HAUSA NOVEL

GAMO DA KATAR Complete Hausa Novel

Nuraim mizan gani mikake san cewa yar mutane ta bata yar Amana marainiya Allah nayi sakaci Nuraim da na barka da ita miyasa nai haka Ya ubngiji kasa ba gsky bane mafalkine ba Abinda nuraim yake sai kuka mmy d’akinta ta’shiga tarude nema Narim din take qarshe dai ba Narim sai ta fashe da matsanecin kuka ta ta shi ta shiga toilet Narim yata Narim yata karki man haka kina ina duk ta zauce da tafito toilet ta zame jiki ta fadi ta suma;

Da gudu Nuraim ya yi d’akin dadin shi daman Alhj isah tun da yayi sallar Asuba yake zaune yana’tajiran tsammani ya jishuru;

Kai lafiya ya cewa Nuraim Nuraim bai ce mashi komai ba sai qofa da yake nuna mashi da hannu kai buda baki kai man magana miya’faru cikin tashin hakali Nuraim ya bude bakin shi da yai mashi Nauyi yace Dadi” Narim mmy yana yi yana hutai shedar shi kamar zata dauke idanunshi sun juye yatafi lum kafin Alhj isa yai wani yunqauri ina Nuraim ya kai qasa”

Hankalin shi ya tashi ba kad’an ba; ruwa ya dauko ya yayya’famashi aman bai” tashi ba dan haka ya dauke shi yai wajan mota da shi. maigadi da yan sanda sukayo kanshi subahanallah Alhj lafiya miya faru cikin rawar murya yace ba lafiya bude man mota yasa shi ciki

Kuma ya koma gida d’akin momy ya nufa yana sa kanshi kukan Narima ya cika mashi kune sai tsalla kuka take ita kade ya duba bai ga uwar ba haka d’akin ta bata ciki ddayan d’akin ya sameta ,, kwance some haka ya isko ta ruwa ya zuba mata ta tashi zumur Alhj yar mutane ta bata wasu sun dauke ta yanzu ni Asama’u ta zube jikin shi jijjigata yake Yana kiran sunanta Aman bata ta shiba daukarta ya yi itama yai waje da ita hullar kan shi har faduwa take aman bai kula taba bata ita yake ba” cikin mota yasata itama yana fadin kubude man get gidana ba lafiya ,sukan su masu gadin hankalin su ya tashi to miya faru?” tun da safennan”? Allah ya basu lafiya, suka bude mashi ya fita gudu yake da mota kamar yatashi sama yana tuqi yana leqan su bayan mota gasu kwance kama gawa ba mai motsi cikin su

Allah dai ya kai shi Asubiti lafiya cikin gaggawa Aka A mashe’su mmy dai anyi nasara ta shin ta aman Nuraim kau har yanzu bai tashi ba mmy Alhj ina Narim”? taya za ai ace Narim ta6a sai kace wata Aljana” sai dai in daukar ta Akayi hajiya nifa ban gane mikike fad’a ba ina Narim din take?” kamarya za a ce ta6a Abin da mamaki nifa hankalina atashe yake mutum ya bace gidana dolle hankalina ya tashi in’kaga yanda ya tada hankalin shi kai kace da gsky bai son komai ba

Bilhaqqi da gaske yanuna tashin hankalin shi A fili mmy taso zargin shi gani yanda hankalin shi ya tashi ta fidda zargin da take mashi ina Narima ina Nuraim sukade muka baro yace innalillahi Narima nace na baro Nuraim kuma tare muke da shi shima An bashi gado
Wayar shi ya fiddo yai kira hello difio kazo gidana akwai matsala dan Allah” hjy bari naije muyi bincike Akai

Tace” to shikenan Allah yasa Adace Ameen yafita jiki na tai mashi rawa mmy ta yarda bashi ya dauke Narim ba

Kafin yaje difio ya riga shi zuwa nan ma aikantan gidan sukasan mike faruwa bin cike ya tsane ta inda kowa yace bai ga yarinya ba to” yariya dake jaririya ba fita take ba wazai dauke ta sai dai in daukarta Akayi”

