsayawa rufe motar batayi ba, da gudu ta shiga gidan direct tayi bedroom d’inta ta fad’a kan bed ta saki kuka mai cin rai.

Dakyar ya mik’a hannu yana daga kanta ya lalubo wayar, yayi picking ko magana bai kai dayi ba yaji muryar Ammi na kuka tana cewa ” Zaid kazo gida yanzu ba lafiya ta fad’a had’i da hanging wayar, a firgice ya mik’e ya shiga maida kayan sa, da sauri Lubnah ma ta tashi tana tambayar sa lafiya, yana saka kayan yana bata amsa ” ban dai sani ba amma nasan ba lafiya da sauri ta duro daga kan gadon tana cewa ” innalilahi wa’inna ilaihir raji’un Allah dai yasa koma meye yazo mana da sauk’i ” Amin yace yana fita.

Wani irin mahaucin gudu Zaid yake tsalawa harya isa gida da sauri yayi parking ya fito da gudu ya nufi cikin gidan, bai iske kowa a parlor ba dan haka ya nufi sama, daga bedroom din Abba yake jiyo kukan Ammi, da sauri ya nufi dakin ko salama babu ya danna kai ciki, cak ya tsaya ganin Abba kwance a mimmik’e dubansa yakai ga Abraham dake Zaune rungume da Abba yana zubar hawaye, cikin mutuwar jiki ya k’arasa wajen, a gaban Abba ya durk’usa ya kasa yin komai, shi bai yi kukan ba balle yayi magana, da sauri Doctor ya shigo da sallama babu wanda ya samu damar amsa masa.

Ganin yanayin da suke ciki ne yasa shi nufar Abban ya fara duba shi, cikin kuka Abraham yace ” wanne kuma duba shi kake bayan ya riga da ya mutu,Doctor ya ci gaba da abinda yake yi ba tare daya saurari Abraham, yakai 30mnt yana duba shi, sannan ya d’ago ya dube su yace ” bai mutu ba, cak Abraham ya tsaida kukansa ya k’urawa Doctor ido “kamar ya maganar ta sub’ucewa Abraham ba tare daya sani ba, Doctor ya d’ago yana kallansa fuskarsa cike da mamaki yace ” eh kamar dai yadda kaji, ya juyo ya kalli Zaid dake ta faman sauke ajiyar zuciya yace ” yanzu zamu kai shi Hospital a duba shi acan kafin ya gama rufe bakinsa Abraham ya mik’e ya sungumi Abba yayi k’asa dashi da sauri suka mik’e suka bi bayan sa, Doctor yabi bayansa da kallo yana murmushi.

Direct Emergency aka wuce da Abba manyan Doctors sukai 6 akan shi su duba shi, basu fito ba sai da sukayi gud 3hrs sannan suka fito tare dashi special room suka kai shi duk su Zaid suna bin bayan su, Family Doctor ne ya jiyo ya kalle su yace ” heart attack Abba ya samu ” what heart attack like how? Zaid ya fad’a a firgice “eh, magana ta gaskiya Abba yana cikin matsananciyar damuwa kuma hakan ya samo nasaba ne da rashin jituwarku ya fad’a yana nuna Zaid da Abraham jikin Zaid a matukar sanyye ya zauna a gefe gadon ya rafka tagumi, shi kanshi Abraham jikinsa yayi sanyi gaban Ammi yaje ya zauna a hankali ya d’ora kansa akan cinyarta, sumar kansa Ammi ta shiga shafawa a hankali Abraham ya sauke ajiyar zuciya, kukan da Ammi ke dannewa ne ya kwace mata, ta sake shi da k’arfi.

Cikin tashin hankali Abraham ya d’ago kai yana kallon Ammi ganin da gaske kukan take cikin matsancin bak’in ciki da takaici, da sauri Abraham ya mik’e ya zauna a kusa da ita ya rungumo ta jikinsa ya shiga rarrashinta game da kwantar mata da hankali cikin kuka tace” wallahi idan kuka sake bak’in cikin ku ya kashe Abba har abada bazan tab’a yafe muku ba kuma wallahi bani ba ku duniya da lahira, haba uwa d’aya uba d’aya amma ku zama kamar Annabi da kafiri, ku duba yadda bak’in cikin ku ya mayar da mahaifin ku har yana neman rasa rayuwarsa wad’anne irin yara ne ku wallahi dana sanin haihu…. da sauri Abraham yasa hannu ya rufe mata baki yana zubar da hawaye, ya k’ara kwantar da kanta a k’irjinsa, in banda kuka babu abinda Zaid yake kamar ransa zai fita a hankali ya mik’e ya tako har gaban Ammi da Abraham ya k’ura musu ido ya kasa cewa komai sai kukansa dayaci gaba dayi a hankali ya rungumo Abraham da Ammi jikinsa, ” please Ammi kuyi hak’uri in sha Allah zamu gyara, zamu zamo muku abin alfarahi.

Mukhtar dake bakin k’ofa yace” Alhamdulillah Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar ya fad’a yana goge hawayen dake zubo masa, murmushi Abraham yayi yana mik’a masa hannu alamar ya taho da sauri ya nufe su duk suka rungume juna, wannan kenan.

Ni ko nace yanzu aka fara wasan ma

Teemah kai 4hrs a d’aki tana faman aikin kuka kafin daga bisani ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka, ta shirya, wata muguwar yunwa ce ta saukar mata, a hankali ta mik’e ta nufi kitchen d’inta ta dafa indomie ta shad’o, taci ta k’oshi ta mik’e, Lubnah nacan ta kasa zaune da tsaye tun da Zaid ya fita hankalinta yak’i kwanciya ta shiga damuwa ita gashi bata da number sa balle ta kira shi, tunanin taje part d’in ta karb’i number sa ne yazo mata aiko da sauri ta mik’e ta nufi part d’in, da sallama ta shiga ta iske ta a parlor a hankali Lubnah ta gaida Teemah had’i da tambayarta number Zaid, murmushi tayi sannan ta karb’i wayar, juya wayar ta shigayi a hannunta dan ganin iPhone 8+ sabuwa dal, murmushi tayi had’i dasa mata number ta mik’a mata, Lubnah tayi mata godiya ta koma part dinta, zama tayi ta nutsu sannan tayi dialing number sai da ta tsinke ta sake kira ta kuma tsinke sai a karo na 4 sannan ya d’aga wayar, ido ta lumshe ta bud’e a hankali sannan ta gaida shi ajiyar zuciya Zaid ya sauke da k’arfi har sai da Lubnah ta ji, tambayar shi tayi abinda ya faru, cikin nutsuwa yace mata Abba ne ba lafiya, sosai ta nuna damuwarta had’i yi masa addu’a, sannan tace ya bata Ammi, sai da ta gaishe da Ammi sannan ta duba Abban.

Sai wajen k’arfe 11:00pm Zaid Ya dawo direct bedroom ya wuce yayi wanka ya shirya sannan ya shiga part din lubnah, parlor ba kowa an kashe wutar, bedroom dinta ya nufa akan bed ya ganta sanye da rigar bacci k’aunar tsirara, a hankali ya nufe ta cikin bacci Lubnah taji ana tsotsar mata nono, a gigin bacci tayi murmushi had’i da cewa ” I LOVE YOU ZAID cak Zaid ya tsaya ya daina abinda yake yi, ido k’ura mata ya kasa yin komai a hankali ya rad’a mata repeat it again, murmushi tayi had’i da turo bakinta tace” I LOVE YOU ZAID wani irin sanyin dad’i mai gauraye da matsananin farin ciki ne ya ratsa Zaid tunda tafin k’afarsa har kwakwalsa, murmushi yayi Ya manna mata kiss, had’i da rungumo ta jikinsa yaja musu bargo cike da annashuwa.

Ciwon Abba sai k’ara rikicewa dan tunda aka kawo shi asibiti bai motsa ba yau kusan 1 week kenan, anyi-anyi amma abu yak’i dan haka Family Doctor su ya bada shawarar akai shi America, ba musu suka amince, kasancewar su masu kud’i kuma sanannu shiyasa ba’a wani sha wuya ba aka aka gama komai, Ammi da Family da Abraham ne zasu yi tafiyar yayinda Zaid da Abraham zasu ci gaba da kula da Business, ranar tafiyar su harda Lubnha aka je rakiya Airport, basu baro Airport d’in ba sai da suka ga tashin sannan suka dawo gida,a parlor Lubnah ta zube, Zaid ya kalle ta yace ” kin gaji ko? murmushi tayi tace ” a’a, ” yunwa nake ji Zaid ya fad’a kallansa tace ” ok ina zuwa bari na dafa mana abu mai sauk’i,, 10:00pm ta gama dafa dafadikan shinkafa da taji kayan lambu da bushashshen kifi, ta hada coconut drink, ta jere a dinning table, ta shiga wanka, sai da ta shirya sannan ta kira shi a waya, ba’afi minti 5 ba ya shigo sanye da jallabiya, ba k’aramin dad’in abincin Zaid yaji ba dan haka ya zage yaci sosai, sai da suka gama sannan ta gyara wajen ta wanke komai ta kalle shi tace “gana Aunty nan fa “ok kawai yace ya mike ya koma kan sofa ya kunna CNN kallan shi ta kuma tace ” please ka kai mata mana, dan baya son ta fahimci abinda ke tsakanin su ne ya sashi mik’e had’i da d’aukar food flask din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button