Alhji ya shiga gida ya barsu suna ta binciken su Narima ta gajida kuka ta yi barci daukar ta yayi tausayi ta duk ya kama shi duk ni nasaku cikin wannan halin kuyi haquri Abinda nayi shine dai dai yanzu zaki samu soyayyar uwa da ta dan uwanki cinda wadda ta dauke masu hankalin yanzu bata nan tabi ruwa ko ta mutu cikin ranshi yake wanan tunani bayan ya dauki Narima yace ma difio kuci gaba da bincike ko ina ko mun sumu wata Alama bara na kai yariyar nan na dawo ok sukace mashi hospital ya nufa momy na zaune ta yi tagume Abin duniya duk ya isheta hawaye kawai kema ta zuba gashi likitoci sunce danta fa bai motsaba sai dai zuciyar shi na halbawa kad’an su dai tai mashi Adu,a hjy haquri zaki komai zayi dai gashi can Ana bin cike Akai” kayya Alhj in’ba yarinya nan nagani ba ina hankali na zai kwanta ta sake fashewa da kuka;

kiyi haquri insha Allahu za a ganta dan Allah ki daina kuka

Hummmm tace ta Amashi Narima ya dubi Nuraim dake kwance kamar gawa me’sukace hajiya suncce mu tayashi da Adu.a dan sai wani ikon Allah ta shin shi Aman yanajin komai Ake cewa hawaye ne na tausayin Nuraim suka zuboma Alhj isah daman yasan sai haka tafuru dan shaquwar Narim da Nuraim sai Allah Aman nan da dan wani Lokaci yasan komai zai zama tarihi ya share hawaye; yanshi hjy muna cikin tashin hankali Allah ya kawo mana mafita tace Ameen yace” bari na koma can gida naji yanda Ake ciki tace” to

Bincike ya yi bincike bawani labari bawani sheda da aka samu kuma Abin yabama jami’ an tsaro’mamaki inda Alhj isa yace nidai jiya nafita Akan kayanan da suka shigo to ko bayan fitata kun bar gidan bude har wani yasa mu nasara shigowa cinda inba ta get dinan ba bata inda za,a shigo gidanan”

Kokuma dai An rufe gida da barawon cinda mudai ba mubar get bude bah to cikin byu anyi daya ko kun bar get bude bayan fitar shi ko kuma da shi Aka rufe gidan Aman komai kenan zamuci’gaba da bincike yanzu Abamu photon yarinyar mutai da shi shine zai tai maka mana wajan bin’cikin mu”

Gsky basu da photo inji Alhji isah ya fada masu kaji matsala yanzu kai Alhj wanan zamani Ace yara basuda photo kunyi kuskure

Wallahi yanzu da da photon komai zai zo da sauqi yace bari dai A tambyi uwar ko tanada shi to shikenan bara mutafi zamu dawo zuwa anjima to shikenan na gode Allah yasa dace harda kwallan muna finci suka zubo mashi kowa ya tausaya mashi Ahankali 6atan yar shi ya cika ko ina sai jaje Ake mashi Ana fad’in Allah yas Adace cikin xuciyar shi na fad’in ba Ameen bah Afili kuma fadi yake Ameen”

Abuji tunda safe Narim ta tashi dan kukan tane ya tada su inna ta tashi ta dauke ta Narim kin tashi ko to yishuru kinji yata”
Malam yanzu ya zamuyi ina madara mubata kafin nafara shan magani

Yace” to yana yasa hannu shi yana lalubar madara sai gata yagani yace Amshi kiji ko itace naga kamar goran ruwa ta Amsa ta buda sai taji wani tsini kamar kan nono tace inaji fidace inna tace zuba ga hanun ta harda zafi ga qamshi madara na tashi tace ikon Allah malam harda zafin ta to miye na mamaki cinda kin san komai” bata kawai tasha

Bari intai inyi sallahi malam ya fito sai yaji Ana salama dan haka yabi ta inda yake jin murya yana dogara sandar shi har yakai zaure

Cikin lalube ya samu kuba yabude yace nan ake salama?” mutum yace bayan ya bude sun gaisa yace d’a zun na fito sallar Asuba sai na hadi dawani bawan Allah yake ceman gidana na haya ansamu masu haya sannan kuma har sun shiga ya bani haquri abisa shi shigi da akayi mani aka shiga ban’saniba nace ba komai yace man yan uwan shine ku zuwan dare kuka yi to daman ya san gidan na hayane shisa kuka shiga Aman yace inyi haquri nace ba komai yabani kudin hayar ku na shekara goma shine nace bara nazo naga mazauna gidan malam yace eh anyi haka to na gode yace bakomai anzama yan uwa shekara goma ai ba yau bace malam ya yi dariya yace hakane bayau bane awajan mu aman A wajan Allah kamar gobe ce Allah yasa mudace yace Ameen ni sunana malam haruna mai kaba inka fito kace yara sukai ka runfata sai murunqa hira malam yace na gode nikuma sunana malam halliru to masha Allah sunan namu kusan irin dayane to sai kafi ya tafi shikuma ya koma ciki yanemi toilet ya shi Alwalla yayi yai sallam Narim tasha madara ta qoshi ta koma barci inna itama tayi sallah

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button